Showing 39001 words to 42000 words out of 175193 words

Chapter 14 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

568

miki raina zai Saci.

Ajiyar zuciya hajja tayi tare da Wauko wayarta ta mi?awa auta tace

"Kirawo min ita yanzun nan.

Da sauri auta ta Waga wayar tafara ?o?arin kiran yaya karimatu.

Ringin Waya biyu uku ya karimatu ta Waga wayar da sauri.

Tana karawa a kunne tace "hajja barka da yamma.

Murya babu amo hajja ta amsata da cewar barka kadai.

Har ya karimatu ta buWe baki zata fara gaisuwa hajja ta katseta da cewar "kina ina?

Da sauri ya karimatu ta kalli ?ar bukkar datake ciki tace. "Amm....ina gida hajja.

?an murmushin gefen baki hajja tayi tace "to babu laifi, daman inason ganinki ne dan akwai wata mahimmiyar magana da nakeao muyi dake, saboda haka kizo yanzu nan.

Gaban ya karimatu ne yafaWi, da sauri ta Wan cire wayar daga kunnenta ta sauke numfashi tanason tayi tunanin mafita, sai kawai ta mayar da wayar tace

"To hajja gani nan Insha Allah.

Batare da hajja tace komai ba ta kashe wayar tana jan huci a hankali.

*Ya karimatu*

Da sauri ta mayar da wayar jaka ta mi?e jikinta har rawa yake tacewa malam, bara naje na dawo gobe malam.

"Kallon rashin nutsuwa malam yayi mata yace "haba Hajiya karimatu ina kuma zakije? Na kusa gama haWawa fa, ai ya kamata ace kin bari na ?arasa kitafi dashi.

"Uhummm, ya karimatu tace san nan ta fara yafa mayafinta daya zame tace "kaga malam, bazan iya jiran sai angama haWa kayan nan ba, saboda hajja ce takemin kiran gaggawa, dan haka dole ne na tafi yanzu nan koda zuwa na kenan.

Cikin mamaki malam yace "ikon Allah, haka kike jin tsoron hajjan nan taki? Tunda nake ban taSa ganin wani abu ya kiWi maki haka ba kamar yadda hajja ta kiWi maki, ai da kin zauna sai mu san abinyi, tunda dai kinsan babu maganin da bamu dashi, ina tabbatar miki ita kanta hajja Win muna da maganinta, dan tsaf zamu saka mata tsoronki ta dunga ganin kwarjinin ki.

"Zaro ido ya karimatu tayi tace "amma gaskiya malam ka cuceni, kaf duniya na rasa wanda zaiyi asiri sai hajja? Mahaifiyata, uwatace fa, itace ta kawoni duniyar nan dahar na haWu dakai, amma gaskiya banji daWin Abinda kayi min ba, dan haka sai an jima.

Ya karimatu ta faWa tana ficewa daga bukkar ranta duk a Sace.

Daga geza zuwa kwandila da akwai nisa, gashi ita sam bata iya gudu da mota ba, kuma gashi tafiyar tata tana bu?atar hanzari dan tasan koda fuka fukai tatafi bazata isa ?asa da minti talatin ba, ga gosulon a baban hawa, shiyasa kawai ta komai bukkar ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????tacewa malam, zata bar motarta anan zata hau napep domin tanason ta isa gida da wuri, da to malam ya amsa mata san nan ta wuce tafita domin isa bakin titi, dayake gidan nasa da titi babu nisa nan da nan ta isa kuma cikin ikon Allah sai gashi tana fita ta samu drop Win napep ta haye yafara zugaga gudu da ita.

Nan da nan sai gashi sun isa kwandila ?ofar gidan hajja, wata ajiyar zuciya mai sauti ya karimatu ta sauke san nan tafito da kuWin mai napep ta bashi , tana bashi ta shige gidan shi kuma yaja napep Winsa yayi gaba.

Da sallama ya karimatu ta shiga gidan tana rarraba idanu, gaba Waya ta rasa nutsuwar ta dan gani take hajjan na kallan idanunta zata san Abinda taje ta aikata, sosai takeson ta saisaita hankalin ta kafin tashiga falon hajjan.

Tana shiga kuwa sukayi ido huWu da hajjan, sallama tayi ?asa ?asa dan batajin hajjan da auta dake zaune sunji Abinda tace, daga cen ta nemi guri ta zauna tana maida numfashi kamar wacce tayi tseren gudu.

" Hajja ina wuni, ya karimatu ta furta tana kallon hajjan.

Da lafiya ?alau hajja ta amsa san nan tace "daga ina haka naga kinata mai da numfashi?

?an murmushin ya?e tayi tace "daga gida nake hajja, daman ina girki ne shiyasa banzo tuntuni ba amma dan Allah a gafarta min.

Murmushi hajja tayi san nan ta kalli auta tace "auta ki kula da gida ina zuwa.

Tashi hajjan tayi tacewa da ya karimatu bissimillah mushiga ciki.

Ba yaune suka fara shiga Waki da hajja su tattauna ba, amma na yauWin sai take ganin kamar akwai banbanci da waWan cen, shiyasa zuciyar ta ta shiga lugude saboda batada gaskiya.

Suna shiga Wakin suka turo ?ofa, zama hajja tayi akan kujerar dake Wakin ita kuma ya karimatu ta zauna a ?asa wajen ?afarta, maganar da hajja ta jehowa ya karimatu ne yasa tayi saurin zabura tace "iyi?

Kallonta hajja ta kuma tare da maimaita mata maganar tace "ki bani jakar ki nace.

Hannu na rawa ya karimatu ta mi?awa hajja jakarta dakyar har tanayin baya baya da ita, har hajjan ta gane batason bata sai kawai ta fuzgi jakar tana aika mata harara.

Hajja na kar Sar jakar ta buWe ta zazzage ta, abubuwan da suka faWo a cikin jakar ko wanne da rubutu a jikinsa shine ya Wagawa hajja hankali, da sauri ta kalli ya karimatu idanunta na zubda kwalla tace.

Yanzu wan nan ?ar harda ke za'a haWa baki domin cutar da baiwar Allah? Me yasa kikayi haka? Wan nan ba irin tarbiyyar dana baki kenan ba, kin cuceni karimatu.

Da sauri ya karimatu ta Wago da kanta tana kallon hajja, tunda take a rayuwar tun daga fara wayonta har girmanta zuwa yau bata taSajin hajja ta faWi sunan ta ba sai yau, karimatu fa tace? Lallai wan nan karan hajja takai ?ololuwa wajen Sacin rai, dan haka da sauri ya karimatu ta buWe baki zatayi magana.

Kuma a wan nan ta?in kafin takai ga maganar hajja ta Waga hannu ya wanke fuskarta da mari, mari, mari, ya karimatu taketa maimaita wa a cikin zuciyar ta, batajin akwai ranar da zata iya tunawa wanda hajja ta taSa marinta, hajja bata duka sai da tsintsiyar kwakwa shima suna yara, tafi ganewa taja kunnen su shima sai sunyi mata Abinda taji zafinsa sosai, kuma duk da rashin dukansu da takeyi bai hanasu Waukar cikakkiyar tarbiyyar data basu ba, dan haka marin da hajja tayi mata yayi masifar dakar mata kwakwalwa.

Hawaye hajja ta share tana Waukar wata roba mai cike da ba?in rubutu, san nan an nannaWe robar da ?atuwar takarda da aka rubuta.

"Maryam, Nasir, sai akayi wani rubutun larabci a tsakiya san nan daga ?arshe aka rubuta

"farra?u.

Hawaye hajja ta share tace "yanzu karimatu har kinyi zarar dazaki iya fito na fito da Allah ki raba mata da miji? Ashe daman duka aurarrakin mijinki da suke mutuwa bayan ba?in kishinki harda asiri kike haWawa?

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, Ya Allah, idan mafarki nakeyi Allah kasa na farka naga ba gaskiya bane.

Ashe lalacewar taki takai haka karimatu? Kin cutar dani karimatu, dan ba irin tarbiyyar da nayi miki ba kenan, bazance bazan yafe miki ba tunda niba Allah bace, amma bazan daina takaicin hurumin Allah da kika shigaba na raba aure, ke shaiWaniya ce karimatu, domin shaiWanne kawai yake iya raba aure, ina tayaki jimami da kuma rasa imanin ki da kikayi, wallahi ban taSa nadamar haihuwar kiba sai yau karimatu, nibamai saSoce, ban kumayi zatan zan haifi mai saSoba dan danasan zan haifi mai bijirewa umarnin Allah danayi addu'ar Allah yahani haihuwa a duniya, kaicona ni Halima, banyi daceba, ta ?arasa tana kifa fuskarta akan tafin hannunta tana fashewa da kuka mai sauti.

Tashin hankali iya tashin hankali ya karimatu ta shigesa, itama tayi kuka yafi cikin carbi, tarasa da wane kalami zata bawa hajja ha?uri ta gafarce ta, ha?i?a ta aikata abubuwa na son zuciya saboda duniya, tayi tunanin ta daina kafin asirinta ya tonu gashi har tana neman taimakon ?ar uwarta da asiri, itakam yau tashiga uku.

Da sauri ta rarrafa ta ri?e ?afar hajja tana kuka tana cewa

"Dan Allah hajja ki gafarce ni, na rantse da girman Allah bazaki kuma kamani da laifi makamancin wan nan ba, natuba hajja, wallahi nabi Allah nabiki, dan Allah kar kiyi fushi dani hajja, idan kikayi fushi dani Allah ma zaiyi fushi dani.

?agowa hajja tayi tare da ri?e hannunta tace "sallar ki ta kwana arba'in karimatu Allah bazai taSa karSa ba, wayasan iya sallar shekaru nawa kikayi asara? Na yafe miki karimatu, kije ki nemi yafiyar mijinki da kuma tafiyar Ubangiji, taskokin Allah yawane dasu, Insha Allah zai gafarta miki, kuma kiyi tubatun nusuha, tuban da idan kika yishi bazaki kuma waiwayar baya ba.

San nan abu nagaba da nakeso dake shine, karki kuskura ki ?ara bin hanyar boka ko malam domin taimakon Wan uwanki, idan bazaki iya taimaka masa da addu'a ko shawara ba to kizuba masa idanu, banda ma shashanci irin naki, taya zakibi hanyar saSo domin taimakon wani? Kinje kin karSowa Rashida a sirin dazata kori ?ar mutane a gidan aurenta.

Shin kin manta ?unci da ba?in cikin da ake shiga idan aka raba mutum da nasa? Ko kin manta irin tashin hankalin da muka tsinci kanmu a lokacin da uwar Rashida Allah ya ji?anta ta rabamu da ubanku? Idan sauran ?annen naki basu saniba ai ku kun sani tunda kune manya, shekara nawa mukayi a cikin ?unci kafin Allah ya warware ?ullinta? Ko duk kin manta? Amma wai yau kece kike taimakawa Rashida da asiri domin ta raba miji da mata, kin ban mamaki karimatu.

Nice uwar data kawoki duniya, a cikin mahaifata kika kwanta har tsawon wata tara, san nan nayi wahalar na?udar ki na haifeki san nan kikasha nono na kuma kika ginu a tarbiyya ta, bantaSa tunanin jinina zai yi wan nan ta asar ba, baki kyauta minba kuma baki kyautawa kanki ba, ai ko ita Rashida dabani na haife ta ba nonona kawai tasha bazatayi wan nan abin da kikayi ba, dan haka kitashi ki bani waje, kuma kar na?ara ganin ?afar ki a Cikin gidan nan ko kuma ganin kin kirani a waya indai banice na nemeki ba, kitashi nace, hajja ta faWa cikin karaji tana nuna mata ?ofa.

Da sauri ya karimatu ta zari wayarta ta fice dan kota kan jakar bata biba bare kayan cikinta, ficewa tayi daga gidan tana sharar hawayen sukar Da zuciyar ta take mata.

Ajiyar zuciya hajja ta sauke tabi bayan ya karimatu da kallo tana furta addu'ar shiriya ta har abada a gareta.

*Maryam*

" Da sauri ta kalli samira tare da buga ya?e wanda ake cewa yafi kuka ciwo tace

"Ba haka bane Samira, taya zan zauna wahalar da kaina alhalin nasan bana gaban sa, ai tunanin wanda ya damu dakai ya kamata kayi bawai wanda bai damu da kaiba, nifa gaba Waya tunanina yana kan umma, so nakeyi kawai naje na ganta, shiyasa kikajini shiri tun Wazu amma ba wani tunanin nakeyi ba.

*Samira*

Murmushi tayi tace "Maryam kenan, kozaki Soyewa kowa komai ni bazaki iya Soyemin ba, kallonki fa kawai nakeyi, tun ranar da ya Nasir yazo gidan nan na lura gaba Waya kin rage walwala da sukuni, ba wani abinne ya sakaki kuma a wan nan damuwar ba illa zaman jiran sa da kikeyi, to bara kiji na faWa miki, Nasir bazai zoba, koda zaizo kuwa bazai taSa cika al?awarin sa na zuwa da Rashida ba, dan haka idan kin gaji da jiransa kawai ki shirya na rakaki gidan ki, muje mubawa Rashida ha?uri akan tayi ha?uri tabarki ki zauna, kinga daga nan sai ki fara zaman ha?uri da juriya dan kuwa zubar da mutunci ne mun runga munyi shi.

Girgiza kai Maryam takeyi hawaye na sauka a cikin idanun ta tace

"Bazan yi hakaba samira, kawai dai inason ki ?issima hakan a matsayin kece yake faruwa dake, ya zakiji dan Allah? San nan dame zaki fassara makomar auren ki? Ki iya tunawa fa watana nawa a matsayin matar Nasir? Idan ina lissafi dai-dai wajen watana huWu da auren sa a kaina, amma har yanzu ace ban tsinci komai a gidan aurena ba sai takaici da ba?in ciki, tayaya bazanyi tunani ba? Kuma tayaya bazan saka abin a cikin raina ba? Wallahi tallahi Samira badan mutuwar babana ba da yanzu yaci ace tura takai bangon dazan tona masa a siri a wajen babana dan yasan halin danake ciki, sai ta fashe da wani sabon kukan mai sauti tana cewa.

"Ya Allah kaji?an babana da rahama, Allah kasa yana aljanna.

Rungume ta samira tayi a cikin jikinta itama ta fashe da kukan tana shafa bayanta, sai da sukayi mai isar su tukunna suka share hawayen suka fara tattauna hanyar da mafita zatazo musu.

*****

Jingum jingum akayi tsakanin Maryam da samira kowa da Abinda yake sa?awa a cikin zuciyar sa.

Ita samira sa?awa take a ranta muddin Nasir bai zoba nan da kwana biyu kiransa zatayi a waya taji matsayar sa, dan tagaji da ganin ?awarta kuma ?ar uwarta a cikin halin damuwa, ita shaida ce ta Maryam bata samun barci, a tsaye take kan ?afafunta wajen salloli da addu'a, dan haka yakamata ace ta samu sau?i ko yaya ne, sai tasaki ajiyar zuciya tace "ya Allah ka duba ta.

Ita kuwa Maryam Abinda take sa?awa shine "zata bawa Nasir nan da sati guda, muddin bai zoba wallahi bazata ?ara koda yini Waya bane a wan nan garin, zata tattara ta koma garin su gidan su wajen ?an uwanta masu so da ?aunarta, kuma tabbas tayi al?awarin muddin ta koma gida ta koma kenan, zata zauna ta sanar da yayanta da kuma ummanta irin zaman datayi a gidan nasir da kuma gidan samira, san nan ta rantse da girman Allah sai Nasir ya saketa idan ba hakaba kuwa ta makashi a kotu.

*****

?arar bugun gate Win itace duka ta dawo dasu hayyacin su, zumbur samira ta mi?e tana tunanin wanda yazo domin kuwa tasan ba mijinta bane dan shi ya daWe da shigowa gidan, yanacen yaci abinci ya ?ule a Wakin research yana karatu.

Amma duk da haka sai ta tashi ta nufi gate Win da furta kalmar waye? Nine. Aka bata amsa daga cen Sangaren, dafatan da mijinta yayi yasa tai saurin jiyowa, ashe shima yaji bugun Ya fito, sai kawai yayi mata nuni data koma zai buWe saboda jin muryar namiji da yayi, komawar samira tayi ta zauna a kusa da Maryam wacce take a nutse kamar koda yaushe.

Sallamar da akayi a ?ofar falon itace taja hankalin su Maryam baki Waya, da sauri suka kalli ?ofar kuma da sauri suka mi?e tsaye baki Wayansu

Da mamaki Maryam ta buWe baki har yana mata rawa tace

"Rar..rar..rashida.

Itama rashidan da sassarfa ta nufi wajen maryam tare da rungume ta ta fashe da kuka tace

" ?ar uwata.

Nan aka shiga kallon kallo tsakanin samira da mijinta da kuma Nasir wanda ke tsaye yanata faman buga uban murmushin mai cike da samun nasara.

*KUTSE*

*PAGE 18*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


Jugum  jugum mutanen falon sukai, babu wani mai kwakwkwaran motsi a cikin su balle magana, bawai basu da abin faWa bane sai dan gaba Waya nasir da kuma Rashida sun goge musu hadda da Abinda sukayi, ashe da gaske Nasir yake da yace tabbas zaizo da Rashida domin su tafi da Maryam?

Samira ce ke wan nan tunanin a ranta tana cewa "gaskiya akwai wata mana?isar a wan nan zuwan na Rashida? Taya duk bala'in ta da a zababen kishinta amma har tatako wajen matar datake kira data mata kutse wai tazo tafiya da ita? Sai ta girgiza kai tana kallon Maryam wacce kanta ke ?asa ta kasa koda kwakwkwaran motsi saboda das karewar da tayi, wani tausayin tane ya ratsawa samira a cikin zuciyar ta tana me nemawa Maryam Win tsari da dukkan sharri da kaidin da Rashida tazo mata dashi.

Rashida

Sakin Maryam tayi tana murmushin dayake bayyanar da hakwaranta, hannun Maryam Win ta kama tare da zaunar da ita kan kujerar data sameta akai san nan itama ta zauna, tana zama kuwa kamar haWin baki duka mutanen falon suka zauna har da Nasir wanda ya zuba musu idanunsa yana murmushi ko ?iftawa ido ba yayi.

Hannun maryam duka biyun rashida ta ri?e tana mai kallon fuskarta tace.

"A madadina da kuma madadin baban Halima muna baki ha?uri kuma munzo tafiya dake, dan Allah Maryam kiyi ha?uri da dukkan abubuwan da suka faru damu a baya, kiyi min adalci kuma ki iya tunawa idan kece a madadina ya zaki ji? Ya zakiji kuma me zakiyi a lokcin da mijinki yayi Aure kuma yakawo miki matar har gida batare daya gaya miki ba sai daga baya matar ta tona musu asiri? Duka ma ba wan nan ba? Banason a maida zancen baya yadawo yanzu saboda na manta da komai kuma kema ina fatan ace ki manta da komai Win.

Nayi nemanki nayi cikiyar ki Maryam a lokacin daban san inda kikaje ba, dan Allah kiyi ha?uri ki yafewa mijinmu, kinsan Wan adam tara yake bai cika goma ba, dan haka muma ?an Adam ne kuma ajizai kinga kenan a koda yaushe zamu iya aikata kuskure ko muna sane ko bama sane, nidai na yafe miki Abinda kukayi min keda mijinmu, Saboda haka duka muyi ha?uri mu yafi junan mu koma kafa kyakkyawar zamantakewa a tsakanin mu.

Ba Maryam ba, hartaya samira dasu Nasir Win sai da suka saki ajiyar zuciya dajin daWin magan ganun Rashida, duk da awani Sangaren na zuciyar samira tafi kyautata zaton Abinda rashidan takeyi tsantsar kissa ce da kuma iya bariki, banda haka macen data kusan rasa ranta saboda kishi shine zata wani lallaSo tazo bikon kishiya?

Hnmmm, Samira ta sake sauke ajiyar zuciya tare da fatan wata zuciyar tata zata kyautatawa rashidan zato mai kyau, kuma tana fatan koda ?arya da makirci Rashida ta shirya yazama gaskiya ko ?awarta tasamu cikakken ?anci a cikin gidanta.

Maryam

Kasa magana tayi sai hawaye dake zuba akan kuncinta na farin cikin kalaman da taji Rashida na furtawa akanta, wai mijinsu, lallai kura tayi lafiya kenan, saboda tsabar kyakkyawar zuciyar da maryam keda shi ita bama ta hasaso ko makirci ne Rashida ta ?ulla ba, dan a iya saninta da Rashida da kuma Wan zaman da tayi da ita tasan muddin tace bazatayi abuba to babu mahalu?in daya isa ya canza mata ra'ayinta, kenan Rashida da kanta tayi ra'ayin zuwa gurinta dan ta mayar da ita wajen mijinta? Idan kuwa haka ne tabbas ita Maryam zata basu mamaki, tayi Al?awarin da ikon Allah zata zauna lafiya dasu kuma tasamar musu farin cikin da suke fata daga gareta, dan tasan cikakken ya?inin da suke dashi akanta ne yakawo su wajenta, kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login