Showing 48001 words to 51000 words out of 175193 words

Chapter 17 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

555

a cikin gidan nan muddin yanason zama dani, kuma asanin da nayiwa Nasir akan ya rabu dani gwaran masa ya rasa uwar data kawo shi duniya ma, dan haka keba kowa bace face banza ballagaza wacce bata da ?anci, idan kin isa ki fito mana, wallahi kina fitowa sai nayi miki duka na haWa miki jini da majina, kuma wallahi sai naga bayanki.

*Maryam*

Wani irn duka ?irjinta yayi a lokacin da Rashida take cewar sai taga bayanta, baza tace bataji zafin magan ganun taba amma cewar sai taga bayanta shine Abinda yafi dukan ruhinta, Waga kai sama tayi tana kallon silin tana cewa "ya Allah, kajin Abinda baiwar ka take faWa a kaina, Allah idan tafi ?arfina nasan batafi ?arfin kaba, Allah na barka da ita a dukkan Abinda da zatayi min na sharri, ya Allah ka shiryar da ita kuma ka ganar da ita.

Ita dai Maryam batasan sanda Rashida ta gama haukarta tabar jikin ?ofar ba domin air piec ta saka a kunnenta ta ware ?ira ar shek sudais tana saurara cikin suratul ba?ara mai girma .

*Nasir*

Koda ya fita rasa inda zai nufa yayi, yarasa mashi meke masa daWi a rayuwar sa, har zai nufi office Win Ramadan sai ya fasa ya canza hanya, tafiya mai nisa ya Wanyi san nan ya tsaya a dai-dai inda babu hayaniya sosai, kansa ya kifa a jikin sitiyari yana tunanin farawar rayuwar sa zuwa yanzu da yake shan yajin rikici a wajen Rashida.

*Tuna baya*

Nasir haifaffen Wan garin daura ne, su uku ne mahaifan su suka haifa, shine babba san nan zulai take bimasa sai kuma autar su Jamila, mahaifiyar su ta rasu ne tun lokacin Jamila bata fi shekara biyar ba a duniya, tun daga nan ri?on zulai da Jamila ya koma hannun ?anwar babar su nafi dake cen garin roko, shi ya zauna ne a wajen babansu badan komai ba saboda shi namiji ne kuma yana da ?ulaficin babansa san nan yana da burin yin karatun boko mai zurfi, rayuwar ala?ar sa da gidan su Maryam yafara ne sanadiyyar mansur abokin sa, mansur shine babban amininsa kuma Wan uwan da bashi da kamar sa kaf duniyar nan, su kansu iyayen su sanadiyyar sune suka ?ula zumunci mai ?arfi wanda yasa har su iyayen suka zama aminan gaskiya da gaskiya.

Mansur yasan babar Nasir ta rasu, kuma su su biyune a cikin gidan domin tunda babar su ta rasu baban su ya ?ara aure bai taSajin daWin auren ba saboda matar bata da kirki kuma bata taSa Waukar Nasir matsayin Wanta ko Wan mijinta ba, tana masa kallo Wan ri?o shiyasa kullum sai Abinda Ya ?aru a game da gallaza masa, amma a hakan dai sai da matar ta shekara goma suna tare da baban nasa da daWi da kuma babu daWi har Allah yakawo rabuwar su daman bata taSa haihuwa ba.

Hakan yasa mansur da baban sa harma da ummansu suka Wauki Nasir kamar sune suka haifeshi, komai anan yakeyi kwana ne kawai yake kaishi gidan su, shi kansa baban Nasir Win kwanon sa na safe rana dare a gidan su mansur Win yake tunda bashi da mata, haka dai suka dunga rayuwa komai tare a keyi da mansur da kuma Nasir, akan idonsu aka haifi Maryam, kuma tunda aka haifeta Nasir yake nuna kulawarsa a gareta, ita kanta sun sha?u da juna har makaranta ma wataran shine yake kaita.

Suna tsaka da rayuwar su mai daWi Allah ya aikowa da baban Nasir a jalinsa, ranar Nasir ya tabbatar bashi da kowa a rayuwar sa, kuma bayan ya ta'allaka hakan ne baban su Mansur ya nuna masa cewar shima yana da gata har yanzu tunda suna raye bai rasa iyaye ba.

Wan nan dalilin yasa rayuwar nasir ta koma gidan su mansur gaba Waya.

Bayan sunyi candy sun zana jamb kuma zaman yafara canza salo, shi Mansur yayi nasara kawo duk makinsa da ake nema, shi kuma nasir bai yi nasarar kawowa ba, koda mansur yafara zuwa makaranta sai zaman da Nasir yake yi haka yafara damun baban su Mansur, hakan yasa ya ro?i wani makwancin su akan yafara zuwa da nasir kano cen kantin kwari yana Wan zama a shagonsa kafin nan da wani lokacin dazai sake zana jamb Win, ma?ocin bai ?iba da yake baban su Mansur mutumin kirki ne.

Sai da Nasir yayi shekara biyar yana zuwa kasuwanci a kano, badan baba ya tilas ta masa akan yaci gaba da karatu koda a Kanon ne da bazai cigaba ba tunda yanajin daWin kasuwar, hakan yasa ya jajirce ya samu admission a B.U.K, cikin ikon Allah da taimakon baban su Mansur da kuma Wan Abinda yake tarawa har Allah yabashi ikon yin degree kuma still yana zuwa kasuwar sa.

Sanadin haWuwar sa da Rashida kuwa shi ne .

Lokacin bikin Ramadan, shine babban abokinsa, ita kuma Rashida itace babbar ?awar amarya, sai ya kasance tsakanin Rashida da kuma Nasir sun samu connection mai kyau, har akayi biki a ka gama suna tare sai bayan an gama biki ne Rashida ta tasowa da Nasir kalmar tanason shi, dan Allah ya taimaka yabata kyautar zuciyar sa, har ga Allah shima yana sonta domin Rashida kyakkyawar macace son kowa ?in wanda yarasa, dan ko a cikin gidan su tafi kowa kyau da kuma fari, dan farin tama har wani yashi yashi yakeyi da kyalli, ga hanci da ido kamar ita ta zanawa kanta, gashi kuwa ba'a magana dan Rashida dar ce wajen yalwar gashi da cikararsa .

amma idan ya kalli yanayin gidansu sai zuciyar sa ta tsinke domin yasan ita ba tsarar sa bace dan tafi ?arfin sa, sosai Nasir ya janye mata saboda bayason a samu Matsala dan dayawa masu kuWi basa ?aunar talaka ya daSe su, Rashida kuwa da taga haka da kanta ta sanar da abban su halin da suke ciki da Nasir.

Alhaji Bello tabo ya kasance mutumin kirki kuma bashi da kyamar talaka, kai duk wani Wan Adam ma dazai raSeshi baya da kyama ko kaWan.

Ba?aramin daWi Rashida tajiba a lokacin da abban su hace yanason ganin Nasir, ranar kuwa da Nasir zaizo sai da yayi ta tsula gudawa saboda far gaba, mansur yayiwa waya ya sanar dashi yayin da ya sanar da Ramadan shima, takanas suka tawo da Mansur kano suka haWu da Ramadan suka amsa gayyatar abban Rashida.

Dattako iya dattako sun ganshi a gidan su Rashida, kuma daga yanayin da sukaga hajja suka ?ara tabbatar da cewar Lallai aure a gidan su Rashida babban arzu?i ne.

A wan nan shekar aka Waura auren Rashida da Nasir bayan uwar soyayyar da suka sha, dan ji suke rayuwar kamar babu wasu masu farin ciki sai su, duk da Nasir yace bashi da gida kuma shi yaron shagone san nan bai samu aiki ba amma a hakan Abban Rashida yace karya damu kansa yayi Abinda yake dai-dai halinsa.

Akwatina huWu Nasir ya samu yayiwa Rashida duk da abban nata yace basai yayi ba amma Nasir yace shi sai yayi saboda ya nuna jin daWin halacci da kyautatawar da akayi masa, babu Abinda zai cewa Abban Rashida sai Allah ya gafarta masa ya yalwata masa kabarin sa kamar yadda shima ya yalwata masa, dan gida sukutum Abban Rashida yabawa Nasir kuma halak malak ba aroba domin ya zauna da ?arsa, har taya kichen Win Rashida sai da aka cikasa da kayan abincin da sai sukai shekara Uku basu ?are ba, ga wata garar arzu?i ta mallaka masa shago guda Waya a kantin kwari aka cika masa su fal da kaya.

Wan nan abu da Abban Rashida yayi masa shiyasa yake ganin mutunci da darajar Rashida kuma yake ?ara sonta tunda duk Abinda Ya zama a duniya a sanadiyar Rashida ne.

Sai da sukayi shekara Uku da aure san nan Rashida ta haifi Halima, kuma tana haihuwar ta Nasir yayi mata la?abi da Halima domin kuwa hajja mutuniyar arzu?i ce dan tana nuna masa ?auna kamar uwarsa.

Haihuwa ta biyu ma da Rashidan tayi mace ta haifa, kuma tana haihuwar yayiwa yarinyar la?abi da saudatu , ba?in ciki iya ba?in ciki Rashida ta ?unsa wai akan me za'a sakawa ?arta saudatu sunan ?an ?auye?

Shima Nasir cikin Sacin rai yace "kin manta sunan uwar data kawoni duniya ne? TaSe baki Rashida tayi tace "to sai me dan sunan uwarka ne? Nima ai sunan tawa uwar nakeso a saka min, kuma ma meyasa da zaka saka sunan bakayi shawara dani ba? Nidai gaskiya babu wani suna da za'a sakamin wai saudatu.

Wani malulun ba?in ciki ne ya ishi Nasir, bai saba dukan mace ba da a lokacin nan wallahi sai ya kwakw kwaWawa Rashida mari, amma madadin haka sai ya daure yayita addu'a, sai daya nutsu daga baya san nan tace

"Nine dai uban yarinyar, kuma a matsayina na ubanta na saka mata suna saudatu, idan kinga dama ki kira sunan ta idan baki ga dama ba karki kira.

Haka yatafi yana tunanin daman Rashida ta raina ?an uwansa a rayuwa, bata ?aunar taga wani nashi ya ziyar ceshi, ko matar Mansur tasha wula?anci a wajen Rashida, amma basa zuciya a hakan dai suke ziyar tar su, shima kuma koyace tazo suje sai tace ita baza tajeba, haka suma suka ha?ura suka janye zumunci dasu, dan ko Mansur yanason zuwa wajen Nasir sai dai ya sameshi a kasuwa amma baya zuwa gidan sa, idan yace sujema ca yake bazai jeba saboda matarsa bata da mutunci, dan ko ada da suke zuwa suna gaisawa take tashi ta baWesu da ?ura ta basu waje, wataran ma ko fitowar su gaisa batayi.

Bazai manta yadda take wula?anta ?annensa da ?an uwansa na rogo idan suka je gidan ba, tana ganinsu zata fara fesa air freshener da turaren wuta, kuma ko kaWan bata bari su hawo sama sai dai a sauke su a Wakin ?asa da yakasance na ba?i maza, haka ko saman ma suka hau da niyar suWan zauna ko kuma su gaisa haka zatayi saurin shimfiWa musu tabarma a ?ofar falon ta rufe falonta da mukulli, kuma ko kadan bata bari su taSa yaranta, idan kuma Nasir yayi magana sai ta saka kuka tace

"Ita wallahi suna takura mata, ita fa batason a kutso rayuwar ta, meyasa kowa bazai zauna a gidan su ba? dole ne sai anzo inda suke? Wula?anci iya wula?anci babu irin wanda ?an uwan Nasir basa gani a rayuwar su, tun suna nacin zuwa har suka daina, ita kuwa sau Waya tataSa zuwa rogo dan ko haihuwa ?annensa sukayi bata zuwa, san nan ko bikin dangi a keyi bazata jeba , shima zuwan datayi sau Wayane da ?anwar babar tasu nafi ta rasu, kuma koda taje ?in sauka tayi a kowane gida, suna gama gaisuwa tatashi wai ita sai dai Nasir ya kama mata hotel, shi kuma yayi rantsuwar wallahi tallahi muddin bazata kwana anan gidan ba sai dai ta kama da kanta, ai kuwa haka ta kwashe ?a?anta tatafi ta kama hotel da kanta suka kwana , washegari kuwa sai yayi tafiyar sa yabarta a garin.

Ita kuma data tashi sai kawai taita kiransa ya?i dagawa, daga baya kawai sai yayi mata text akan cewa yawuce idan taga dama sai tatawo, wan nan maganar ta bala'in ?ona ranta, shiyasa koda ta dawo bata zarce ko inaba sai gidan ya karimatu.

Tana zuwa kuka ta fashe mata dashi akan ta taimaka mata akan Nasir, kamar basuyi soyayya ba, ita sai take ganin kamar yadaina sonta ne, abu kaWan sai faWa, abun kaWan zuciya, ita dai ta samo mata taimako Nasir yadaina yi mata wan nan halayen, san nan dan Allah ya daina musu da ita, kuma ya dunga ji da ita da riritata, kai ita a san samunta ma ya kasance a mallaka matashi a tafin hannunta sai yadda tayi dashi.

Dariya ya karimatu tayi a lokacin, tace "karki damu ?anwata, kinzo inda za'a share miki hawaye, shin kin manta yadda mijina ya zama solo Siyo a kaina? ?aga kai Rashida tayi tace "inafa zan manta yaya, ko yanzu danazo gidan nan ai nagani, murmushi ya karimatu ta sauke tace "to kema haka Nasir zai koma.

Wan nan shine labarin Nasir da haWuwar sa da Rashida.

*Cigaban labari*

*KUTSE*

*PAGE 21*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Nasir*

Ranshi gaba Waya yagama Saci kuma yagama dugun zuma saboda tunanin daya yayi, taya ma zai bari shashancin Rashida yashafi amanar daya Waukar wa uban ri?onsa, taya zaiyi wa sarare da Maryam alhalin shi lokacin da yake bu?atar taimako a rayuwar sa babanta ne ya tallafeshi har zama wani Abin acikin rayuwar duniyar, to shikam ya Wauki aniyar zai ri?e Maryam hannu bibbiyu ya darajata kodan darajar Mahaifin ta da Wan uwanta koda kuwa Rashida zata zarge shi.

Kan motar ya juya yafara shara tafiya domin isa gida dan yau ya Wau niyar komai tafan jama fanjam, dan akan inganta rayuwar Maryam babu Abinda bazai iya yiba yanzu, sai da yatsaya ya sayi kayan daWi san nan ya nufi gidan da niyar ayita ta ?are, amma yana shiga sai yaga babu kowa a falon, har taya fitilun gidan ma an kashe su dan dare yayi lokacin.

Fitilar ya kunna yana ?arewa ko ina kallo, babu Alamar mutane sun zauna a falon, dan haka sai yayi cikin Wakin sa domin ya watsa ruwa yaji daWi, koda yayi wankan fitowa yayi ya tsane jikinsa tare da Waukar jallabiya ya zura, ?ofar Wakin nasa ya buWe ya fito yana kallon Wakin su Halima yana tunanin ko mai Maryam takeyi yanzu?

Kasa buga ?ofar yayi sai yayi wajen dining domin yaci abinci dan yunwa yakeji, yana zuwa dining Win kuwa sai ga fulasan abinci suna kallonsa harda fulas Win shayi, da sauri ya zauna ya buWe fulasan abincin sai yaga dankalin turawa harda kwai a ciki, fulas Win shayin ya fuWe sai yaji ?amshin kunun gyaWa, da sauri ya tsiyaya kunun yanajin daWi a ransa, duk da kunun babu zafi sosai yaji daWinsa kuma yana gani yasan Maryam ce tayi ba Rashida ba, dan Rashida bata taSa dama masa kunun gyaWa ba dan batashan sa dan haka tace bazatayi Abinda bazata shashiba.

Duk da dankalin ma yayi ba kamar yadda aka soyashi ba amma haka ya tutturashi domin yunwa yakeji, bayau Rashida ta fara ?in bashi abinci ba idan suna rigima daman ya rigada ya saba, dan haka baiji komai ba sai Allah ya sawake daya furta.

Sam hankalin Nasir ya?i kwanciya da rashin jin Maryam da yayi, dan haka sai ya le?a ta windown baya domin yaga ko lafiya take, yana le?awa kuwa ya ganta ri?e da wayarta tana karatun Alkur'ani a ciki, wani sanyi yaji yana ratsasa domin gurin addini da ri?o dashi yasan Maryam ba daga nan ba, gyara tsayuwar sa ya Wanyi san ya kira sunanta.

Maryam, Maryam,

Da sauri Maryam ta Wago ta kalleshi a tsorace dan bata gane muryar saba dan yayi ?asa da Muryar tashi sosai.

Suna haWa ido ya sakar mata murmushi ita kuma sai tayi saurin mi?ewa ta buWe banWaki ta shiga ta rufo ?ofar, har ran Nasir bai ji daWin Abinda tayi ba, sai kawai ya girgiza kai ya bar wajen yana tunanin kotaci abinci?

*Maryam*

Yunwa ta dameta dan tun Wan dankali da kunun da tasha da safe har zuwa ?arfe tara na dare bataci abinci ba, har wani hazo hazo da jiri jiri takeji don daman tana da ulcer mai sar?e mata numfashi, ganin numfashinta na sar?a yasa taita Wurawa cikinta ruwa wai dan taji daWi, ruwan kuwa baiyi mata aikin komai ba sai ma ?ulle mata ciki da yayi yazo mata har ?irji, juyin ciwon ciki ta dungayi kamar ta sume har daga baya dai Allah ya taimaketa ta fara kwara amai har sai data amayar da da ruwan dake cikinta.

Ajiyar zuciya kawai ta dunga saukewa har wani wahalallan barci ya Wauke ta akan daddumar datake kwance.

Sai misalin wajen biyu na dare ta samu ta farka san nan ta mi?e da kyar saboda jirin dake Wukarta, a hankali ta kunna fitilar wayarta ta buWe Wakin tafita da sanda har ta nufi wajen dining Win, tun kayan abincin data jera da safe suna nan ba'a Wauke ba da azama ta ?arasa wajen ta zauna ta buWe, taga anci abincin amma da saura Shiyasa tafara ci hannu baka hannu kwarya, duk da kunun ya tsinke amma bai lalace ba, kai ita ko ya lalace ma a haka ta kwankwaWi kayanta dan yunwa bata da hankali.

Tana gamaci kuma tayi azamar tashi ta koma Waki tare da bankowa.

*Nasir*

Ya Wanji motsi kaWan saboda tunanin halin da Maryam take ciki bai barshi ya runtsa ba, tunanin kotaci abinci yafi damunsa shiyasa ya kasa barci, a lokacin dayaji kuma an rufe ?ofa sai yayi sauri ya buWe dan yaga kowaye, sai dai baiga komai ba, sai ya Wan taka jikin Wakin su Halima dan ya duba Maryam Win.

Itama Maryam taji fitowar mutum amma bata saniba Nasir ne ko Rashida, faWuwa gabanta ya shigayi tana tunanin kodai Rashida ce zatayi mata wani abin tunda ta furta sai taga bayanta? Shiyasa tayi saurin saka wayar a ?ar ?ashin ta tayi lamo takasa koda kwakwkwaran numfashi, tayi niyar ta raya daran nan tana kaiwa Allah kukanta amma ta rarrabi da tsoro sun hata taSuka abin arzu?i

*Washegari*

A zahirin gaskiya sallar asubahi ba wani damun Mutanen gidan tayi ba, Nasir bai fiya fita Masallaci ba sai da kwakkwaran dalili, dan wataran yanaji ana kiran sallar asubahin amma bai tashi ba sai dai ya gayara ma kwanciyar sa, ballantana Rashida wacce har ?arfe bakwai ma sallar safiya takeyi da rana gatsalar gatsalar, shiyasa koda Maryam tatashi da asubahi sallar asubahin tayi bayan tayi azkar ta mi?e tanawa Allah hamdala, da sauri tafito ta le?a falo taga babu kowa sai tayi wuf ta fito ta nufi kichen dan tasamawa cikinta Abinda zataci, dan tayi rantsuwa sai ta kwan biyu bata fitoba saboda lamarin gidan yana bata tsoro.

Da sauri ta dafa shayi tana daga tsayen tasha cikin hanzari, haka ta dunga ?one harshen ta amma sai data shanye dan sosai takeson shan shayin dan dama ita mayyar shayi ce, kafin tagama shan har Indomie data Wora ta dahu sai kawai ta sauke ta nemi fulas ta juye a ciki, da sanWa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login