Showing 138001 words to 141000 words out of 175193 words

Chapter 47 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

549

ba?in talauci da kuma rashin abinci yayi ajalinki, shashashar banza da hofi.

*****

*Rashida*

Da kyar ta lallaSa ta fara tafiya tana waigen gidan wanda ?an uwanta suke cewa wai tafita daga cikin sa kenan, to shin muddin su hajja suka wanke hannu a kanta ai ta kaWe har ganyenta san nan ta mutu ta lalace ba?i Waya, tana tafe tana share hawayen ba?in ciki har tazo bakin parking space san nan ta dakata ganin malam ado driver ya Wauko mota yana ce mata ta shiga ya kaita gida, da kamar bazata shiga ba sai kawai ta shiga dan bata da wata mafita idan ba wan nan ba, suna tafe tana kuka malam ado na bata ha?uri dayi mata nasihar irin rashin jin da takeyi, yana kuma ?ara nuna mata mahimmancin su hajja a wajenta, shiru Rashida tayi batayi magana ba, dan da dane wallahi sai taci mutuncin malam ado ?ila harda guzurin mari sai ya samu.

Mamakin rashin maganar ta yayi akan furucinsa a ransa yace Lallai ruwa ya daki babban zakara, ashe akwai ranar da bakin Rashida zai mutu da rashin kunya? Haka dai shima malam ado yaja bakinsa ya tsuke har ya kaita gida bai kuma tanka mata bata ya ajiyeta ya juya abinsa, yana tafe yana tunanin tsarkin zuciya irinta hajja domin shi amintaccen driver Alhaji ne kamin ya rasu, kuma tunda ya rasu ya zama amintaccen drivern hajja wanda ya wancin lokuta suna tafe tana Wan bashi labarin Abinda ya shige mata duhu ko yake damunta, dan haka ne yasa har yasan wasu ?an abubuwan game da Rashidan wanda suke faruwa shiyasa har yayi mata ?ar nasiha, kuma shi bama ya kusa yaWan fitane hajja takira sa, kuma tana kiransa ya gane babu Lafiya ko daga Muryar ta zaka gane hakan, kuma yana tambayar ta lafiya tace masa yazo gida yanzu yanzu idan yana kusa yakai Rashida gida, karya bari tafita tatafi ita kaWai kada ta cutar da kanta a hanya, wan nan shine dalilin sa na zuwa ya kawota amma badan Rashida ta isa a wajen sa ba, Saboda a bayyane yake kowa yasan bata da mutunci kuma bata kallon kowa da gashi.

Rashida kuwa tana shiga Wakinta ta faWa kan gado tana sakin wani sabon kukan da tunanin cutar da maman mu tayi mata, da kuma cin zarafin da ya Aliyu yayi mata hajja tana kallonsa da sauran ?an uwansa, sai ta fashe da kuka tare da tashi ta Wauko wani ?aton hotonsu dake ma?ale a Wakinta suna cikin farin ciki ta fara shafawa hawaye nata ambaliya a fuskarta.

Hajja ce a tsakiya da ita da Abban su, sai ya karimatu a gefen hajja shi kuma ya Aminu a gefen Abba, daga gefen ya karimatu kuma rashida ce da nusaiba auta a kusa da ita, Sangaren Abba kuwa bayan ya Aminu dake kusa da Abba sai ya Aliyu da kuma Ahmad a gefen suna dariya, wan nan hoton ya ?ara tayarwa da Rashida sabon tsumin ?aunar hajja da ?an uwanta wanda tanada ya?inin kaf duniya babu mai sonta da ?aunarta bilha??i da gaskiya sai su.

Ganin kukan bazai kaita ba sai kawai tatashi ta faWa wanka tare dayo alwalar sallar azahar dataji anata kiranta, abin mamaki yau Rashida wacce salla bata dameta ba wai ita ce ta tada kabbara wai zatayi sallah, ita kanta kunyar Allah ce ta rufeta saboda harta manta rabon data kalli gabas wanda sharaWi ne a cikin sharaWan damai duma yabata akan cikar burukanta, koda zatayi sallar ma a kwai waWanda ya ?iyace mata data sallata, yace zata iyayin sallar amma banda asuba da kuma la'asar su sauran zatayi su amma bako yaushe ba, wan nan dalilin nema yasa sallar t????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? afita daga kanta dan haka sai tayi wata da watanni ma batayi ba.

Kuka Rashida ta saka a lokacin datazo karatun sallar taji bakinta ya?i buWuwa, daga baya datayi ?o?arin buWe bakin da ?arfin tsiya dan tayi kabbarar harama ma wallahi sai takasa ballantana karatun sallar, sai kawai taji bakinta yana cewa mai duma, damai tsidau.

Kuka sosai taci ta gode Allah san nan tatashi tanason ta furta kalmar istigfari amma sheWan nayin kutse cikin zuciyar ta ya hanata taSuka abin kirki, itakam batasan me zatace ba, amma kan tana cikin masifar da ita kanta tasan idan ta mutu a haka wallahi ita da samun rahama sai tsananin rabo da ikon Allah.

Shikkenan tun daga wan nan ranar Rashida bata ?ara kuskuren Waukar mayafi ko hijab tace zatayi salla ba, dan jitayi gaba Waya ma gwara ta ha?ura da gwadawar har lokacin da zata koma gurin mai duma daya warware sihirin da yayi mata akan sallar.

*Bayan wata biyu*

Abubuwa da yawa sun faru ciki harda Rashin lafiyar da Rashida tayi kamar bazatayi rai ba kuma duk damuwace ta jefata a wan nan yanayin, gashi duk sanda ta gwada wayar hajja kota ya karimatu bata shiga, haka idan ta gwada ta nusaiba itama bata shiga, ko ya Aminu da Ahmad suma duk sunyi blocking layinta wanda ya nuna mata cewar duk sunyi blocking Winta daga cikin rayuwar su.

Batasan me zatace ba, amma tabbas tana cikin shiga ukun da warwarar ta sai wani ikon Allah, ita kanta zita taga canze canze a wajen Rashida marassa lissafuwa wanda har take tunanin rashin lafiyar datai ne ya sakata a wan nan yanayin, ko yawan magana yanzu batayi sai kallon waje Waya ta dunga sakin hawaye.

Ga babban Abinda takeson gani yanzu sune yaranta, kuma tashin hankalin tama shine aurenta, ita gata a zaune a waje guda ita ba mai aure ba san nan ita ba sakakkiya ba, a ranta take cewa wan nan halin bala'in da take ciki duk Maryam ce sila, dan a sanda bata shigo rayuwar su ba ?alau take zaune da mijinta da yaranta da kuma ?an uwanta, shigowar maryam rayuwar su shine Abinda ya dagula mata lissafi har ta rabu da mahimman abubuwan da take ganin sune rayuwar ta.

To tayama zata iya rabuwa da Maryam taci bulus? Ai wallahi duk wanda ma yace ta rabu da Maryam batare data Wauki fansa akanta ba Allah ya tsine masa.

Da wan nan tunanin Rashida ta Wauko wayarta domin kiran ?awarta mai son ganin farin cikin ta dason taimakonta.

*****

*Maryam*

Tasan Nasir na sonta da ?aunarta fiye da tunanin mai tunani, to amma irin buWaWWun alamun da yake nuna mata na yanason matarsa ne suke dagula lissafin ta, bai taSa buWar baki yace yanason Rashida a gabanta ko yanason dawo da ita ba, amma yadda idan sun zauna dasu halima yake zancen Rashidan yasa take fuskantar inda tunanin sa yake tafiya, ita kawai tasa a ranta zatayi masa magana tare da bashi gwarin gwiwar dawo da matar sa kota huta da sambatun da yake na kiran Rashida, ita dai tana ganin kamar mafarkinta yake, domin yawancin ranaku idan yana barci cikin dare zakaji yanata juye juye yana kiran sunanta, idan kuma ta tashesa akan ya gyara kwanciyar sa ko wani Abin sai kawai kaji yana kiran

"Na'am Rashida, me kikace Rashida?

Yauma kamar kullum suna zaune bayan sun gama cin abincin dare sai kuwa sauda tace.

"Abba yaushe zamuje wajen maman da kace zamuje? Da sauri Nasir ya kalli Maryam wacce ta Wauke kai tayi kamar bataji Abinda saudan tace ba, Wan basarwa shima yayi yana satar kallon Maryam yana cewa sauda ta kawo kunneta taji, kunnen nata kuwa ta kawo kome ya raWa mata oho! sai ji Maryam tayi sauda ta fashe da dariya harda buga tsalle tana thank you Abba.

Tashi tsaye Maryam tayi da kyar saboda yanayin cikinta daya ?ara girma, takaici ne fal ranta na irin ?umbiya -?umbiyar da nasir yake mata, dan haka sai kawai tayi Wakinta tare da bawa kulu umarnin ta kwashi ?an biyu takaisu Waki itama taje ta kwanta.

*Nasir*

Yanason Maryam kuma yana tsananin girmama ta da kuma bata daraja, bai san dawace fuska zai kalleta yace yace yanason dawo da Rashida ba duk da ba sakinta yayi ba, amma abin da nauyi, musamman idan ya tuna da irin balahirar da aka sha da Rashida da kuma irin tashin hankalin data tsunduma su a ciki, amma ya zaiyi? Yanason Rashida sosai a cikin ransa, kuma tabbas yasan soyayyarta ita ce babbar jarrabawar da Allah yayi masa, dan haka kuma har yau matarsa ce tunda bai saketa ba, shidai yanajin a ransa cikamakon samun nutsuwar sa shine ganin Rashida a kusa dashi, dan haka dole Maryam tayi ha?uri ta kuma cigaba da juriyar kar Sar wata ?addarar wacce yake da ya?inin wan nan karan baza'a samu matsala da Rashida ba, tunda ta faWa masa haka ba sau Waya ba ba kuma sau biyu ba.

Ko ajiya haWuwar da sukayi da ita a wajen cin abinci sun tattauna, kuma ta sanar dashi wallahi tallahi a wan nan karan tabbas zata zauna da Maryam lafiya san nan su cigaba da rainon yaran su cikin aminci, kuma ya yarda da hakan domin yaga tsagwaron nadama da kuma dana sani a cikin idanunta.

Tunda suka dawo bai taSa zuwa gidan taSa tsawon wan nan lokacin, duk yadda take damunsa a wan nan karan na yaje ?in yarda yayi domin bayason duk wani Abinda zai tayar masa da hankali da kuma tuna masa abinda ya faru ya wuce, shiyasa ya gwammace idan tayi masa waya tace tanason ganinsa baya musa mata, san nan baya yarda yaje gidan sai dai su haWu a wajen cin abinci.

Murmushi Nasir yayi a lokacin daya tuna yanayin da suka tsinci kansu a jiya shida Rashida, sai ya dungaji daman kullum ta kasance a kusa dashi ya dunga jin Wuminta.

Yana zaune a kasuwa ta kiras tana kukan tanason ganinshi da gaggawa, baiyi wata wata ba yatafi wajenta inda tayi masa kwatancen tana tahir guesst palace tana jiransa, da kamar bazai je ba dan a wayar har faWa yayi mata akan me zataje hotel bada izinin saba? Kwantar dakai tayi taita bashi ha?uri harya sauko yatafi hotel Win a matsayin iya karsa minti goma, amma sai gashi wan nan yinin sir Nasir ya ?arar dashi ne a cikin hotel Win a Wakin da Rashida ta kama musu.

Abin da ya faru kuwa yana kwankwasa Wakin Rashida ta buWe, yana shiga ta faWa jikinsa tana sakar masa kuka tare da goggoga mata jikinta a jikinsa, wani irin shock Nasir yaji hakan yasa yayi saurin cireta a jikinsa yana matsawa baya, kuma tun karosa tayi a lokacin yaga wata shaiWaniyar riga dake jikinta wacce a sufar da tsarin jikinta babu Abinda ba'a gani amma sunan wai ta saka riga, rigar iya cinyace kuma sharara ce dan Sulolin jikinta yafi kama da Sulolin net, wato gidan sauro da muke shiga yayin barci, wani zulzul Nasir yaji marar sa nayi ai kuwa da sauri ya cacumota yana sakar mata kiss a kowane Sangare na jikinta, ita kuma nan take tafara nuna masa bu?atar ta da yadda tayi missing Winshi tsawon watanni, nasir bai ?iba dan haka nan ya karSi tayinta suka faWa kan gado suka fara gudanar da wasan dambe.

"Murmushi Nasir yayi a karo na babu adadi wanda tunanin Rashida kaWai ke jefashi cikin shau?in mararin ganinta a cikin gidansa, baisan lokaci yaja haka ba, dan yana duba agogo yaga har biyu saura na dare, hakan yasa yayi saurin tashi tare da zarar su sauda domin yakai su Wakinsu, dan kafin yatafi tunanin ya barsu suna wasane amma gashi har barcin su yayi nisa.

*KUTSE*

*PAGE 60*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Nasir*

Ginin sabon gidan da zasu koma tuni ya kankama dan ya kusa kammala shi, ?aimin gama ginin ma bai tasar masa ba sai da yaji yanason mai da Rashida Wakinta, kuma saboda bazai iya komawa wan nan tsohon gidan nata ba yasa aka fara ?arasa sashen da zata zauna tunda an kamala sashen Maryam, daman so yayi kafin Maryam ta haihu ya zama sun koma gidan ta haihu a sabon gida, amma sai gashi wata ?adarar tason dawo da Rashida ta ratso Cikin zuciyar sa, so yake yagama ginin baki Waya sai su koma duka tunda saura kaWan a gama.

Yau sati biyu kenan rabonsa da ganin Rashida sai dai suyi waya, a wan nan wayar Rashida tana ?ara dugun zuma shi da kaWa masa gangin son kasancewa da ita, haka yasa yau yabar duk wani Abinda yakeyi yace mata su haWu dan yanason jin Wumin jikinta, daman ita Abinda takeso kenan, take kuwa ta amince masa tare da kayyade lokacin da zasu haWun.

*Rashida*

Tana kwance jikin nasir yanayin ya mata daWi domin sam batason matsawa daga jikinsa, gashi da dukkan alamun haramar tafiya yakeso yayi, shiyasa ita kuma ta nane masa ta?i sakinsa, daga bayama ta ?ara tsunduma shi cikin ruwa dan so take yaje masa har wuya, sai bayan sun nutsa san nan Rashida fatara shashshe?ar kuka wanda yake cike da makirci tace.

"Ha?i?a ina tsunduma cikin jin nauyinka da kuma kunyar ka a duk lokacin dana tuna Abinda ya wakana a tsakanina daku, tabbas na cika azzaluma wacce ba kowa zaiso ?ara kusantar lamarina ba a karo na biyu, sai ta ri?e hannun Nasir tace " dan Allah ka yafemin ka gafarceni Nasir, na rantse da girman Allah na canza bazan kuma tayar maka da ?ayar baya ba, acen bayan ma tsabar sonka ne da kishinka da kuma rashin wayau ya tsunduma ni a duk wani hali na son zuciya dana tsinci kaina, amma wallahi tallahi na Wau al?awarin bazaka ?ara kamani da wani mummunan aiki makamancin wanda na aikata ba, ta ?arasa tana ?ara sautin kukanta tare da Wora kanta akan kirjinsa tana shasshe?a.

Cikin tausayawa Nasir ya Wago da fuskarta yafara share mata hawayen dake zuba kamar ana tun?uWo mata su yace.

"Ki daina wan nan kukan san nan ki daina damuwa, ha?i?a Allah ma muna masa laifi kuma ya yafe mana idan muka ro?i yafiyar sa, dan haka nace na yafe miki kuma a madadin Maryam na ari bakinta naci mata albasa itama ta yafe miki, dan haka banason kina tado da Abinda ya wuce dan Allah.

?agowa Rashida tayi tare da sakin murmushin jin daWi da kuma nasarar datake hangowa a tafiyar tasu tace

"Nagode sosai da afuwar ka gareni, amma duk da haka ina cikin kiWima da jimamin daWin baki kake min, tunda a ganina da ace ka yafemin tabbas da ka karSi kokena na komawa cikin gidana da kuma ?ara raba kwana tsakanina da ?ar uwata Maryam, ta ?arasa da muryar karaya a kalaman ta tana lan gwaSar dakai.

Fuskarta Nasir ya Wago yana kallon cikin idanuwan ta wanda suka cenza kala saboda kukan munafurcin da takeyi tare da mutsittsike su dan suka bada kala, magana Nasir yayi yace

"Kalleni Rashida. Kallon nasa kuwa tayi tana Wan taSe baki da marairai cewa da kuma ?ifta danuwa, murmushi Nasir yayi yace "me kike so nayi wanda zai tabbatar miki da cewar na yafe miki Rashida? ?an murmusawa tayi cikin kunya tace

"Ranka ya daWe, da za'a taimaka min dai a dawo min gidan a kuma bani kwanana danaji daWi, kuma wan nan shine zai tabbatar min da cewar yafiyar da akayi min taje ma?ura.

Shidai Nasir tsintar kansa yayi da cewar ki shirya wani satin zaki koma sabon gidan danake ginawa a yahaya Gusau.

Da sauri Rashida ta Waga kai tace "Abban Halima, daman kafara ginin filin nan? Kai ya Waga yana murmushi yana cewa "kwarai kuwa harma na gama sashe Waya, sashe Wayan kuma ?arasawa ake yi.

Murmushi kawai Rashida tayi ranta na suya da wan nan maganar gidan ta Nasir, kanta ta russunar tana tunanin ashe da anyi tashin balagar tsintsiye da ace Maryam ta koma wan nan gidan data ciwa buri da yawa a rayuwar ta.

Taya Nasir zai mata haka alhalin dashi da ita ne suka sai filin san nan suka tsara yadda fondation Win zai kasance, duk da bada kuWinta aka siyaba amma ai a lokcin Nasir ne ita, ita kuma itace Nasir dan haka wallahi tayi al?awarin sai Maryam ta WanWana kuWarta a hannunta.

Sosai Nasir ya tayar da hankalin sa akan ?arasa sauran gyare gyaren Sarin Maryam wanda Anan zai saka Rashidan, idan yaso Maryam Win ta koma Wayan wanda yake ginawa Rashida idan an kammala, ko sati Wayan daya furta ba'ayi ba sai gashi gida yayi fess ya fito gwanin sha'awa, a lokacin da Nasir yacewa Rashida zaizo ya Wauketa suje suga gidan sosai ta nuna murnar ta danji ta dungayi kamar ta jawo Nasir ta rungume shi ta nuna masa soyayya ta cikin wayar.

Suna gama wayar kuwa ta zari mayafinta wanda ke kusa da ita ta fice daga gidan ta nufi gidan Amina wanda ke unguwar sharWa pess 2.

Cikin farin ciki Amina ta tareta tana Waga mata gira Alamar daga wajen Nasir take? Kai Rashida ta girgiza tace badaga cen nakeba ?awata.

Ai baki saniba, yanzun nan Nasir ya kirani yake sanar min an gama gyaran inda zan zauna dan haka zaizo ya Waukeni muje nagani, ni kuwa nace bafa zanje ni ka Waiba saina zo mun tafi tare, dan haka yanzu zan masa text na faWa masa ina gidanki yazo ya Waukeni.

Murmushin ya?e Amina wacce take cikin shiga uku tayi dan bata daWe da gama karSar gashi ba a wajen Alhajin nata, yanzu haka duka ilahirin jikinta bala'in ciwo da raWaWi yake mata wanda da Rashida zata kula da za taga shatar bulala a jikin damtsen hannunta duk da mayafin data yafa rufe tabon.

?an jijjiga kai Rashida tayi cikin Wan mamakin ganin ya?en Amina tace

"Amina ya naga duk kin canza ne? Kodai akwai wata damuwa ne? ?aga kai Amina tayi da kyar saboda azabar ciwon da yake mata tace

"Kedai bari ?awata, wallahi banajin daWi yau Win nan, bakiga idanuwa na sun canza sunyi jaba? To wallahi kaina ne yake tsananin ciwo shiyasa kika ganni haka, kuma ina mai baki ha?urin bazan iya fita daga gidan nan yanzu ba saboda jiri da zazzaSin dake neman kaini ?asa, amma kije Win Insha Allah kafin ki koma zanje lokacin na samu warwara.

Cikin tausayi Rashida ke kallon Amina wacce bama ta kula da canjinta ba sai yanzu data faWa, hannun Amina ta ri?e tana kallon cikin idonta wanda hawaye sukacika tab suka fara zuba tace.

"Ayya ?awata, wallahi sam banma kulaba sai yanzu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login