Showing 12001 words to 15000 words out of 175193 words

Chapter 5 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

525

faru a gidan Nasir suna da yawa dan wasu ma bazasu fad'abu saboda haushin su da k'unsar takaicin su, haka zalika a wan nan sati biyun kwata kwata Rashida batabar Maryam ta huta da masifar saka idonta akanta ba, ga tsangwama da gwasalewa wanda har sun fara sauya zuciyar Maryam tana ganin indai ba'ayi wasa ba ta kusa tayi free falo ta fasa kwan da Nasir yake tattalawa da b'oyewa.

Wani Abin takaicin da bak'in ma shine " a wan nan satikan shi kansa Nasir wani hali na banzatar wa da kuma rashin kula yake nunawa Maryam d'in, ko gaisheshi tayi wataran haka zaiyi banza da ita ko kuma ya amsa mata a shagub'e kamar mai ciwon baki.

Haka Maryam taita danne zuciyar ta tanayin hak'uri da kawaici na rashin sukuni da takeyi a cikin gidan, baya ga haka babban takaicin ta rashin kunyar da sadiya ke mata kamar wacce aka zanawa wasu magan ganu marassa kyau a kanta, tasha kama yarinyar tana galla mata harara da murgud'a mata baki a maban banta lokaci, ko a gaban babarta ne takanyi hakan kuma ko d'aya bazata tab'a kwab'ar yarinyar a kan hali marar kyau datake na raina mutane ba.

****

Yau kimanin kwanakina talatin kenan a gidan Nasir ina cikin ba'kin cikin zaman danake a cikin gidan, yanzu takai takawo ma bana ganin Nasir sai zai fita koya dawo shima sai nakasa na tsare dan na nuna masa inafa cikin gidan kuma ina k'ark'ashin inuwar auren sa san nan yake tunawa dani.

Ina zaune akan kujerar falon ina d'an danna wayata kawai naji an zuba min ruwan sanyi a cikin jikina, a furgice na d'aga kaina ina sauke ajiyar zuciya ina kallon sadiya wacce tayi tsilli tsilli da idanuwa tana min kallon raini da wulakanci, kallon yarinyar nakeyi cikin b'acin rai ina wassafa shekarunta da duka duka basu haura tara ko gomaba amma take min wan nan izgilancin, kuma saboda tsabar idanun yarinyar ya ginu da rashin kuya haka ta kafeni tana kallona kamar sa'ar fad'anta.

Cikin zafin nama da tuk'uk'in bak'in cikin da zuciya takeyi na fizgota tare da d'aga hannu na zabga mata wani mari wanda bani dake kusa ba hattaya uwarta Rashida data fito sai da hankalin ta yatashi ganin yarinyar ta kid'ime ta gigice tanata diri a k'asa da k'afafunta dan ko kuka ta gagara yi, sai data luma ta lume san nan ta fizgo kukan dakyar wanda daga ganinsa mak'alewa yayi san nan ta falla da gudu ta nufi gabas tayi arewa san nan ta dawo kudu inda k'ofar falon take ta sab'e ta fita da gudu tana kururuwar ihu da kiran sunan Abba.

Dagani har Rashida a kid'ime muka rufawa sadiya baya muna kiran sunanta, nice nafara k'arasawa gaf da ita shine yabani damar rik'eta ina jijjiga ta ina cewa "sadiya, ke sadiya, wani irin fincika Rashida tayi wa hannuna daga jikin sadiya idanunta jawur kamar gauta tana aikamin wata masifaffiyar harara, a zafafe ta d'aga hannunta takawo fuskata da niyar ta zabga min mari nima nayi sauri ta rik'e hannunta nace.

"Saurara dakata, karki kuskura hannunki yatab'a fuskata da sunan mari Rashida, idan kika sake kika mari fuskata zakiyi na dama da Dana sanin marin da kikayi min, kibar ganin ina kyaleki kina cin karenki babu babbaka a kaina kiyi tunanin tsoronki ne ya saka hakan, tunda na duro gidan nan ban tsinci komai ba sai bak'in ciki da takaicin ki keda wan nan 'yar taki, kullum cikin kunsa min bak'in ciki da takaici kikeyi kuma kina turo wan nan 'yar taki tana min cin kashi kamar ba 'yar Adam ba, tona gaji, nagaji da Abinda kukeyi min a cikin gidan nan.

Cikin bala'i Rashida ta figze hannunta dake rik'e cikin na Maryam tace "wacece ke? Wacece ta kawoki duniya dahar zaki samu zarrar tab'amin yarinya kuma nazo d'aukar mata fansa ki rik'e hannuna kina koramin wurning? Cikin rashin abinyi Rashida ta saka d'an yatsa a cikin bakin ta tanajin kamar ta fashe da kukan bak'in ciki.

"Kaiii, kaiii, kaiiii, Rashida ta fad'a tanajin Maryam tayi k'ololuwar raina mata hankali.

Rasa Abinda zata kuma cewa Maryam yasa ta figi hannun sadiyan wacce keta kuka da shasshek'a suka wuce falon a zafafe dan ji takeyi kamar ta kashe Maryam idan tacigaba da ganinta.

Tana isa d'aki ta zaro wayarta tare da dannawa Nasir kira, bai d'aga ba saboda a dai-dai lokacin suna sallar azahar ne, kiran ta cigaba da jera masa babu k'ak'k'autawa tana safa da marwa tare da girgiza jiki.

Nasir na d'aga kiran Rashida tayi saurin fashewa da kuka tace "baban Halima kana ina? Kayi sauri kazo gida babu lafiya ga Maryam nan ta samu sadiya tanata dukanta da marinta gashi nan duk ta farfasa mata jiki ta canza mata kamanni.

Bata bawa Nasir damar yin magana ba ta kashe wayar dai-dai nan Maryam tashigo jikinta a sab'ule kamar wacce kwai yafashewa a ciki tana kallon Rashida wacce ke safa da marwa tana share hawaye.

Sand'a sand'a maryam ta karaso gaban Rashida harda d'an tsugunna wa tace

"Dan Allah maman Halima kiyi hak'uri, bansan meya hau kaina ba na mari sadiya, kuma ma ruwa ta zubamin mai sanyin gaske a cikin jikina, shiyasa ni kuma nakasa daurewa na mareta amma in Sha Allah hakan bazata sake faruwa ba.

Hannu Rashida ta d'agawa Maryam cikin d'acin rai tace "dakata min, karki kuma cemin komai a wajen nan, ai na kira wanda ya kutso min dake gida kike neman wargazamin iyali, yanzu nan zaizo gidan, zai gayamin alak'ar zaman ki a cikin gidan nan ko kuma wallahi naci uwarki anan gidan, na rantse da girman Allah babu wanda ya isa ya kutso har cikin gidana ya hanamin zaman lafiya da kwanciyar hankali nida yarana, ban ga uwar data haifeshi ba, saboda haka yau sai dai Nasir ya zab'a koni koke a cikin gidan nan, ke ko bai zab'a ba dole ne kibar gidan nan a yau d'in nan tunda dai ba gidan ubanki bane.

Nasir

A gigice ya shigo gidan dan ko motarsa a waje yabarta ya b'alle murfin motar ya shigo, idanuwa yake wurgawa domin yaga sadiyar da akace an lak'adawa dukan kawo wuk'a, a zaune ya ganta akan kujera tana shan yoghurt tana sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali .

Kallon sa ya mayar kan Rashida da Maryam dake cen zaune tayi ta gumi tana rarraba idanuwa, gaban Rashida ya nufa yace

"Me sadiyan tayiwa Maryam d'in harta daketa?

A zafafe Rashida tatashi tace "au wai tambaya ma kakeyi? Kaga yarinyar duk ta fita hayyacin ta san nan ka zauna tambayar Abinda tayi aka daketa maimakon ka d'auki mataki?

Kansa ya d'auke gefe san nan yadawo da kallonsa kan Rashida yace.

Amma dai sanin kanki ne ni bana shari'a bisa son zuciya, kuma kinsan ko tsakanin halima da sadiya bana shari'a batare danaji daga bakin kowa a cikin suba, balle Maryam wacce takeda hankali da tunani nasan bazatayi Abu bisa son zuciya ba.

Wani irin tuk'uk'in bak'in ciki ne ke zarya tsakanin k'irjin Rashida da zuciyar ta, kallon rashin mutunci takeyi wa Maryam tanajin kamar ta shak'o shegiya ta kashe ko zata huta da Abinda takeji .

A zafafe takewa Nasir magana tana cewa "kasan dai banda darajar ka da mutuncin ka babu yadda za'ayi nabar yarinyar nan ta zauna min a cikin gidan nan, kuma kasan dai niba a zuwar min gida a tare batare dana bawa mutum dama ba, amma haka kawai ka kutso min da wan nan yarinyar cikin gidana gashi har tana neman ta wargaza min gida ta rushemin ginin dana jima inayiwa ahalina, to wallahi baku isa ba daga kai har ita, bawai kana tutiya k'anwar kaba Allah yasa kashin awaki kuke wallahi sai tabar min gida.

Tun kafin Nasir yace wani Abin tuni Rashida tashige d'akin Maryam tafara watso mata da kayanta a haukace tana cewa

"Wallahi sai tabar gidan nan, Billahillazi bazata zauna ba, idan kuwa ta zauna wallahi sai dai ni bar gidan Nasir.

Watsowa Maryam kayan taitayi a jikinta tana kai mata duka.

A fusace Maryam tatashi tace "

"Bazan bar gidan nan ba Rashida, na shigo gidan nan ne bada niyar tafiya ba, nashigo ne kamar yadda kika shigo da sunan matar Nasir.

Da sauri Nasir ya isa gaban Maryam tare da toshe mata baki yana zazzare idanu, da sauri Maryam ta zame hannunsa daga bakinta tace

"Kabarni na fad'a mata, nagaji Nasir, nagaji, babu yadda za'ayi nida gidan mijina a mayar dani banza shara bola, taya zan cigaba da zaman b'oyewa matar ka nima matar kace saboda kana tsoronta ko gudun fushinta? Ai bahaka kukayi danawa iyayen ba saboda haka

"Ni matar Nasir ce Rashida, gwara ko wane b'oye, b'oye da k'un biya k'unbiya ya dakata haka, yana da kyau a fuskanci rayuwar gaskiya da gaskiya kowa yasan matsayin sa.

Rashida

Jakar hannunta tayar ta zubawa Nasir ido ko k'iftawa batayi, wani ruwa ruwa ne yake neman kwararo mata a kuncin ta tai saurin mayar dashi a kid'ime muryarta na rawa tare da in..ina tace.

Ai...ai...ai nasan k'arya takeyi ko? Nasan dan ta kashemin zuciya ne kuma ta wargaza min gida shiyasa take fad'ar haka ko? Ai nasan k'anwar kace.

Shiru Nasir yayi dan bashida bakin magana gashi Rashida ta tsattsare shi da ido tanason gano gaskiyar sa, bai san mataki na gaba dazai d'auka ba tunda dai Maryam ta ruga ta caka masa wuk'a a ciki, shi kansa yasan a wan nan lokacin Maryam ta sako masa kura mai wuyar sarrafuwa.

Rasa yadda zaiyi da kallon da Rashida take masa yayi sai kawai ya tsinci kansa da d'aga kai sama Alamar "Eh haka ne, dan cigaba da k'aryar ko b'oye b'oyen bazai hai far masa da d'a mai ido ba tunda Maryam ta jik'a masa aiki.

Rashida

Wani irin kallon tashin hankali take bin Nasir dashi dan ji takeyi kamar mafarki take shiyasa take wurwurga idanunta ko ina a cikin jikinsa har tana lallatsa hannayen sa, ji da ganin a zahiri ne ba mafarki take ba yasa ta daddage ta zabgaga wani uban ihun dayasa dodon kunnen su kusan mutuwa baki d'aya.

Dan kwalinta ta fuzge daga kanta tare dacin d'ammara, tana fuffuzga tare da daddagewa ta shak'o Nasir tafara kartar sa da farcenta cikin fitar hayyaci tana cewa

"Ki...ki... kishiya kamin Nasir batare da sanina ba? San nan ka kawota gidana Nasir kuka cigaba da cin amanata da yaudarata da raina min hankali?

Duk yadda Nasir yaso ya b'an b'are hannun Rashida daga wuyansa kasawa yayi saboda yadda ta ruk'un k'umeshi tana cisgar fatar wuyan nasa tana zare idanu kamar ta samu katifa.

Sai da kanta ta sakeshi ta juya tare da k'ure Maryam da kallo wacce jikinta ke rawa da ganin haukar da Rashida keyi.

Wani irin ihu Rashidan ta kuma kurmawa a haukace tayi kan Maryam zata dan k'eta Nasir yayi saurin rik'eta dan yaga gaba d'aya tafita daga hayyacin ta.

Tun kan yayi mata wata magana ta d'aga hannu tare da zabga masa mari a haukace takai masa cizo ya kwafce yana daka mata tsawa da cewa.

Rashida, ki nutsu ki dawo hayyacin ki, ki saurareni nayi miki bayani dan Allah.

Girgiza kai tayi tana kallon Nasir tana kallon Maryam sai kuma ta d'aga dan yatsa tana nuna Maryam tace "ki shiyata, kishiya ta Nasir? Sai tatafi luuuu zata fad'i Nasir yayi saurin tarota dan tuni ta sume a wajen.

Da gudu itama Maryam tatawo wajen da Rashida ke zube tana kuka wiwi tana cewa

"Kagani ko? Ka gani ko Nasir? Shiyasa tun farko nace karka b'oye wan nan maganar, wan nan maganar ba'a bar a b'oye bace saboda duk nisan b'oyo watarana zata bayyana.

Nasir

Jajaye kuma rinannun idanuwan sa ya watsawa Maryam wanda sai data tsorata da irin kallon dayake mata, da sauri ta d'an matsa baya dan ta tsorata sosai da ganin yanayin sa.

Cikin bala'i da karaji yake wa Maryam magana yana cewa

"tashi daga nan kibani waje, kuma wallahi tallahi ki sani idan wani Abin ya samu matata wallahi bazan yafe miki ba Maryam, wallahi sai na shayar dake gubar mamakin d'an yan kan da kika nuna min, banda baki da hankali kin nunamin ban isa ba har in baki umarni ki k'i bi ki gudanar da abinda kika dama.

Wallahi maryam..... Kasa k'arasa maganar yayi saboda wani zullo da zuciyar sa tayi na ganin Jini na sulalwo daga hanci da bakin Rashida.

PLEASE COMMENTS AND SHARE.
KUTSE

PAGE 8

? ? Na

? ?? Mom Haneef

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Asibiti a cikin d'akin gaggawa

Likitoci sun shiga tako ina suna kai kawo domin su samu su tsayar da jinin da Rashida ke zubarwa da kuma samun nasarar farfad'o warta.

Maryam

Tana tsaye a gefe da hawaye fal cikin idanunta zuciyar ta na cike fal da nauyin laifi da Kuma juyayin halin da Rashidan zata shiga a dalilin ta.

Nasir

Yana tsaye ya jingina da bango ya zuba tagumi hannu bibbiyu tare da zubawa k'asa idanu yana fizgar numfashi dan ji yakeyi kamar an shak'eshi da kunya.

Suna tsaye a haka sai ga likita yafito fuskar nan tasa babu yabo babu fallasa, da sauri Nasir ya d'ago ya kalli likita dan ji yake kamar bazai bashi labari mai dad'i ba..

Kallon Nasir likita yayi da d'an sanyin murya yace "kaine mijinta ko?

D'aga kai Nasir yayi da sauri kamar tsohon k'adan gare yace "nine.

Sai da likitan ya kalleshi sosai san nan yayi gaba da sassarfa yace "ka biyoni office.

Harda gudu gudu Nasir ya had'a saboda yadda yake saurin bin likitan kamar Rashida na biye a bayansa.

Guri Nasir yasamu ya zauna kamar yadda likitan ya umarce shi da yayi, yana zama kuma likitan ya turo masa takardun file d'in Rashida yace.

"Wan nan shine sakamakon gwaje gwajen rashin lafiyar matarka, kuma Alhamdulillahi munyi Nasarar samun tsaida jinin dake mata zuba, amma farfad'owar ta sai nan da 'yan awanni idan Allah ya nufa, saboda haka bazamu gane jinin dake zuba ya tab'a kwakwalwar ta ko bai tab'aba har sai ta farfad'o muga yanayin data farfad'o dashi.

Nasir

Kurawa likitan ido yayi kamar ya samu TV yanajin zuciyar sa na cigaba da tsalle akan samun Sakamakon da zaiyi na Rashida? nan da 'yan a wanni mai kyau ko akasin sa, bai san cewar likitan yatashi har ya nufi jikin k'ofar office d'in zai fita ba har sai da likitan yace

"Amm...nace shikkenan ko? Sai mu jirayi farkowar tata.

Da sauri Nasir ya mike yana mirgina kai tare da jin wani zazzafan hawayen tausayin Rashida ya tsirga masa, har yazo zai fita sai likitan yadafa kafad'ar sa yace " karka kajiya dabawa kanka kwarin gwiwa, domin da kwarin gwiwar kaine Had'i da addu'a'oi zai saka Rashida ta samu tsira da yardar Allah.

Kai kawai Nasir ya iya d'agawa san nan yaja kafafunsa wanda sukayi masa nauyi suke neman kadashi yafice daga office d'in yana jin zafin Maryam na kuma k'aruwa a zuciyar sa.

Nasir na fita sukaci karo da Maryam dan sam takasa yadda da zaman shirun da Nasir da likita sukayi a wan nan office, shiyasa ta lallab'a tare dajan k'afa ta isa bakin office d'in tana jiran taga lokacin fitowar su, ai kuwa suna fitowa Maryam tayo kan Nasir da sauri tana share hawaye tace.

"Lafiya baban Halima? Me yake faruwa?

Nasir

Kallon bak'in ciki yabi Maryam dashi yanajin zafinta har cen cikin ransa, shiyasa yaji bakin sa ya kulle bazai iya yimata magana ba dan idan yace zai mata magana to tabbas Abinda zai fita daga cikin bakinsa bamai dad'i bane, hakan yasa yayi saurin d'aga mata hannu tunkan tak'araso gabansa.

Maryam

Idanuwa fal hawaye tabi bayan Nasir da kallo wanda ya dakatar da ita daga zuwa gareshi kuma batare dayace mata kanzil ba ya wuceta a wajen yatafi yabawa banza ajiyar ta, ganin tsayuwar bazai kai mataba sai kawai tabi bayansa domin komawa wajen dasu ke zaune d'azu suna jimami.

Koda ta isa kuma tana zama ana gangarowa da gadon Rashida zuwa wani d'aki daga cen gefen data zauna za'a shigar da ita.

Sai da tabari nurses suka fito san nan ta tashi da niyar shiga d'akin taga Nasir ya rigata.

Da sauri ta k'araso dan ganin zai rufe k'ofar ta saka hannu ta rik'e tana masa magiya da hawayen idanunta akan yabari tashiga

Nasir

Runtse idanunsa yayi wanda suka kaWa sukayi jawur kamar gauta, yayi wajen second biyu a haka san nan ya bud'e idanun nasa ya zubawa Maryam su wanda ganin su yasa sai da 'yan hanjin ta suka kaWa sosai har ta tsinci kanta da d'an matsawa baya dan kar yakawo mata duka.

Nasir

Duk da yaga ta matsa amma hakan bai hanashi daga yatsan sa manuni yanuna ta dashi ba tare da buga mata wurning d'in ta sake ta shigo wallahi sai tatafi gidan su daga nan zaman su ya kare har bada.

Duk da haka sai yagashi tana k'ok'arin durkushe wa a wajen dan ta nemi gafarar sa yabarta taga Rashidan dan jin ciwon ta takeyi kamar jininta dake zagayawa a gangar jikinta.

Ganin zata b'ata masa lokaci da kuma b'ata masa rai yasa yayi saurin fitowa daga d'akin ya rufe tare da nufo Maryam a zafafe kamar tsohon kumurci, da sauri Maryam ta matsa baya tare da durk'u shewa? baki d'aya tayi k'asa da kanta tana kuka tare da d'aga hannu ta mik'a masa Alamar neman yafiyar sa bisa laifin datai masa.

Akace duk wanda yayi nisa bayajin kira.

Haka Nasir ya rufe idanun sa ya d'aga hannu tare da kama damtsen Maryam yad'aga ta tsaye yafara janta suna tafiya da sauri har sai da suka iso wajen reception san nan ya wullata waje tare da sakin hannunta cikin d'aga murya yace.

"Bazance na tsaneki ba Maryam, haka bazance banason ganinki ba kodan martaba da mutunci irin na iyayen ki a gareni, amma daga ranar da kika fallasa sirrin danake tattalawa saboda farin cikin matata da kwanciyar hankalinta yasa nafara miki kallo abaibai wanda wan nan kallon naki shi yake bud'e mini babin littafin ki guda a cikin zuciya ta.

Kiyi nesa dani Maryam, ki kumayi nesa da Rashida, ban saniba ko kalaman data fad'a dai-dai ne nake musu kallon abaibai a wajena.

"Mema tace? Yad'aga kai yana tunanin kalmar Rashida saboda tashin hankalin da yake ciki ya girmi ya rik'e abubuwa dayawa akansa.

K'ara d'aga hannu yayi ya saka akai yana cewa "mema tace? Sai ya juyawa ya kuma juyawa domin tunowa.

"Maryam

Cikin shasshekar kukan daya ci k'arfin ta tace "kutse.

"Yes" kutse, Nasir ya maimaita yana wurgawa maryam mugun kallo, Rashida tasha fad'a batasan kutse, batason wani Abin yakutso mata cikin iyalin ta saboda gudun tashin hankalin da wargaje war tunanin ta, ina ganin shirme ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login