Showing 141001 words to 144000 words out of 175193 words

Chapter 48 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

543

Allah yasawa?e ya kuma baki Lafiya kinji, bara natafi muje danga kiransa na gani Insha Allah idan nadawo zan biyo na kuma dubaki, da sauri Amina ta Waga kai tana tashi da sauri cikin gudu gudu ta toshe baki tayi cikin banWaki tare da turo ?ofar irin aman nan ne ya taso mata.

Murmushi Rashida tayi a ranta tana ayyanawa anya kuwa Amina ba ciki ta samuba shine tafara galabaita tun yanzu?

Ita kuwa Amina a sanda Rashida ke mata magana dauriya kawai takeyi domin wani irin ?ai?ayin bala'i ne yafara sassoka mata jiki dan dukan da taci Wazu Dole ma jikinta yayi mata ?ai?ayi, so kawai take Rashida tatafi tafara sosa jikinta da bayanta dake mata raWaWi kamar an shafa mata karara, ganin Rashida bata da niyar tafiya kuma masifar ?ai?ayin da jikinta ke mata ya ta'azarra idan har bata sosaba zata iyayin hauka, shiyasa tatshi da gudu tayi banWaki tare da rufe baki dan Rashida ta zata amai zatayi

Tana shiga banWakin kuwa tayi saurin wullar da mayafin jikinta ta jingina jikin ta tafara susa kamar mahaukaciya tana kuka wiwi, har tsalle takeyi da zabura idan wani wajen ya soka mata, ganin ta kasa sosa bayan ta yadda ya kamata sai kawai ta kwaSe riga a hanzarce ta jin gina jikinta da bango kamar a kuya ta dunga gogawa har sai data fara jin fatarta tana yankewa saboda bangon mai ?urzunu ?irzunu ne san nan ta ha?ura, kuka sosai Amina ta dungayi a banWakin nan tana tunano rashin imanin data saka Alhaji ya dungawa hajiya a baya gashi yanzu abin ya dawo kanta.

Babu irin asirin da batayi akan Alhaji ya saki hajiya ba amma ya kasa sakinta, dan haka tasa boka mai tsidau ya juyar da hankalin sa ya manta da hajiyan da yaranta ya juya musu baya, duk hakan bai isheta ba sai data saka aka wanke masa hannu da ruwan dukan dorunar aljannu dan Alhaji ya dunga zane Hajiya daji mata ciwo saboda ta gaji dan kanta ta gudu, amma duk da hakan bata samuba haka Hajiya ta daure taci azaba amma takafe ta nace ta?i barin gidan, hawaye Amina ta share a lokacin data tuno maganar da hajiya tayi mata wataran tace

"Shi sharri Wan aike ne Amina, duk inda kika aikashi zai dawo gareki, san nan hausawa suna cewa idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere wata ?ila kaine zaka faWa, san nan duk shukar da kikayi wataran da hannunki zaki girbeta indai muna raye.

Kai Amina ta girgiza tana na shiga uku na lalace, Allah ka dubani, in har Abinda nayiwa hajiya za'ayi min wallahi mutuwa zanyi, bazan iya jurewa ba, wayyo Allahna.

Bugun ?ofar da ake mata da ?arfi ne yasa ta zabura da gudu ta sakawa banWakin mukulli domin tasan idan Alhaji ne ya dawo gareta murWe mata wuya zaiyi ta mutu, kai ta jingina a jikin bango tana sosa wuyanta tana tuno watannin baya da Rashida ta kirata a waya akan ta taimaka mata idan ba haka ba zata kashe kanta.

Cikin tashin hankali Amina tatashi tafice daga gidan duk da kashedin da Alhaji yayi mata na ko ?ofar Wakinta ta kuma fitowa bada izinin sa ba sai ya bata mamaki, amma haka ta share ta nufi gidan Rashida dan tabata taimakon da take bu?ata, a wan nan ranar kuwa taga bala'i ganin idonta, dan dukan mutuwa Alhaji yayi mata san nan ya wullota daga bene, inda Allah ya taimake ta data tashi faWowa akan mota ta faWo badan haka ba da tasan labarin wata ake ba dai ita ba, amma duk da haka ta daku dan a take hannunta ya Salle wanda sanadiyyar haka yanzu bata iya aiki da hannun sai dai da guda Waya, san nan tana a karyen bai tausaya mata ba ya siyo mari ya kafa mata a ?afa dan karta kuma fita kamar wata dabba.

Bazata manta ba Hajiya har kukan ganninta a haka tayi, kuma har tsugunnawa tayi ta dung bawa Alhaji ha?uri akan ya daina mata azabar da yake mata karya kasheta idan kuma son ganin tane baya yi kawai ya saketa ta tafi gidan su kar ha??in ranta ya rataya a wuyansa, a lokacin murmushi kawai yayi yacewa hajiya ta barshi yasan Abinda yake yi.

Haka yauma batasan hawa ba tasan sauka ba kawai sai jitayi an wullota daga kan gadon da take kwance san nan aka fara taf karta babuji babu gani.

*Rashida*

Cikin farin ciki take kallon ?aton part Win da take tsaye a cikin sa wai nata ne, part Win ya haWu iya haWuwa wanda faWar sa a baki ma Sata baki ne, dan haka kawai tsintar kanta tayi da rungume shi tana zuba masa godiya.

Daga nan Nasir ya biya da Rashida kamfanin SDK Furniture dake gandun Albasa kusa da gidan Bashir tofa, haWaWWen wajene da suke sai da kayan furnitures kala kala ?an yayi wanda yanzu duniya take damawa dasu, ai kuwa da isarsu Rashida ta kar kace ta kwashi kayan ?an gayu haWaWWu irin na matan da suka isa, tun a wan nan ranar suka kai kayan aka haWa komai da niyar jibi zata tare a cikin gidan.

*KUTSE*

*PAGE 61*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Ya zulai*

Cikin fushi tatashi har ?irjinta na Wagawa sama da ?asa saboda yadda numfashin ta ke fuzgar ba?in cikin maganar da Nasir yazo mata dashi, kasa magana tayi saboda ji take idan ta buWe baki zatayi magana bazatayi mai daWi ba, shiyasa sai kawai ta koma ta jingina da bango ta dafe ?irji tana nanata kalmar innalillahi wa'inna ilaihirraji'una.

Da fata Jamila tayi cikin tarin takaici itama tace

"Ki zauna ya zulai, kiyi ha?uri ki sanyawa zuciyar ki salama dan Allah, saboda kinga kinada hawan jini sosai karki jawo ya kuma hayewa don Allah.

Dakyar ya zulai ta zauna tana kallon Nasir wanda yayi ?asa dakai saboda shi bai san Abinda zaiyi ba, shifa kawai yazo ne yafaWa musu Rashida ta koma matsayin ta saboda duk duniya bashi da waWanda suka fisu, kuma yana ganin sunada ha??i a kansa shiyasa ya faWa musu badan komai ba, amma da dukkan alama so sukeyi su Sata ransa ya koma kano da fushinsu.

Cikin danne zuciya da kuma son tsamo nasir daga halakar da take tunanin Rashida zata kuma tsunduma shi tace

"Haba ya Nasir, kai Yanzu ko wanine yazo maka da shawarar ka cigaba da zama da Rashida basai kayi Shari'a dashi ba, gaskiya mudai bamu yadda da dawo da Rashida ba, nifa jinake ma ka daWe da sakinta tun wan nan lokacin data jefa rayukanku a cikin masifa.

?ago kai Nasir yayi ya kalli Jamila wacce ta haWe rai ta ta?ar?are tana magana, shiru tayi dan taga kallon da yayi mata bana mutunci bane, dan haka sai ta kalli ya zulai wacce fuskar ta tayi jawur saboda Sacin rai tace

"Wai ya zulai bazaki ce komai ba? Naji kinyi shiru.

A hasale ya zulai ta kalli Nasir tace

"Ai abinne na jishi wani ban barakwai wai namiji da suna hajara, banda ka tsabar raina mana hankali ko kunyar mu bakaji ba zaka Wauko wan nan fankon kannaka wanda babu komai a cikinsa sai tarin gida humanci kazo mana nan da maganar Rashida, to bari kaji, kasan Allah ban yarda ka ?ara alaka da Rashida ba, wallahi kuwa idan ba haka ba zanyi fushi dakai mai tsanani Nasir, ba nice uwarka ba amma inada power uwarka tunda nice babar yayar ka san nan uwar taka ta rasu, kuma tabbas nasan da inna tana nan wallahi bazata barka kaci gaba da zama da annoba ba, dan haka nima bazan yarda ba.

Zuciyar Nasir ba ?aramin Saci tayi ba da mugayen magan ganun da ya zulai ta faWa akan Rashida ba, wai harda ce mata annoba, taSSijan, dan haka sai ya buWe baki yace

"Gaskiya ya zulai bazan taSa iya rabuwa da Rashida ba, haba dan Allah, meyasa zaku tsani Rashida alhalin tanason Wan uwanku, gaskiya banji daWi ba, kuma fa karku manta Rashidan nan uwar manyan ?a?anace dan haka dan Allah karku ?ara ce mata annoba, dan wallahi banajin daWi, kuma naga ai bansaki Rashida ba, to akan me zaku hanani sauke nauyin ta a kaina?

Ya zulai bata taSa zagi ba tunda take bare a shariya, badan bata iyaba sai don haka ba Wabi'ar ta bane, amma tabbas yau idan batayi zagin nan ba tanajin zuciyar ta bugawa zatayi ta fashe, dan haka da sauri ta mi?e ta isa gaban Nasir tana haki tace.

"To wallahi Nasir sai ka saki Rashida dan kutumar ubanka, Wan iska marar tunani, anya kuwa akwai fankon kwakwalwar a cikin kanka? To wallahi idan baka rabu da Rashida ba wallahi babu mu babu kai Nasir, kuma wallahi bamu kaWai ba hattaya Maryam bazata cigaba da zama dakai ba, shashasha marar tunani.

Ya zulai tana gama wan nan banbamin faWan sai kawai taja hannun Jamila sukayi Waki tare da banko ?ofa suka bar Nasir Anan, kan Nasir kuma ?ullewa yayi da wan nan lamarin, banda masifa taya yanason raya sunna amma a dunga dizgashi da wula?anta shi irin haka? Matar sace fa, kuma ya za'ayi ace lallai sai ya saketa, shifa wallahi bazai iya sakinta ba komai za'ayi, jiki dai a sanyaye haka Nasir ya fita daga gidan ya zulai ya hau motarsa yabar garin rogo.

Yana isa garin kano kuwa bai zame ko ina ba sai wajen amininsa kuma Wan uwansa Ramadan, kamar abin arzu?i ne ya kawo shi suka gaisa cikin mutunci tare da taSa zancen kasuwanci, sai da suka Wan nutsa san nan Nasir yace

A bokina daman fa nazo ne akan Maganar Rashida, Zaro ido Ramadan yayi yace ikon Allah, ashe akwai lokacin da zaka nemi rabuwa da ita, to saki nawa kayi mata? Girgiza kai Nasir yayi cikin takaici yace, nifa ba haka nake nufi ba Ramadan, wai meyasa da nayi zancen Rashida kowa burinsa yaji na saketa?

KafaWa Ramadan ya Wan Waga yana kallonsa yace "to kana da zaSin daya wuce haka ne? Ai sakinta shine mafutar ka tunda bata da alkairi a cikin rayuwar ka.

Kujerar da yake kai Nasir yaWan janye ya tashi yana kallon Ramadan yace

"Magana Waya nazo na gaya maka shine

"zan komawa Rashida, bazan iya rabuwa da ita ba, dan haka nazo gaya maka ne dan karkaji daga baya kace ban kyauta maka ba.

Wani irin shocking kalaman Nasir sukayi wa Ramadan har baisan sanda ya matsa baya ba, idanun Nasir babu wasa a ciki kuma babu fargabar komai yake furta masa wan nan maganar, da sauri Ramadan yatashi daga tashi kujerar shima yana watsawa Nasir mugun kallo kafin daga bisani ya tsinkeshi da mari.

A makankace Nasir ke kallon Ramadan bayan yadafe kucinsa yace "nika mara Ramadan?

Za gayowa Ramadan yayi kusa dashi yana Wan duba jikin Nasir yace " bana mareka bane saboda son raina, na mareka ne saboda na tabbatar da cewar a cikin hankalin ka kake wan nan maganar ko kuwa tuwo ne akan naka, kuma ba shakka naga Alamar a hayyacin kane kake wan nan maganar, dan haka wallahi tallahi Nasir muddin kayi kuskuren ?ara tunkarar Rashida a karo na babu adadi billahillazi sai ta baka mamakin da bata taSa baka irinshi ba.

Hannu Nasir ya Wagawa Ramadan yace

"Dakata min Ramadan, daman batun yau ba na fahimci babu ?auna tsakanin ka da Rashida, to kasani, wallahi duk wanda bazai ?aunaci Rashida ba to wallahi nima bazan ?aunace shiba, dan haka haka kowa ya ri?e addu'ar sa da fatan Alkairin sa a garemu, dan nasan idan Allah ya saka mana Alkairi to babu wanda ya isa ya kwace hakan.

Kallo Ramadan yabi bayan Nasir dashi bayan Nasir Win yabar shagon shi, zama yayi daSas akan kujerar dake bayansa yana furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, Rashida again? Tabbas ka shiga haula abokina, zan tayaka da addu'ar da zaka iya kwatar kanka a wajen wan nan SheWaniyar matar.

*****

Yau ne Rashida zata koma sabon gidanta, dan haka shiri takeyi sosai kamar wata sabuwar amarya, dan daman ta daWe tana shirya jikinta da magungunan sabon bokan daya bata, ita kanta tana jin ta tsumi ta Winku kuma ta dafu kuma a wan nan karan bazataje gidan Nasir da wasa ba, tayi al?awarin fatali da dukkan wanda zai zamar mata damuwa a zaman ta da Nasir, dan yanzu Nasir shi kaWai ne fitilarta shine haskenta, san nan shine danginta, daWin da Wawa tayi al?awarin Maryam bata isa ta shigo wan nan sabon gidan ba, sai dai ta zauna a tsohon muddin Nasir bai saki shegiya wahalalliya ba.

Babu Abinda zata koma dashi gidan nan sai kayan jikinta, domin hattaya tsofaffin kayanta duk tayi gwanjonsu harda sababbin ciki ta Winka wasu sababbin, dan haka sai ta Waga katifar kan gadonta tare da jingina ta a jikin bango ta yaye likafar gadon, murmushi tayi ganin ?o?on da tafi wata da ajiyeshi yana nan a inda yake ko kusa ban gusa ba san nan bataga alamar wani abu ya raSeshi ba, hannunta na hagu ta saka ta Wauki ?o?on take taga murfin jikinsa ya buWe wani haya?i ya fito daga ciki, kewaye fuskarta haya?in yafarayi san nan daga bisani sai ya dun ?ule waje Waya ya faWa cikin ?o?an, batayi wani mamaki ba dan tasan me hakan yake nufi sai kawai ta zura ?o?an a cikin jakar hannunta ta fita tanawa gidan nata kallon ?arshe.

A sabuwar motar da tasaka Nasir yasai mata ta zura ledar ta shiga motar ta nufi sabon gidan zuciyar ta fal farin ciki, amma kuma awani Sarin na ranta tana tunanin maman mu da kuma dukiyar ta, so take ta nutsa a gidan Nasir san nan ta waiwayo maman mu, dan wallahi tayi rantsuwar ko maman mu zata mutu sai ta bata kuWin ta.

*Nasir*

Ya rasa da wace kalma zai buWi baki ya sanarwa da Maryam halin da ake ciki na komawar Rashida sabon gidan sa, shi kansa yasan bai yiwa Maryam adalci akan Abinda yayi mata ba, binta da kallo yayi a sanda ta shiga kichen domin kawo masa abincinsa yana tunanin farin cikin da tayi a sanda sukaje wajen filin.

Harda ita ka tattauna damai ginin gidan kafin yafitar da fondation Win, a waya ya nuna mata kala-kala da tsarikan gidajen da suke ginawa, a take ta zaSi wani tsarin part da yayi bala'in tafiya da ita tace shine za'a gina mata, kuma komai da Nasir ya saka a cikin part Win na Maryam ne domin itace ta zaSesu da hannunta.

Ajiyar zuciya yayi yana tunanin anya yayi mata adalci kuwa? Sai da tagama saka rai da wan nan wajen san nan ya Wauka ya dam?awa Rashida wacce batasan komai akan ginin ba.

Yana wan nan zancen zucin ne Maryam tatawo da kayan abinci a hannun ta tana sakar masa murmushi shima ya mayar mata da murmushin wanda bai kai zuciba.

Ya kasa koda kwakkwaran loma biyu ta abincin, gashi Abinda yake matukar so ta dafa wato burabusko da miyar agushi wacce taji tantakwashi, tausayin Maryam yakeji domin baisan a yadda zata karSi zancen nasaba a lokacin da yake sanar da ita, a gefe guda kuma yana tunanin Rashida wacce zumuWin ganinta dason kasancewa da ita yake fusgar zuciyar sa, baya yayi da kansa tare da rufe idonsa yana tunanin yadda zai magance wan nan matsalar shi kaWai batare da wani ya shigo ciki ba.

*Maryam*

Tun shigowar sa ta gane akwai Matsalar dake damunsa, kuma batason matsa masa da tambayoyi tunda bai sanar da ita ba, shiyasa tayi shiru itama tana Wan murmusawa duk dan taWan Webe masa kewa, amma ganin ya?i bata hankalin sama ya kula da ita kawai sai ta share tatashi ta shiga sabgar ta da kula da yaranta.

*Nasir*

Furgit ya mi?e daga Wan barcin daya saceshi a wajen yana kallon agogo, goma da kwata yafaWa a ransa yana saurin Waukar hularsa ya saka, kallonsa Maryam tayi wacce ke karatun ?ur'ani a cikin zuciyar ta tace

"Lafiya dai? Kai Nasir ya Waga yanajin yaWan masa nauyi yace lafiya ?alau, bara naje na dawo, ya juya ya fita har yanajin ?afarsa tana harWewa saboda sauri, kai Maryam ta girgiza a ranta tana masa addu'ar duk Abinda ke damunsa Allah ya warware masa.

Koda nasir yafita kasa Waukar motarsa yayi dan jiyake jikinsa ya masa nauyi bazai iya tu?i ba, dan haka sai kawai ya ?arasa bakin titi yatari napep ya haye tare da faWa masa inda zai kaishi.

Ita kuwa Rashida ta luma ta lume da Sacin ran rashin ganin Nasir a cikin gidan, tasan yanacen a wajen waccen makirar yarinyar ya manta da wanzuwar ta a cikin gidan, dan haka sai tatshi tana safa da marwa tanajin kamar ta fice taje gidan ta Waukoshi, tana tsaka da wan nan tunani da ba?in cikin taji buWe ?ofar part Win nata Alamar an shigo, da sauri ta falfala da gudu ta shige Waki tare da feshe ko ina na ilahirin jikinta da hatsabibin turaren da boka yabata, murmushi tayi tana tunanin boka yace mata muddin Nasir ya sha?i turaren nan bazai ?ara sha'awar kasancewa da wata macen ba har abada idan ba itaba.

Rashida na fitowa falo sukaci karo da Nasir, tana kallon sanda ya lumshe idanuwa yana ?ara zu?ar ?amshinta da hancinsa yana ?ara jan numfashi, murmushi tayi ta ?arasa gabansa tana mai rungumar sa tana masa sannu da zuwa, shima rungume ta yayi a jikinsa yanajin sonta kamar ya tsaga ?irjinsa ya zurata a ciki.

Bayan sun zauna suna nane da juna Rashida ta kalleshi tace "ban ganka da kazar amarci naba huby? Murmushi Nasir yayi yana mai son tuno Abinda zaice mata amma gaba Waya kwakwalwar sa ta toshe ya kasa tunanin komai, dan haka sai kawai ya kama kafaWarta tare da tashinta tsaye yace mata suje su siyo, da kant ta tu?asu suka fita cikin farin ciki suna hira har suka dawo.

Tabbas Rashida ta samu Abinda takeso domin kuwa ta gani a wajen Nasir, daman boka yace mata idan ya kusanceta zaiji kamar bai taSa kusantar wata ?a mace ba, dan sabuwa dal zata dawo masa kamar yarinya ?ar shekara sha biyar, hakan kuwa shine yafaru domin taga rikita da gigitar da bata taSa ganiba a dangane da Nasir, shiyasa koda taga ya sharSe yana barci bata tasheshi ba saboda tasan yaje ?ololuwar da yake bu?atar hutu, dan haka sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login