Showing 54001 words to 57000 words out of 175193 words

Chapter 19 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

550

gida kiWan runtsa saboda zaman asibiti akwai gajiya.

Murmushi Rashida tayi tace "babu komai ai, duk Waya ne, Anjima zan tafi in dawo Insha Allah.

******

Sai da Maryam tayi kwana biyar dindi a asibiti ana bata kulawa, tasha ruwa tasha allurai kuma tasha magun guna, kuma tunda Rashida take tafiya ta dawo bata taSa tafiya tabar Nasir a wajen Maryam ba, haka kullum da safe tare suke zuwa kuma sutafi da daddare domin koda Rashida tace zata zauna ta dunga kwana da Maryam ?in yarda Nasir yayi, saboda samira ta kashe wan nan rigimar yasa tace ita zata dunga kwana, da wan nan maganar ta samira takashe maganar.

Haka tunda Maryam ta farfaWo taga irin rawar jikin da Rashida takeyi da ita ta kuma tsorata, a ranta take cewa lallai matar nan bata tsoron Allah wallahi, matar da tayi niyar kasheni itace take wannan lallaSanin, samira na lura da Maryam kwata kwata ta?i sakewa da Rashida duk da abin Alkairin da take mata, haka ta lura duk irin abincin da Rashida zata kawo Maryam bata taSa gigin WanWanawa ba balle takai ga cinsa sai da ayi mata takeaway a cikin asibitin.

Yau ma hakace tafaru, faten dankalin turawa Rashida ta dafa yasha ganye gwanin ban sha'awa, samira tasan sarai Maryam nason wan nan cimar, amma sam fafur Maryam ta?i koda WanWanawa bare taci kuma gashi duk dan ita Rashidan ta kawo.

Zaune Rashidan take da filet a hannunta da cokali a ciki, kallon Maryam take tana hawaye tana cewa

"Bansan me zan miki na burgeki ba Maryam, nasan duk Abinda nai miki ban biyaki ba da irin Wawainiyar da kikayi dani nima dana kwanta a cikin asibiti, meyasa bazaki yarda dani ba? Me nayi miki ne? Kullum haka zankawo abinci saboda ke amma ki?i ko taSawa balle kici.

Dan Allah idan wani abin nayi miki kiyi ha?uri Maryam, duka duka duniyar ma gudanawa take? Wata rana fa sai labari Maryam, dan Allah ki karSi abincin nan kici.

Murmushin ya?e kawai samira tayi tana harar Maryam tace "wai kodai akwai wani abinne da kike Soyewa Maryam? Ya kamatafa ki duba ?o?arin baiwar Allahn nan, idan fa baki gode mata ba bazaki sace mata gwiwa ba, haba Maryam, ai kagaida mai gaisheka ko bazai amsa ba.

Murmushi ?arfin hali Maryam tayi tace "itama maman halima tasan babu wani abin tsakanin mu sai Alkairi, kuma sanin kanki ne bana iyacin abinci sosai, badan haka ba mai zai hanani cin abincin ?ar uwata kuma yayata?

Murmushin makirci Rashida tayi tace "yauwa, ai nasan haka Maryam, to indai kin yarda babu komai a ranki game dani dan Allah kici abincin nan.

KarSar filet Win samira tayi tace ai kuwa zataci wan nan abincin yanzu kuwa Insha Allah, wajen Maryam samira ta nufa tare da Webo faten tace

"Haaaahh bakinki, dariya Maryam tayi tana cewa "haaaaah kamar wata yarinya? Dukansu dariya sukayi san nan Samira takaiwa Maryam cokalin bakinta, sai da Maryam tayi bissimillah san nan taci faten, taci sosai dan ba ?aramin daWi yayi mata ba.

Wani ?aya taccen murmushi Rashida tayi tana cewa

"shikkenan tafaru ta ?are nayiwa mai dami Waya sata, lallai tanada da ya?inin Maryam daga nan sai gidan tsofaffi.

HaWa idanuwa Maryam sukayi da Rashida, itama Maryam murmushin tayiwa Rashida tana ayyana komai tazo dashi Allah yafita, saboda Allah ba azzalumin bayin sa masu imani bane.

*Rashida*

Bayan tattaunawar da sukayi da ?awarta Amina ne suka samu mafita.

*Amina*

Dariyar takaici ta jefi Rashida dashi tace "amma Rashida gaskiya kin bada mata, taya zaki zauna kina haukan kishi kamar bamai ilimi ba? Gaskiya kin Saro da mutuncin iyayen gida, ai wan nan haukan da kikayi bazai taSa zama masalaha a gareki ba, na farko tsanarki mijin zaiyi wallahi, na biyu kuma raini zaki jawowa kanki a wajen kishiyar ki, ai yanzu kishin ?arkashin ?asa akeyi yadda babu mahalu?in dazai zargeki da wani abin, amma yanzu fa duk Abinda yasamu Maryam koba ke bace ke za'ace saboda kin fito kina nuna ?arara bakya ?aunarta, amma da ace tun farko kin nemi shawarata wallahi da kishin sumumi kasau zaki Wora kanki akai, kinga salin alin karatun fatiha daga Nasir Win har jakar Maryam Win zakici ubansu la'ada waje, amma yanzu gaskiya kin Sarar da damar ki.

Ta gumin da Rashida tayi ta sauke tace "to yanzu Amina ya zanyi dan Allah menene mafita?

Ajiyar zuciya amina tayi tace "to akwai mafita gaskiya, kinga dai kafin kikai ga zuwa agadez Win mu fara zuwa katsina, dan katsina dar ne akan dukkan wani asiri, kinsan kano fa suna ta tara a wajen asiri, sudai kano barsu da ilimin addini da kuma son manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, amma wajen bokanci basu iya komai ba, ke ko sun iya wallahi tsananin addu'ar da malamai magada annabawa sukeyi wa garin kano to duk wani asiri da tsafi da akayi a garin ?onewa yakeyi ?urmus komai ya ?one ya zama toka.

Ajiyar zuciya Rashida tayi tace

"ke kuma wallahi haka ne ?awata, kinsan irin maganin kuwa da akayiwa Nasir? Kinsan nawa na ?ona a kansa, sai gashi tashi Waya kamar tsinkewar tsuntsu ya tashi sama nayi asarar komai, ke idan kinga Abinda Nasir yakemin wallahi sai kinji tausayi nafa.

Dan haka kawai a gwada na katsinan ko za'a yi dace .

Dariya Amina tayi tace "ai kinzo gidin maganin ?awata, kyama zauna biyewa wata ya karimatu Alhalin kinsan duk inda Wan uba yake sonka ba kamar soyayyar uwa Waya uba Waya ba, dan haka kawai ki shareta ba?in halin ?an ubanci kawai ta nuna miki.

Kwafa Rashida tayi tace "kedai bari kawai, ai shiyasa daga ita har hajjan na fita sha'anin su saboda akwai wani abin a ransu game dani, ke mubar wan nan maganar ma kinji , gwara muyi wacce zata fisshe mu, nifa gaskiya bazanje katsina ba, sai dai na baki kiyi min komai.

Babu damuwa ?awata, Amina ta faWa tana gyara zama, tace Yanzu zan kira malam nasanar dashi, idan yaso sai ki zayyana masa duk Abinda kikeso.

Da wan nan matsayar aka kira malam aka rattaba masa bayanai, dan ita Rashida a yadda ta zayyana wa malam ma kwata kwata batason Maryam ta koma gidanta, son samune daga asibiti tayi gidan su ko kuma ta wula lahira.

Amma Abinda yabawa Rashida tsananin mamaki shine, yau likita yazo yace ya sallami Maryam, dan haka nan da nan samira ta haWa musu karen su suka nufi gida.

Kuma tunda suka nufi gidan Rashida tayiwa samira sallama tace kanta na mata ciwo, sai da safe.

Tana shiga Waki kuwa ta rarumi wayarta ta dannawa Amina kira, kiranta taitayi amma bata Waga ba, zama Rashida tayi a bakin gadonta tana cewa

"Nifa ban ganeba anyi yamma da kare, wai meke faruwa ne? Kodai maganin kaWan na zuba bada yawa ba.

*KUTSE*

*PAGE 23*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION.*


*Nasir*

Yana zaune ya tasa Maryam a gaba yana bata abincin da tun Wazu yake fama da ita tace bazataci ba bata sha'awarsa, shine ya zauna Yanzu ma yake bata yana haWata da Allah taci tace ita bataci.

Aje filet Win yayi ya zuba mata ido yana cewa

"To yanzu me zakici? Kinsan dai baki isa ki kwanta bakici komai ba ko?

?an ya tsina fuska Maryam tayi tace

"Nifa bana sha'awar cin wani Abin, kawai dai da zan samu kaza da youghout dana ji daWi.

Da sauri Nasir yatashi yace "me zai hana ki samu? Ai yanzu ma kuwa zakiga nazo miki dashi.

Murmushi Maryam tayi tana yaba yadda Nasir ke kulawa da ita tun daga asibiti har zuwa gida, sai kuma ta sauke ajiyar numfashi tana tunanin tasan tana warkewa a bubuwa zasu dawo kamar yadda suke tun farko, amma tana ro?ar Allah daya sau?a?a musu lamarin yasa ?arshen sane yazo.

*Rashida*

Tana zaune kan kujera tana danna waya taga fitowar Nasir da sauri zai fita, shi baima kula da ita ba sai data tayi magana tace

"Ina kuma zakaje haka kaketa sauri?

Batare daya tsayaba yace "zan siyowa Maryam kaza da youghout ne, shine nake sauri dan karsu tashi.

Da sauri Rashida tatashi tace "tohfa, shi kuma abincin dana dafa fa kenan bazataci ba? Shidai Nasir cigaba da tafiya yayi yana cewa "tace bata sha'awarsa ne, shine dalili, ya faWa yana ?arasa fita daga falon.

Juyawa Rashida tayi tana kallon Wakin da Maryam ke ciki tace

"CaSSijan, lallai ma wan nan yarinyar, ni kike Satawa aiki? Ai kuwa wallahi baki isa ba saboda haka bari kiga, wallahi sai naci ubanki kafin ya dawo gidan nan.

Babu sallama kawai Rashida ta bankaWa Wakin Maryam ta shiga, a zaune ta sameta ta lumshe ido kamar mai bacci, wani malolon ba?in ciki ne ya tokarewa Rashida a wuya, musamman yadda taga abincin data zuba mata yashe a cikin filet ko taSawa ba'ayi ba gashi da alamar ma yafara sanyi, cikin jin haushi Rashida ta saka ?afa ta shuri Maryam tana faWin ke jaka.

"A zabure Maryam ta Wago tana kallon Rashida, sai tai saurin cewa "a'uzubillahi minasshai Wanirrajim, dan ba ?aramar tsorata Maryam tayi da shurin da Rashida tayi mata ba.

HaWe rai Rashida tayi tana cewa "nice shaiWan Win? Ni kike kira da shaiWan?

Tashi tsaye Maryam tayi tana harar Rashida duk da gabanta dake faWuwa, amma haka ta daure ta iso gabanta tace

"Koke ba shiWan bace ai mai take masa bayace Rashida, wai me kike ji danine Malama, nafa gaji haka dukan sata.

Ban tsare miki komai ba kidunga bina da jafa'i kala kala, to bari kiji, wallahi kibar ganina haka nima bani sauki, shikkenan ke baki da aiki sai tayar da husuma? Kwata kwata ke bakyason zaman lafiya?.

Cikin jin haushin magan ganun Maryam Rashida ta saka hannu ta buge mata baki tana cewa "ke jaka dabba, dalla rufe mana baki shashashar banza, bora marar rabo.

Dan ubanki dani zaki tsaya kina sa'insa? To wallahi baki isa ba, na rantse da Allah sai nayi miki duka a daren nan naga uban da zai kwace ki.

*Maryam*

Jinin dake zuba a bakinta ta domin buge bakin da Rashida tayi mata yayi sanadiyar fashewar bakinta, duk da jinin dake zuba kuma bai hana Maryam magana ba cikin kuka tana cewa

"Ni kika fasawa baki Rashida? Wallahi bazan yarda ba, kuma ko ubanki kema bai isa ya hanani fito na fito dake ba, wallahi muddin kika taSa lafiyar jikina wallahi saina taSa taki, kuma kece jaka dabba wacce ke faWa da ikon Alla.....

Tun kan Maryam ta rufe baki Rashida ta zabgawa Maryam mari tana kama ta da kokawa tana cewa

"Wallahi yau sai nayi miki illa Maryam, na rantse da girman Allah sai naga bayanki.

Itama Maryam ?o?arin tarewa takeyi amma ?arfin ba Waya ba wan nan yasa Rashida taci galaba akan Maryam, ta kuwa wujijjigata tare da wan cakalar da ita gefe, tana wullar da ita Maryam ta faWa kan wani glass dake Wakin ta baya, take kuwa kanta ya yanke jini yafara zuba, duk da haka kuma Rashida bata ha?ura ba sai data ?ara cafko Maryam tana cewa

"Wallahi sai na kasheki, Shegiya tsinanniya .

Ihu Maryam ta saka domin kuwa wani irin jiri ne ke kwasarta saboda jinin dake zuba a kanta, duk da ihun da Maryam keyi kuwa bai hana Rashida jawota ba ?iiii, kamar kayan wanki tayi falo da ita.

Ko a falon Rashida bata tsaya ba direct kawai hanyar step tayi da ita da niyar ta jefata ta mutu kowa ya huta, ai kuwa batayi wata wata ba sai ta saketa a kan step Win tare da hankaWa Maryam ta fara gare akan benen.

Wani salati Maryam ta saka haWi da kwala ihu, kuma dai-dai wan nan lokacin Nasir ya buWe gate tare da turo ?ofar zai shigo.

Rashida na ganinsa ta daka wani uban tsalle ta isa inda Maryam ke kwance tana fashewa da kuka tana cewa.

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una, subhanallahi, Maryam, sannu, sannu kinji subhanallahi, Allah yasa dai bakiji ciwo ba maryam, sai kuma ta saka salati tana shafo jinin dake zuba akan Maryam tace

"Innalillahi, wallahi kanki ya fashe Maryam, subhanallahi, sai ta kalli Nasir wanda jin ihun su baki Waya yasa ya bankaWo ?ofar ya shigo yace

"Maza riketa mukaita chemist baban Halima, wallahi kanta ya fashe, sannu Maryam, daman sai da nace miki anya zaki iya tattakin nan kikace zaki iya, gashinan kin samu tsautsayi mai muni wallahi.

Cikin tashin hankali Muryar Nasir na rawa yace

"Wai menene ya sameta ne? Ya akayi haka? Yana ri?e Maryam wacce har jinin dake zuba a kanta ya Sata mata wuya da riga.

Kai dai muje baban Halima a fara bata taimakon gaggawa kafin wan nan, sannu Maryam, da yake Rashida doguwar rigace a jikinta sai kawai ta cire Wankwalinta ta yafa a jikinta, ita kuma Maryam a haka suka fita da ita har waje.

Da yake akwai wani babban chemist a layin gidan, cen Win suka kaita likitan ya karSeta yana salati, da sauri ya saisaye gashin wajen domin raunin yayi girman da sai an mata Winki, Winkin kuwa yayi mata duk da jijjiga kai da kuma ?an?ame Nasir da tayi tana zubar da hawaye masu zafin gaske.

Rashida jitake kamar ta ta zari allurar da akayiwa Maryam ta caka mata a ?ahon zuciyar ta saboda yadda takejin Sacin ran ?an?ame Nasir da tayi, a fili kuma sai faman jerawa Maryam sannu takeyi harda tayata hawaye tana cije leSe da runtse idanunta irin tanajin Winkin da akewa Maryam Win har jikinta.

Magun guna likitan ya haWa mata san nan Nasir ya ri?ota ita kuma Rashida ta ri?e ledar magun gunan.

Suna shiga Nasir yayi Waki zai shigar da Maryam domin ta huta , da sauri Rashida tace, sannu Maryam Allah yabaki lafiya sai kuma tayi shiru, duk bala'en'en kishin dake cin zuciyar Rashida amma saboda kar asirinta ya tonu haka ta daure ta cije ta cewa Nasir.

Ka tafi da ita Wakinka baban Halima tunda kaga tsautsayin daya sameta bai kamata abarta ta kwana ita kaWai ba.

*Nasir*

Har cikin ransa yaji daWin abinda Rashida tayi, a zuciyar sa yake cewa ya gode Allah da zuciyar rashida tafara sanyi gashi har tanajan Maryam Win a jiki.

Murmushi Nasir ya sakar mata yace "nagode Rashida.

Itama murmushin ta sakar masa tace babu komai, ai yiwa kaine, amma a ranta harar shi takeyi tana cewa

"?an iska kawai gafalalle.

?akinsa Nasir ya shigar da Maryam yanajin tausayin ta, tsawon sati biyu kenan abubuwa sunata samunta, Allah yakawo mata Wauki ya faWa yana ajiyeta bakin gadon nashi.

Rashida na ganin sun shiga Waki tayi saurin nufar Wakin da Maryam take ta kulle, da sauri ta shige banWaki ta Wauko tawul Win sauda tare da kaWa ruwan kumfa tafito, glass Win daya fashe ta fara tattarawa ta kwashe ta watsa a dosbin san nan taware fanka tafara goge wajen.

Yana bushewa ta fice daga Wakin tanajin kamar tafasa ruwa ta watsawa su Nasir ta window su babbake kowa ya huta .

?akinta ta wuce tana banko ?ofar saboda yadda zuciyar ta take azalzalar bakin ciki.

Tana shiga ta zauna a bakin gadonta ta fashe da kuka, tunanin yadda zatayi da Maryam a cikin gidan nan kawai takeyi, itafa gani take kamar shima malamin Amina bai wani iya aiki ba, amma ace har yanzu zance Waya ake yi shine zata bar gidan.

Gabanta ne kuma a karo na farko yayi mummunar faWuwa, a zabure ta mi?e tana tunanin kar Maryam ta tona mata asiri awajen Nasir, idan ta tona mata a siri a wajen Nasir yaya zasuyi dashi?

Sai kuma ta zauna jin wani abu ya tsarga mata a cikin zuciyar ta saboda tunanin magan ganun Amina da malam da tayi.

Amina ta samu zuwa katsina, kuma koda taje sunyi magana da malam akan Maryam da Nasir, malam bai Soye mataba ya sanar da ita akwai tsananin wahala asiri yaci Maryam saboda tsananin addu'a, amma baice bazai cita kwata kwata ba, zai iya cinta a lokacin datake jinin al-ada, dan haka duk ranar data fuskanci nata jinin al-ada to tasanar dashi da wuri dan akwai sririn dazai tura mata wanda Wayan biyune, kodai ta haukace ko kuma ta makance.

San nan ya?ara dacewar , asiri bazai yi wahalar kama jikin Nasir ba saboda bashida da ibada da kuma addu'a da tsari, dan haka idan ta yarda to za'ayi masa asirin.

Da sauri Rashida tace "karkayi masa asiri yanzu, nafison na dasa yarda ta a cikin zuciyar sa akan Maryam tukunna, idan ya yarda dani daga baya komai ma sai ya biyo baya, amma inason ita a saka mata shakkata da kuma tsorona, kuma inason ya kasance duk Abinda zan mata bazata iya taSuka komai ba bare ta rama ko kuma ta shaidawa wani.

Dariya boka nakan tudu yayi yace "karki damu wan nan kan za'ayi nasara a kanta.

Ajiyar zuciya Rashida ta sauke tanajin wani sanyi kaWan kaWan a cikin ranta.

*Maryam*

Hawaye kawai take sharewa ta gefen idonta, shi kuma Nasir sai lallaSata yakeyi akan ta daure tasha maganin saboda zugin ya ragar mata.

Da kyar ta buWe bakin ta ya saka mata maganin ta shanye tana haWiyewa tare da zubar hawaye.

Goge mata hawayen Nasir yayi yana mai ?arewa fuskar ta kallo, Maryam ba?ace amma irin ba?in nan mai kyau, kuma ba ba?i cen ba normal ba?i dai kamar yadda aka sani, rungumo ta jikinsa yayi yanajin tsananin tausayin ta na kuma kamashi, wani iri Maryam taji a cikin jikinta amma duk da haka sai da ?an?ameshi tana kuka mai sauti kuma irin mai raWaWin nan a cikin zuciya.

Shi kansa Nasir sai da yaji wan nan kwa?umar da Maryam tayi masa, hakan yasa shima ya kuma ri?e ta sosai yanajin kamar ya mayar da ita cikinsa dan kar wani Abin ya kuma samunta.

Sai data Wan tsagaita da kukan san nan tace " Babana, ya Nasir Babana, inama babana bai rasu ba na gaya masa dukkan Abinda ke damuna, ya Nasir kaWaici na damun rayuwa ta alhalin ban rasa k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?omai da kowa ba, amma tabbas lamarin dake zagaye da rayuwa ta babban lamari ne mai girma wanda sai dai Allah ya dafamin.

Kanta Nasir ya dafa yace.

"Maryam bazakiyi maraici da kaWaici ba muddin kina tare dani, da ikon Allah zan kasance mai yi muku a dalci tsakanin ki da Rashida, inason Rashida kema inason ki Maryam, dan haka bazan taSa yarda wata a cikin ku tayi kuka ba alhalin kuna dani, dan Allah ki share hawayen haka.

Fita tayi a cikin jikinsa tanajin irin wucewar da magan ganun sa suke yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login