Showing 18001 words to 21000 words out of 175193 words

Chapter 7 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

526

da mota kamar zai tashi sama dan Allah ne kad'ai yakaishi gida lafiya, tunanin Rashida duk yabi ya cike zuciyar sa, tunanin Abinda yasa ya karb'i auren marar kunya haka yakeyi, meyasa ma ya yarda? Meyasa bai musawa babanta ba? Ai ba shi kad'ai ne namijin dazai iya tallafar rayuwar taba, gashi nan ai shi bai tallafi rayuwar taba ita ta watsa masa gida, jiyake daman hannun agogo ya dawo baya da wallahi ko ak'afa aka d'aura masa Maryam bazai ja zaran ba, da wan nan irin tunane tunanen yasamu Allah ya kaishi gida lafiya.

Tunkan yayi parking ya hango su Halima a tsaye sunyi cirko cirko tare da dungule wa waje d'aya kamar masu jin sanyi, da sauri ya kashe motar dan ko parking bai gama dai-dai tawa ba yafice daga motar cikin sauri ya k'arasa wajensu, suna ganinsa suma sukayo kansa da gudun gaske tare da rungume shi suna furta ina momy?

Cikin zafin da zuciyar sa keyi ya dafa kansu yana shafawa tare da cewa

"Kuyi hak'uri momyn ku tana samun sauk'i sosai, insha Allah gobe kamar haka tana gidan nan tare daku kunji? Da sauri suka d'aga kai Alamar sunji.

Rike hannun su yayi tare dafara jansu dan sushiga cikin gidan, har sun fara tafiya sai Halima ta d'aga kai ta kalleshi tace

"Abban mu ina Aunty?

Wata irin fad'uwar gabace da sakko masa a kirji har yanajin zuciyar sa na tsalle duka lokaci d'aya, sai alokacin hankalin sa yafara da wowa jikinsa yafara tunanin halin da suka kasance d'azu shida Maryam da kuma irin magan ganun daya jajjefa mata cikin fushi.

Da sauri ya k'arasa jansu zuwa falo ya zaunar dasu, suna zama sauda tace

"Abba yunwa mukeji tunda mukadawo daga makaranta bamuci komai ba.

Kansa ne ya doka yayi saurin dafe goshin sa yana furta kalmar

"ya salam.

Bakuci komai ba kuma? Sai ya kalli halima yace.

"Ke Halima yanzu ko indomie nan baki iya dafawa ba bare ki dafa muku?

Kai Halima ta d'aga da sauri tace "Abba na iya mana.

Da sauri sauda tace

"karya takeyi Abba, wallahi bata iya ba ko jiya da aunty tayi girki nace bazan ciba sai dai ta dafa min indomie zuwa tayi tana ta kallon yadda take dafawa, shine bayan auntyn ta gama dafamin taje kichen wai zata gwada ai kuwa taita konewa da wuta daga baya indomie ta K'one taita k'auri. Sauda ta k'arasa tana kyalkyale wa da dariya.

Wani huci mai zafi Nasir ya sauke san nan ya yar far da hannu yanajin nadamar barin Maryam da yayi ta sauka daga motar, zama yayi akan d'aya daga cikin kujerun falon yana mai zurfafa tunanin inda Maryam zata nufa ita dabatasan ko ina ba.

Ina wai zata nufa a daren nan? Ita ba kud'i bare yace garin su zata nufa, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya furta a sanda ya tuna alk'awarin daya d'aukar wa baban Maryam na zai kular masa da ita tamkar tafi kowace mace gata a rayuwar duniya.

Yana wan nan tunanin ga gumi dake faman tsattsafo masa sai jiyayi sauda ta kwala ihun kukan ruwan zafin daya kwaro mata a hannu, da gudu ya nufi kichen ya gansu tsaye Halima takama hannun sauda ta tara a cikin sink ruwan na kwarara a hannun, gashi sai tsala kuka sauda take duk ta kid'ime.

A jikin k'ofar ya jingina yana furta hasbunallahu wa ni'imal wakeelu , sai da yadawo nutsuwar sa nan ya tattarasu ya d'ure a motar ya figesu suka fara zaga gari bayan yakaisu wajen cin abinci kuma yakai sauda chemist domin aduba hannunta.

*Not*

_Sadiya ta koma sauda_ _ne bisa dogon_ _nazarin danayi nacewar_

_"Halima da sadiya duk_ _sunan d'aya ne lak'abinne kad'ai ya_ _banbanta, hakan yasa_ _sunan Halima ya zauna sadiya kuma_ _ya canza da suna sauda, dafatan za'a gafarce ni=?O?
*KUTSE*

*PAGE 10*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*


*Samira*

Yanayin yadda taga kukan Maryam yak'ici yak'i cinyewa shine dalilin daya saka ta samu waje ta zauna tare da zuba mata idanuwa tana kallonta, sai data bari kukan yad'an tsagaita san nan cikin sauri ta rufe bakin Maryam da cewar.

"Dan Allah dan Annabi kiyi hak'uri da wan nan kukan Maryam, taya mutum zaita kuka kamar wanda yake saka ran k'arshen rayuwar duniya? Kinfi awa uku kina wan nan kukan, abinci kink'i ci, ruwa kink'i sha shi kansa wanka kink'i yi wai duk saboda me?

Tun d'azu mijina yadawo amma nakasa nutsuwar zuciya na bashi hankali na duk saboda ke Maryam, inda Allah ya rufamin asiri mijina mai fahimta ne da wanine daba wan nan zancen akeyi ba, kuma dad'ina ma da Allah yasa yau night duty ne dashi a asibiti da ban san yadda zanyi dake ba, tunda kona tafi wajensa gangar jikina ne kad'ai a wajensa amma nasan tabbas duka ruhina yana nan wajenki.

Dan haka na rok'eki da girman Allah kibar kukan nan haka komai ya dakata haka don Allah mu fuskanci matsalar dake gaban mu.

*Maryam*

Share hawayen idanunta tayi tace "bazan daina kuka ba samira har sai ranar da Allah yanufa matsalolin gidan aurena ya yaye, aurena ba irin kowanne aure bane samira, aure na yazo da abubuwa da yawa wanda bansan ma damai zan fassara su ba, haka zalika ba kowacce macace zata jura zama bora ba a rayuwar zaman aurenta muddin tasan Abinda takeyi, dan haka dole ne nayi kuka samira saboda yadda nake hangowa kaina zama bora agidan Nasir da kuma rikita-rikitar gidan aure.

Baki sake samira ke duban Maryam tanata auna magan ganun ta dan duk yadda ta bajesu a fai-fai bata gano wata tsakuwa guda d'aya wacce zata d'aga tace itace amsar magan ganun taba.

Dan haka sai samira tayi namijin k'ok'arin cewar

"me yake faruwa ne Maryam? Kin barni cikin duhu fa, ni sam bangane Abinda kike son ganar dani ba, kinsan ba bawai kwarewa nayi akan maganar zarwance ba ni sai an min b'aro-b'aro nake fahimtar lamari, dan haka sanar dani komai ko ina da hanyar taimaka miki kifita cikin matsala.

*Maryam*

Nan take babu wata kwana kwana ta zayyanewa samira yanayin da aka k'ulla aurenta da kuma yanayin dasuke ciki a halin yanzu, ta k'arasa tana cewa

"wallahi tallahi samira tunda nake ban tab'a had'uwa da namijin danakeji idan babu shi a rayuwa ta bazan rayuwa ba sai Nasir, ke hasalima wallahi bantab'a jin soyayyar namijin tafarad' d'aya tashiga raina da jijiyoyin jinina ba kamar Nasir, sai kuma tafashe da kuka tare da kamo hannun samira tace

"Dan Allah samira kitaimakeni ki samamin mafitar hanyar da zanbi na samu Nasir ya soni koda d'an kad'an ne, ni koda bazai iya had'ani da matarsa a waje d'aya a ransa ba yasamamin matsugunni ko bakin hanya ne indai wata bazata zo ta wuce takaina ba.

*Samira*

Cikin mamaki take kallon Maryam harda kuma lek'a fuskarta dan Abin al-ajabin yayi mata yawa, yanzu duk wan nan ruwan wulak'ancin da Nasir ya yayyafa mata a cikin jikinta da zuciyar ta wai har son koma masa takeyi, ajiyar zuciya samira ta sauke dan bazata iya wani zafafa tunani ba kawai sai ta mik'e tare da cewar Allah ya sawak'e ta fara tafiya.

Da sauri Maryan ta rik'e hannunta tace "Allah ya sawak'e fa kikace samira? Kina mufin duk bayanin danai miki na banza ne kenan?

Girgiza kai samira tayi tace "bayanin ki bana banza bane Maryam, inason na d'an nutsune na warware magan ganun ki sai nasan ta ina zan kamo bakin zaren naki, yanzu dai inason kiyi hak'uri kici abincin nan kizo kiyi wanka mu samu mu kwanta insha Allah zuwa safiya zamusan abinyi kinji?.

A sanyaye Maryam ta d'aga kai san nan ta tad'an fara gutsurar tuwon tana sakawa a cikin bakinta kamar mai cin magani tafara taunawa a hankali, kad'an taci tasha ruwa ta mik'e ta nufi d'akin da samiran ta nuna mata idan ta gama ta biyota.

*****

*Nasir*

Tafiya kawai yakeyi dan bai san inda ma zai jefa motar ba, kallon su Halima yayi wanda duk sunyi barci a motar sai k'arar numfashin su ke fita Alamar barcin nasu ya Dad'e dayin nisa, sau wajen goma yana zuwa wajen daya sauke Maryam yana dubawa ko zai ganta amma shiru babu ita babu alamar ta, kansa yayi bala'in d'aukar zafi da tunanin inda tatafi ga tunanin Rashida da halin daya barota a ciki, shi baima san hawaye yakeyi ba sai da yaji gishiri gishirin ruwan hawayen yana shiga bakinsa san nan ya duba idanunsa yajishi jagab da lema, hawayen ya share san nan ya kuma tada motar a lokacin daya kalli agogon jikin motar yaga har d'aya saura na dare yana zagaye a titinan kano domin duban Maryam da inda ta shige, sannu a hankali ya dunga tuk'in nasa har ya isa gida yanajin kamar zazzab'i na neman rufe naman jikinsa.

Yana isa kuwa ya kwashe yaran da suka Dad'e dayin barci ya shigar dasu d'akin su san nan ya koma nasa d'akin da nufin yayi wanka kozai samu kwari a cikin jikinsa, yana shiga d'akin wayarsa ta fara ruri, da sauri ya zarota a gaban al-jihun rigarsa ya duba wanda ke masa wan nan kiran.

Da sauri ya zaro ido yana kiran sunanta da cewar

"Rashida? Rashida dai? Ya k'ara fad'a hannunsa na rawa da niyar d'aga wayar kuma sai ta tsinke.

Da sauri ya danna kiran wayar domin yabi bayanta dan baisan kiran ba kona gaggawa ne.

Bugu d'aya biyu aka d'auki wayar kuma sai shiru ya ratsa sai saukar numfashi a hankali, jin ba'ayi magana ba a wancen b'arin yasa Nasir saurin cewa

"Matata" matata kece? Ya jikin naki? Ko sauke numfashi ba yayi yake ta jera wan nan maganar da sauri da sauri.

" *Rashida*

ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace

"nice. "Zan iya ganinka yanzu?

Batare da Nasir ya tuna k'arfe nawa ba kuma san nan bai damuwa ya tuna d'in ba yayi saurin d'aga kai kamar tana kallonsa yace

"Me zai hana kuwa? yanzun nan ma kuwa gani nan.

Bai jira cewar ta ba ya zari mukullin motar ya rufe gidan duk da yasan da yara a gidan amma bai damu ba yasan Allah zai tsare masa su ya figi mota ya fice yanajin wani sanyi da nishad'i na shiga cikin zuciyar sa.

Sai wajen biyu saura san nan ya isa asibitin kuma yana zuwa d'akin da Rashida ke kwance ya tura ya shiga da sallama d'auke a bakinsa, yana shiga suka had'a idanuwa da Rashida wacce ke zaune ta buga uban tagumi tana jiran taga zaizo d'in ko kuwa Maryam zata hanashi yazo wajen nata.

Wata sassayan ajiyar zuciya Rashida ta sauke, a lokaci guda kuma ta sauko daga gadon tare da fad'awa jikin Nasir ta fashe da wani mugun kuka mai cin zuciyar mai yinsa.

Bai hanata ba haka yabari ta gama kukanta san nan ya kamata suka zauna akan wan nan gadon nata ya had'ata da jikinsa yana cewa

"Shikkenan, ya isa haka, ai gashi nazo, menene?

D'aga kai tayi ta kalleshi da idanunta da suka kod'e lokaci guda tace

"Ina take?

Yasan sarai wa take nufi amma sai ya basar yace "wa?

D'an murmushin tak'aici tayi tace "waccen kutsattsiyar.

Da sauri Nasir ya rufe mata baki da nasa dan bayason yaji ta ambaci sunan Maryam, badan komai ba sai dan bayason farin cikin data fara samu yakau a wan nan lokacin dayake ganin kamar Alamar salama a wajenta.

Sai da ya tsotse mata bakin tas duk da cewar an kwan biyu ba'a wanke shiba Sakamakon jinyar datake amma bai dameshi ba dan a wurinshi ko kashi Rashida tayi tace sai dai ya sid'e mata to tabbas zai sid'e matan muddin da ranshi da lafiyar sa kuma muddin hakan zai sakata farin ciki.

Bai bari ta sake wata magana ba haka ya kwantar da ita shima ya kwanta akan gadon suka nane da juna ya tallafeta tare da rungume ta tsam a cikin jikinsa ya zagayeta da hannayen sa har barci ya d'auke su basu saniba, don tun kowa na sak'e, sak'e a cikin ransa har zuciyar ta saki tunanin ma ya kwanta barcin ya kwashe su.

*Washe gari*

Tun misalin k'arfe biyar na asuba Maryam ke zaune akan Abin sallarta tana kaiwa Allah kukanta, addu'a take da yak'inin Allah zai kar b'ar mata kuma yabata zab'in alkairin data nema a wajensa, tun daren jiya da suka tattauna da samira takejin wani nauyi ya ragu daga rad'ad'in datake ji a cikin zuciyar ta, tabbas samun K'awa tagari ba abune mai sauk'i ba a wan nan zamanin, ta tabbatar da hakan a lokacin data fara amfani da shawarar samira tun daren jiyan ta fara ganin canjin a damuwar ta.

*****

Koda Maryam ta shiga d'akin tarar da samira tayi tana salla a kan dadduma, kuma tana shiga ta idar tana kallonta da murmushi tace

"Kin ganni damuwar ki ta hanani sukuni wai sai yanzu nake sallar isha'i, da sauri Maryam ta zaro ido tare da dafe goshi tace

"Subhanallahi, wallahi niko la'asar ban yiba, Wayyo Allah, da sauri ta shige wata k'ofa inda take tunanin ban d'aki ne, tana shiga ta saki shaya a jikinta dan ko kayan bata samu sukunin cirewa ba, dan tasan jikinta ma bazai yi salla ba dole sai tayi wanka dan d'azu tana wan nan kukan idan ta tak'ar k'are zata saki kukan tanajin sanda fitsari yake kufce wa ya tsiyayo a jikinta saboda azabar kuka, dan haka sai data bari tagama jik'a kayanta da jikinta baki d'aya san nan ta cire kayan ta silla wanka da soso da sabulu, tana fitowa kuwa taci karo da kaya samira ta ajiye mata sai kawai ta saka tare da zura hijabin ta ta hau jera sallolin dake zagaye a kanta.

Sai data idar da sallar san nan taji wani haske da kuma iska na ratsa zuciyar ta wanda batasan daga inda yake zuwa ba, da sauri ta kalli samira wacce ke kallonta da murmushi.

Ajiyar zuciya samira ta sauke tace "

ya kikaji? Itama Maryam ajiyar zuciyar ta sauke tace

"Sauk'i, dan tabbas taji sauk'in akan tarin abubuwan dake mata yawo.

Cikin murmushi samira ta rik'e hannunta tace

"hak'ik'a nasan ke mai ibada ce Maryam, san nan ke mai yawan addu'a ce ga kuma alkairi da dukkan wanda ya kusance ki, meyasa hakan ya canza a lokaci k'ank'ani?

Damuwar Nasir ce ko kuwa rikicin Rashida ne yafara canza akalar ki?

Shiru Maryam tayi tana tunanin rabon data tashi tsakar dare tace zata gana da ubangijin ta har ma ta manta, sai kawai ta girgiza kai, hak'ik'a wad'an nan damuwar da kuma rashin nutsuwar zuciya sun sanya tafara manta da wacecec ita?

Cigaba da magana samira tayi tace.

"hak'ik'a kuka rahama ne ga zuciyar data raunana, san nan tsayuwa kan ibada kariyane ga gangar jikin data jirkita, haka addu'a makamine ga lamarin daya saurara, kinsha fad'a min haka sau da dama Maryam, nasan ba mantawa kikayi ba saboda d'an adam ajizine.

Wan nan kalaman dakike nusar dani a abubuwa da yawa sune makamin dazaki rik'e har Allah yakawo miki mafita akan lamarin gidan aurenki.

Bazance ki rabu da Nasir da matar saba saboda kema matarsa ce kuma Allah shine masanin b'oyen Abinda ya b'oye har ya k'ulla auren ku a lokacin da babu wanda yake da tsammanin hakan, dan haka ki sani Maryam

"Da aure, da haihuwa, da mutuwa, da arzuk'i, da talauci duk na Allah ne, kuma sanin lokacin faruwar su duka Allah yabarwa kansa sani.

mudai namu addu'a ne da kuma fatan samun alkairi da dacewa a duka wad'an nan abubuwan, ita kanta addu'a takan canza k'addarar daba mu san da ita bama, dan haka.

Ki rik'i addu'ar zaman alkairi tsakanin ki da Nasir, idan da alkairi a tsakanin zaman ku Allah ya dai-dai tsakanin ku, haka idan babu alkairi so gaibune Allah ya rabaku cikin ruwan sanyi batare da cutuwar d'ayan kuba Maryam.

Haka zalika Rashida, kiyi addu'ar zama da ita lafiya idan da Alkairin zaman tsakanin ku, idan kuma babu alkairi duka dai Allah ya sallameku salin Alin batare da b'acin ran wani ko takurar zuciyar wanin kuba.

Ki jingine soyayya a gefe Maryam ki fuskanci gaskiyar al-amarin ki kafin kikai ga yankewa kanki hukunci, a ganina d'aukar so ko k'i da zafi yakan haifar da d'umbin nadama alokacin da lokaci ya kuracewa mai yinsa, dan haka wan nan itace shawarar da zan baki a wan nan zaman naku.

Zaki koma gidan Nasir maryam, amma akan tsani guda biyu.

"Tsani na farko shine

"sai ya nemeki dakaran kansa yanemi sulhu dake dan bakece kika wulakanta shiba bare ki nemeshi kibashi hak'uri.

"Tsani na biyu kuma shine

"Muddin yanason ki zauna dashi sai ya zauna da matarsa ya san irin kalaman dazai mata ta yarda dake a matsayin matarsa ba k'anwarsa ba, kuma tabbas sai ta yarda da hakan san nan ne zaki koma gidan sa kici gaba da zama, ruwansa ne ya canza miki gida ruwansa ku cigaba da zama gida d'aya da Rashida tunda dai duk a k'ark'ashin inuwar auren sa kuke, amma tabbas koda zai nema miki gida ki zauna saifa Rashida ta yarda ta d'auke ki a matsayin matarsa dan bazai yuwu ace a cigaba da gini a tubalin tokaba.

Dan haka idan kin yarda dani saiki yimin bayani naji makamar da zamu d'auka.

*Maryam*

Cikin wani farin ciki da annushuwar data dad'e bata tsinci kanta ba tun lokacin data duro garin kano taci karo da Rashida ta samu kanta a ciki, kanta ta d'aga sama tare da damk'e hannun samira a hankali ta furta

"Alhamdulillahi.

Sai kuma ta sauke kan k'asa ta fara share hawayen da suketa gangaro mata, murya na rawa Maryam tace.

"Hak'ik'a ke k'awa ce ta gari samira, shiyasa bantab'a haufi koda nasanin sanar dake dukanin damuwa taba, daban had'u dakeba dabansan halin dazan shiga ba, nagode Allah daya banike.

San nan Insha Allah zanyi duka amfani da shawar warin da kika bani 'yar uwata, tabbas zan manta da Nasir samira, zan bari harya nemeni naji matsayata a wajensa, banason ya duba iyaye ko amintar dake tsakanin sa da yayana, zahirin zuciyar sa nakeson sani na zama dani a wan nan karan.

Rungume ta samira tayi tana shafa bayanta tana cewa

"Mukwanta haka Maryam k'arfe d'aya saura, ma d'ora da safe Insha Allah.

Murmushi Maryam tayiwa samira san nan tace

"Ki kwanta'yar uwata, zangana da ubangijina tukunna.

Wan nan shine Abinda yafaru tsakanin maryam da samira a daren jiya, kuma tun wan nan daren Maryam bata runtsaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login