Showing 153001 words to 156000 words out of 175193 words

Chapter 52 - KUTSE COMPLETE HAUSA NOVEL

07 Feb 2026

536

zai kasheka wallahi, kuma muje zuwa ni daku Wan halak ka fasa.

Nasir bai ?ara tanka Rashida ba Saboda jin haushi kawai yafice yana tunanin Abinda yasa ya ?ara raSar wan nan matar jarabar, bata da komai a yanzu duk wata kimarta da mutuncinta ya zube a wajensa, san nan gata ?andas babu mamora ta ko'ina, gaba Waya jiyake ta salamce masa shiyasa tun washegarin da Maryam ta korasa wajenta bai ?ara saurararta ba dan ya lura ha?ilo kawai da bawa kai wahala yakeyi.

Tsaki Rashida itama ta saka san nan tatashi ta nufi Wakinta domin ta aiwatar da abinda boka cika aiki ya sakata koda zataga canji.

Magun gunan wanka da tsugunno dana barbaWawa daya bata sune ta fiddasu tare da Waukar matakin yadda zata gyarawa Nasir zama da mallakar sa na har abada wanda bazai kuma suSuce mata ba.

*KUTSE*

*PAGE 66*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Rashida*

Tasan lallai yanzu bata gaban Nasir, haka zalika gab yake da wula?anta tata a gaban mutane, dan haka shiyasa son ta allikafa tafara haWa kayanta tana kuka domin tabbas taga Nasir bada wasa yake ba da yace tabar gidan, kuma ko Wazu da safe dayazo ya ?ara jaddada mata wallahi idan bata kwashe kayanta kafin yadawo gidan nan ba sai dai tatafi gidan su, dan wallahi ko mutuwa zatayi idan yasaketa sun rabu kenan har gaban abada, san nan yace mata tayi asiri da tsafin duk dataga zata iya dai-dai yake da ita, dane taci galaba akansa amma Yanzu yasha tabara yasha yasin duk iya shegen dataga damar yi tayi lokacin tane, kuma wallahi yana Waga mata ?afane kawai Saboda darajar yaran da suka haifa tare amma bawai danta isa ba saboda ta rigada tagama zubar da kimarta a wajensa.

Kallon zita Rashida tayi wacce ta zuba uban tagumi tana kallon ta tace "dan uwarki bazaki tashi ki rufemin waWan nan akwatinan ba? Jiki na rawa zita ta mi?e tafara zugewa dan yanzu ba ?aramin tsoron Rashida takeba saboda Wan bazan dukan datake lakaWa mata idan muguntarta ta motsa.

*Maryam*

Umma ta kalla tana cewa "yanzu dan Allah sai kubari na?ara raSar Rashida? sanin kanku nefa ta cutar dani babu adadi, san nan yanzu kuma na yadda na haWa gida da ita bayan irin abubuwan da suka faru a baya, nidai dan Allah umma kiyi ha?uri kibar maganar nan, nidai kawai gwara ya Nasir yabarni a cikin gidan nan wallahi da dai na koma kusa da Rashida.

Girgiza kai umma tayi tana mai ri?e hannun Maryam tace "inada ya?inin ibadar da kikeyi da kuma zama da ita da zuciya Waya bazai bari ta cuceki ba, da ace ta isa ta cutar dake da tuni tayi galabar cutar dake harma da raba ki da numfashin ki tuntuni, dan haka ki saka a ranki ita bata isa ta cutar da rayuwar kiba, karkiga kamar inason turaki ramine Maryam, inason nayiwa kowa adalci ne kamar yadda ko yaushe nake nusar dake da kikasance a haka kema.

Na farko idan Nasir ya haWe ku waje Waya zai samu nutsuwar zuciya Maryam , domin duk wani namiji mai mata biyu bayason yaga ya rarrabawa iyalan sa muhalli musamman idan yana da wajen ajiye su, san nan itama Rashida idan akace za'a fitar da ita daga cikin gidan ba'ayi mata adalci ba Maryam, dan itama zataso ace ta zauna a sabon muhalli, dan haka dan Allah kiyi ha?uri ki bata dama domin kiga gudun ruwanta san nan kiyi addu'a ki haWata da Allah kiga ikonsa a kanta babu Abinda zata iyayi miki.

Kai Maryam ta rausayar duk da ba haka tasoba amma tabbas maganar umma a kan dai-dai take, to amma zata iya ha?uri ta barwa Rashida wan nan part Win ta Wauki Wayan ko kuwa? Kamar umma tasan Abinda take tunani sai kuwa tace mata.

Abin duniya fararre ?a rarre ne Maryam, kiyi fatan samuun muhalli mafi kyawun gaske a gidan aljanna, nidai idan zan baki shawara ki yarda Maryam kibar Rashida ta zauna a inda ta fara zama ke ki Wauki sabon, na tabbatar sai kinfi farin ciki domin yadda Rashida take babu Allah a ranta wallahi tabbas nasan idan a kace tatashi daga wan nan part Win zatayi duk Abinda tasan zatayi domin ta hanaki farin ciki ko ta hanaki zaman lafiya, dan haka kibar matashi ke ki Wauki sabon dan hakan sai yafi miki Alkairi Insha Allah.

Ajiyar zuciya Maryam tayi tace "naji umma, banida niyar cutar Rashida amma a wan nan karen naso na cusa mata takaici da ba?in cikin da bazata iya fita a cikin sa ta sau?i ba, sai dai kuma gashi kash! Duk wata damar da nakeso nayi Amfani dashi kin juyar dashi baya kin hana, amma dan Allah umma unarni kike bani ko shawara?

Ajiyar zuciya umma ta sauke tace "ba umarni nake bakiba Maryam, shawara nake baki wacce nake miki fatan ta Sulle dake Maryam.

?aga kai Maryam tayi tanajin wani sanyi a ranta na game da magan ganun umma, sai ta saki murmushi tace "Nagode sosai da shawara umma, kuma tabbas zanbi shawarar ki nayi aiki da ita. Ita ma umman kai ta Waga tace "Allah yayi miki albarka Maryam, kuma Allah ya rabaki da sharrin mutum da aljan yakare rayuwar ki data yaranki baki Waya, da Amin Maryam ta amsa tanajin kewar umma saboda yau zata tafi, daman tazo ganin jikinta ne na kwana biyu, haka dai umma ta wuce tatafi da niyar sai Maryam ta haihu san nan zata dawo.

*Nasir*

Baiyi mamakin canzawar maganar Maryam ba, yasan cewar Maryam macace tagari kamila kuma mai kyakkyawar zuciya, shiyasa kawai sai yayi murmushi yana kamo hannunta yace

"Tabbas Maryam ke mutuniyar kirki ce, san nan ke ?ar aljanna ce Maryam, kuma wan nan shawarar da kikayi shine dai-dai Maryam, Allah yayi miki albarka, kuma kishirya Insha Allah wani satin zaki koma dan kayan furnitures kaWai ya rage a siya.

?an murmushi Maryam tayi tanajin daWin addu'ar da Nasir yayi mata, dan abune mai kyan gaske ace mijinka na saka maka albarka.

Yanzu wane kalar kayan kikeso a zuba miki a wajen naki? Murmushi Maryam tayi tace "duk wanda ka zaSamin zanyi farin cikin dashi, hira sosai Maryam da Nasir sukayi a wan nan karen wanda rabon dasu yi irinta tunda kafin Rashida ta dawo, amma duk da wan nan hirar Maryam ta?i bashi dama daya keSe da ita.

*Rashida*

Kallon boka cika aiki tayi tana cewa "bakaga koran karan da yayi minba boka, nifa nafara sarewa da wan nan aikin gaskiya, gashi sai Sarnar kuWi nakeyi akai akai kuma babu biyan bu?ata, nifa a yadda nake gani kamar aikin nan bai kama Nasir ba dan wani irin wula?anci yake shukamin yanzu

Zazzare ido boka cika aiki yahau yi yana soshe soshen jiki, san nan daga bisani yace "tabbas bake babu barin gidan nan muddin kikayi Abu Waya, amma indai bakiyi ba to wallahi barin gidan nan kamar da ?asa, san nan sai Nasir ya wula?anta ki ya tozarta ki, dan Wallahi ?arshen ki bazaiyi kyau ba dan sai kin ?are dayin bara akan titi..

Da sauri Rashida ta sharce gumi har tana haWawa da dafa cinyar boka cika aiki, bata an kara datayi kato Saraba sai dataji yafara shafa jikinta san nan ta lura kusa dashi take zaune har hannun ta nakan cinyar sa, da sauri Rashida tayi baya tana girgiza kai, rai boka cika aiki ya haWe yace "maza tashi ki tafi tunda ba Abinda yakawo kike nema ba, to kisani Abu Waya da bikiyi ba shine rashin bani kanki da bakiyi ba, kuma muddin kinason kisamu biyan bu?ata tosai nayi mu'amala dake ta awa huWu san nan ne zaki samu biyan bu?ata, idan kuma baki yarda ba tashi kifita ki bani waje kafin na saka Wan autan aljani ya cire zuciyar ki ya cinyeta Wanya a gabanki.

Rawa jikin Rashida yafara duk da bayaune rana ta farko data bawa boka kanta akan biyan bu?atar taba, amma a ranta jitake Abinda take babu kyau kamar idan nasir yaji ranshi zai Saci yayi fushi da ita, amma kuma wata zuciyar tace mata ai koma menene kikayi shiya jawowa kansa, tunda kuna zaman zaman ku lafiya yaje ya kutso wata cikin rayuwar ku tabi ta damal mala muku rayuwar jin daWi da kukeyi, kawai kiyi komai ba komai ba indai zaki samu biyan bu?ata kiga bayan Maryam.

Da wan nan tunanin Rashida ta mallakawa boka cika aiki ragamar ta yayi yadda yaso da ita, awa huWu yace zaiyi amma rashin test Win Rashida yasa ko awa biyu baiyi ba ya janye jikinsa yakoma gefe yana danna mata harara.

Sai da komai ya lafa san nan suka dawo wajen aiki boka cika aiki ya kalleta yace "dole mijinki ya dunga wula?anta ki Rashida, haba, aba salam kamar an sulala kaza babu gishiri da maggi, gaskiya idan kin bar nan ki samu maganin matan dazai gyaraki malama, idan ba hakaba kuwa kina ganin mata suna shagali banda ke, sai ya wulla mata wani ?ulli dake tsumman yadi a ?ulle yace "idan kinje gidan ki barbaWa masa a cikin abinci yaci dashi, ammafa kaWan zaki zuba saboda yanada yaji sosai, sai yabata wasu ?ullukan a cikin wani kalar yadin guda biyu yace "wan nan ki Wau Waya ki bunne a cikin falon naki Waya kuma ki bunne a cikin Wakin kwanan ku, muddin kikayi yadda nace to Nasir bazai ?ara tada zancen kibar gidan nan ba.

Da sauri Rashida ta kwashe magun gunan tana susa dan sotake taje tayi wanka dan gaba Waya jikinta ya Wumame da ?ai?ayi da warin wani turare marar daWin sha?a. Amma haka ta daure tace "to boka wane magani za'a bani na matsi wanda zan dunga matsawa Saboda WanWanon nawa ya dawo?

Dariya boka ya saka yace "ai kin riga kingama salamcewa Rashida, kawai kije ki rungumi wan nan asirin dana baki kuma kiyi biyayya, domin a zahirin gaskiya wan nan magun gunan da bokaye barkatai suka baki kika dunga matsawa sun rigada sun lalata miki nama dan haka sai dai ha?uri.

Rausayar dakai Rashida tayi,san nan tatashi zata fita daga ?ar bukkar tasa boka cika aiki yace "ke malama baki biya kuWin aikinki ba, maza zubosu anan ki wuce , yafaWa yana nuna mata wani ?o?o mai shegen girma, kamar Rashida zatayi masa musu kawai kuma sai tabuWe jakarta ta ciro bandir ?an dubu Waya ta jefa a ?o?on san nan ta fice tana jefa masa Allah ya isa a cikin ranta.

Tana fita boka ya kyalkyale da dariya yace "shege ni Zubairu, Allah ka shirye ni don Allah, Wallahi inason daina wan nan harkar amma shegiya talatu ta?i barina kullum dulmiyani take a cikin halaka, sai kuma yaWan le?a yana hango Rashida tana tafiya tana susa, ?asa ?asa yayi da murya yadda bazata jiyoshi ba yace.

Wan nan ?ullin danace ki barbaWa masa acikin abincinsa fa yajine mai Wan banzan faWa, gashi kuma babu magi da gishiri a ciki dan haka ki zuba kaWan, sauran ?ullin kuma kiyafeni wallahi ?asa na ?ulla, yafaWa yanajan baya tare da fashewa da dariyar mugunta.

Rashida tana zuwa gida batayi wata wata ba ta faWa wanka tana kwalawa zita kira akan ta Waura mata ruwan zafi a gas, sai da ta saSe jikinta sosai ta anbula turare san nan tafito ta shimfiWa dadduma domin tayi sallar magariba ta ro?i Allah yafiya akan Abinda takeyi dan ita kanta tasan ba dai-dai bane, dan Allah mai yafiya ne a kowane irin laifi.

Duk irin bar baWen da boka cika aiki yace Rashida ta gunar saida ta gunar, dan dakanta tasamu ta sassa?e wani tile dagacen ?arshen bango tayi rami ta zura wan nan ?ulin guda Waya, shima Wayan haka tayi masa san nan tazo ta barbaWa na barbaWawar a cikin abincin.

Dan haka shiyasa ta dunga kallon Nasir a lokacin da yake cin abincin domin taga yadda fuskarsa zata tunana, bataga komai ba amma kuma bayan yagama cin abincin nasa sai ya kalleta yace.

"Kin gama parking Win kayan ne? Rass gaban Rashida yafaWi san nan a hankali tace "Eh na haWa .

Kallon yadda tayi maganar cikin karaya ya sakashi murmushi yace "toki maida kowanne inda yake kinfasa barin gidan, zaki zauna itama Maryam zata dawo gidan nan ta zauna amma a Wayan part Win, duk da ran Rashida yayi fari kuma ta tabbatar bata bawa wani ?ato kanta a banza ba, amma wallahi taji bala'in ba?in ciki da Nasir yace zata zauna a wancen part Win, dan haka sai Rashida ta gyara zama tace

"To tunda daman nan ne part Win da takeso mai zahana ta dawo nan ni kuma na koma cen? Kallon bakida hankali Nasir yayiwa Rashida yace.

"Ai har abada Maryam bazata ?ara saka kuncen kiba Rashida, ko kuwa kin manta idan kika tashi daga nan Maryam ta dawo kunce ne? Ai wuce nan yarinya, yana faWin haka ya tashi yabata waje tare da shigewa Wakinsa.

KafaWa Rashida ta Waga domin ko banza aiki yaci tunda har Nasir ya tsallake bar baWen datai masa kuma ya kama shi tunda gashi yace ta zauna tafasa barin gidan.

*KUTSE*

*PAGE 67*

*NA*

*MOM HANEEF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

Kwanci tashi babu wahala a wajen Allah, yau kimanin kwana biyu kenan da Maryam ta haifi zan kaWeWen Wanta mai kama da baban sa sak kamar yayi kaki, babu Abinda Maryam zata cewa Allah sai Godiya daya rabata da cikin nan lafiya duk da alkabi da kuma son cutar da cikin ?arara da Rashida take nunawa, bazata manta washegarin data dawo sabon gidan ba, ranar tana tunanin Rashida batayi barci ba dan ?arfe huWun asuba Maryam na zaune akan sallaya tana ganawa da Ubangijin ta sai kawai ganin Rashida tayi a tsaye a kanta tana yayyafa mata wani ruwa, zumbur Maryam ta mike tanajan a'uzubikalli matullahi tammat min sharri makalak, kuma tana wan nan addu'ar Maryam taga Rashida ta wullar da kofin dake hannunta tana sakin ?ar ?ara da kuma yarfe hannu, kuma babu kunya babu tsoron Allah sai Rashidan ta wuce tafita daga part Win baki Waya ko tsoron daren bataji.

Da yake Nasir ba a wajenta ya kwana ba yana wajen Rashida shiyasa bata damu data sanar dashi Abinda yafaru ba, washegari kuwa yana shigowa sai Maryam ta zauna dashi tace tanason ya karSi duk wani mukullin part Winta dake hannun Rashida ya dawo mata dasu hannun ta, Nasir bai tsaya bin ba'asi ba dan a wajen hankali da tunani tuni yabawa Maryam lambar yabo sai kawai ya amsa mata da to, kuma sanin halin Rashida yasa bai tambayeta ba kawai yaje inda mukullan gidan suke baki Waya ya kwashe na Sangaren Maryam san nan ya ajiyewa Rashida nata itama Maryam yakai mata nata, haka duk son kakalo rigima da Rashida takeyi Maryam bata saurarenta dan ita ibada takeyi ba salon zubda mutunci ba.

Kafin Maryam takai ga haihuwa duk wani rashin mutunci da wani salo nason Satawa Maryam babu wanda Rashida batayi ba saboda ganin ta Satawa Maryam rai, ita dai Maryam sai dai tayi dariya kawai dan lambar yabo ta fannin mahaukata tuni Maryan ta naWawa Rashida kambunsa, haka a wajen Nasir ma Rashida duk yadda taso taci galaba akansa abin ya faskara, tabi malaman tabi bokaye na gaibu dana gaskiya amma abin sam ya gagara, badan komai ba sai don shima yanzu Nasir ya gane cewar dole ne ya tsaya kan ?afafunsa da addu'ar kariya shida iyalansa kamar yadda Ramadan amini nagari yabashi shawara a lokacin da Nasir Win yaje neman sulhu dashi, dan sosai Ramadan Win yaWau fishi dashi ko wayarsa ya daina Wagawa duk kuwa da kiran dazai masa, ?arshe ma Ramadan Win blocking Win layinsa yayi dan tuntuni ya shaida masa muddin ya maida Rashida to zumuncin su yazo ?arshe.

Koda yaje Win dakyar ya shawo kan Ramadan Win ya saurare shi bayan yayi masa al?awarin ri?e addu'a a duk yanayin daya tsinci kansa, shiyasa yanzu shima Nasir yayi mugun gagarar Rashida duk kuwa da ?o?arin ta na sake samun galaba akansa.

Ta bangaren yaran Rashida kuwa tunda suka dawo gidan suna wajen Maryam sun?i komawa wajen Rashida, dan haka wataran Rashida ta murzawa idonta kwallin rashin mutunci duk da daman ba mutuncin ne da ita ba tashige wajen Maryam tana taunar cingam kamar tsohuwar karuwa ta tsaya kansu Maryam ?erere suna cin abinci san nan tace.

Kutaso kuzo ku wuce kutafi gurin uwarku.

Kallon kallon aka shigayi tsakanin halima da sauda sunajin haushin maman nasu na?in tsayawa takula dasu da tayi, sai yanzu zata wanizo tace wai su taso su tafi? Ma?ale kafaW halima tayi tace "nidai bazan bikiba a wajen auty zan zauna.

Ganin Abinda halima tayi itama sauda sai tama?ale kafaWar ta tace itama awajen auty zata zauna.

Cikin Sacin rai Rashida ta lailayo ashar tana cewa "dan bura ubanku ita Maryam Win uwarku ce? Zaku taso mutafi kosai na tsine muku albarka?

Sai a lokcin Maryam tayi magana tace "subhanallahi, ki tsine musu albarka saboda me? A'a wallahi, kobana kusa baki isa kiyiwa yaran nan bakiba balle ina zaune, sai ta kalli su halima tace

Yaran kirki kutashi kuje wajen maman ku kunji? Ai ina cikin gidan duk sanda kukaso zakuzu ku ganni nida ?annen ku, Maryam ta faWa tana nunasu hassan da husaina, kumama gashi ai na kusa kawo muku wata ?anwar nasan zakuyi farin ciki ko? Sai a lokacin Rashida tayi magana tana wani juya idanuwa tace "idan kin haife cikin ba?

Murmushi Maryam tayi tana tsattsare Rashida da ido tace "tabbas kuwa zan haifeshi Rashida, kuma Insha Allah haihuwa mafi ban mamaki wanda ko ?uda yana barci zanyi ta balleke shaiWaniya.

Cikin zafin nama Rashida tayi kan Maryam tana maimaita Abinda kika ce dan uwarki.

Tsam Maryam tatashi batare data gama cin abincin ba tayi hanyar Wakinta tana sakarwa Rashida murmushi na banida lokacin ki.

Zagi ta uwa ta uba Rashida ta dunga surfawa Maryam kamar zata ari baki amma sam Maryam bama jinta takeba dan tuni ta shige Wakinta ta fara karatun Al?ur'ani, sai da Rashida tayi bala'in tayi masifar san nan tagaji tayi shiru dan kanta ta tasa ?eyar su halima suka wuce sashenta suna matsar hawaye.

Suna shiga sashen nata tafara mammarin su akan wallahi duk sanda ta ?ara ganin koda ?afarsu ne tashiga wajen Rashida sai ta SaSSala musu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login