Showing 75001 words to 78000 words out of 182745 words

Chapter 26 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

108

da wani abin nunawa balle ta kara da jinina."

Ta inda take shiga daban da inda take fita. Ran Ahmad ya gama Saci da su ka gama wayar. Yana jiran dawowarta ya nuna mata kuskuren sanya Mami tayi masa irin wannan faWan.

Bayan Mami ta gama dashi kan Salwan ta koma tana yi mata nata faWan na rashin Waukar shawararta. Kissa ba ?aramar makami bace a wajen mata.

"Ki bari sai kamar shaWayan dare ki kira shi ki gigita shi da kalamai masu daWi."

Sunkuyar da kai tayi tana murmushi.

"Ki nuna masa yafi kowanne namiji ba tare da kin zubar da ajinki ba."

Sai da ta gama kwasar huWuba sannan ta shige Waki. Ta gama komai da wuri ta zauna jira. ShaWaya da kwata na dare kuwa ta doka kira wayar Taj.
RAYUWA DA GI?I 21




Batul Mamman=ؖ?



This page is sponsored by _Scentmania_ by Sana. A Kano take, amma ?amshi babu ruwansa da gari ko ?asa. Wuyarta ciniki ya faWa. Za ku sami undiluted oil perfumes Winku a duk inda ku ke. Bayin Allah babu cika baki. Talla ne daga abin da na gani, na gwada kuma na amince dashi. Gashi babu ruwanki da jiran sai asusunki ya cika ya tumbatsa kafin ki shiga jerin mata masu aji. Da dubu biyar ma za ki haWa kwalabe daban daban ki gigita waWanda ya halatta su ji ?amshin jikinki da yawan tambayar wane irin turare ne wannan. Scentmania by Sana, na Naana Hauwa'u queen of oil perfumes. Domin neman ?arin bayani a tuntuSeta a wannan layin 07065525409 .





***

Da farko da taji ?arar wayar cikin baccin da ya fara Waukarta tsorata tayi don ta manta da ita. Niyyarta ta barta ta gama sai ta kashe, ko waye ya kira da kansa. Ita ba mai son amsa wayar mutane bace. Wani kiran ne ya sake shigowa immediately bayan na farkon ya katse. Ta daure ta wartsake idanu ta kalli sunan mai kiran SALWA B. Wani irin tunani ne ya shiga karakaina a ?o?on ranta. Meye ma'anar B Win? Bichi, Bunkure? Ba dai brother bane tunda sunan mata ne. To ko dai baby yake nufi? Ko bestie? Haba! Zuciyarta tayi wani irin kumburi ta taso mata har wuya. Harda wani Waci-Waci kamar ta tsotsi flagyl. Mantawa tayi da maganarsu da Abba a karo na biyu yau ta amsa kiran ido rufe. Garin sauri harda _record_ ta danna a rashin sani da ta mannata a kunnenta.

"Ya Taj na tasheka ko?"

Salwa tayi magana da sassanyar murya da ta sha kwaskwarima domin yin tasiri a zuciyar wanda ake yiwa.

"Ayya ba shi bane. Ya manta wayar ne." Hamdi ma ta mayar da zu?a??iyar murya.

Ba shiri Salwa ta zabura ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi. Da ta gama shirin yadda za ta dinga mirginawa hagu da dama saboda daWin murya da hirar da za su yi da Taj.

Gabanta na faWuwa ta ce "Wace ce ke?"

Tana buWe murya normal, Hamdi ta gane wannan wayar ba ta ?ar uwa bace. In ma ?ar uwar ce to tabbas cousin ce.

"Suna na Hamdiyya." Ta ce a kunyace "manta wayar ya yi a wajena Wazu."

Tsakin Salwa taji wanda ya yi mata ciwo matu?a kafin ta ji ta ce,

"Wai ?ar gidan Wan daudun da ya aura last week ce?"

"Laahhh, ashe kin sanni."

Hamdi ta amsa da sauran fara'a a muryarta kamar gaske. Bata so tayi saurin kwafsawa kuma ya kasance Salwan ?ar gidansu ce.

Cikin huWubar Mami harda kada ta ragawa yarinyar da ya aura. Tunda ance musu sakandire ta gama sun tabbatar babu wayo da wayewa a tare da ita. Tsorata ta da nuna mata ita Win ba komai bace zai taimaka sosai wajen samawa Salwa ?anci idan ta shiga gidan Taj.

"Da alama kina da rawar kai. To amma ba zan hana ki ba. Lokacinki ne. Ki dai sanya a zuciyarki cewa nan ba da jimawa ba wadda ta fi ki son Taj za ta shigo rayuwarsa."

Hanci Hamdi ta ja kamar mai shirin kuka "Anti Salwa nayi muku laifi ne har ku ke son bashi wata daga aurenmu? Ita wadda za ku bashi Win bana jin ta kai ni son shi. Don dai bamu haWu bane da kema sai kin yaba min. Tarbiyya da iya kula da miji duka Wan daudu da miskiniyar da su ka haife ni sun koya min."

Amsar Hamdi ba ?aramin tayar mata da hankali tayi ba. Kai tsaye ta faWa mata magana ta rama wadda tayi mata. Tana so ta ce mata ita da kanta za ta auri Taj amma gani take faWin hakan zubar da aji ne sai ta gimtse fuska cike da takaici.

"Ni ba ?ar gidansu bace."

"Ikon Allah. Kuma naga ya yi saving sunanki da Sister Salwa? Cousin Winsa ce ke kenan?"

"Sister Salwa???" Ba?inciki ya mamaye zuciyar Salwa a lokacin da take nanata kalmar "haka ya rubuta?"

"Uhm, da capital letters."

Tsanar Hamdi ta sake ruruwa a zuciyarta yayinda ta bata amsa.

"To ko ma dai mene ne kada ki saki jiki don ba zan zauna da kishiya ba."

"Lahhhhhhh, ko ke ce wadda ta suma ranar aurenmu?"

Salwa ta haWiyi yawu da ?yar saboda jin da alama suna da yawa masoyan nasa "suma kuma? Shi ya ce miki akwai wadda ta suma a kansa?"

"Ba ke bace kenan." Hamdi ta faWi da rashin damuwa "Allah Sarki. Kada ki damu fa. Ni bani da matsala ko ya ce zai ?ara aure don na san a danginku dole a bashi wata. Tunda na samu na shiga sai dai in ce Allah Ya bawa mai rabo sa'a. Mu kwana lafiya."

Katse kiran tayi ta ajiye wayar a kusa da tata tana murmushi. Za ta so ganin idanun Salwan nan. Irin yadda taji tana sauke numfashi da tana bata amsa ya kusa sanya ta dariya. Ta riga ta san mahaifinsa baya sonta. Abba kuma ya faWa mata mahaifiyarsa tana maraba shi yasa ma ta nemi ganinta. Duk da haka ba sakin jiki zata yi ba. Dole dama ta sa rai da ganin wula?anci kala kala kafin ta bar musu danginsu. Ko banza dai bata bari an ?untata mata ba ta ce a ranta tana faWaWa murmushinta. Zee ta kalla tana ta sharar bacci. Ina ma idonta biyu. Yau da sun mannawa wannan cousin Win hauka. Don Zee dake sakandire ma ta fita sanin irin waWannan abubuwan. Zamani na turawa, na baya suna zuwa da wayo da dabarun da waWanda su ka gabacesu basu taSa sani ba. Bata san lokacin da tayi bacci ba saboda yadda abin duniya ya dameta daga baya. Shin ?an mata gare shi ko kuwa a dangi ake son aura masa daidai da shi? Zuwa gidansu jibin nan kuwa shawara me kyau ce?

Da kuka Salwa ta kwana. Ba kuma na auren Taj ba wannan karon. Yadda yarinyar da ta raina ta Sata mata rai ba tare da ta rama ba ne yake damunta. Wai bata da matsala ko zai sake aure. Kenan ma alfarma za ta yi mata ta bari a aurota.

?wafa tayi "sai zaman gidan Taj ya gagareki indai ni ce."

***

Da Abba zai fita kamar yadda ta faWawa Taj ta bashi wayar. Ya dubeta da kyau ganin fuskarta shar babu damuwa a tare ds ita.

"Hamdi kada ki manta da maganarmu. Bana son abu ya yi nisa Alhaji yasa a Wora miki zawarci mai ciwo. Gara ma ace ba kya son shi zai fi miki sau?i."

"In sha Allahu Abba" ta faWi tana mai sunkuyar da kai don ta san jiya dai bata wani taSuka abin kirki ba.

"Garin yaya ya manta wayar?"

"Ina jin daga aljihunsa ta fito. Sai bayan tafiyarsa na gani."

"To shike nan. Ki kula dai. Sai na dawo." Tsayar da ita ya yi kafin ta koma ciki "wannan hijabin Hamdi gaskiya ko dai ki ha?ura dashi ko kuma kada ki yarda wani ba?o ya ganki da shi."

Da sauri ta kalli jikinta "Abba wani abin ya yi?"

"Ki duba madubi."

A dawo lafiya tayi masa a soron da su ke tsaye su biyu sannan ta koma ciki. Hannu ta Wora a ka da ta ?arewa kanta kallo. A haka fa ta fita wurin Taj jiya. Da ta tuna an Wauke wuta ne ma ta sami nutsuwar kama aikinta na yau. Zee ce da girki idan ta dawo daga makaranta. Ita kuma wanke wanke da shara. Halifa kuma kullum shi ne da wankin banWakuna da sharar tsakar gida zuwa soro da harabar gidan. Duk wanda ya san gidan Abba ya shaide su da tsafta. A kansu Anti Labiba ta ?ara gane cewa babu wata ?wa??warar ala?a tsakanin talauci da ?azanta. Kowanne zaman kansa yake yi.

*

Yana cire lock Win wayar abin da ys fara gani shi ne (save - discard) na recording call. Ya san da wuya Hamdi ta iya yin kira da wayarsa tunda yatsansa ne mabuWin wayar. Amma wa ya kira shi ta Wauka har su ka kwashi waWannan mintuna suna magana? Saving ya yi sannan ya shiga call log. Nan ya tarar da missed calls Win Salwa kafin wanda aka Wauka.

Da saurinsa ya nemo recording Win ya shige office Winsa ya kunna. Shi kaWai ya dinga dariya. Hamdi bata da dama. Ta kuma burge shi. Bata cikin irin ?an matan nan da su ke zama a taka su son rai su shiga Waki su yi kuka. NishaWi fal zuciyarsa. Salwa ce ma yaga dacewar ya taka mata burki kafin ta kai su ga Sacin ran da wani zai ji su. Kiranta ya yi kamar tana jira ta Wauka. ?in magana tayi gudun maimaicin abin da ya faru jiya. Sai da ya yi sallama ta saki rai ta amsa ta gaishe shi.

"Kin kirani jiya ashe. Hope ba matsala bace?"

"Eh wallahi." Ta gyara zama tana murmushi "babu wata matsala. Kira nayi kawai mu gaisa. FaWa maka tayi na kira?" Ta ?arashe maganar a hankali.

"No, missed calls Winki na gani. Sai kuma naga alamun kun yi magana da Babe Wina har na kusan five minutes. Lafiya dai ko?"

Wai Babe? Siririn tsaki tayi kuma yaji. Ba don yana son a yau ya da?ile komai nata ba da ya ajiye wayar.

"Na ce lafiya ko?"

"Naga kwana biyu baka nema na ne."

"In ce miki me Salwa? Muna gida Waya nayi aure ki kasa yi min fatan alkhairi."

Tsayar da zuciyarta tayi wurin daina kwana-kwana a kansa.
"Ohhh, wai har kana saka wannan a jerin aure Ya Taj? Ba ance babanta Wan ..."

"Yes, Wan daudu ne a da. And one of the most wonderful people alive today. Mamanta kuma is physically challeged. Polio ya yi affecting posture Winta sosai."

"Ta faWa min jiya" ta ce don bata ga amfanin maimaitawar ba. Mutane irin waWannan mene ne abin tin?aho dasu? Idan iyayenta ne za ta yi bakin ?o?arinta wurin guje musu don ma kada ace ta san su.

"Ina sake faWa miki duk da na fahimci kin sani ne don ki gane cewa duka waWannan abubuwan da wasu ke gudu ni su ne su ka sa Hamdi ta zama the most special girl alive. I love her Salwa. Bana kuma son duk wani makusancina ya dinga ganin kamar wannan abu ya isa dalilin da zai rageta a matsayin mace. She is everything I want."

"Kirana kayi ka ci min mutumci saboda ina son ka? To my face ka ke faWa min kana son wata?" Salwa tayi magana da rawar murya.

"To your ears dai. Amma in kina so zan maimaita miki in mun haWu. Ba ke kaWai ba kuma, duk family Win Maitakalmi, babu wanda zan ragawa akan mutumcin matata."

Iya wuya ran Salwa ya gama Saci. Za ta iya rantsuwa basu taSa wata doguwar hira da Taj a waya ba idan ta kira shi kamar wannan. Saboda ?ar gwal ta kai masa gulmar wayarsu ta jiya.

"Abin da Yaya Ahmad ya ce Alhaji da bakinsa ya gaya masa wata uku ya bawa babanta ya kashe auren don ka koma gida. Na san akan mace ba za ka zaSi dawwama a haka ba" Ta faWi kai tsaye don da alama kukan ba zai kaita ko ina ba "Ya Taj zamu yi aure kuma za ka bani ha?uri akan wula?anta soyayyata."

Ita ta fara kashe wayar ta barshi da wani irin sanyin jiki. Bai taSa zaton yayan nasu zai Wauki sirrinsa ya faWawa ?anwarsa ba. Kowa matsayinsa daban. Maganar da ko Kamal bai samu ya faWawa ba saboda rashin lafiyarsa. Su Innarsa da Amma da sisters Winsa duk basu sani ba. Shi ne zai sanar da Salwa? He felt disappointed and betrayed. Tun farko abin da ya yi ta gudu game da ita kenan. Tunda baya so dole yayan nasu ya sami Sangare guda da zai fi tausayawa. Sai ya musgunawa Wayan kuma? Duk da haka ya ?udurce ajiye abin a ransa har ya gano yadda aka yi taji zancen.

Bayan sun kammala wani emergency order na taro an fitar da abincin ya tafi wurin Kamal. Mutumin da kullum idan ya shiga shagon nasa har mita yake masa na rashin hutu yau a zaune ya same shi yana gyangyaWi. Ya kan ce masa mene ne amfanin ?an zaman shagon dake nuna kaya da waWanda ke wurin biyan kuWi. Shi kaWai ya yi nan, ya yi can. Sai gashi hayaniyar kwastomas bata hana shi baccin ba. Yana zuwa hannu ya kai ya taSa wuyansa da goshi. Abin da ya farkar da Kamal Win da sauri don ji ya yi kamar an Wora masa ?an?ara. Tsigar jikinsa har tashi tayi ya buWe ido a firgice.

"Happiness kaji jikinka kuwa? Tashi mu koma asibiti" Taj ya ce yana kai hannu gefe ya Wauko masa wayarsa.

Hamma Kamal Win yayi "bacci ne fa. Bari na shige ciki na kwanta" ya nuna nasa office Win.

"Kada ka raina min hankali mana. Bacci ne yake kawo zazzaSi? Muje don Allah."

Wasa ya mayar da maganar ya ce "Sai dai in kai ka. Dama na faWa maka yau Wanin motarka zanyi. A adaidaita sahu ma na taho saboda son banza."

"In ka bari mu ka je asibiti Allah zan yarda mu yi musanye. Saboda na san kai mayenta ne na saya."

Wani irin kallo Kamal ya yi masa. Taj is just selfless akan duk abin da ya shafi Kamal. Abubuwan da ya yi masa iyayensu basu sani ba ba za su ?irgu ba. Ciki harda bashi jarin da ya gina boutique Winnan. Ya rufa masa asiri a lokacin da Alhaji ya bashi miliyan goma yaja jari. Allah Ya haWa shi da ?an damfara su ka wanke shi. Abu kamar rufa ido. Ya shiga ?uncin rashin sanin yadda zai tunkari Alhajin. Kawai sai Taj ya ce ya sayar da filinsa da su ka saya tun da daWewa. Filin da Mama take jira a fara gini. Filayen biyu su ka kama miliyan shabiyar. Ko ?wandala Taj bai karSa ba duk yadda ya so hakan. Ya kuma so ayi rubutu idan ya samu zai biya nan ma Taj ya ce kyauta ce. Baya fatan har abada a sake tada zancen.

"Tashi mana"

Muryar Taj ta dawo dashi daga duniyar tunani. Mi?ewa ya yi cikin dauriya ya ce masa mura ke son kama shi. Shi yasa yake zazzaSin.

"Ni kuwa sai nake ganin kamar kana Soye min wani abu Happiness. Kwanakin nan kamar fa baka nan. Komai ni kaWai nake yi."

"You are married Happy. Ya kamata mu fara rage wasu abubuwan. Da banyi tunanin ba sai da Abba ya ankarar dani."

Taj ya taSe baki "yanzu zancen Mal. Sule har wani abin Wauka ne?"

"Ai kuwa dai ya fi mu gaskiya. Nan gaba kaWan sai kaji ana Malama hide my ID. Brother Win mijina kullum suna tare. Ko unguwa zamu sai ya kira Wan uwansa. Bamu da wani lokaci irin na mata da miji saboda ya kankane komai. Don Allah a bani shawarar yadda zan Sullo musu ba tare da mijin nawa yaji haushi ba."

Dariya sosai Taj ya yi.
"Kamal mai malaman ig. Wato har salon tura sa?on ka iya. DaWinta dai ba Hamdi bace za ta yi wannan. Daga ji Doctor ce ta fara ?orafi. Tell her I'll make myself scarce in kun yi aure. Ayi soyayya lafiya."

Daga nan sai zolayat juna. Kamal ya dage va zai je asibiti ba wai yunwa ma yake ji. Cikin Happy Taj su ka koma. Kamal ya yi odar shinkafa da gasasshen kifi. Kamar yadda Taj ya koyo, yawancin abincim Asia duk da hannu ake ci. Masu zuwa ko sun so gayu suna fara ci sai kaga an yi yadda yake a hoto da bidiyo da suke a lungu da sa?on wajen ana ci da hannu hankali kwance.

"Kawo masa kaza" Taj ya ce da waiter Win.

"Ban gane ba. Ka dai sanni da kifi ko?"

Wani article Taj ya nuna masa sannan ya tura masa a waya. A ciki anyi bayanin yawancin abincin dake kawo allergy. Akwai gyaWa da dangoginta. Kifi, kayan da aka sarrafa daga madara, ?wai, kantu da kayan fulawa.

"Za ka daina cin duka. A hankali sai mu dinga gwada Waya muna gani. Wanda a kansa reaction Winka ya dawo kaga mun san shi ne. Nima zan daina ci don ma kada ka ce mugunta na shirya maka."

Yawun bakin Kamal Waukewa yayi. Ya shiga damuwa amma dole ya mayar da ita dariya. Sam baya jindaWin Soye Soyen nan. Amma yanzu da zarar sun sani ?arshen duk wani farinciki na gidansu ya ?are. Baya son ya zama silar daina walwalar kowa akan lafiyar da kuWi kawai ba za su iya saya masa ba.

Abincin da yake masa WanWanobda magani saboda rashin jindaWin abin da yake yi ya dinga tutturawa harma yafi Taj ci.

***

Office Win an rubuta Dr. Kubra Hayatu a jiki. Wani private asibiti ne mai tashe na mata da yara da su ka buWe ita da ?awayenta biyu. Wurin yana samon mutane fiye da zato saboda ?warewar aikinsu musamman akan mata. Zaune take tana harhaWa wasu takardu kafin ta fita don ta gama shift Winta taji bugu a bakin ?ofar. Umarnin shigowa ta bayar inda wani matashi ya shigo ya gaisheta. ?aramin kwali da aka yi wrapping ya mi?a mata.

"Ban sayi komai ba. Bana tsammanin delivery." Ta ce masa.

"Ance na wani Kamaluddeen Hayatu ne amma ke ake so ki fara gani."

"Wa ya aiko ka?" Ta tashi tsaye.

"Idan kin duba ciki za ki gane. A tashi lafiya"

Fita ya yi kafin ta sake yin magana. Ta Wauki kwalin taji babu nauyi sai Wan girma. Ta jijjiga taji abu kamar magani. BuWewa tayi da sauri sauri. Sunayen magungunan da hotunan dake jiki su ka sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login