Showing 27001 words to 30000 words out of 182745 words

Chapter 10 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

74

yi mata.

"To ko mu zauna ke ki je?"

Diriricewa tayi don bata tsammaci furucinsa ba. Ta ce "Haba Yaya ba haka nake nufi ba."

Su na tafiya ta sake kiran Kamal ya ce mata jikin Taj da sau?i. Don ya ?ara rura wutar da ya fahimci ta soma cinta ya ce
"Yanzu dai ya gama amai wallahi. Ya galabaita sosai don ko zama ya kasa. Amma dai da sau?i za a ce."

"Kace ina masa sannu don Allah" ta ce da muryar kuka.

"Ban gane ba. Ba za ki zo ba?"

Da sanyin murya ta ce "Ya Ahmad ya ce na zauna."

Tausayi ta bashi ya daina Worata. Yana ajiye wayar ya yi murmushi "shege Happy. Daga zuwa ya yi Sarna a zuciyar ?ar mutane."

Wasa wasa sai da Taj ya yi kwana biyar aka sallamo shi. Kuma tun washegarin kwanciyar tasa kullum sai Salwa ta je. Duk wani motsinta Ahmad ya kafa ya tsare har ya tabbatar da zarginsa. Hankalinsa kuwa ya tashi don yana jiye mata abubuwa da dama.

***

Takarda ce cikin foolscap Hamdi take ta karantawa tun wajen kwana uku tana son haddacewa. Speech ne malamar English ta bata wanda za ta yi ra ranar taron. Cikinta har ?ullewa ya yi yau da aka kira assalatu saboda tana da tsoron yin magana a gaban mutane. Har aka gama yayin monitoci da mataimakansu da ma prefects bata taSa karSa ba. Komai na mutane gudu take. Sai gashi wannan karon Principal da kanta ta ce a bata. Wai jawabin godiya ne a matsayinta na overall student ta makaranta. Da shawarwari ga ?an uwanta Walibai akan hanyoyin bi domin samun nasara.

Ga dai takarda ko daga bacci ta farka za ta iya kawota tas da ka, amma da zarar tayi tunanin mutanen da za ta fuskanta sai taji kan ya koma fanko. A haka ta janyo jiki ta zo wajen taron tamkar mara lafiya. Ana tsakar gabatar da shirye shirye ta tashi kafin a zo kanta. Bayan Admin block taje ta sami wuri ta zauna tana ta bita kamar mai zuwa musabaqa.

*

A cikin dandazon mutanen da su ka zo taron harda ?a?a da jikokin Alh. Hayatu Sule. Akwai jikarsa Firdaus ?ar wajen babbar ?arsa Hajiyayye cikin masu fita. Yarinyar mutuniyar Taj ce sannan bata san ya zo gari ba. Rabonta da shi tun tana ?ar ?arama. Shi yasa da Hajiyayyen ta gayyaci ?an uwanta zuwa graduation shi ya fara amsawa zai je. A cikin hayaniyar programs Win da ake gabatarwa da hirar ?an uwansa yaji wayarsa tana vibrating. Sunan Amma ya gani ba shiri ya tashi yana neman wurin da zai iya amsa wayar ba tare da hayaniyar ta hana shi jin me take cewa ba. Kamar ance ya kalli damansa ya hango wata yarinya tana tafiya da sauri sauri ta nufi bayan Admin block. Sanye take da ankon ?an graduation Win da gown Winsu. Ta ri?e hular a hannu. ?aurinta na Maryam Babangida ya zauna as a kanta. Sai Wan mayafi da ta yafa a kansa ta rufe wuyanta da shi.

Numfashinsa kusan Waukewa ya yi da ganin yarinyar kamar yau ya fara ganin mace. A kallon farko ya iya tantance tsayinta da yake matsakaici. Fatarta da yake iya gani a fuska tayi daidai da wankan tawarWa da ake kiran masu sirkin fari da ba?i. Fuskar ya sake kallo wadda ta fizgi duk wani rational tunanin dake yawo a kansa. A cike take da duk wani abu da yake muradi a wurin mace. Ga ?arin kwarjini da nutsuwa da yake da ya?inin tana da su daga yanayin tafiyarta. Wayar da yake son Wauka tuni ya manta da ita har ta katse.

Kamar ana ingiza shi ya bi ta. Idanunta a rufe lokacin da ya hangota. Ta sanya hannu ta rufe kunne tana karanto abin da ta haddace.

Sannu a hankali ya dinga takowa gabanta har ya rage babu nisan kirki a tsakaninsu.

?amshin da Hamdi taji yana ta kusanto ta ne ya hanata buWe ido. A zuciyarta ta gama tsorata don an saba faWin akwai ?wan?wamai a bayan Admin block. Wai ba a ganinsu sai dare. To me ya fito dasu da hantsin nan lokacin da ake ta kai kawo a makarantar?

Taj na jin yadda ta ja numfashi ta kasa saukewa da ya matso. Ya saki murmushi.

"BuWe idonki."

Hamdi ta tsuke baki don in ta sami wuri akwai tsiwa. To yau dai aljanu za ta nunawa bata tsoronsu don kada su maketa a banza. Ta sha jin labarin idan baka nuna tsoronsu ba, ba sa yiwa mutum komai.

"An?i Win. Tsakanina da aljani nan gani nan bari. Na ri?e Ayatul Kursiyyu."

Dariya Taj ya yi a hankali ya a jin wani irin abu na bin jikinsa.

"Ni ba mai cutarwa bane so you can open your eyes."

Ido Waya ta Wan buWe a hankali ta tabbatar mutum ne sannan ta buWe Wayan. A lokaci guda idanuwansu su ka sar?e cikin na juna sai dai Hamdi bata iya zurfafa kallon ba ta kawar da kai. Babu abin da zai sa ta iya jurewa kallon idanun mutumin dake gabanta masu kaifi da su ka tsareta. A zuciyarta kuwa sai da ta kira sunan Allah saboda tunda take bata taSa ganin wani namiji taji ina ma ace....ba sai a kan wanda yake gabanta.

A daidai lokacin su ka ji sanarwa ta sipika.

"Bayan wannan gajeriyar diramar da za ayi mana mai taken Ilimi a Karkara, za mu saurari speech daga bakin overall student Win makarantar nan Hamdiyya Habib."

Wani haWaWWen ruWani Taj ya gani a idanun yarinyar gabansa. Da haka ya gane ita ce aka ambaci sunanta.

Takardar hannunta yaga ta kalla kamar za ta yi kuka.

"Kin taSa ganina?"

"A'a."

"Good. Ki yi imagining ni ne duka mutanen wurin can sai ki yi speech Win naki na ji."

Kamar ta ce a'a sai dai ta gyara tsayuwarta. Ta rufe ido.

"Open your eyes and think of ..." ya kalleta "Wa ki ka fi so a duniya?"

"Iyayena."

"To ni ne su. Ki sa a ranki su kaWai ne a wurin."

Sallama tayi da rawar murya ta soma da gabatar da kanta amma ta kasa faWin sunanta ma. Sai komawa baya take yi. Taj ya karSi takardar ya dun?uleta a cikin hannunsa bayan ya karanta a gurguje.

"Bayan godiya ga school da iyayenki za ki bawa students shawarar karatu. Do you realy need a paper to say all that?"

Hamdi ta ?ifta idanu "no."

"Then say what you truly want to say from your heart. You will be fine in sha Allah."

Haka kawai magana da shi ta sanya mata wata irin nutsuwa. Ta tattare doguwar rigarta sama kaWan ta dube shi da murmushi a fuskarta.

"Thank you."

Ya so sake cewa wani abu amma tunawa da ya yi tana bu?atar nutsuwa kafin ta iya yin abin da ke gabanta sai ya barta ta tafi. Ya raya a zuciyarsa idan an gama taron zai nemeta.
RAYUWA DA GI?I 10



Batul Mamman=ؖ?





***

Numfashi ta sake saukewa a hankali bayan ta karSi loudspeaker Win sannan ta rufe ido ta buWe da sunan Allah. Da ido ta lalubo Taj wanda har ga Allah tayi matu?ar mamaki da ta iya gano shi a cikin mutane. Bata sani ba ko hakan yana da ala?a da sahun gaba da ya dawo ya tsaya a jikin ?arfen canopy bayan kusan kowa a zaune yake. Ya yi mata murmushi gami da gyaWa kai kamar mai bata damar yin magana.

Mantawa tayi da kowa da komai ta yi ta?aitaccen speech Winta mai ma'ana wanda kalmominsa su ka dinga zuwa kamar daga sama. Wuri kuwa ya kaure da tafi. ?alibai ?an ajinsu su ka dinga kiran sunanta da ?arfi suna tafi. Haka kawai tauraruwarta ta ?ara haske a idanunsu tun bayan da ta kare martabar iyayenta.

Idanunta lokaci lokaci su na kan Taj har ta gama. Tana addu'ar gamawa taga Taj ya kalli wayarsa sai ya kara a kunne ya bar wajen. Za ta sauka aka dakatar da ita. Mai Girma hakimin Gabasawa da kansa ne zai bata kyaututukan da aka tanada dominta. Wani ?ayataccen kwando ne aka saka komai aka lulluSe da ledar ado aka Waure. Ya mi?a mata aka yi musu hoto tare sannan ya ce tasa kyautar ita ce kujerar Makka a Hajjin shekara mai zuwa in sha Allah.

"Allahu Akbar" Malamin da yake MC ya faWi, sai Walibai da iyayen yara su ma su ka amsa.

Murna a wajen Hamdi kuwa ba a cewa komai. Ta sauko daga stage Win idanunta cike da ?wallar zallan farinciki. Wurin da su Sajida su ke zaune ta nufa da sauri. Banda Sajida da Zee harda ?a?an ?an uwan Abbansu mata tsararrakinsu. Halifa ma ya baro Sangaren maza aka yi murnar tare da shi.

"Hamdi ina kayanki? Yaya ta ce kada mu yarda mu wuce ?arfe biyu nan."

Halifa ya ?ara da cewa "ana can ana haWa miki ..."

Kafin ya gama magana Zee ta dage ta doke masa ?eya.

"To fesal uban zance."

Hannu Hamdi tasa ta sa?alo kafaWarsa tana dariya "rabu da ita Halifa. Idan ka faWa min me ake yi zan bar maka duk ragowar provision Wina."

Da sauri Zee ta riga shi faWa.
"Walimar ?an gida za ayi miki"

"Kin dai ji kunya wallahi. Da kayan ?walama za a sayeki cikin sau?i" cewar Sajida tana taSe baki.

Kayan nata ta nuna musu su ka haWu da cousins Win nasu aka kwaso cikin ?an?anin lokaci. Ta koma cikin ?an uwanta Walibai aka yi hotuna harda malamai da musayar lambobin waya. Wasu harda kuka sosai. Ita dai bata yi ba don sabon da tayi da abokan karatun nata na iya lokacin jarabawa ne. Kewar rayuwar makaranta tafi damunta.

Duk abin da take yi hankalinta yana komawa ga tunanin ina mutumin nan na Wazu. Ta gaji da juyawa ko za ta gan shi Allah bai yi ba. Ga Sajida ta damu su tafi don ita za a yiwa faWa idan su ka Sata lokaci. Haka ta tafi zuciyarta tana begen sake ganin sa.

*

Wayar Amma ce ta sake shigowa, ita ce dalilin da yasa ya bar wajen. Kuka take yi wanda ya matu?ar tayar masa da hankali. Ta sanar dashi surukarta Hajjo ta ce lallai ta zaSi tsakanin aure da aiki amma ba za ta haWa biyu ba. Mijinta shekarsa huWu da ritaya ya koma gida gabaaya.

"Wai zaman me nake yi a nan. Taji an ce kai ma ka dawo."

"Ba ki faWa mata ba daWewa zan yi ba?"

"Nayi mata bayani duk ta?i ji. Yanzu don Allah 7 months to my retirement sai nayi resigning? An yi min adalci kenan?"

Ta maza ya yi bai nuna mata damuwarsa ba ya dinga rarrashinta. Da ?yar ta ha?ura bayan ya yi mata al?awarin zuwa Abuja ya sami Hajjo a gidan mijin Amma Win inda take zama da amaryarsa da yaransa.

Yana dawowa cikin ?an uwansa Firdaus ta janye shi tana ta nunawa ?awayenta Uncle Taj. Daga hoto Waya sai da aka yi yafi goma. Masu ?yasawa da yawa su ka kasa Soyewa. Shi dai ya biye mata ne kawai saboda ko a cikin jikokin gidan ita ce ?ar gaban goshinsa. Indai ana hutu tana yawan kiransa. Ana hoton da hayaniyar amma idanunsa yarinyar nan Hamdiyya Habib su ke nema. Da bai ganta zuciyarsa bata kawo komai ba tunda yana da ya?inin Firdaus ba za ta kasa saninta ba. Bai san Hamdi bata da ?awa ba. In ka cire sunanta ko sunan unguwarsu babu wadda ta sani.

***

Washegari jirgin ?arfe bakwai ya bi zuwa Abuja. Idan bu?ata ta biya so yake ya dawo a ranar don yanzu ya matsu ya koma wurin Amma. Da yake tun dare ya sanar da Daddy mijin nata cewa yana tafe, yana isa direba ya zo ya Wauke shi.

Iyalan gidan ba ba?insa bane tunda su na yawan kai ziyara America har Hajjo. ?an mata uku ne ?a?an kishiyar Amma da ake kira Anti. Su ma duka sun saba da shi. Dama tun zuwansa yana son tahowa Abujan su gaisa amma aiki ya hana. Tarba mai kyau ya samu daga Antin da ?a?anta. Sai da ya ci abinci ya ?oshi sannan aka yi masa ido Wakin Hajjo.

A hakimce kan kujera ya sameta ta kashingiWa tana danna remote.

"Wannan zuwan na san na Jamila ne ba don neman albarkar tsofaffi ba."

Taj ta sosa ?eya "tuba nake Hajjo tawa ni kaWai."

?ar tsohuwar ta yatsina fuska "bana son daWin baki. Ai da uwarka Jamila ce a gidan nan ba za ka saka aiki a gaba ka kasa zuwa ba."

Anisa babbar ?ar Anti ta nuna rashin jindaWin wannan furuci "abin kuma harda zagi Hajjo?"

"Fita ko ban guri ai ba kiranki nayi ba."

"Ya Taj na biyo."

Hajjo ta haWe fuska tana neman abin duka "Duk gidan nan babu wanda ya isa ya yi min iko da Waki saboda haka get out."

Taj da Anisa su ka saka dariya. Ita tana cewa "yeeyyyy, Hajjo ta tuno zama cikin turawa."

"Zan zagi babanki wallahi. Zo ki fice."

KafaWa Anisa ta no?e ai kuwa Hajjo ta bita da da?uwa hannu bibbiyu.
"Na iyayenki su uku."

Alamun rashin jindaWi Anisa ta nuna wanda Taj ya lura. Da ka ya yi mata ishara ta fita daga Wakin.

"Hajjo sai ki yi ta zagar mana iyaye saboda Allah? Kinga bata jidaWi ba daga Wan yin wasa da kakarta."

Lura tayi shima kamar bai jidaWin ba sai kuma ta saki fuska. Ita a dole Taj ne kaWai jikanta namiji na wajen babban Wanta. Tunda ya koma hannun Amma bata taSa canja masa ba. Saboda tun asali dama kakarsa wadda ta haifi Alhaji da ita ?awaye ne da su ka yi ?an matanci tare.

Ita ta fara zayyano masa ?orafinta akan zaman Amma ita kaWai a gida ga mijinta a wata uwa duniyar.

"Saura bai fi sati uku ba na koma in sha Allahu. Kuma zan zauna har tayi ritayar. Ai na san zamana ne sharaWin da yasa ki ka yarda ta cigaba da aikin."

Hajjo ta ?ara sakin fuskarta saboda Taj akwai iya tsara zance.

"Ka san ita mace bata tsufa da bu?atar kulawa. Yau ko ?wan fitila ne ya mutu wata idan babu namiji a gidan sai dai ta zauna a duhu."

Ha?uri ya sake bata da yaga ya samo kanta kuma ya yi mata bayanin gininsa da ya yi nisa.

"Shi uban taurin kan har yanzu baku daidaita bane?"

Dariya Taj ya yi. Kamar ba ita ta nuna ta daina ?an mintuna ?adan baya ba.

"An dawo kansa kuma?"

Ko a jikinta ta ce "Ai Hayatun ne akwai wuyar sha'ani sai ka rantse ni na haife shi. Don ita babar tasu haka take ba cas ba as."

"Ahhhh. Ni fa Hajjo zan tashi wallahi. Harda kakata kuma."

Yadda ya Sata fuska sai da tayi dariya. Daga nan aka kashe maganar dawowar Amma. Sai kuma ta sako zancen da yake cin ranta. Dama can ba dawowar Amman bace a gabanta. Tafi kowa sanin halinta tunda a gabansu ta tashi. Ita ce ma ta haWa auren nata da Wanta. Da gangan ta tayar mata da hankali yanzu kawai don Taj Win yazo. Don tayi imanin indai yaji ba zai ?asa a gwiwa ba zai zo neman sulhu.

"Tajo."

Babu yadda ya iya. Dole yake amsa sunan nan da baya son a faWi indai daga bakinta ne.

"Nace wai me zai hana ka nemi ?anwarka Anisa ku daidaita? Karatunta sai gudu yake har an shiga aji huWu a jami'ar nan."

Gabansa yaji ya faWi. Duk kirkin Hajjo kowa ya san rigimammiya ce ta buga misali. Yanzun nan sai ta yiwa mutum dabaibayin da zai sar?e wuyansa bai sani ba.

?ofa ya kalla tana gama maganar "Hajjo daina faWa kada ta zata gaske ne ta soma jin haushina don na tabbatar ba za ta rasa masoyi ba."

Shan kunu tayi harda yi masa da?uwa.
"?aniyarka Tajo."

Ya sunkuyar da kai yana sauraron sababinta.

"Da akwai wanin ai ka san ni ba mai yiwa jikoki shisshigi bace. Sannan na tabbata da daga cikin Jamila ta fito ba ma za ka ce komai ba."

Hankalinsa tashi ya yi ya mi?e tsaye yana Wan tausar kafaWarta.
"Allah Ya huci zuciyarki. Ba haka nake nufi ba."

"Za ka yi mata maganar ko na kirata yanzu?"

Gani ya yi za ta rushe masa ginin da bai fara saka tubali ba akan yarinyar nan Hamdiyya. Shi yasa da saurinsa ya ce ta bari shi zai yi.

"Al?awari fa za ka yi min."

"In sha Allahu zan yi mata magana."

Tana jin haka ta washe baki hankali kwance. A ranar da washegari da zai taho bata sake tada wata rigimar ba. Daddy kawai ta kira ta ce masa tayi mai wuyar. Ya fara shiri don ba za ta zuba ido ya bar ?an mata a gabansa babu aure ba. Da yaji waye zaSin da ta yiwa Anisa sai taga ya fita farinciki. Kuma da murnarsa ya kira Amma ya faWa mata. Sai ta nuna masa ta fishi jindaWi domin ita ba butulu bace. Duk wata gudunmawa da ta dace financially da morally ya bata wajen kulawa da cikar burin Taj.

***

Rayuwa ta fara tsanani ga iyalin Abba. Da yake mutum ne mai sakarwa iyali aji daWi da abin da Allah Ya hore masa, yanzu da ajiyar ta soma ?asa sai suke ?untata. Yawancin samunsa in ka cire bu?atun gida to anyi amfani dasu wajen tarin kayan Waki da yake yiwa ?an matansa. Komai na mutum uku yake saya. Yaya bata san yiwa ?a?a komai ba ta wannan fannin don bata sana'ar komai. Tun da ?uruciya babu irin nacin da bata yi ba amma sam ya?i yarda tayi saboda a cewarsa ta gama aikinta da ta aure shi. Nan kuwa yana tausayin lafiyarta ne. A ganinsa rashin imani ne zai sa ya sanya rai da ta dinga neman kuWi a yanayin da take ciki. Gashi dama bai tsira daga dariya da surutun mutane ba. Idan ya bari tana shiga jama'a da sunan sana'a babu mamaki a karyar mata zuciya da zancen lalurarta. Shi yasa ya yiwa tufkar hanci da wurwuri.

Sau?insu Waya yanzu a gidan shi ne kitson da Sajida take yi. Hamdi kuma satinta biyu da dawowa gida Anti Labiban Abuja da ta zo Kano ta ro?i alfarmar tafiya da ita idan za ta koma. Kowa ya san miskilancin Hamdi idan ta so. Suna ta zaton za ta ?i. Sai gashi da kanta ta amince za ta bita. Weekend na zagayowa kuwa su ka tafi.

*

Abin haushi da takaici da Taj ya tambayi Firdaus game da yarinyar da ta kasance overall a makarantarsu wai bata san komai a kanta ba.

"Ba ?awarki bace?"

"Hamdiyya ai bata da ?awa ko Waya. Sai da case Win

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login