Showing 57001 words to 60000 words out of 182745 words

Chapter 20 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

128

taji ?afafunta suna narkewa su kaWai za su kaita ?asa. Kafin ta gama faWuwa aka tallafota zuwa falo. Akan doguwar kujera aka kwantar da ita. Ana yi mata fifita. Daga nan ba za ta iya tuna me ya faru ba.

***

?an uwa da abokan arzi?i dafifi su ka yi wajen taya Abba murna a masallacin. Yadda al'amura su ka kasance ma?iyi ne kaWai zai ce bai jidaWi ba.

Baba Maje baki har kunne shi da Baballe. Murna yake yi, ya sami damar kyautatawa amininsa bayan abin da Ummi tayi. Don tun daga lokacin shi da Iyaa su ka ja baya da iyalin Abba. Suna masu jin kunyar abin da ?arsu tayi. Duk rashin son fita sai ya zamana Yaya ce mai ?o?arin zuwa. A yawan ziyarar da take kai musu ne Baballe yaga Zee ya ?yasa. Ashe rabonsa ce bai sani ba.

A Sangaren Taj kuma inda mahaifinsa yake ya zauna tare da ?an uwansa. Kawunnai ne na Sangaren Alhaji shi kaWai sai ?an uwansa su Ahmad. Yadda ya hana Taj faWawa su Inna tun jiya, haka ya tsallake ?an uwansu maza da dukkanin abokansa.

Mutane na ragowa ya tashi da sauri ya fita. ?aninsa Baba Amadu ya tare shi ganin sun nufi wurin motocinsu.

"Haba Yaya Hayatu. Ba za mu tsaya mu gaisa da baban amaryar ba za mu tafi?"

"Baka gane shi bane? Habibu ne fa. Meye abin gaisawa a nan?" Ya amsa a wula?ance

Daga nan gaban Taj ya faWi. Su ka haWa ido da Kamal kowannensu da tunanin da yake ransa. Yaya Babba kuwa haWe rai ya yi.

"Da alama akwai manufar da ta sanyaka amincewa auren nan bagatatan. Dama nayi mamaki da ka sanar dani jiya a ?urarren lokaci. To amma saboda Taj ne shiyasa na zo don kada sai an zo Waurawa ka ce ka fasa don kawai ka muzanta shi."

Alhaji ya yi murmushi "bani da wata manufa. Auren fitar da ubangidansa a daudanci daga kunyar al'umma yake son yi kuma nayi masa don kada ma a sami bakin zagina."

Kallon tsananin mamaki Taj ya bi shi da shi. Bakinsa ya mutu. Tun ba a je ko'ina ba ya gane shigo-shigo ba zurfi Alhaji ya yi masa.

"Alhaji don Allah ka tsaya" Ahmad ya ro?e shi don baya jindaWin ganin manya su na sa'in'sa.

"Kaima ban maka izini tsayuwar ba. Yanzu ku sai ku yi musabaha da mutum irin wannan?" Ya nuno Abba da yake tahowa inda suke da ?an abokansa.

Abin ban sha'awa babu Wan daudu ko Waya. Dama su ?ar Ficika ne. Shi kuma tunda a gabansa mahaifin Safwan ya ci mutumcin Abban sai ya ce shi da yaransa ba za su Waurin auren ba don kada a sake samun matsala.

Bawan Allah bai san wainar da ake toyawa ba. Da ya iso hannu ya mi?awa Yaya Babba gami da rissinawa sosai cikin girmamawa. Har sai da Taj yaji wani iri.

"Yaya barka da rana?"

Fuskarsa shi ma a sake ya ce "Sannu Habibu. Shekaru da yawa. Gashi mun zama surukai."

Abba ya murmusa "ina ni ina surukuta da ku Yaya? ?a taku ce. Sai dai ace ta bar gida ta sake komawa gida."

Ragowar ?an uwan Alhaji su ka ?arbi musabaharsa saboda Yaya Babba ya buWe musu hanya. Ransa fari ?al ya sake rissinawa ya mi?a hannu ga Alhaji.

"Yaya Hayatu ..."

Kallon da Alhaji ya yiwa hannun yafi ?arfin a kira shi na wula?anci. Sai dai a ce ?as?anci. Domin ba ma da duka ?wayar idon ya kalle shi ba. Duniya bai ga abin da zai sa ya kama wannan hannun da ya gama lalacewa da bleaching ba. Knuckles Win (gaSoSin yatsu) duka ba?a?e ?irin. Ragowar hannun kuma fari da Wigo Wigon ba?i.

Yawu mai Waci Taj ya haWiya ganin Abba ya shanye abin da aka yi masa tamkar babu komai. Hannun kawai ya mayar ya ?ara du?awa.

"Barka da rana."

"Kaga tashi don Allah. Bana son wannan Wabi'ar taku ta gaisuwa kamar maro?a."

"Alhaji" Taj ya kira sunansa da Wan ?arfi ba tare da tunanin komai ba sama da son ya tunatar da shi me yake aikatawa a gaban mutane.

Ko kallonsa Alhaji bai yi ba. Yaya Babba ne ma ya yi masa alama da ya yi shiru kawai.

Ba tare da nuna Sacin rai ba Abba ya mi?e yana murmushi. Zuciyar Taj ta kasa jurar ganin wannan abu. Barin wurin ya so yi. Hannun Kamal a jikin babbar rigarsa ya hana shi motsawa.

Alhaji ya ce "Ina son ganinka yau bayan Isha'i. Ai ka san gidana ko?"

"Gaskiya ban sani ba. Amma ko Taj sai na biyo in sha Allahu."

Alhaji ya yi irin murmushin nan na Sacin rai. Yana magana ciki ciki "na manta yanzu kai ne uban. To kada ku wuce Isha dai." Ya kalli Taj "kai kuma kada ka manta dokar gidana a kanka. Da ishan ma don ni na kiraka ne."

Mota ya faWa abinsa direba ya ja. Abba ya sake yin murmushi yana Wagawa motar hannu tare da faWin "Allah Ya kiyaye hanya."

Hannun nasa Taj ya sauke masa ya nuna masa Baba Maje "Abba kaje ga abokinka can ina jin kai yake nema."

Sai da ya tafi ?an uwan Alhaji su ka soma bashi baki. Baki ma kasa motsawa ya yi saboda Sacin rai. Ya dai dinga gyaWa kai kawai. Yaya Babba ne ?arshen yi masa magana.

"Ina so ka sani cewa a musulunci iyaye suna da babbar daraja. Bana so abin da Hayatu yake yi maka ya zama sanadin da za ka mayar da martani. Domin idan kayi haka lallai kayi asara. Baka jidaWinsa ba a duniya kuma a lahira ma ba za ka sami rangwame ba."

Godiya sosai ya yiwa Yaya Babban sannan su ka tafi.

Ahmad na ganin babu sauran manyan ya ce masa "mu tafi gida mu san yadda za mu yi da matan gidan. Na san dukkaninmu ba za ta yi mana kyau ba. Ace kayi aure babu wadda ta sani."

Kafin yanzu da wannan tunanin Taj ya kwana. Amma ?ullin da Alhaji ya soma yi masa ya sa ya daina damuwa.

"Baka ji yana yi min tuni akan kada na shigar masa gida ba?"

"Ni kuma a ganina wannan shi ne lokacin da ya dace ka take wannan dokar ka shiga gidan. Rayukansu za su Saci. Sannan bana jin za su yarda su biyoka gidan Yaya. To a ina ka ke jin za ku haWu har ka yi musu bayani na fahimta? Don ni ban hango sun amsa wayarka ba balle su saurareka" cewar Abba wani sarkin zuciyar.

Bishir Wan salihin cikin mazan ya ce "?auko sun dai ya dace ayi su haWu a gidan Yaya ko gidan Yaya Babba."

Agogo Ahmad ya kalla. Lokaci na ?urewa kuma ba su sami matsaya ba.

"Mu je gidana ayi shawara. Zan kira su Yaya Hajiyayye dukkaninsu yanzu a hanya. Idan ya so ko mu kaWai ne sai mu je mu yi musu bayani."

Shi dai Taj bashi da ta cewa. Motar Kamal ya shiga Abba kuma ya ja motar Ahmad su ka tafi da Bishir. A hanya Ahmad Win duk wata yayarsu ta kusa da ta nesa ya kira ta ya sanar da ita. Bishir aka bari da kiran sauran. Duk wadda ta sami hali ta taho gidan Ahmad. Amma banda na cikin gidansu su uku. Idan aka kirasu dole a zargi wani abu. Yadda shawara ta kaya za su haWu su je gida wuraren biyar na yamma.

*

Kamal na tu?i ya Wan kall Taj "Yanzu ka fahimci me yasa nace ka bar maganar auren nan Happy? A gaban jama'a kana ganin yadda Alhaji ya tasarma wula?anta Abba."

Kamar bai ji shi ba sai ya yi masa tambaya.
"Me yasa idan na zo da abu baya bani zaSi Happiness? Sai dai ya bari nayi sannan ya Wauki hukunci mai tsauri a kai."

"Saboda baka tsayawa kayi hangen me zai je ya dawo. Har cewa nayi zan auri Sajida duk don ka ha?ura da gaggawar nan amma ka ?i."

"Ko bana son Hamdi ba zan yarda ka auri Sajida ba. Yadda ya sallama ni haka zai yi maka. Sannan kuma ya Wora laifin naka a kaina."

Kamal ya haWe gira "akan me zai Wora maka?"

"A dalilin kafi kowa kusanci dani mana." Taj ya bashi amsa.

Tunanin bai zo masa ba a baya sai yanzu. Tabbas da ya yi auren laifin su biyu Alhaji zai rabawa. Yana ma mamakin da ya ?yale shi ya buWe boutique a wurin Taj. Bai zaci zai sami goyon bayansa da wuri ba.

Taj ne ya yi magana bayan dogon shirun da su ka yi.
"Happiness, ba fa zan bari ya wula?anta Abba ba. Ni ban ga dalilin da zai sa mu dinga kasa yiwa mai tsohon laifi uzuri ba. Hakan zai iya sawa su koma ga laifin."

Tausayinsa Kamal yake ji. Sai dai kuma yana ganin kamar harda taurin kan Taj. Da zai sauke nasa kambun ya yiwa Alhaji biyayya da tuni an jima da wuce wannan wajen.

"Na sani. Amma akwai hanyoyin samun lada da yawa sama da zaSar wanin mahaifinka."

Idanun Taj sai da su ka yi ja kafin ya bashi amsa.
"Baka ji me nace bane? Happiness, Alhaji bai taSa bani zaSi ba. He just pushes me away and gets angry when I comply (ingiza ni yake yi kuma ya yi fushi idan nayi yadda yake so). Auren nan ina faWa bai wani ja ba ya amince min. In baka manta ba certificate kawai naje na nunawa Yaya Babba shi kenan ya koreni. Da cewa ya yi in zaSi girki ko zaman gidansa kaima ka san ba zan taSa barinku ba. Ba don Amma..."

Zaro idanu ya yi waje ya shiga karanto Innalillahi hankalinsa a tashe. Ya kai hannu ya dam?i hannun daman Kamal dake ri?e da sitiyari tunda yafi kusa da shi.

"Kamal...ya zan yi? Amma. Ya Rabbi." Ya faWi cikin tashin hankali.

"Me ya same ta?" Kamal Win ma duk ya gama ruWewa.

"Ya za ta Wauki zancen nan? Ga maganar Anisa. Kada hakan ya janyo mata matsala da Daddy." Ya kuma faWi, damuwarsa na ?aruwa.

Har su ka ?arasa gidan Ahmad suna jimamin yadda za su tunkari Amma da zancen nan. Kamal ya ?ara tayar masa da hankali da ya ce ya tabbata cikin kawunnansu ba za a rasa wanda zai faWa mata ba.

"Kenan ba a bakina za ta fara ji ba? Shinenan. Na gama yawo."

Yadda ya marairaice Kamal dariya ya yi masa.

***

Falon gidan Ahmad ya cika ya tumbatsa da ?a?an Alh. Hayatu. Duk wadda take cikin garin Kano ta na zaune a wurin.

Yaya Zulaiha ce ?a ta biyu a gidan. Ita ta karSe girman daga hannun Hajiyayye don ta fi ta zafi. Ta yiwa Taj faWa sosai.

"Don kana son taimako bai dace ka dinga yin abin da zai cigaba da Sata masa rai ba. Mahaifi ne fa."

Ha?uri ya bata da al?awarin zai yi ?o?ari a nasa Sangaren yaga al'amura sun daidaita. Ya ?ara da nanata musu cewa abin ne ya zo akan gaSa. Yana son Hamdi tun farkon haWuwarsu. Ya yi haka ne saboda sanin halin mata tunda cikinsu ya tashi. Idan ta kuskure musu, tsaf za a goranta mata wata rana.

Babbar yaya Hajiyayye tana jin an kashe wancan zance sai cewa tayi,

"Ya maganar lefe? Ya kamata kafin a soma zancen tariya mu haWa wanda zai fiddo darajar gidanmu."

"Kai jama'a, Ya Hajiyayye ana ga ya?i kina ga ?ura. Wa yake ta lefe alhalin uwayen ango basu san anyi auren ba?" Wata yayar tasu ta ce.

Duk sai su ka kama dariya. Hajiyayye dai ta fuske abinta ta ce a samo takarda tayi list. Tunda dai an riga an Waura auren sannan bata fatan ace saki ya biyo baya ai kuwa zancen lefe ya zama tilas. ?an son biki irinta su ka goya mata baya. DaWi ya isheta domin ?annen nata wani sa'in tamkar ?a?anta ta Waukesu.

"Sai ka tambayar min ita size Win takalmi da undies. In su Mama sun bamu goyon baya da wuri kaga ba sai an yi wani jinkiri ba."

"Ya Hajiyayye ki bar min sayen undies Win. Jibi tafiyarmu UK da Abban Farouq. Kin san na ce miki sati biyu kawai za mu yi." Wata ?anwar tasu ta faWi da zumuWi.

Taj ya rasa me ya kawo wannan zance a cikin mutane haka. Kunya sosai ta kama shi don bai taSa tunanin yin irin wannan maganar da Hamdi ba. Da su ka farga da discomfort Winsa kuwa su ka dinga yi masa sha?iyanci.

***

Kamar kullum idan magana tana da mahimmanci a wajen Alhaji, Wakinsa yake kiran matansa ya sanar dasu. A yanzu gidan nasa ya sha gyara mai kyau irin wanda ba a taSa yi masa ba. Idan ka jima baka shigo ba sai ka kasa gane shi. Duk da cewa fasalin shi ne dai na da, amma an sabunta tsari da kaya yadda zai shiga sahun farko na kowanne maikuWi. Saboda yanayi na girma, ya fitarwa kansa da wani Sangaren ta baya inda ya yi sabon sashensa manne da babban falon ?asan gidan. Saman ya barwa ?an matan da basu yi aure ba da jikokinsa matasan mata dake yawan zuwa su kwana.

Haka kawai Inna ta dinga jin faWuwar gaba akan wannan kiran. Jikinta ya bata ba zai wuce akan Taj ba tunda ya zo jiya. Tana son sanya ranta yayi murnar ?ila an shirya tsakanin uban da Wansa, amma kuma duhun fuskar Alhajin ya sare mata gwiwa.

Haka su ka zazzauna har ya gama tsakurar abincinsa na rana sannan ya dube su.

"Yau bayan sallar juma'a na Waurawa Taj aure da ?ar gidan Habibu Simagade."

Isashshen lokaci ya basu zancen ya zauna musu. Cike da fargaba da tashin hankali su ke dubansa. Mama tayi ?arfin halin tambayar ko wani laifi ya sake yi.

"Da farko dai yana aiki tare da Habibu saboda ya nuna min ban isa ba. Banda haka ko masu girki nawa ne a garin nan da har sai ya nemo Habibu?"

"Alhaji ina ganin ire iren matakan da kake Waukarwa Taj ba za su samar da biyan bu?ata ba. Shi fa Wa komai shekarunsa indai yana da iyaye to fa yana bu?atar laluma da ja a jiki." Cewar Hajiya.

Cikin fushi da faWa Alhaji ya ce "an ?i a lallaSa shi Win." Sannan ya faWa musu abubuwan da ya binciko da dalilin auren.

"Yaron da yake da hankalin son fitar da wani kunya ne zai kasa gane dacewar ya kiyaye Sacin ran mahaifinsa?"

Umma ta ce "Kayi ha?uri. In sha Allahu za mu yi masa magana."

"Bakin al?alami ya riga ya bushe tunda an Waura auren."

Sai da kowacce ta gama rarrashin Alhaji akan ya yafewa Taj shi kuma yana botsarewa sannan Inna ta dube shi ido cikin ido.

"Yanzu da ka tara mu wane hukunci ka yanke masa."

Dukkaninsu sun girgiza da kalamanta da ma yanayin fitarsu. Babu wannan ladabin da kiyaye harshe da kowacce cikinsu bata isa ta ?etare ba.

"Abu? Da ni kike?"

Ko gezau bata yi ba ta ce "Alhaji na gaji ne. Ina son sanin matsayarka ta uba kafin na sanar da kai tawa ta uwa."

Hajiya sai ta Wan taSata don tayi shiru. Ita kuwa ta kafe Alhaji da ido. Mamakinta ya hana shi motsin kirki. Da yaga da gaske take ne ya iya yin magana.

"FaWa min naki hukuncin. Ai kema kin isa da shi. Wata tara ai ba kwana tara bane."

Gyara zama tayi ta hakimce abinta domin a yau Alhaji ya gama kaita ma?ura.

"Tunda ka aurar dashi ni kuma in sha Allahu zan yi masa biki irin na Wan da mahaifiyarsa take so kuma take alfahari da shi."

"Da kyau Inna Abu." Umma ta faWi cikin farinciki tana tafa hannuwa. Da Hajiya ta kalleta ta kaWa kai tana dariya. Yau ji take kamar ta zuba ruwa a ?asa ta sha.

"Biki? Yanzu ke sai ki yi bikin Wanki ya auri ?ar Wan daudu? Auren da baki ma san da shi ba sai yanzu?"

"Aure ka ce, halattacciyar ala?a. Kuma da kake zancen ban san dashi ba ai ba laifinsa bane. Na yarda da tarbiyar da mu ka bawa ?a?anmu. Yaron nan bai taSa yin wani abu gaba gaWi kamar mara mafaWi ba. Tunda har kai ne ka jagoranci Waurin auren na tabbata ba a hanya ka tsinci zancen ba."

"Haka ne" ya ce da wani irin disbelief. Wai yau Abu ce take kallon idanunsa tana faWa masa maganganu irin waWannan.

"Na kuma jima da sanin cewa duk abin da zai yi yana turo maka sa?o ya sanar da kai."

Bai yi mamakin yadda aka yi ta sani ba
"Shi ya faWa miki ko?"

"A wayarka na gani."

"Bincike kike min?" Ya Waga murya.

"Ni na nuna mata" Mama ta bashi amsa ita ma yau da nata ?warin gwiwar.

Inna ta dube shi bayan ya gama yiwa Mama nata kallon za ki gamu dani Win.

"Abu guda nake nema daga gareka. IZINI. Duk wani abu da ya kama na bikin nan wanda zai fitar dani ko ?an uwana..." ta nuna su Hajiya "daga gida ina ro?on ka sahale mana. Sannan ranakun taron su ma ka barmu mu je. A gidan nan kai amarya ne kaWai uwa bata zuwa. Amma komai tare muke yi ka sani. Ko sisi ba na nema a wajenka. Alhamdulillah ina da abin hannuna na fitar da Wana kunya."

"?anki? Wai yau Abu kin sha wani abu ne?" Alhaji ya ma kasa yi mata faWa saboda ta shayar dashi mamakin da bai taSa zato ba.

"?ana Tajuddin ba. Wanda a kansa na fara sanin daWin zama uwa. Yaron da tsabar taurin kai irin nasa ya la?aba min suna Inna tun da sauran ?uruciyata." ta faWi cikin tuna baya da tasowar zazzafar ?walla "a wajen yi maka biyayya da son kyautatawa na dinga danne ha??insa dake wuyana. To amma daga yau in sha Allahu an gama. Ba zan bari wata a?ida mara tushe tasa ya rayu da fushin iyaye biyu har ma rayuwar tasa ta kasa albarka ba."

Tana gama magana ta tashi za ta fita don hawayen da take yi ya hanata cigaba da faWa masa irin damuwar da ta jima tana dannewa a zuciyarta.

"Zainab."

Dakatawa tayi ta juyo su ka haWa ido da Alhaji.

"Ban yi miki izinin fita yin duka bu?atun da ki ka nema ba. Haka ma ku" ya kalli inda su Hajiya ke zaune suna murmushin jindaWin wannan abu.

Inna ta goge hawayenta ta kalle shi.

"Samun izinin shi ne kaWai abin da zai sa na yafe maka rabani da Wana da kayi sama da shekara goma alhalin ba Allah Ya saSawa ba."

Ficewa tayi ko kallon inda yake bata sake yi ba. Umma da Mama su ka bi ta. Hajiya da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login