Showing 120001 words to 123000 words out of 182745 words

Chapter 41 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

85

ya yi saving numbar.

"Alhajina ina wuni?"

Alhaji ya cire wayar daga kunnensa ya duba sunan don ya fara kokonton wa ya kira.

"Alhajinki kuma?"

"Au...lahhh...Alhajinsa nake nufi" Hamdi ta sake gigicewa da ?arfin amon muryarsa.

"Shi wa?" Ya tambayeta yana yafito Inna da hannu. Wayarta ya karSa zai kira Taj Win. A zatonsa ko ya daina amfani da wannan layin da ya sani.

Aunawa tayi taga idan ta ce masa Taj kai tsaye zai ce bata da kunya. Kuma ita ma dai nauyin sunan take ji.

"Shi Win dai" ta ce da ?aramar murya. Ta ?ara da Wan bayani a fakaice "uhmm...Hamdiyya ce"

Kai tsaye kuwa ya ganeta ya ce "Hamdiyya ina Taj? Bashi wayar."

?an taSa shi tayi ta ce masa Alhaji ne sai ya nuna mata kansa. Rabonsa da ganin sunan mahaifinsa a allon wayarsa ace ya kira shi ba zai iya tunawa ba. Sai dai kuma yau ya kira a yanayin da ba zai iya magana ba.

"Ba ya iya magana saboda ciwon kai."

Katse ta ya yi kafin ta ?arasa "bashi da lafiya ko? Me ku ke yi baku kai shi asibiti ba? Ba shi wayar na ce!"

Muryarsa da take tattare da tashin hankali ta fito mata da sauti na umarni kuma cikin faWa. Sai ta share ta sanar dashi cewa ba zai iya tu?i ba. Amma Abbanta ya tafi neman wanda zai ja motar a ma?ota.

"Shi me yake yi da ba zai tu?a motar ba? In bashi da ita ya ja ta Taj Win mana."

Da ?aramar murya ta amsa masa "bai iya tu?i ba."

Fargabar Sata lokaci da halin da Taj zai iya shiga ne su ka saka shi juyawa ga Inna ya yi magana wadda ta shiga raWau kunnuwan Hamdi "kinga illar daudanci ko? A shekarun Habibu ace bai iya tu?i ba kamar ba namiji ba."

Wannan magana ta sanya Hamdi jin nauyi da wani irin zafi a zuciyarta. Idanunta kuwa su ka soma zafi tunda dama kukan a kusa yake a dalilin ciwon Taj. Da hawayen ya zubo sai idon yayi kamar an baWa barkono saboda tsananin ?uncin da take ji. Abban nata yake faWawa waWannan maganganun? Ta tuna dama ya so a kashe auren. Babu mamaki sai da ya faWa masa abin da yafi wannan ciwo a gaban idonsa. Kasa daurewa tayi tana ganin kamar in tayi shiru ta yarda mahaifinta bashi da daraja. Sai da ta kalli fuskar Taj taji kunya, amma duk da haka bata ji a ranta za ta fasa faWa masar abin da yazo bakinta ba.

Numfashinta har canjawa yayi saboda Sacin rai. Ta buWe baki za ta yi magana Taj ya tashi zaune ya karSe wayar. Jiran abin da zai ce tayi sai taga ya mi?awa Abba da ya dawo yana tsaye a ba?in ?ofa wayar.

"Alhaji ne" kawai ya ce ya dam?a masa wayar.

Magana su ka yi akan asibitin da za su haWu su jira isowar Alhajin.

Ita dai Hamdi ta bi Taj da kallon da har zuciyarsa bai yi masa daWi ba har Halliru ya tada motar su ka hau titi. Duka wayar yana iya jiyo abin da Alhajin yake faWi. A daidai lokacin da take shirin bada amsa ya daure ya karSi wayar saboda a ganinsa idan ta yiwa Alhaji rashin kunyar da ya tabbatar tana gab da yi, to babu makawa gazawar Abba zai cigaba da gani. Har ma ya ce ya kasa yiwa ?a?ansa tarbiyya.

Hannunta ya ri?e ya Wan matse ta zare abinta ko kallonsa bata yi. Ya dinga ?o?arin su haWa ido nan ma ta fuske. Ba don an fara tafiya ba kuma ga dare da tabbas sauka za ta yi. Fahimta Waya ta yiwa abin da ya yi. Ya shigarwa mahaifinsa kamar kowanne Wan halak, amma ita ya hanata tsayawa nata uban. Wata zuciyar ma tayi mata nuni da cewa ?arshenta shi ma bai Wauke shi cikakken namiji ba. Abin da take ji na ba?inciki ya?i sauka. Har su ka isa banda sharar ?walla babu abin da take yi.

*

Da Bishir yana parking Alhaji bai yi mamakin ganin motar Kamal a wajen ba. Shi kaWai ma ya lura sai bai faWawa ?a?an nasa ba saboda a tunaninsa dama dole Kamal ya sami labarin halin da Wan uwansa yake ciki.

Suna fitowa daga mota su Hamdi su ka iso. Bishir da Abba su ka ?arasa bakin motar su ka taimakawa Taj ya fito.

"Ya kuke kama ni ne kamar wani gurgu. I can walk on my own" ya zame hannayensu daga kafaWunsa.

Hannun wanda bai taSa zato bane ya maye gurbin nasu. Inda Alhaji ya janyo shi jikinsa ya kuma tallafe shi ta hanyar ri?e kafadar damansa da hannunsa na hagu. Sai ya zamana Taj na manne da jikin mahaifinsa. Bishir da Abba kallon juna su ka yi cikin mamaki da jindaWi. Shi kuwa Taj neman ciwon kan ya yi ya rasa. Komai ya tattara ya koma zuciyarsa. Inda ta cika fam da wani irin farinciki mara misaltuwa.

"Mu je ciki a duba ka." Alhaji ya faWa yana mai soma takawa a hankali don kada ya wahalar dashi.

Taj ya juya ya haWa ido da Hamdi zai ce ta taho su shiga sai kawai yaga ta Wauke kai. Abba da Halliru ta fuskanta.

"Abba ku taho mu tafi kada mu rasa abin hawa."

"Ki bari mu ji abin da yake damunsa mana."

Fuskarta a cunkushe ta Waga kai daga kallon wayarta ta kuma cewa "Shabiyu ta kusa fa kuma ba abin hawa garemu ba."

"Hamdi ki kwantar da hankalinki na kira Bawalle (mai adaidaita sahu ma?ocinsu) zai zo ya Waukemu."

Abba Habibu ya faWi yana duban Alhaji da yanayi na ban ha?uri game da kalaman ?arsa. Kada ace bata damu da mijinta ba.

"Ba sai ka kira kowa ba. Zan kai ku da kaina ma" Cewar Bishir.

"Ka bar shi mun gode. Adaidaitan ma ya ishemu." Ita ce amsar da Hamdi ta bashi kai tsaye.

Kallon nutsuwa Alhaji ya yi mata sai tayi saurin kawar da kanta gefe amma bai kasa gane tana cikin Sacin rai ba. Bata so tayi kuka a gaban mutane. Cigaba da tsayuwarta a nan kuwa tana ganin yadda Abbanta yake takatsantsan hatta wajen yin motsi sai taji duk ta tsargu. Auren ya zo mata wuya har tana tunanin makomarsa. A haka ma bata da labarin ala?arsu da juna kafin a haifeta. Ba a son ranta su ka shiga ciki har likita ya zo ya bu?aci ya shiga office Winsa.

Ko da Alhaji ya tayar dashi za su shiga wajen likitan can jerin kujerun baya inda ta zauna ya kalla yana sake nazartarta. A take kuma wata irin kunya ta saukar masa. Hamdiyya bata ce komai ba amma yanayin komai nata a yanzu yana yi masa nuni da cewa anyi mata abin da bata ji daWi ba. Ba tare da tsawaita tunani ba ya san waye da wannan aikin.

'Lallai Habibu ya haihu' ya faWa a ransa. Yayinda duniya take ?yamar irinsu har ta kasa karSar uzurinsu in sun tuba, ?arsa ta ture girma da yawan arzi?in gidan aurenta tana mai nuna ba za ta lamuncewa taka darajarsa ba. Abin da bai taSa zato bane yaji a ransa. Hamdiyya ?ar Habibu ta burge shi har wani sashe na zuciyarsa yana kamanta wannan hali nata da abin da yake tsammata daga jininsa.
RAYUWA DA GI?I 29




Batul Mamman=ؖ?


***
Wata doguwar allura Mubina ta zare daga tsakiyar cikin Kamal ta ajiyeta akan kwanon tasa daidai girmanta. Ta koma gefe ta haWa yatsunta na hagu da dama ta sar?esu, sannan cikin dabara ta cire gloves Winta. Duk abin da take yi kwata-kwata ta?i yarda ta haWa ido dashi. Umarni kawai take bawa Nos Win da ya taya ta aikin akan abin da zai yi. Shi kuwa yana ta kallonta har ta gama bai ce uffan ba. Canjawar yanayinta ya sanya zuciyarsa tsirgawa don ya san bashi da nasaba da kasancewarsa babu riga a wajen.

Baya ta bashi yana daga kwance ta harWe hannuwanta a ?irji.

"Sau?in da za ka samu yanzu ba mai Worewa bane. Daga shi sai dialysis wanda shi ma tasirinsa ba ya wuce lokacin da za a sami ?odar da za a dasa."

Numfashi kawai yaja da ?arfi yana mai rufe idanuwansa. Zuciya da jikin nasa duka sun gaji. A ?o?arinsa na ganin bai Wagawa kowa hankali ba yayi exhausting Win kansa. Duk wata lakar jikinsa mutuwa tayi sakamakon jin abin da tace. Tashi ma sai ya gagare shi. Ji yake kamar lokaci zai cimmasa yanzu yanzu. He badly needed a shoulder to cry on. A Wan rarrashe shi a bashi baki. Sai yanzu yake nadamar ?auron bakinsa. Sunan Happy yake kira a zuci domin shi ne zai iya bashi shawarar yadda za su fasa ?wan a gida.

Shirun da ya yi ya sanya Mubina yin gyaran murya.

"Bari na baka wuri ka shirya."

Da sanyin jiki ya yi mata magana kafin ta fita.

"Kada ki tafi Mubina. Bana son zama ni Waya don Allah. Not when you just told me I don't have much time left."

Tsayuwa tayi amma bata ce komai ba har ya mayar da rigarsa ya sanar da ita. Ta juya a hankali ta dube shi. Idanunsa sun kaWa sun yi ja sosai. Sai wata ?walla da take barazanar wanke masa fuska. Koma mata Wan yaro ya yi mai jiran rarrashin uwa. Komai nata da ya danganci juriya a take ya ?wace. Jikinta ya kama rawa a yayinda ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai.

"Yaya za ka yi da ha??ina da ka Wauka Kamal?"

Idanunsa ko buWewa da kyau basa yi ya Waga kai ya kalleta.

"Me nayi miki kuma?"

"Ka san baka da burin rayuwar duniya me yasa ka bari na kamu da son ka? Me yasa kake azabtar dani ta hanyar nuna min kanka a yanayin ciwo amma ka ?i bani haWin kan nema maka magani?"

"Ashe kina sona..." Kamal ya tattaro ?arfin hali yayi murmushi gami da komawa ya kwanta "kinga har naji ?arfi a jikina. Bari na huta sai na tafi."

Wani irin kallo Mubina tayi masa "ka san ?arfe nawa kuwa? Ko ka manta za a sake allurar ?arfe shida na asuba?"

"Kada ki damu zan dawo in sha Allahu."

Mamaki ya bata. Ta zata gaskiyar da ta faWa masa mai ban tsoro za ta sa ya soma tunani da yin abin da ya dace. Rai a Sace ta ce
"You are simply unbelievable! Me za ka je yi a gidan bayan dare ya raba? Kai da ka zo a sume ne kake zancen zuwa gida."

Ya za ayi ya manta? Dama dauriya ya dinga yi a wajen dinner Win. Taj na fita da Hamdi ya kirata. Lokacin ta kusa gida ma tunda ita ma taje dinar. A asibiti su ka haWu sai dai kafin ta iso ya suma a mota. Wurin parking ta dinga dubawa har ta gano motarsa tasa aka Wauko shi.

"Zan fa dawo da gaske. So nake in sanar da Alhaji lalurata. Ko ba haka kike so ba?"

"Kada ma ka faWa mana. Ni ina ruwana? Na daina damuwa."

Kamal ya yi murmushi "to wallahi ki canja taku don soyayya babu nunawa juna damuwa bata da armashi. It won't even last."

?walla ta goge da ?asan mayafinta ta harare shi "kai Win lasting zaka yi balle soyayyarka?"

"Ahhhh, abu na Allah...ki ka san ta inda sau?i zai zo min? In warke muyi aure. Duk shekara na raka ki labour room Win can naku na sama."

Ba lokacin wasa bane amma sai da Happiness ya sanyata murmushi sannan su ka fito daga Wakin.

*

Alhaji bai yi mamaki ba da bincike ya nuna banda jinin Taj da ya hau babu wani abu da likitan ya iya gani da zai zama silar ciwon kai mai tsanani irin wanda yake fama dashi. Ya duba ido da kunne har ma ha?oransa domin ciwonsu kan jawo ciwon kai amma duk ?alau suke. Kuma ya ce yana bacci.

"To ko stress Win biki ne?" Likitan ya tambaya da damuwa.

Mi?ewa tsaye Alhaji yayi "kada ka damu doctor. Kawai ka rubuta masa pain reliever mu tafi." Idan sihiri ne ba a asibiti za a gani ba.

Rubutawar ya yi su ka fito. Taj yana mai ?ara jin mamakin mahaifin nasa. Yadda yake abubuwa kai ka ce babu abin da ya taSa faruwa a tsakaninsu.

Kowa tasowa yayi da ganinsu banda Hamdi. Da farko tana ganin ?ofar ta buWe ta tashi da sauri. Tana haWa ido da Alhaji sai ta koma ta zauna ta kama kallon gefe. Kama kanta tayi don kada ya faWi abin da zai sake damunta.

Taj Win ma ?in kallonsa tayi wanda Alhaji ya karanci yadda hakan ya dame shi. Da alama kasancewarsa a wajen ce kawai ta hana shi ?arasawa gareta. Ita ma kuma dauriya ce da taimakon fushin da tayi tun a hanya ya hanata ko da satar kallonsa.

Murmushi Alhaji ya yi ba tare da ya sani ba. Wannan yarinya anyi rigimammiya. Wato ita nan maganarsa ce har yanzu ba ta ha?ura ba. 'To ai shikenan. Na san maganinku daga ke har Taj Win.'

"Abba zo ka kaisu gida sai ka taho da motar Taj Win."

Zumbur ta mi?e tayi gaba. Taj ya auna yaga idan ya bari ta fita fa akwai matsala a gaba. Kai ya Wan sunkuyar ya?i kallon Alhaji da Abba ya ce,

"Ina zuwa Alhaji."

"Ina za ka je?"

Hamdi da ta kusa ?ofa kuma taji maganganun da suke yi sai ta tsaya cak. Kuka kawai take son yi. Wato umarnin kada ya bita aka bashi yanzu kuma. Bata juya ba ta sake Waga ?afa ita ma Alhajin ya tsayar da ita.

"Kema ina za ki je a daren nan kike ?o?arin fita ke kaWai?"

"Tafiya za mu yi Alhaji. Dare ya raba sosai." Abba Habibu ne ya bashi amsa.

"Ai na san daren ya yi shi yasa nace Abba ya kai ku gida kai da wanda ya tu?o motar."

Ba shiri Hamdi ta juyo. Taj ma dai Alhajin yake kallo.

"Ku kuma ku wuce mu tafi gida."

"Mu su wa?" Taj ya yi tambayar a gaggauce.

"Kai da matarka mana. Ko kana tunanin a daren nan zan bari ka tafi gidan Ahmad ka tashe su?" A zahiri kuwa baya son yaje ne ya sake haWuwa da Salwa ta ?ulla wani abin. Bai ga abin da zai sa ya bar Taj ya kwana nesa da gida ba yau Winnan.

Furucinsa Halliru mai tu?o mota ne kaWai bai bawa mamaki ba tunda bai san komai ba. Fuskokinsu su duka abin dariya don dai ma Alhajin yana gudun raini a gaba da ya dara. Idanun Hamdi ?ara girma suka yi. Na Abbanta kuwa da Taj sun yi micimici kamar ya ce zai yanka wani.

Taj baya son saka rai a banza sai cewa ya yi "ban taho da mu?ullan gidan ba."

"Naku gidan ba da gayyar mata ku ke shigarsa ba?" Alhaji ya ce yana tafiya har ya wuce Hamdi ya fita.

Bata iya tafiya ba sai da Taj ya ?arasa inda take ya ri?o hannunta. Suna zuwa bakin ?ofa ta ?wace hannun ta fito. Abba Habibu dai ya shiga duhu dole ya nemi ?arin haske.

"Alhaji ina za su je ne?"

"Gidana." Ya amsa kai tsaye.

Hankalin Hamdi sai yanzu ya yi asalin tashi. Ta dubi Abbanta tana girgiza kai kamar ????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
zata cire shi.

"Bishir mu?ullin motar yana wajenka ko?"

Nuna masa mu?ullin ya yi shi kuma kai tsaye ya yi gaba ko jiran wani ya yi magana bai tsaya yi ba. Ya sakar musu bomb ya barsu da haya?i.

"Abba don Allah ba za ni ba" cewar Hamdi harda hawaye.

Taj kuwa kai ya girgiza masa cike da murna "Abba ku tafi sai da safe."

"A yi haka?"

"Abba kana ji fa Alhaji da kansa ya ce in zo gida na kwana ba ro?a nayi ba." Ya kalli Hamdi, kallo na girmamawa "albarkacinki naci. Wallahi albarkacin aurenki ne. Nagode Hamdi."

Shi ma Abba sai lokacin ya fahimta sosai. Ya ri?e hannuwan Taj su ka yiwa juna murmushi na farinciki.

"In sha Allah daga yau waccan magana sai dai a tarihi kuma. Allah Ya cigaba da toshe dukkan Saraka."

"Amin Abba. Nagode. Nagode" Ya amsa da murmushi.

"Ni fa ba zan..."

"Bi mijinki ku tafi Hamdi. Sai da safe." Abba ya katseta da sauri.

Yana gama magana yabi bayan su Halliru. Aka barta da Taj. Hannunta ya kamo kada su yiwa Alhaji laifin barinsa jira. Suna zuwa su ka samu ya shiga gaba. Su biyun su ka zauna a baya. Motar tayi tsit. Alhaji ne kaWai yake jin wani irin farinciki na kasancewa tare da Taj a wannan yanayin.

Ribas Bishir ya yi idanun Alhaji su ka sake sauka akan motar Kamal. Da sauri ya ce da Bishir ya tsaya. Bai yi musu magana ba ya fita ya koma cikin asibitin. Shaf ya manta yaga motar lokacin shigarsu. To me yake yi a ciki basu gan shi a reception ba sannan bai neme su ba? Mota kuma tasa ce babu tantama.

Yana shiga ciki ya nufi wajen Receptionist Win sai ga Kamal da Mubina suna fitowa daga koridon inda Emergency room yake.

"Kamal?"

Hantar cikin Kamal sai da ta kaWa da ya tabbatar Alhaji yake gani. Ya yiwa Mubina kallon tuhuma sai tayi saurin girgiza kai.

"Baka da lafiya ne?" Alhaji ya tambaye shi.

"A'a. Dawo da ita nayi daga wajen dinner."

A tsanake Alhaji ya kallesu sannan ya ce "Me ka zauna yi to? Naga motarka tun zuwanmu kusan awa guda da ta wuce."

Kamal ya rasa ?aryar da zai gilla sai Mubina ce ta ?wato shi saboda yadda taga ya gama ruWewa.

"Emergency case na samu Baba. Sai yanzu na fito."

"Allah Ya bada lafiya. Amma duk da haka da shi sai ya tafi gida tunda dare ya yi."

Ha?uri Kamal ya bashi. Yana shirin tambayar waye babu lafiya Alhaji ya sake yi masa tambaya.

"Me ma ya zaunar da kai? Ko akwai ala?a a tsakaninku da ban sani ba?"

KaWan daga aikin Alhaji kenan. FaWin magana kai tsaye ba tare da Soye Soye ba. Mubina ji tayi kamar ?asa ta buWeta shige ciki. Kamal kuma da yake neman mafaka tuni ya cafke wannan damar ya nuna hakan ne.

Tsaf Alhaji ya haWe rai kuwa.
"To ni bana son irin haka? Idan kana neman mace sanar dani ya kamata ka fara yi saboda nayi magana da manyan ta. Amma haka kawai ka Wauko ?ar mutane ka zauna a wajen aikinta da talatainin dare irin wannan ai bai yi ba."

"Ayi ha?uri Alhaji."

"Kema da ki ka biyo shi baki kyautawa kanki ba. Na yarda da tarbiyar Kamal a matsayin uba amma ku ?a?an zamani ba a ci muki laya. Allah dai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login