Showing 162001 words to 165000 words out of 182745 words

Chapter 55 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

119

girmansu yasa ta sake fashewa da kuka ba. Hakan ya bayyana musu cewa ba su kaWai bane. Ta rungume Hamdi tana rarrashinta amma kuma ita ma Win kukan take yi sosai.

Alh. Hayatu ya kira Abba Habibu ya kai shi gaban Dr. Hadifi. Nan da nan aka shiga ciki da shi. Aka bashi riga da dukkanin kayan kariya ga mara lafiya domin kada a shiga da ba?uwar cuta. Sai da ya shirya tsaf aka bashi damar ?arasawa gaban Yaya. Sannan Alh. Hayatu ya matsa gefe yana kallon what it truly means to be a great person. KuWi, mulki, lafiya, mazantaka da suna do not make a man. Habibu Umar Simagade ya nuna masa haka daga airport zuwa yanzu. Kuma duka abubuwan da yake ta?ama dasu a yau ba su hana shi jin nauyi da kunyar wanda ya raina a baya ba. Zuciyarsa ta karaya matu?a da ya tuna wani shuWaWWen lokaci da Abba Habibu ya zo neman taimako wajen sa a kasuwa. Akan ce idan maye ya manta, uwar Wa ba za ta manta ba. To shi dai da kansa mayen bai manta ba.

***

SHEKARUN BAYA


Abba Habibu ne yake tafiya a cikin kwanonin tsakiyar Kantin Kwari da gammo a kansa wanda ya Worawa madaidaiciyar cooler. Kayan jikinsa jamfa ce da wando kuma gwargwadon iyawarsa yana ta kamanta taku irin na maza, sai dai ko kusa baya iyawa. Tafiyar tasa tafi kama da rangwaWa irin ta ?an matan dake ji da kansu. Nauyin kayan da ya Wauko ko kaWan bai Soye yanayinsa na Wan daudu ba.

Da kwatance saboda daWewa da sababbin gine-gine a kasuwar ya gano jerin shagunan Alh. Hayatu. Cikin farinciki ya shiga da sallama daidai lokacin da yaran shagon su ke ganiyar ciniki da wasu kwastomomi. Alh. Hayatu kuma yana magana a gefe guda da ?an mazan ?a?ansa su uku. Dukkaninsu sanye su ke da shadda wagambari tana Waukar ido. Ahmad, Kamal da Taj. Kamar kowacce Juma'a, Alhaji ya tura an Wauko masa su daga gida bayan sun dawo daga makaranta domin zuwa masallaci.

Alhaji na ganin Abba Habibu yaji tamkar an Wauke masa wutar jikinsa. Sam baya son abin da zai haWa su waje guda saboda yadda yake ?yamarsa. Idan ya tuna Habibun da ya sani, ya kalli wannan sai yaji wani irin takaici.

Da ?yar ya amsa sallamar da yayi. Kuma gabaWaya ya tsargu da kallon su da mutanen cikin shagon su ka kama yi. Yana ji a jikinsa yau shi zai zama jigon gulmar cikin kasuwar.

Fuska cike da fara'a da jindaWi Abba Habibu ya mi?a hannu zai dafa kan Ahmad yana cewa "girman Wan mutum ba wuya. Yaya Hayatu haka Ahmad ya girma?" Ya kalli su Taj "waWannan ?annensa ne?"

Kafin hannunsa ya taSa Ahmad tuni Alh. Hayatu ya janye Wansa gefe ya kuma bi shi da kallon me-ya-kawo-ka?

Abba Habibu ya Wan rissina gami da mi?a masa hannu sai dai haka ya koma da abinsa da bai mayar da musabahar ba. Still with a smiling face ya gaishe shi ya kuma tambaye shi lafiyar iyali.

"?alau! Aiko ka aka yi ne?" Alh. Hayatu ya tambaya a ?agauce.

"Dama magana na ke so mu yi"
Abba Habibu ya bashi amsa da sanyin jiki. Attitude Win da yake yi masa yasa shi shan jinin jikinsa. Shi Win ba ba?on da ake maraba da zuwansa bane.

Wata kusurwa a cikin shagon Alh. Hayatu ya ja shi maimakon su keSe a office. Yadda mutane suke yanzun nan zai iya jin an yi masa muguwar fassara.

Cikin jin nauyi Abba Habibu ya keta billensa ya ro?e shi akan ya taimakawa rayuwarsa.

"Wallahi ban iya komai ba sai girki. Na fara koyon Winki amma saboda zama sai naji ba zan iya ba tunda na saba da kai komo. Ni kuma ba karatu na gama ba balle na nemi aiki."

"Me ka ke so?"

"Ba na son zama cima zaune. Idan da hali ko yaron shago ka Wauk..."

Ko direwa bai yi ba Alh. Hayatu ya hau shi da faWa.
"A'a...kada ma ka yaudari kan ka. Ta yaya zan bari mutumcina ya zube a wajen sana'ata saboda kai? Ban gaya maka zaka yi nadamar wannan hanyar da ka Wauka ba?"

"Ka faWa Yaya Hayatu. Ba kai ba ma. Kowa ya faWa kuma na gani."

Idanuwansa su ka ciko da ?walla. Hakan ya sake Satawa Alh. Hayatu rai. Namiji har namiji amma mai saurin kuka. Tirrr da daudanci wallahi ya ayyana a ransa.

"Habibu ka san ban iya munafurci ba ko? To ba za ka zauna min a shago ba. Ana girmama ni a wajen nan."

Abba Habibu ya yi murmushi "nima kaina ina ?yamar yadda rayuwa ta kasance min amma wallahi girki kaWai nayi a cikinta. Duk sauran shiriritar da kake tunani ban taSa yi ba. Kuskurena biyu ne. Na farko da nayi tunanin dole sai na koma mace zan sami damar yin girkin da nake so. Na biyu kuma da na bari son girkin ya rinjayi zuciyata zuwa ga saSon Allah."

Ya haWa hannuwansa biyu
"na tuba ga Ubangijina Yaya Hayatu. Ko zan mutu ina yawo a titi ba zan ?ara daudu ba. Tafiya, magana da wannan karya jikin ma don dai na rasa yadda zanyi na daina ne. Don Allah Ka taimaka min ko da jari ne."

Zuciyar Alh. Hayatu ta fara karaya da zantukan Abba Habibu a wannan lokaci. Yanayin tamke fuskarsa ma ya sassauta. A lokaci guda yaji makamansa sun fara ?arewa. Ya ja gwauron numfashi ya sauke.

"Ba zan iya zama da kai a kasuwa ba Habibu amma in sha Allahu zan taimaka maka." Ya sami kujera ya zauna sannan ya dube shi "Yanzu idan na baka jari wace sana'a za ka yi?"

Murna, nutsuwar zuciya, Woki da girmamawa ga Alh. Hayatu su ka taru su ka mamaye zuciyar Abba Habibu. Bakinsa har yana rawa don tsabar farinciki.

"Girki!"

Alh. Hayatu yaji wani irin haushi da takaici sun lulluSe shi. Girkin dai zai koma wa?

"Sana'ar abinci zan cigaba da yi domin a nan nake da ido. Kada na dulmiya kuWin a inda zai salwata saboda rashin sabo. Ko yaya ka gani?"

?aga murya ya yi "Baka shirya gyara rayuwarka ba Habibu. Ka zo ka fita. Fita na ce!!!" Ka nuna masa waje.

Abba Habibu ya waiga hagu da dama a rikice don bai san me ya sake tunzura Alh. Hayatu ba.

"Yaya Hayatu..." ya soma kiran shi da sigar magiya.

A yadda Alh. Hayatu yake Waga murya yanzu da yaran shagon nasa, kwastomomi da mutanen dake haraba kowa ya dawo da hankali garesu.

"Girkin ba shi ya kawo ka wannan mummunan matsayin na Wan daudu ba? Shi ne za ka kalli tsabar idona ka ce min idan na baka jari shi za ka cigaba da yi. Anya Habibu kana da hankali kuwa?"

"Shi ne kaWai nake ganin zan yi ba tare da mutane sun guji mu'amala dani ba. Yanzun nan fa kace min ba za ka iya zaman shago dani ba. Kana ganin akwai sana'ar da zan yi a saya a wannan zamanin namu da ake ?yan?yamin masu rayuwa irin tawa? Abincin mu ne kawai na san ba a gudu."

"Habibu ka fita na ce. Kuma ko a hanya ka ganni kada ka kuskura kayi gangancin nuna ka taSa sani na. Aikin banza."

Jiki a sanyaye Abba Habibu ya ya juya zai fita. Idanuwan dake kallonsa sun fi ashirin. Nan take zuciyarsa ta sake raunana. ?walla ta cika masa idanu taf sai dai bai bari ta sauko ba.

A wula?ance Alh. Hayatu ya kalli cooler Win da ya shigo da ita. Ya sa ?afa ya zungureta.

"Dawo ka yi mantuwa."

Murmushin ya?e Abba Habibu ya yi "dama kawo maka nayi a bawa yara."

"A bawa yara? Me?" Ya sake tambaya yana taSe fuska.

"Zabi ne aka soya"

Katse shi yayi da sauri
"Allah Ya kiyaye jini na su ci girkin Wan daudu wallahi. Ba ma tare da yunwa Habibu. Ka kwashe kazantarka."

Abba Habibu ya kalli kular ya koma ya kalli mutane suna ta ?ananun maganganu a gefensa. Jikinsa yaji duk ya mutu kamar anyi masa duka. Wannan kular ya tabbatar a yadda yake jin kansa ba iya Wauka zai yi ba. ?wa??waran motsi idan yayi zai iya yin hawayen da Alh. Hayatu zai sake aibata shi a kansu. Rago zai kira shi.

"Don Allah ko a nan ne ka bayar."

"Ai ba ni ba, wanda ya raSe ni ma yafi ?arfin cin abin hannunka." Ya kalli biyu cikin yaransa "ku Wauka a kaiwa karnuka tunda ba ya so."

Jin haka Abba Hayatu ya koma ya Wauki kular kafin su taSa. Mahaifiyarsa ce ta dafa sai dai baya jin Alh. Hayatu yana bu?atar dogon bayani irin wannan. Da ya fita bai sake waigowa ba.


*

In ya tuna, shi da Abba Habibu basu sake haWuwa ba sai da maganar auren Taj da Hamdi ta taso sai yaji a ransa tamkar Abba Habibu yayi nasara a kansa har sau biyu. Na farko izzarsa ta kife a ?asa a yayinda Wansa mafi soyuwa a gare shi ya zaSi girkin da ya tsani gani a wajen Wa namiji a matsayin sana'a. It was as if karma came knocking and laughing at him lokaci guda. Na biyu kuma shi ne yadda ?addara ta sake haWa Wan nasa da yar Habibu. Abu kamar almara. Idan ya ce bai yi tunanin ko asirice masa Wa Abba Habibu yayi ba tabbas yayi ?arya.

A karon farko zazzafar ?walla ta dinga kwaranya daga idanun Alh. Hayatu. After all these years, abar ikon Abba Habibu ce ta zama silar warakar gudan jininsa. Yau idan Kamal ya cigaba da rayuwa, Allah ne Ya yi ikonSa amma matar Habibu ce sila. Habibun da yake ganin bai cika mutum ba.

Wasu cikin kalamansa gare shi masu zafi su ka dinga dawo masa da wata irin amsa kuwwa. Shi ya faWe su amma yau yafi Abba Habibu jin zafinsu. Nadama da tulin dana-sani su ka sar?afi zuciyarsa. Tabbas tun a jiya zuciyarsa ta shiga alhini da jin nauyin abubuwan da ya yi a baya. Amma a wannan sa'ar, da Habibu ya zo gabansa amma ko kusa fuskarsa bata nuna alamun zuciyarsa na Soyon ba?incikin sadaukarwar matarsa ba. Hasalima tuhumar kukan ?arsa yake yi har yana shawartar ta da kada tayi abin da su da aka yiwa alfarma za su ji babu daWi. Sai ya ji komai ya kwance masa. Babu sauran jin kai da ?afafa. Shi Hayatu ya yarda ?addara bata fi ?arfin kowa ba. ZaSin yadda Wan Adam zai tafiyar da halin da ya tsinci kansa shi ne ma'aunin dacewa.

"Alhaji lafiya? Me ya faru kuma?"

Firgigit Alh. Hayatu ya dubi su Hajiya dake tsaye da wasu cikin ?a?ansa suna kallon shi. Kawar da kansa ya yi gefe bai cewa kowa uffan ba.

Kallo guda Inna ta yiwa yaran nasu su ka fahimceta. Kafin wani lokaci dukkaninsu sun bar wajen. Masaukinsu Ahmad ya ce su zo su tafi saboda asibitin ba a jinya. Kamal kuma yana bu?atar hutu sosai tunda ko magana bai fara yi ba. Ya dai dawo hayyacinsa amma yana cikin magagin ciwo.

"Mubina tare za mu tafi ki samu ki Wan yi bacci ko yaya ne." Ya dubi Taj "ka zauna da Hamdi sai ku taho tare da su Alhaji."

***

Tsaye a bakin gadon Yaya, Abba Habibu ne da wata nurse. SharuWWan shiga ICU Win ta bashi wanda a ciki ta nanata masa banda Waga sauti cikin magana ko kuka. Ya tambayi ko zai iya taSa ta tayi masa izini amma shi ma ba ri?o mai ?arfi ba. Komawa tayi table Winta a can tsakiyar Wakin ta barshi gefen da aka keSewa Yaya.

Abba Habibu ya daure sosai ya hana kansa kuka ko da a zuci. Gani yake da zarar ya karaya wani abu zai iya samunta. Hannunsa ya Wora akan nata ya ri?e kamar zasu yi musabaha.

"Ashe waliyya nake aure ban sani ba? Gaskiya ki tashi haka nan in kwashi tubarraki."

Kamar daga sama yaji muryar Yaya tana magana a hankali sosai. Salati ne take yi da sauri-sauri cikin kiWima. Abba
Habibu ya ran?wafo kansa su ka haWa ido. Ai da ya tabbatar ta tashi da saurinsa ya juya zai fita domin ya kira nurse. Ita kuwa Yaya ta sake dam?ar hannun tana mai jin tsoron kada ya fita ya barta.

"Sannu. Nurse zan kira a zo a duba ki."

A hankali ta rufe ido ta buWe cikin nutsuwa. Sai a lokacin ta dawo hayyacinta.

"Yaushe ka zo?" Kafin ya amsa ta kaWa kai "kai ne Win dai ba gizo idanuna suke ba ko?"

"Ni ne Jinjin. Yau na zo. Yaya kike ji a jikin naki? Ki bari na kira Nurse."

Cikin ?an?anin lokaci likitoci biyu da nurse su ka tsaya akanta. Aka duba lafiyarta sosai su ka tabbatar cewa babu sauran matsala. In sha Allahu bata cikin haWari. Sannan aka bata awa guda ta sake hutawa kafin a mayar da ita Waki.

Wannan abu ya farantawa Abba Habibu rai sosai. Bayan fitar likitocin waWanda su ka jima suna yabonta kafin su tafi, Yaya ta dubi Abba Habibu. Bayani ta so yi masa yace sam bai yarda tayi magana ba.

"Ki bari sau?i ya samu shine babban burina. Ina so dai ki saka a ranki cewa kin yi jihadi kuma ko kaWan baki Sata min rai ba."

Lokaci na cika ko minti biyar ba a ?ara ba aka gangaro Yaya zuwa Wakin da hukumar asibiti ta tanadar mata na musamman domin karramawa. VIP wing aka nufa da ita wanda sai an shiga lift an sake ?ara hawa uku akan inda su ke. Tun a ?ofar ICU Win Hamdi ta kama mata hannu tana biye dasu. Idanunta jazur duk ta fita hayyacinta amma a haka take ta murmushi saboda kada ta karyar mata da zuciya.

Taj tsayawa yayi tare da Alhaji. Yana kallo su Hajiya su ka bi su a baya.

"Ka bi su mana" cewar Alhaji gare shi.

"Abin da ya hana ka bin su nima shi ya hana ni Alhaji." Ya kalli Alhajin da Wan murmushi a fuskarsa "na san ba surukuta ce ta hana ka bin su ba."

Alhaji ya numfasa yana bin hanyar da aka gangara gadon Yaya da kallo. Ya jinjina kai sannan ya zauna a kan kujerar. Taj ma kusa dashi ya zauna su ka kasance gefe da gefen juna sun jingina baya da bango.

"?an Adam ba ya gane cewa ba a bakin komai yake ba sai ya ga ikon Allah a inda yake tunanin wayo ko dabararsa sun ishe shi."

Kallonsa Taj yayi yana sauraronsa da kunnuwan basira amma bai ce komai ba. Alhaji ya cigaba da magana.

"Idan wani ya ce min Wan cikina mace ma ba namiji ba zata ci abinci da sana'ar abinci wallahi zan ?aryata Taj. I was so confident cewa Allah Ya lamunce min rayuwata akan tsarin da nake so. Ina da kuWi kuma nayi muku tarbiyya daidai gwargwado. Fitintinun zamani da ake kuka dasu babu ko Waya a cikin gidana. ?a?ana duk inda su ka shiga ana alfahari dasu. Na zata..."
muryarsa ta kama rawa
"Taj na zata gobe na kamar yau zata cigaba da kasancewa muddin rai. Hmmm"
Ya sauke ajiyar zuciya da ?arfi.
"Tajuddeen Hayatu sai ka zaSi kitchen. Sana'ar da bayan ?iyayyar da nake yi mata ban taSa hango wani nawa cikinta ba. Kuma kamar da gayya sai ga ka da auren ?ar Habibu. Wato Taj da ace zan iya fito da zuciyata ka ga tsanar da na yiwa auren ku a dalilin Habibu, da ko da wasa ba za ka tunkare ni da maganar Hamdiyya ba."

Taj ya yi kasa?e yana jin furucin mahaifinsa dalla-dalla.

"Subhanallah! Komai yana tafiya cikin tsari da ?udurin Al-Hakimu. Ba don auren ku ba da babu abin da zai kawo mahaifiyar Hamdi inda muke ko da a asibitin nan take aiki. It's like everything happened for this day Taj. Allah Ya rubuta da ?odar matar Habibu kuma surukarka Kamal zai cigaba da jan numfashi a duniya. Kuma duk tarin shekaruna sai a yanzu na gane wannan izinar."

"Tsarki ya tabbata ga Sarkin da gyangyaWi da bacci ba sa cikin siffofinSa." Taj ya faWi cikin shau?in alawar imani wadda za?inta yakan tashi a lokutan da bawa ya yaba wa sarautar Ubangijinsa, gatansa, majiSincin lamuransa.

Alhaji ya gyaWa kai sai da raunin murya ya ce "Zuciyata ta cika da kokonton karSuwar dukkan alkhairi na na baya."

Wani irin kallo Taj ya yi masa ya ce "Alhaji me ya sa za ka yi wannan tunanin? Don Allah ka kyautatawa Allah zato."

A gurguje Alhaji ya bawa Taj labarin abin da ya gama tunawa Wazu akan zuwan Abba Habibu neman taimako wajensa a shekarun baya.

"Ka san Annabi SAW ya gargaWe mu da gujewa girman kai da illarsa akan ayyukan ladan mu."

"Haka ne." Cewar Taj da sauri yana jiran yaji sauran abin da Alhaji zai ce.

"Dole na daina yaudarar kaina idan ina son ganin daidai. Tabbas tuntuni na jima da ji a raina cewa Habibu ya tuba. A zuciyata ina muradin janyo shi jikina in inganta masa rayuwa. Amma a gefe guda ina tunanin makomar mutumcina a idon duniya. Ina ?yamar a ce ina mu'amala da mutum irinsa." Muryarsa ta koma abin tausayi a yayinda yake cewa "kaga gabaWaya fushin nawa ya zama ba don Allah ba. Girman kai ne kawai ya hana ni yin abin da ya dace ba wai don ban san ya dace Win ba. Tun girma da arzi?i ban nemi shiri da shi ba gashi yanzu dole in ?an?antar da kai a gaban sa tunda girman da arzi?in nasa ne. Kowa ya?i sharar masallaci..."

"Yaya Hayatu dai ba zai yi ta kasuwa ba!"

Tare su ka juya da jin muryar Abba Habibu a gefen su. Abba Habibu ne tsaye shi da Hamdi. Ganin su ya sa su mi?ewa su ma.

Tun shigar su Waki, Yaya ta ce Hamdi ta koma su dawo tare da Taj. Ta hango shi yana ja da baya. Mama ta ce musu tana tunanin yana jin nauyin fuskantarta ne bayan ta gamu da lalura a dalilin Wan uwansa.

"Ai kuwa ba zan yarda da wannan tsirfar ba. Maza bi shi ki ce ina nemansa."

Da ta fito sai ta manta a hawa na nawa su ka baro su. Ta koma tambaya shi ne Abba Habibu ya hana Umma da tayi yun?urin rakota biyota. Ashe rabon za su ji maganganun su Alhaji ne.

"Habibu..." Alhaji ya fara cewa da wata ?aramar murya kamar ba shi ba. Sai dai Abba Habibu bai jira ya gama magana ba ya girgiza masa kai.

"Ko me za ka ce don Allah ka bari indai ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login