Showing 66001 words to 69000 words out of 182745 words

Chapter 23 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

99

ta soma magana saboda tsoro.

"Kinsan ina girmama shi sosai. Ba zan yi komai ba tare da shawartarsa ba."

Ganin zai Sallo mata ruwa ba shiri ta ce "to a bar zancen nan don Allah."

"Kin fasa karSar takardar?"

Ta sha kunu "na fasa."

"Za mu je asibitin?" Ya kanne mata ido.

MurguWa masa baki tayi "na ma zama abar tsokana ko?"

Ya rasa me yasa komai tayi yake burge shi. Wannan tsiwar ma da ba don dare ba da zai yi ta zurma ta ne tana yi masa.

"Gobe zan yi tafiya. Ki min addu'a don Allah."

"Allah Ya tsare hanya" ta furta kamar an matse bakin.

"Baki ro?a min samun nasarar abin da zai kai ni ba."

"Me zai kai ka?"

"Maganar aurena da wata ?anwata. Tunda ke ba sona kike ba gara na kawo wadda za ta so ni, nima na so ta."

Yana kallon yadda fuskarta ta haWe kamar hadari. Ya gimtse harda yi mata sai da safe ya wuce. A mota ta sami damar yin murmushi mai haWe da dariya. Ya gama ganota. Tana so tana kaiwa kasuwa. Birkita mata lissafi kawai zai yi ta ha?ura don kanta ta karSi zuciyar da ya jima da mi?a mata.

A nata Sangaren tana shiga gida ta sauke ajiyar zuciya. Wato da ya mi?o takardar da take barazanar nema anya za ta iya karSa kuwa? Ita kaWai ta dinga sa?e sa?e. Sai kuma ta kama murmushi da ta tuna maganganunsu. Ko ba a faWa ba ta san tsokana ce da shi. A ?arshe dai ta gaji da kokawa da zuciyarta ta amince za ta bashi dama. She will give this pure feeling she has for him a chance.

?ofar Wakinsu ta kama za ta buWe taji kira daga Abba. Soro ya ja hannunta su ka koma don a nan ne kawai ya san babu kunnen da zai ji su. Ya gama ninke Yaya ya nuna mata babu matsala don ta kwantar da hankalinta. Tsoron da yaji yanzu shi ne na ganin dawowar Hamdi daga wajen Taj. Idan ya bari ala?arsu tayi nisa ?arsa zai bari da jidali. Ya rasa abin yi sama da faWa mata halin da ake ciki. Cikin hikima ya bata labarin Taj tun daga farko har zuwa aurensu. Taji wani irin tausayinsa da kwaWayin ya daidaita da babansa. Hankalinta bai ?arasa tashi ba sai da Abba ya faWa mata tsakaninsa da Alh. Hayatu da yadda aka yi aurensu. Da kuma sharaWin da ya gindaya masa.

"Ko mahaifiyarku ban sanarwa gaskiya ba. Shi kuma Taj nayi imanin ba zai taSa sakinki ba idan yaji daga ina umarnin ya fito. ZaSi Waya ya rage min..."

Kuka take a lokacin ta ce "mene ne Abba? Me za mu yi?"

"Ki nuna masa na kya sonsa. Na tabbatar idan yayi tunanin da gaske kike zai sauwa?e miki. Ni kuma zan baki goyon baya. In ta kama sai ya fita daga rayuwarmu bakiWaya ya sami salama."

"Abba kada ka saka kanka a ciki. Yanzu banda ?an uwansa kana cikin waWanda yake yiwa kallon uba. Ya ma faWa min. Idan ka juya masa baya it will break his heart."

"Ki yafe min Hamdiyya. Koma mene ne ni na cuceku. Rayuwa tana gaba amma kullum ana yanke muku hukunci da abin da na shuka a baya."

Zuciyarta rauni tayi mara misaltuwa. Bayan shuWewar lokaci tana gudun mahaifinta yau da kanta ta rungume shi tana kuka. Shi kaWai yake ta haWiyar abubuwa domin farincikinsu amma kullum ?orafi take yi.

"Abba ka yafe min nima. Ba zan ?ara faWin aibun sana'arka ba. Kuma in sha Allahu babu mai jin zancen nan. Zan yi ?o?ari in ga ya ha?ura da auren da kansa."

"Allah Ya yi miki albarka. Allah Ya bamu ikon sakawa Taj da abin da yafi bu?ata a rayuwarsa wato albarkar duka iyayensa."

Amin Win a zuci ta iya faWinta. Ta shige Waki ta kwanta tana zubar da hawayen damuwar da tafi ?arfin shekarunta.
RAYUWA DA GI?I 19




Batul Mamman=ؖ?






***

Bayan sallar asuba Taj ya kira Kamal domin su yi sallama. Jiya basu sami haWuwa a gida ba. Ya yi ta waya shiru Kamal Win bai Wauka ba. Wanka ya yi ya gama shiri da sauri ya sake duba wayar. Abin mamaki Kamal bai bi kiran nasa ba. Da wahala hakan ke faruwa. Jikinsa sai ya bashi ko ba ?alau ba. Abba ?aninsa ya kira ko tunawa da lokaci bai yi ba.

"Happiness ya fito sallar asuba kuwa?"

Abba ya Wan wartsake idanu "ya fito amma yau ya riga kowa baro masallacin. Sa?o ne?"

"?an le?a min shi please."

Abba baya son fita don bacci ne sosai a idonsa ya ce "Ya Taj ya dai kamata ku rage wayar asubar nan. Kai kayi aure, idan shi ma ya yi wallahi za ku dinga samun matsala da matanku."

"Za ka tashi ko kuwa?" Taj ya Wan Waga murya da ?o?arinsa na Soye yadda ya damu.

Yana jin ?un?unin Abba har ya isa ?ofar Wakin Kamal. Sallama ya haWa da ?wan?wasawa.

Da ?yar Kamal ya iya buWe jajayen idanunsa da su ka kumbura kamar wanda ya kwana yana kuka. Jikinsa gabaWaya ciwo yake yi. Kansa kamar ana sara guduma saboda azabar ciwo.

"Waye?" Muryarsa ta fito a dusashe.

"Ya Taj ke nemanka." Abba ya faWa yana saita bakinsa da ?ofar yadda za a ji da kyau "na sanar dashi. Can I go back to bed now?"

"Thanks" Taj ya ce da kulawa.

Wayar Kamal ya sake nema. Yadda yaji muryarsa ya tayar masa da hankali. Amma Kamal Win ya tabbatar masa da mura ce ta kama shi da zazzaSi.

"Allah Ya ?ara sau?i. Ko na bar tafiyar yau muje asibiti?" Hamdi ce ta faWo masa ya yi murmushi.

"Ka tafi kafin Amma ta sauka a garin nan duk mu shiga tara."

"Don Allah ka je asibiti dai. Bana so ana raina mura da zazzaSi. Ciwukan gaske ne."

"To doctor." Kamal ya zolaye shi.

Suna gama wayar ya Wauki ?ar jakarsa ta goyo (backpack) wadda ya sanya duka abubuwan bu?atarsa a ciki. ?ananan kaya ya saka ya koma matashi sosai. Haramar tafiya ya yi sai ya tuna yadda Kamal ya damu kada Ahmad yaji babu daWi akan halin da Salwa ke ciki. Lokaci ya duba akwai an saura. Ya fito falo ya kira wayar Ahmad Win.

"Yaya na shirya zan tafi."

Ahmad ya mi?e da sauri. Dama bai koma bacci ba tun sallar asuba.

"Bari na zo na kai ka airport."

"Ka barshi. Zan sami adaidaita sahu."

Fitowa Ahmad Win ya yi. Su ka gaisa sannan ya mi?a masa key Win motar Kamal.

"Incase ban sami dawowa akan lokaci ba, ina sa rai jibi motata za ta iso. In bawa mutumin numbarka sai ya kawota nan ya ajiye?"

"Da ina zai kai?" Cewar Ahmad yana zura mu?ullin a aljihun wando.

Zama Taj ya yi ya bu?aci yin magana da shi na mintuna kaWan.

"Yaya akan Salwa ne."

Ahmad ya Wan Sata rai "ka cire lamarin yarinyar nan daga gabanka ka fuskanci matsalolinka."

"A'a Yaya. Idan da kara nima ?anwata ce. Ba kuma zan so ta shiga irin wannan yanayin akan wani ba."

"Shin ka taSa yi mata magana ko nuna mata alamun soyayya ne?"

Ya kaWa kai da sauri "a'a."

"To ka gani. Rigima ce kawai irin ta ta. Tun abin nata bai yi nisa ba na bata shawara ta?i ji. Ya take so ayi mata? Ana forcing soyayya ne?"

Taj dai duk nauyin yayan nasa yake ji. Sai yanzu ya gane manufar Kamal.

"Duk da haka ni dai ka rarrasheta. Allah Ya bata wanda ya fini. Mafi alkhairi."

"Kada ka damu. Dama a gidansu babanta ya yi mata miji. Amma kaga don fitina ta?i komawa gida. Wai tana jiran service kuma."

Dariya su ka yi su biyun. A??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????hmad ya kwantar masa da hankali. Da ace soyayya su ke yi yanzu ya gujeta shi ne zai zama rashin kyautawa. Amma tunda hakan bata taSa faruwa ba babu mai Wora masa laifi. Ahmad ya sako jallabiya ya kai shi airport tunda jirgin sassafe zai bi.

*

Yadda Amma taga rana jiya haka taga dare. Wajajen ?arfe biyar ta sami labarin auren Taj daga wajen matar Waya daga cikin ?an uwanta. Ba don shekaru ba da tabbas ?aryata ta za ta yi. Ta dai daure su ka gama wayar. Yaya Babba ta fara kira ya ce mata haka ne. Ji tayi tamkar an kwaWa mata guduma. Taj ya yi aure bata sani ba. Kuma har dare bai kira ba. Haka ta ?arasa wunin ranar cike da fargabar kada mutan gidan su ji.

Da taga Allah Ya taimaketa har bayan Isha babu wanda ya ce komai shi ne Daddy na gama cin abinci ta ce masa tana son zuwa Kano gobe.

Kamar Anti jira take ta shigo falon a lokacin "Hummm, Maman Ihsan kenan. Kin gaji da Soye Soyen?"

Gabanta faWuwa ya yi amma ta dake.
"?oyo kuma? Wani abin ne ya faru?"

"Kada ki raina min hankali mana. Za ki ce ba da saninki Taj ya yi aure bane? Ko kin zata bamu sani ba?"

Anti ta faWi da matu?ar Sacin rai. Taci burin suruka da shi saboda ya haWa dukkan abin so. Kyau, kuWi, suna da kuma kyawawan Wabi'u. Idan Anisa ta sami miji irinsa ta wuce raini a wurin kowa. A dangi ma sai an dinga bata girma na musamman.

"Yadda ki ka ji maganar nan nima haka na ji ta. Kuma dalilinta nake son zuwa Kanon ma kenan. Babu wanda ya neme ni. Sai aure kawai naji."

"Ai in duk jikina kunne ne ni ba zan yarda ba. Yaudara ce dai an yiwa ?ata."

Ran Amma ya soma Saci ta ce "Ita Anisan ce ta ce ya yaudare ta?"

Hankali kwance Daddy ya gama cin abincinsa sannan ya tsawatar musu.

"Idan kuma ban isa daku ba sai ku fita ku ?arasa."

Amma kwantar da murya tayi ta bashi ha?uri sannan tayi masa bayanin rashin sanin auren.

"Idan haka ne kuwa kema bai mutuntaki ba. Kuma ya nuna bai san alkhairi ba."

Wani irin kallo Amma ta yiwa Anti. Bata son cigaba da rigima a daren nan amma take taken Antin so ta a cigaba da maganar har Hajja ta ji.

Daddy sallamarsu ya yi akan su bar zancen zuwa washegari. Anti na fita ta koma Wakinta inda ta sami Anisa a zaune da waya a hannu. Zuciya ta raya mata Taj take kira ?ila ya?i Wauka. Ai kuwa ta tashi ta nufi Wakin Hajja tana kuka ta karanta mata ?arya da gaskiya. Wani abin idan ta faWa sai Anisa ta ri?e baki don mamakin yadda uwa take yanko ?arya bisa son zuciya.

"Damuwata yanzu yadda ta saka shi a ranta."

"Anti don Allah ki daina kuka. Ni wallahi na ha?ura."

"Ai ba ke ki ka ce kina son sa ba tun farko balle ha?uri ko rashinsa ya zama a hannunki." Hajja ta faWi cikin fushi tana duban Anisa "har ni Jamila za ta yiwa haka? Maza kirawo min ita."

Cin mutumci babu irin wanda Hajja bata yiwa Amma ba. Da Daddy ya shigar mata shi ma ta haWa dashi ta ?are musu tas. Yau har gorin haihuwa biyu kacal sai da aka yi mata.

"Saboda shegen son kuWi da koyi da rayuwar nasara ki ka tsayar da ?wayayen haihuwarki. Gashi nan wanda ki ka Wauko a dangin ya nuna miki shi ba Wan goyo bane. Don na tabbata da sahalewar ubansa ya yi auren."

Allah Yasa ita Win ma ba ?yalle bace. Da maganganun su ka isheta fita tayi daga Wakin. Hajja ta ce dama ta rainasu daga ita har mijin. Banda haka bai kamata tana yi mata magana ta fita ba.

A wannan halin dai aka kwana ranar. Gidan duka babu daWi. Anisa kanta ta sha kuka saboda ta dogara da cewa ko don alkunyar abin da gidansu su ka yiwa Taj, ba zai taSa tsallake aurenta ba. Shi yasa da baya yi mata zancen soyayya bata wani damu ba. Aure ne dai za ayi kamar yadda Hajja ta al?awarta mata.

Da safe ma gidan babu wata walwala. Kowa kai kawo yake kamar ana tura shi. Ga tafiya Kanon da Amma ta so yi Hajja ta hana Daddy yi mata izini.

*

Taxi Taj ya shiga har gidan. Maigadi ya riga ya san shi saboda haka ba a tsaya sanar da mutanen ciki ba ya buWe masa gate. Agogo ya kalla da ya isa ?ofar shiga gidan. Goma da rabi ta Wan wuce. Sanin ba Amma bace kaWai a ciki dole ya sanar da zuwansa don ayi masa izinin shiga. Wayarta ya kira tana gani ta taSe baki, Sacin ranta ya dawo sabo. Har kiran ya katse bata Wauka ba. Ya kira yafi sau shida kafin ta daure ta amsa.

"Ina jin ka." Ta ce a kausashe duk da wani Sangare na zuciyarta yaji daWi. Ta tabbata tana ransa tunda ya yi asubancin zuwa gareta.

Ya san za a rina. Ya kwantar da kai ya faWa mata yana bakin ?ofa.

"Yau kuma gidan sirikinka ne da ba za ka shigo ba?"

"A'a, dama saboda naga safiya ce..."

"Bana son gulma. Shigo ina falona."

"Tuba nake Amma." Ya faWi yana buWe ?ofar.

Abin da ya guda ne ya faru. Anisa da ?annenta duka ya samu a falon suna breakfast kowacce da kayan bacci. Ba abin ya koma ba ya riga ya sako kai. ?auke ido ya yi daga kallonsu ya yi musu sallama. Aka rasa mai amsawa don kishi su ke taya yayarsu, sai ita Anisan. Mai binta ta banka mata harara. ?aramar kuma ta ja dogon tsaki.

"Aikin banza."

Ko kallonsu bai yi ba ya wuce falon Amma. Uzurin ?uruciya ya yi musu kawai. Kuma dai abin kunya ne ya biye musu. Yana ji suna ta tsaki. Ita kuma Anisa tana yi musu faWan basu kyauta ba. Yana wucewa su ka yi rige rigen sanarwa Hajja da Anti zuwansa.

A zaune ya tarar da Amma. Ita ma ko wanka bata yi ba. Komai nata a hargitse saboda rashin kwanciyar hankali.

Jikinsa a sanyaye ya ajiye jakarsa a ?asa ya zauna a gaban ?afafunta.
"Don Girman Allah Amma ki yi ha?uri. Wallahi ba da gangan nayi ba."

Rai na ?una ta ce "Kayi ne saboda ka nuna min irin nawa matsayin a wajenka?"

"Ban isa ba wallahi. A gaggauce komai ya faru."

"Bayan ya faru Win kuma sai ka manta sunan da ka sanya min a wayarka balle ka kira ko? Haba Taj. Aure fa kayi. Nayi zaton ina sahun gaba cikin waWanda ya kamata su sani ko da wacce irin gaggawa ya zo maka."

Shi ma ya san bai kyauta ba. A daren da Alhaji ya yi masa izinin auren ya dace ya gaggauta kiranta. Sai gargaWin Alhajin ya tsaya masa a rai. Shi ya hana shi faWawa su Inna. Idan ya kira Amma ya tabbata sai ta faWawa su Inna. Ita Win sam bata tsoron Alhaji. Akan Taj ma sai ta ?ure take yi masa magana. Gudun kada ta Sallo masa ruwa yasa shi kama bakin nasa. Bai ?ara tunawa ba kuma sai bayan sun kama hanyar gida da Kamal. Duka wannan bayanin babu lallai ita ko wani ya auke shi a matsayin uzuri. Kawai ya yarda bai kyauta ba, ya bata ha?uri shi ne mafi a'ala.

"Don Allah ki yafe min. Ki kuma saurari bayani na ko da ba zai gamsar dake ba."

"Baka da abin da za ka faWa min Taj. Ka koma gaban iyayenka tunda dama na san burinka kenan. A nawa tunanin dai ko me zai faru ba za ka manta dani ba." Tayi maganar da ?walla a idanunta.

"Har yanzu Alhaji bai sakko ba. Su Hajiya ma basu san da auren ba sai bayan an Waura. Ke kuma gani nayi bai dace ba ace ta waya na faa miki."

"Ban yi fushi ba. Ka dai koma Kanon tunda ka zama mijin aure. Allah Ya baku zaman lafiya." Ta mi?e.

"Amma ki yafe min mana don Allah."

"Ai nace raina bai Saci ba. In an tashi bikin ka daure dai ka faWawa ?an uwanka su Ihsan."

Da yaga dai rarrashin ba zai yiwu ba sai ya marairaice mata.

"Amma na baki ha?uri kin ?i. Ina son yi miki bayanin yadda auren ya zo ma ba ki son ji. So ki ke dole ki nuna min ni ba Wanki bane. Banda haka ai ko gudun kada auren ya?i albarka za ki sassauta min." Hawaye yaga ta goge, ta kalle shi a raunane ya cigaba da magana "haihuwata ce fa kawai baki yi ba amma ina ji a jikina ko tsine min ki ka yi sai ta bi ni."

"Tsinuwar lafiya Taj? Kada na kuma jin wannan kalmar a bakinka."

Ya sake kwantar da murya "To ya kike so nayi? Fushinki ba zai barni naga hasken rayuwa ba."

"Allah Ya tsareka Taj. Zauna mu yi magana" ta ce a rikice. Bata son ganinsa a yanayi irin wannan ko kaWan.

Daga bayansu su ka ji muryar Hajja da basu san tun yaushe take tsaye a bakin ?ofar ba tana cewa.

"Shegen baki kamar rainon cikin gari. Na rasa me yasa ba a taSa cin galabarka a magana." Ta nuna Amma "ke kuma da ya soma kalallameki sai ki bada kai bori ya hau. Da Wan cikinki ne ya yi min haka wallahi ba zan masa da sau?i ba. ?an ri?o dama ai ba Wan goyo ba. Kayan aro bai taSa rufe katara."

Bayan Hajja ashe harda Anti da su Anisa. Daddy ne kaWai basu iya zuwa kai wa rahoton zuwan Taj ba.

'Duk zan iya da ku' Taj ya faWi a ransa. Ya je bakin ?ofar ya ri?o hannun Hajja ya zo ya zaunar da ita.

"Na Wauka ko me zai same ni a waje idan na shigo gidan nan Hajja zan sami kwanciyar hankali. A wurin Wanki na sami baban da bai taSa ?yamar sana'ata ko goranta min don mahaifina ya kore ni ba."

"Shi ne ka kasa yi masa alfarmar auren ?arsa ba. Ko don ba Jamila ta haifeta ba?"

Taj ya girgiza kai "kinga inda matsalar take ko? Komai nayi sai kun fassara saboda baku Waukeni Wa ba. Da ace Daddy ne ya haifeni hukunci kawai za ku yi min da faWa akan laifina na. Ba sai anyi ta zancen asalina ba."

Duk fushin Hajja bata san lokacin da tayi murmushi ba "Tajo kenan. Wannan baki dai ba na ubanka bane. Shi banda haWe rai bai iya komai."

"Baki taSa zuwa bayan magariba bane. Da har dariyar Alhajinmu sai kin ji."

"Wa yaga tarangahoma. Dariyar Hayatu ai tsorata mutane za ta yi."

Taj ya yi murmushi "wallahi Hajja ke kaWai za ki taSa min tsohona in share saboda kin isa. Kaka na Wauke ki ba surukar Amma ba."

Kwashewa tayi da dariya. Ta bar Anti da Amma da mamaki.

"?an duniya. To ka gama kalallame mu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login