Showing 48001 words to 51000 words out of 182745 words

Chapter 17 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

93

kujerar sai an zagayo gabanta.

Da yake a office Win ba a jin hayaniya sosai shiyasa wajen ya yi mata shiru. Tunanin yadda aka yi mutumin da ta gani a makarantarsu ya zama Taj Win da ya karaWe bakunan ?an gidansu ta fara. Sai dai bai je ko'ina ba bacci ya yi awon gaba da ita saboda daWin waje. Gajiyar jiya da yau da su ka kusa kwana yin meatpie da samosa ce ta dirar mata gadan-gadan.

*

Taro ya yi taro. Iyaye da yara, matasa da dattijai kowa ka gani nishaWi da farinciki kawai yake yi in banda Salwa. Tunda ta ga Anisa taji komai ya rikice mata. Yarinyar bata da makusa ko kaWan. DaWinta Waya shine gani da tayi ta fita haske nesa ba kusa ba. Anisa black beauty ce. Idanu dara dara da hanci mai tsini. Sai Wan bakinta madaidaici. Ita kuwa irin fararen nan ne da mazan Kano a wancan lokacin su ke fatan samu ko da mayya ce. Maminsu tana da haske bakin gwargwado. Amma mahaifinsu bafullatani ne fari tas daga garin Dambam. ?a?ansa duka babu ba?i. Ga kwantaccen gashi da kyawun fuska. ?an murmushi tayi. Babu yadda za ayi Taj ya tsallaketa ya so wata Anisa. Da wannan ya?inin ta saki ranta aka cigaba da sha'ani cikin walwala.

Kamal Sangaren boutique Winsa ya nufa inda ake ta ruwan ciniki. Shi da yaran shagon babu wanda ya sami kansa balle ayi batun nutsuwa. Tuni ya manta da Hamdi da ya kai office Win Taj.

Ana kiran la'asar mutane su ka fara gangarawa kyakkyawan masallacin dake kusa da garden Win wurin. Wani hafizin matashi Taj ya samu zai dinga limanci a wajen. Saboda haka ko babu niyar siyayya sawu ba zai Wauke ba ga ?an unguwa da su ka sami masallaci mai kyau irin wannan.

Yana jin kiran sallar ya so tafiya yin alwala amma abu ya gagara. Kitchen Win nasu ya rikice da aiki duk da sun gama tanadin abinci kafin a fara zuwa. Ba shi ya sami kansa ba sai biyar saura.

"Subhanallah" ya furta hankalinsa na tashi "Abba ku ?arasa zan je nayi sallah." Ya ce da Abba Habibu da ya naWa Sous Chef, wato mataimakinsa.

Masallaci ya yi niyyar tafiya sai yayi tunanin mutane za su tare shi. Musamman ?an uwansa da su ke ta son ayi hoto. Ciki ya koma. Ya hau sama da bibbiyu. Nan ma a cike yake da mutane. ?akunan taronsu ne kaWai a rufe. ?ofar office Winsa wanda Hamdi bata kula da label Winsa ba da za su shiga an rubuta EXECUTIVE CHEF.

Da sauri ya buWe office Win ya shige ya rufe ?ofar don kada wani ma ya ganshi. Ya faWa toilet yayi alwala. Rigar uniform Winsa ta chef dake fitar da ?amshin kitchen ya Wan tattaro ya kara a hancinsa. Guntun tsaki ya yi ya Salle maSallan da su ka ?awata ta daga wuya har ?asa, daidai saman cinyarsa inda yake daura apron. Wurgi ya yi da ita kan cushion chair Win da ta bashi baya ya nufi closet inda yake da irinsu spare har goma sha Waya. Kowacce set ce farar riga da farin wando. Jerin round maSallen ne kawai ba?a?e. Wata rigar ya Wauko, ya zare ta daga hanger ya mayar da wandonta.

Baccin Hamdi ya soma nauyi don ta fara mafarki mai daWi taji wani abu ya faWo a fuskarta. ?amshin turare mai Wan karen daWi ta fara sha?a sai kuma taji na girki. A hankali ido har lokacin a rufe ta sake danna rigar a hancinta. Ta soma murmushi ita kaWai sai kuma ?wa?walwarta ta farka ta tuna a ina take. Bata san lokacin da ta ture rigar da sauri ta kuma ?walla salati da ?arfi ba. A tsorace ta tashi ta kallo bayan kujerar.

Taj ma saitinta ya kalla da riga a hannu. Allah Ya so shi akwai vest a jikinsa wadda ya yi tuck-in da ita a cikin wandon.

"Abbanaaaaaa" Hamdi ta faWi tana kai hannu ta Wauki throw pillow Win kujerar ta jefa masa. Sakin rigar ya yi ya cafe pillon yana cigaba da ?arasowa inda take. Kallo Waya ya yi mata ya ganeta. Mamakinsa dai me take yi a office Winsa kamar aljanna?

Da hannu ya dinga yi mata alamar tayi shiru amma ta?i.

"Shhhh, zan miki ihu nima."

Kama bakinta tayi ta Same. Sannan ta lura da bashi da riga. Ba shiri ta Wauki wadda ya wurga kan kujerar ta cilla masa.

"Ya Salam!" Ya ce da sauri don ya ma manta yanayin da yake. Ya koma ya Wauki wadda ya fiddo yanzu ya saka. Baya su ka juyawa juna daga inda su ke tsaye har ya gama Salle maSallan.

"Uhmm" ya yi gyaran murya "how did you get here?"

Muryarsa kamar yadda ta tuna ta ba ta mata bace. Irin deep masculine voice Winnan wadda sautinta yake ratsa zuciyar mai saurare.

Gwanar a tsiwace ta amsa. Ba don zuciyarta ta so hakan ba. Sai don kawai tana son yakice shi daga ranta. Saninsa bashi da wani amfani. A dalilinsa yau wanda bai san Abbansu ba ma ya sani. Kuma ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? tabbata haka za a tafi ana cewa Wan daudu ne.

"Wani Kamal ne ya kawoni da ina jin jiri."

"Subhanallah, kin ji sau?i yanzu? Ko a je asibiti?" Taj ya ce da kulawa.

"Na warke."

"Alhamdulillah. Allah Ya ?ara sau?i. Da alama kema ba kya son gatherings. Ni kaina da zan iya da zamana zan yi. Taron mutane indai ba costumers bane bana so."

"Allah Sarki. Amma ni ina son taro, ciwon kan na gajiya ne" Hamdi ta yi magana tana yamutsa fuska.

Taj yana lura da ita. Bai san dalilinta na yin hakan ba. Uzurin rashin lafiyar kawai ya yi mata.

"Bari nayi sallah na baki wuri."

"Hhhhh" ta buWe baki tana kallon agogon office Win. Biyar saura minti uku. Kamar za ta yi kuka ta ce "ban yi sallar ba nima."

Toilet ya nuna mata. Ta tsaya turus tana kunyar shiga banWaki a gaban shi. Murmushi ya yi kawai ya fice. Ita kuma tayi alwala ta fito tayi sallah. A kullum idan sallah ta kama ta a waje tana yiwa Allah godiya da Yasa iyayensu tilasta musu shiga da mutumci. Idan ka gansu dole su burge ka. Ga kyau ga sanin darajar kai.

*

Magariba Taj ya so taro ya watse sai gashi kamar a lokacin ake tuttuWu mutane. Shi da ma'aikatan sun gama kaiwa ma?urar gajiya. Tun suna dafawa a marmace har idan sun ga sabuwar oda sai su ji kamar su ce ba za su karSa ba.

"Don Allah ku saka CLOSE sign a ?ofar restaurant Win." Cewar Taj yana fiddo wayarsa daga aljihun wando. Shugabannin bakery da masu nama ya kira ya ce idan sun gama da mutanen dake gabansu su fara shirin rufewa. Yana gama wayar Abba ya ce masa da ya sani bai ce a sallami mutane ba.

"Albarkar da muke nema ce ta samu kake neman ture ta?"

Taj ya sadda kai "ba manufata ba kenan Abba. Naga gobe za mu fara aiki officially. Idan bamu sami isasshen hutu ba zamu iya farawa a ga gazawarmu."

"Ko kusa. Dagewar yau ita za tasa ma'aikatanka su gane aiki ka ke so ba wasa ba. Maimakon a sallami mutane mu bari komai na yau ya ?are. Babu yafi daWi akan mun tashi."

Taj yaji daWin shawarar Abba. Shi yasa ake cewa tafiya da gwani da akwai daWi. Sannan iyawa kaWai ba ta tafiya daidai sai an haWa da experience. Tsarin wasu ?asashen ya sani akan harkar restaurant. Abba kuwa ya jima cikinta a gida Nigeria kuma garin Kano.

Suna haka aka dinga kiran Abba amma ya?i Wauka. Aikin gabansa yake son kammalawa. Taj sai ya ?arba. Ha?uri yaji ya bayar da al?awarin an kusa tashi. Da ya gama ya dubi Taj yana murmushi.

"Hamdi ce uwar rigima. Wai in fito mu tafi tana jin bacci."

Taj sai yaji babu daWi. Tara saura amma kamar yanzu aka fara aiki.
"Shi yasa nace a tashi. Dare na ?ara yi."

"Kada ka damu, muna fita za mu sami adaidaita sahu. Bana son su tafi su kaWai ne dai tunda duhu yayi. Nayi zaton zamu iya gamawa da anyi magariba."

"Bari na kira Kamal ko sun gama. Motarsa ai za ta ishe ku ko?"

Abba ya yi dariyar jin ana tambayarsa ko mota za ta ishe su "Adaidaita Waya ma yana isar mu. Zee a sama, Halifa a kusa da direba. Mu uku a tsakiya."

"A sama kuma? Saman nan dai na bayan seat?"

"Eh mana."

Abin Waure masa kai ya yi ya ce "Ninke ta za ayi ko lan?wasawa?"

Abba ya dinga dariya. Har su ka gama Taj na mamakin zancen zaman sama. Da su ka fito sai yaga har gara wurinsu. Boutique Win Kamal ya cika da samari da ?an mata. Mu?ullin motarsa ya karSa ya ce masa zai kai su Abba gida.

"Za ka iya dawowa kuwa?"

"Me ka mayar dani ne? Zan dawo mana."

Kamal ya yi dariya "a dinga haWawa da in sha Allahu dai."

Da ya fita shima Abba tambayar da ya fara yi masa ita ce ko zai gane hanyar dawowa. Ya nuna babu wata matsala sai su ka tafi. Abba na gaba, ?a?ansa na baya. Hamdi tana ta faman kumbure kumbure don ita bata son ma a gaba ace suna cin arzi?i.

Waya Abba ya gama da Yaya ya sanar da ita suna hanya. Ya duba missed calls.

"Ashe kin yi ta kira bayan wadda na Wauka Hamdi? Ban ji ba ne."

"Ai Abba ?iris ya rage ka fito kaga tana kuka. Ka san yadda bata son zuwa taro."

Saurin kallon madubi Taj ya yi kamar ta sani kuwa ita ma ta kalla. Maimakon taji kunyar ?aryar da tayi masa sai ta juya idanu ta murguWa baki.

"Kin yi kyau." Ya furta idanunsa har lokacin a kanta ta madubin.

"Wa?"

Abba ya faWi yana kallonsa. Su Sajida ma duk sun zuba masa ido su na jiran amsa.

"Wata mota ce ta wuce yanzun nan. Ba don motata ta kusa isowa ba da ita zan saya."

A haka zancen ya mutu. Lokaci lokaci suna haWa ido ta madubi tana harararsa. Sai bai damu ba. Zuciyarsa tana raya masa tabbas ya yi mata laifi ne. Laifin da yake ganin ba zai wuce na rashin nuna mata ya santa ba lokacin da su ka haWu a Abuja.

Ya kai su gida lafiya amma komawa ta gagara. ?arshe sai Abba ya kira saboda rashin dacewar neman ?an mata sha Waya da rabi na dare. Da kwatancem Abban ya fita daga unguwar. Yana tafiya a hanya yana nanata 'in sha Allah ba zan kuma Sata ba.'

***

Satin farkon buWe Happy Taj lokaci ne da Taj da Kamal ba za su taSa mantawa dashi ba. Sun sami ciniki da yawaitar al'umma fiye da tunaninsu. Taj gani yake hakan ba ya rasa nasaba da addu'ar da Alhaji ya zo ya yi musu daren da za a buWe wajen. Da kuma ta iyaye. Sai kuma saukar karatun da su ka yi shi da Kamal da sadaka domin neman Allah Ya sanya musu albarka. Kuma Ya tsaresu da wurin kansa daga zamewa al'umma fitina.

Duk da ya yi sanarwar gama Waukan ma'aikata to amma fa har lokacin mutane basu fasa kawo takardun neman aiki ba. Ya rufe ido ya ?ara Waukar masu shara da wanke toilets. Da kuma masu wanke-wanke da shara. Irin aikinka, irin uniform Win da za a Winka maka da suna idan an Wauke ka. Bakery ne kawai ya bar space Win Hamdi. Da gaske yana son yin aiki tare da ita. Ya yabawa iyawarta sannan yana kusancinsu zai taimaka masa ya sami soyayyarta.

Baya son yin garajen fara nuna mata soyayya a yanayin da ake ciki. Bai san yadda Abba ma zai Wauki maganar ba don ya kula yana da gudun rigima. Balle kuma Alhaji. Idan ya ?yaleta haka kuma tabbas zai ji labarin wani ya yi masa shigar sauri. Da wannan shawarar ya tunkari gidan ranar wata lahadi, ana saura kwanaki huWu kamun Sajida.

Cikin gidan ya fara shiga su ka gaisa da Yaya. Bayan sun Wan taSa hira ya tashi ya ce ta turo masa Sajida. Kuma sarai ya san Sajidan bata nan. Tun zuwansa aka ce tana wajen gyaran jiki. Zee kuma ta tafi karSo Winki.

"Daddawar Waka ce kawai a gidan."

Kamar bai san wa take nufi ba ya ce "gaskiya a ?annena babu daddawa."

"Ashe baka san Hamdi ba. Kana kallo dai tun shigowarka ta shige Waki. In ba kiranta nayi ba kuma da wuya ka sake ganinta har ka tafi."

Daga Wakin Hamdi ta zumSura baki da kwance zanin da Yaya take yi mata.

"Sai ki fito don na san kina jina." Yayan ta Waga murya.

Taj bai ji ta amsa ba har ya isa zauren ya tsaya. Ya sa rai za ta jima sai gashi bai fi minti biyu ba ta fito. Bakin nan a gaba.

"Kya hua Hamdiyya?" Ya zolaye ta.

Shi yake yaren ita take jin kunya.

"Ba na jin indiyanci."

"Na ga mata suna son movies Winsu. A nan ku ke tsintar kalmomi. Sisters Wina dai na san haka su ke."

"To banda ni. Ba na kalla. Kuma namiji mai gani ma ba kula shi nake ba."

"Allah Ya so ni kenan." Taj ya ce yana neman haWa ido da ita amma ta ki yarda.

Mamaki ya bata don bata yarda da furucinsa ba ta ce "Ba ka gani?"

"Ko Salman Khan Win da ki ka kirani rannan ban sani ba."

"Allah ban yarda ba" ta ce kai tsaye.

Taj ya yi dariyar da amonta ya zauna daram a zuciyarta. Bata sani ba ko ana kiran maza cute. Ita dai da yana dariyar nema ya yi ya sauke mata bangon da take ginawa a tsakaninsu. Shammatarta da ya yi da tambayar da fito daga bakinsa ce ta yanke mata shagalar da ta so yi.

"Laifin me nayi miki ne da ya zamana tsakaninmu babu kallon kirki sai harara? Ko don ban faWa miki na san ki ba a Abuja?"

Shiru tayi. Ya sake maimaita tambayar amma sai ta kawar da kanta. Bai yi fushi ba ya ajiye girma da matsayinsa ya faWa mata abubuwan da su ka wakana tun lokacin da Firdaus ta faWa masa sunanta da biyota gida da ya yi.

"Dalilinki na zo gidan nan amma yanzu ba don ke kaWai na nemi kusanci da Abba ba. Ina ji a jikina zamu amfani juna in sha Allah."

Kasa magana tayi. Sai tunani da yawa da take fama dasu. Da yaga tayi shiru ne ya nemi jin ta bakinta. Sai ta faWi abin da bai taSa tsammani ba.

"Da Abbanmu ya rasa wajen sana'arsa nayi murna ni dai. Na so ace wata sana'ar ya samu ba komawa girki ba."

Taj yaji tamkar ta watsa masa ruwan zafi.
"Kema ba kya son namiji mai girki ne? Ko kuwa wanda ya taSa rayuwa irin ta Abba?"

"Mene ne maraba? Duk namijin dake girki ba Wan daudu sunansa ba? Har yanzu ba sunan da ake kiran Abbanmu kenan ba saboda ya?i yin wani aikin sai na mata."

"Daina magana irin haka Hamdi" Taj ya kwaSeta "yanzu har za ki iya aibata sana'ar da mahaifinki yake yi miki komai cikinta kuma wadda Allah bai haramta ba?"

Kuka ta saka masa "Baka ji muryarsa ba? Idan yana tafiya meye marabarsa da ma..."

"Ya isa..." ya kaWa kai yana mamakinta ?warai da gaske "indai za ki iya waWannan maganganu akansa to waye a waje ba zai yi ba? I thought idan kowa ya ?yamaci mahaifin mutum shi yana son abinsa."

"Nima ina son sa. Amma wallahi bana son sana'arsa." Ta kalle shi ido cikin ido "kuma bana son duk wanda zai taimaka masa akan cigaba da sana'ar girki."

Tunowa da Alhaji ya dinga yi da kalamanta masu Waci. Cikin Sacin rai ya ce "nima ban ce ina son ki ba. So kada ki yarda ki min rashin kunya akan sana'ata. I am a Chef and I love what I do."

Bata san ta Waga murya ba ta ce "to wa ya hanaka dama? Meye na sanya Abbana a ciki?"

A ganinsa bata ma cancanci ya faWa mata kuWurinsa na taimakawa Abba ya rage ko bai daina duka abubuwan mata ba. So yake ya nuna masa zai iya sana'arsa cikin nutsuwa ba tare da ya yi koyi da mace ba. Shi yasa ya Wauki ri?a??un maza waWanda ko magana su ka yi sai an san namiji ne na gaske aiki. Girki daban, daudu daban. Wannan abin yake so hausawa masu fahimta irin ta Alhaji da wannan mara kunyar yarinyar da yake jin soyayyarta har yanzu su gane.

"Saboda na isa." Ya faWi don taji haushi.

"Me kake nufi? Abbana yaronka ne?"

"Uba na Wauke shi mai sawa ya hana. Wanda kuma da ni ya haifa ba zan guje shi ba."

"Na ce maka ina son Abbana. Girkin ne bana so."

Ya zata yi ya fahimceta? Indai Abba bai daina sana'arsa ba, gani take ba zai taSa rabuwa da Wabi'un da ya koyi girki cikinsu ba na daudanci. Idan mutum yana abu maras kyau a ganinta nesanta dashi, shi ne yafi alkhairi.

Shi kuma Taj so yake ta gane cewa sana'ar ba ita ce ta mayar dashi haka ba. HaWa biyun da mutane su ke yi, shi ne musabbabin da yasa mazan dake son girki da dama a ?asar hausa su ke karkacewa su yi koyi da jinsin mata. A ganinsu kamar girki ba zai cika ba sai da waWannan Wabi'un.

Ran kowa a Sace su ka rabu. Don ko amsa bai iya sake bata ba ya fice abinsa. Ita kuwa tana shiga gida taji saukar lafiyayyen mari daga wajen Yaya.

Huci take rai a Sace "ki ka ce ba ki son duk mai taimakon mahaifinki akan sana'arsa Hamdi? Saboda kin tashi duk runtsi duk wuya bai taSa ?in kawo abin da za a ci a yi sutura ba? Ashe baki dawo daga rakiyar zuciya ta ?yamar babanki ba?"

Hannunta akan kumatu tana jin zafi har ranta ta ce "Yaya ku daina yi min irin fahimtar nan. Ina son Abba mana. Girkin ne kawai...Yaya har yanzu muryar mata gare shi fa"

Sai kuka mai cin rai. Yaya ma kukan take yi. Duk cikin ?a?anta dama kafiya da sanya abu a rai babu wanda ya kai Hamdi. Kowa na zaton rigimarsu da Ummi ta kashe mata waccan ?iyayya. Ashe har yanzu bata son sana'ar. To amma wacce take so ya yi? Bayan mutane suna da wuyar uzuri da ?arSar kuskure. A yanayi da Wabi'unsa, duk inda ya sanya ?afa neman taimako ko son fara sana'a sai ace Wan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login