Showing 96001 words to 99000 words out of 182745 words

Chapter 33 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

117

gamo da Amma. Rabonta da shigowa gidan yayan nata an jima.

"Takwara oyoyo" Umma ta ce daga bayan Inna da ta kasa magana.

"Yauwa Takwara" Amma ta ce, ita da su Mama su ka bi Inna da kallo.

Murmushin dole tayi musu gami da yiwa Amma sannu da zuwa sai ta shige Waki. Ta manta da mai kitson sai da ta ganta zaune tana jiranta. KuWin kitson ta bata sannan ta ce ta tafi za ta nemeta daga baya. Matar bata matsa ba don ta lura Inna bata cikin nutsuwa. Uwar Waka ma ta shige ta rufo ?ofa. Wayarta ta Wauka ta kira babban wanta. Tana jin muryarsa ta fashe da kuka.

"Me yake son ya mayar da rayuwar yaron nan? Shi ba fasi?i ba, ba Sarawo ko Wan fashi ba. Amma ace duk wani abu dake nuni da ba a son mutum akansa yake ?arewa?"

Rarrashinta ya yi sannan cikin kuka ta labarta masa abin da ya tunkaro su kuma.

"Ina jin lokaci ya yi da zan nunawa Hayatu bai fi ni zafin kai ba. Turo min lambar baban ita matar Taj Win. Sati na sama in sha Allahu za ta tare. Idan ya kuma barazanar rabasu kuma ni da kaina zan Wauki mataki."

"Yaya ita kuma tsohuwar matar tasa fa?"

Dariya ya yi ta manyan dattijai "kinsan Allah, barazana ce kawai. Hayatu da wuya yake yar da abu ya waiwaye shi. Abin da ya raba shi da Habibu kenan tun farko. A yanzu kuwa ban hango zai taSa yarda babar Ahmad ta zama surukarsa ba. Rabuwarsu ba ta daWi bace."

Nutsuwa ta samu da wannan wayar. Ta fito falonta don zuwa wajen Amma ta gansu duka zaune. Umma ta faWa musu abin da ya faru. Su ka haWu suna bata baki. Tun bata son nuna ai Wan cikinta Alhaji yake yiwa haka har ya kai ta fito tana faWa da bakinta.

Su ka haWu da Amma su ka bata baki. Auren ?ar Mami kuma ko Taj ne ya kwaso da kansa ba za su yarda ba. Suna wannan tattaunawar Alhaji ya shigo Sangaren nasu. Ganin babu kowa ya tambayi ina su ke. Aka ce su na Wakin Inna. Juyawa ya yi bakinsa alekum ya fice, musamman da yaji cewa Amma ta zo. Sake hargitsasu za ta yi ta zuge su tas. ?arshenta in bai yi da gaske ba sai anyi sa'in'sa a gaban mutane idan ya ce zai nemasu yanzu.

***

Sai washegari Taj ya sami ?warin fita sosai. Jiya da su ka yi waya da Hamdi ya ce zai je Happy Taj ta ce ya bari ya ?ara hutawa.

"Kin isa matar Happy. Dama tunda Happiness ya yi tafiya na san ba wani daWin wajen zan ji ba sosai. Da ni Wan gata ne dai sai ki zo ki tayani zama." Yayi maganar a hankali.

"Na?i wayon. So ka ke Abba ya tsireni? Yana wajen sai na zo na wuce."

Marairaicewa ya yi "A misali da ba zai yi faWa ba za ki zo? Uhmm? Allah naji jiki fa. Ga rama."

"Kullum fa ina kiranka."

"Kira daban, gani da ido daban. Kin san fa babu jinya mai daWi kamar kayi a gaban matarka."

Hamdi tayi dariya. Da alama Taj kallon yarinya yake yi mata. Shi ne zai yi mata wayo.

"Allah ko? Saboda me?"

"Ana yi ana petting Win mutum. Ga pecks here and there. Sai ka manta ma da ciwon." Ya bata amsa yana jin dama so samu ne.

Ba?uwar kalmar da taji ta tambaye shi.
"Meye kuma pecks?"

Taj na jin haka ya tashi zaune yana ?ar dariya. Ashe ma wayon da take ta zillewa zai yiwu.

"Peck Win ne baki sani ba? Ko dai kin faWa ne?"

"Allah ban san shi ba. Pecks naji ka ce."

Da fatan kada ta Wago shi ya ce "Da yawa ne pecks. Gashi akwai nauyi da na Wauko miki."

"Idan da rabo sai na gani watarana."

Duk a zatonta wani abu ne da ido zai iya gani kuma hannu zai Wauka.

Dama ce ta zo wa Taj bayan sun gama wayar da yamma. Mama ta kira Yaya ta sanar da ita za su zo washegari ita da su Amma. Wasu daliliai sun janyo suna son ayi biki sati mai zuwa. To dama su ma suna ta Wan shirinsu don ba a zauna haka ba.

Yaya sai ta kira Hamdi ta ce ta tambayi Taj ko gidan Sajida ne gobe ta tafi.

"Idan baki je yanzu ba aka fara biki za ku kwana biyu baku haWu ba."

DaWi ya kama Hamdi. Tana ta murna ta kira shi. Sai ya ce ta shirya shi zai zo ya kaita.

Shi ne fa yau ya shirya yau cikin nishaWi. Happy Taj ya fara zuwa. Akan idon Alh. Usaini ya wuce. Nan da nan ya kira Ummi ya ce aikinsu zai iya yiwuwa yau. Da alama Taj ya dawo aiki. Tunda suna ta kula da shige da ficensa tun bayan sun gama shirinsu. Sai dai bai ?ara zuwa ba sai yau Win.

Kai tsaye Salwa Ummi ta kira. Don dama Alh. Usaini bai yarda Salwan ta san shi ba. Ko ta kwaSe sai dai su ?are tsakaninsu da Ummi. Tana zuwa Ummin ta bata turarukan da Alh. Usaini ya bayar. Guda biyu ne masu wani irin Wan karen ?amshi. ?aya a yadda Ummin ta faWa mata zai haddasa faWa tsakanin Hamdi da Taj. ?ayan kuma zai haWa ?a??arfar soyayya tsakaninta da shi.

"Amma me yasa ki ke taimaka min Ummi?" Salwa ta tambayeta bayan ta karSi turarukan.

"Saboda ba zan taSa sanya ido Hamdi ta zauna a gidan miji alhali ni ta hana ni aure ba."

Da farinciki Salwa ta ce "Allah Ya bani ikon taimaka miki nima a duk lokacin da kike bu?ata."

"Amin"

Bayanin yadda zata saka turaren Ummi tayi mata. Ta fito za ta tsallaka ta shiga Happy Taj sai taga motar Taj Win yana fitowa. Hankalinta ya tashi. Ummi ta ce kada ta damu. Su jira zuwa la'asar domin indai ya shigo ko ya fita da wahala a rufe wurin baya nan. Jin haka sai ta sami wuri ta zauna su ka cigaba da ?ulla yadda za ayi bikin Salwa da Taj bayan sun yi nasara.

***

Zee ce ta yiwa Hamdi light make up sannan ta shirya. Doguwar rigar atampa ta saka wadda take fitted daga sama. Sai kuma aka buWeta daga ciki har ?asa. Turarukanta na scentmania tabi ta shafe jikinta dasu.

"Don Allah Ya Hamdi a dinga ragawa Salman Khan."

"Wallahi zan miki rashin mutunci akan kiransa Salman Khan."

Zee ta dinga dariya. Suna gama Waurin Wankwali ya kirata. Yaya tana son yi mata Wan gargaWin manya amma kuma ta rasa me ya dace ta ce. Miji da mata wane gargaWi kuma za ayi musu wanda ba zai shiga hurumin shari'a ba? ?arshe dai sai cewa tayi,

"A kula da kai dai. Banda yin abin da bai dace ba."

Tunda ta fito ya kasa Wauke ido daga kanta. Yana mamakin yadda ya mallaki wannan yarinyar da ya taSa gani tana practicing speech. Ganin farko ta kanainaye masa zuciya. Ita ce first true love Winsa. Ya kuma yi sa'ar zama mijinta.

Daga ciki ya buWe mata ?ofa. Sai da ta zo shiga ta fara jin faWuwar gaba. Ta kasa gane ta murnar ganinsa ce ko ta tsoron fitinarsa, ko kuwa ta wani abin daban da bata sani ba?

Zama tayi ta rufe ?ofar sannan ta gaishe shi. Tana yi tana kawar da kai daga kallon fuskarsa. Ta san yanzu yana ganin kwalliyarta zai ce kama tsokanarta.

"Mrs Happy yau kuma ?ar Soye fuska ce? Irin yanayin nan da Indians..."

A gaggauce ta Waga fuska su ka haWa ido.

"Kada ka ?arasa. Ka bar Indiyawa su sarara don Allah."

Lumshe ido ya yi ya buWesu akan fuskarta.
"Na barsu. Yau ko su basu da kalaman da zan yabawa Hamdina." Yatsa Waya ya Waga a gaban fuskarsa "In ce awwnnn sau Waya don Allah?"

Riga shi tayi harda fari da idanu "awwnnnnn"

Taj ya sanya hannayensa duka a saitin zuciyarsa "yarinyar nan za ki kashe ni. That was just too cute."

"Tunda kaga ba kai kaWai ka iya ba don Allah ka daina."

"Ban yi al?awari ba. Atleast zan cigaba kafin na samu wani abin tsokanar taki."

Tu?i ya fara a hankali suna tafiya Hamdi ta sake yi masa sannu da jiki.

"Ka rame da gaske fa."

"Sauron garin nan wasa ne? Jiya na kira mai kula da gidanmu na ce su duba duk wata ?ofa ko window a saka net." Don jin me za ta ce ya ?ara da cewa "ko mu je ki gani?"

"Allah Ya baka ha?uri. So kake Yaya ta ce a biyoni da kayana kada na dawo gida yau?"

"To ba shikenan ba. Kowa ya huta."

Cewa tayi bata yarda ba. Ya ce sai ya kaita. Dama ya kamata su gaisa da Amma. Tunda tana can da su Umma kafin su je wajen Yaya sai su haWu. Hamdi ta rikice sosai don ya auke hanya daga inda ta kwatanta masa gidan Sajida. Ya gama janta sannan ya ce Happy Taj za su fara zuwa.

Narke masa fuska tayi "so dai kake dole yau nayi laifi ko?"

"Ba zama zamuyi ba. I just realllyyy need to show you that peck."

Zazzaro masa idanu tayi "da ka bari ma kawai..."

Taj ya kama dariya "yau wata za ta yiwa Abba bayani. Ki ka ce min baki sani ba."

"Muna gama waya na duba a google." Ta bashi amsa da ?aramar murya.

"Wannan fassarar google ce. Ni dai sai na nuna miki."

"Don..."

"Shhhhh. Ba a faWa miki babu kyau ro?o ba?"

Wanda baya jin magiya biye masa kawai ake yi. Daina zancen tayi ta karkata zamanta ta zuba masa idanu yana tu?i.

"Mene ne?"

"Jira nake muje ka nuna min peck Win nan."

"Haaa, shi yasa nace kalarmu Waya. Ni dake duk fitinannu ne. Allah dai Ya shiryemu."

Juyo da abin kanta ya yi ya dinga tsokanarta har su ka isa akan idon Salwa don ta riga Ummi ganin motar tasa. Nan gabanta ya cigaba da faWuwa kada su haWu da Abba. Taj ya buWe mata wata ?ofa ta baya wadda directly office Winsa za ta kai mutum.

"Emergency exit ce for naughty people like us."

"Banda ni."

"Kin ganki fa." Ya janyota ya rungumeta a jikinsa gabaWayanta "ke da aka ce ki tafi gidan yayarki kin biyo miji office."

"Laifin wa don Allah?"

"Naki mana" ya soma magana a hankali. ?amshin jikinta ya tayar masa da kewar sati guda "I miss you so much."

Idanunta sun soma raina fata don akwaita da tsoro ta ce "ka zo mu tafi."

"Uhm uhmm" peck Win da ta ce bata sani ba ya soma sauke mata a fuska.

"Happy" ta daure ta kira shi. Tsoro ne fal a zuciyarta. Na zuwa wajen da kuma na shi kan shi mijin nata.

"Mrs Happy"

Daidai lokacin su ka ji an ?wan?wasa ?ofar. Hamdi ta ?wace daga hannunsa a firgice. Shikenan, idan Abba ne ta gama yawo a wurin Yaya ba shi ba.

Muryar wani yaronsa yake ji yana rantsuwar baya nan. Sai kuma ta mace da ya tabbatar Salwa ce tana cewa taga shigowarsa. A buWe mata ta jira shi. To da yake yaron ya santa sai ya ce ta bari ya Wauko spare key.

Ita Hamdi ko maganganun bata ji da kyau. ?ofar kawai da taji an ri?e yasa ta neman toilet.

"Stay with me please. Ba Abba bane."

Ta girgiza kai ta gudu. Idan ba Abba bane ai dai zai iya samun labari.

Tana shigewa Taj ya buWe ?ofar. Salwa ya gani a tsaye yau ita ce da mayafi a kafaWa Waya Wan mitsitsi haka?

"Ya Taj" ta kira sunan shi tana murmushi.

Baya ya yi don ta samu ta shigo saboda kada ta faWi abin da zai kunyata shi. Tana sanya ?afarta a ciki ta rufe ?ofar.

"Salwa me ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ya kawo..."

FaWo masa tayi a jiki kafin ya gama tambayarta. Hannunta hagu da dama kowanne da turaren da Ummi ta bata. Wuyansa ta ri?e da hannayen saboda ance lallai ta taSa fatarsa da turaren ba kaya ba.

Ya sanya hannuwansa zai cire nata sai dai kuma duka hannuwan ta shafesu suma. Saboda haka yana taSawa abin ya sake shigarsa.

"Sake ni Salwa" ya ce yana jin wani irin abu na shigarsa.

"My Taj..." ta sake yun?urin rungumarsa.

Fincikota taji anyi ta baya don bata ji lokacin da aka buWe ?ofar banWakin ba. Ta juya za ta yi magana Hamdi ta tsinketa da mari.

"Ke! Ni za ki..."

Rai a matu?ar Sace Hamdi ta sake marinta sannan ta saka hannu ta rabata da Taj.

"Fita."

"Nace ki fita ko na tara miki mutane. Banza kwartuwa."

"Ya Taj warn this girl." Salwa ta ce tana ?ar dariya "ko na kashe maka jiki ne?"

Shi fa jiri ne ma yake Waukarsa. Amma idanun Hamdi sun rufe da ganin da tayi musu. Me zai sa ya bari Salwa ta rungume shi na tsayin lokaci har ta fito.

?ofar office Win Hamdi ta buWe ta kamo hannun Salwa ta janyota. Inda ta sami ?arfin hali da na jiki ma bata sani ba.

Ita kuwa dariya ma take yi ta ce "Baki ga komai ba ?ar Wan daudu. Sai na zo har gida." Ta yi murmushi ta fita.

Idanu a birkice Hamdi ta juyo ta kalli Taj. Kan da yake ri?ewa ma a wajenta ba komai bane illa pretense.

"Abin da ka kawoni ka nuna min kenan?" Tayi magana tana hawaye masu zafi.

"Hamdi ba haka bane."

"Dama ku maza munafukai ne."

"Ni ne munafukin? Ni?" Zuciyarsa ta harzu?o da wani irin Sacin rai.

"To ko Wayan zan kira ka? Wanda ya dace da mazan dake neman matan da ba nasu ba?" Ta faWa kai tsaye.

Rufe bakinta ke da wuya kuwa ya Waga hannu zai mareta.

"Bismillah. In baka mareni ba baka haifu cikin uwa da uba ba."

Tassss.

Shi da yayi marin da ita da ya mara su ka kama zubar da hawaye lokaci guda. Komai na jikinsu da zu?ata yana nuna musu illar kalamansu ga juna da abin da su ke yi. Amma kuma wani abu daga gefe yana ingiza su da jin haushin juna na ban mamaki.
RAYUWA DA GI?I 25





Batul Mamman=ؖ?






Taurin zuciya ya hana Hamdi kukan da sauti. Sai hawaye kawai da ajiyar zuciya. Ji take kamar ta buWe ido ta ganta a gaban Yaya. Auren za ta ce ta fasa da gaske. Gashi dai zuciyarta tana ?aunarsa. ?auna da son da har yanzu bata taSa faWa masa ba saboda kunya da jan aji na mata. Sai dai tayi abin da zai gane shi Win mai matsayi ne babba. Tana tanadin kalmominta masu tsada zuwa lokacin da za su kasance a muhalli guda. Abin da ya gagareta fahimta bai wuce yadda ta rufe ido ta iya kiran shi munafuki ba. Ha?i?a duk wanda ya santa zai yi mata shaidar tsiwa. Amma rashin kunya irin wannan kuma ga mijin aure, abu ne da ita kanta bata taSa kawowa zata yi ba. Kuma har yanzu yadda take jin son nasa haka kuma wani irin haushinsa yake cin zuciyarta. So take kawai ya sake yin wani abin ita kuma ta cigaba da faWa masa abin da zai ji haushi.

Shi kuwa Taj ya ma rasa me yake yi masa daWi a duniya. Juya mata baya ya yi ya runtse idanunsa. Sai ya yi yun?urin juyawa yaga halin da take ciki, sai yaji zuciyarsa tana tuna masa kalamanta a gare shi. Ransa ya ?ara Saci har wani tafasa zuciyarsa take yi. Muddin za ta cigaba da yi masa rashin kunya yana kyautata zaton zai iya yi mata dukan da sai an Wagata....Duka??? Ai ko ?annensa mata ba za su yi masa wannan shaidar ba yayi saurin kwaSar kansa. Me ya kai shi marinta?

A hankali ya juya su ka fuskanci juna. Kumatunta ya yi shatin yatsunsa raWau. Gabansa ya faWi da ganin aika aikar da ya yi a cikin Wan ?an?anin lokaci. Wayarsa ya Wauko ya kira Sajida don tabbas ba zai iya kai Hamdi gidan a haka ba.

Hamdi na cikin yanayin Sacin ran nan taji yana cewa ba zai sami damar kaita ba. Da haka ta gane da wa yake wayar. Bata san me Sajidan ta ce ba ya bata wannan amsar.

"Lafiyarta ?alau, kawai dai tana cikin yanayin da bai kamata taje ko ina ba. So please ki min alfarma kada ki faWa a gida cewa bata zo ba."

Kallon mamaki Hamdi ta fara yi masa. Kafin kuma cikin fushi ta fara neman karSe wayar. Za ta soma Waga murya ya danne wayar da kafaWarsa ita kuma ya sanya hannu guda ya rufe mata baki. ?ayan kuma matseta ya yi a jikinsa da shi. Ya yi Wan murmushi da Sajidan ta soma cewa ta gane duk da muryarta ta bada ita.

"Ba fa abin da kike tunani bane wallahi. Fitowar ce dai kawai ba zan iya ba."

"Ko dai bata da lafiya ne?"

"She is fine. Bari tayi miki magana."

Kallon gargaWi ya yi mata kafin ya cire hannunsa daga bakinta a hankali ya kara mata wayar a kunne. Ta Waga jajayen idanuwanta ta dube shi. Kalmar 'please' ta karanta a laSSansa. Ranta sosai yake ?una.

"Ya Sajida."

"Alhamdulillah" hankali kwance tunda taji muryarta ta ?ara da cewa "asha soyayya lafiya."

Da sauri Hamdi ta yanke shawarar faa mata me ya faru.
"Mar..."

Bai bari ta ?arasa ba ya cire wayar. Ta buWe baki za ta yi magana da ?arfi yadda zata ji ya zauna tare da ita a jikinsa ya turata ?uryar kujera yana girgiza kai. Dolenta tayi shiru kawai sai harare harare bayan ta tattare ?afafunta ta cure jiki waje guda.

Sam ba zai yarda a ganta da shatin nan har a fara tambayoyi ba. Muryarsa ya gyara ya ce
"Don Allah Sajida. I realy need this favour from you. Kin san dai ba zan cutar da ita ba. Duk da tana ta rigimar sai na kawota."

"Subhanallahi. Ya Taj me ya kawo wannan maganar? In sha Allah babu mai ji. Ita kuma kada ma ka biye mata."

"To nagode."

Akan centre table Win wurin cushion chairs Win mai kyau na gilas ya ajiye wayar ya fuskanceta. Zuciyarsa tana ta kai komo wurin faWa masa ?arya da gaskiya. Ya rasa tudun dafawa guda Waya. Hannunsa ya kai kumatunta zai taSa tayi saurin karewa da nata,tana mai sadda kai ?asa. Bai kulata ba ya ri?e hannun nata ya kai ya taSa inda ya yi marin. Baya jin za ta kai shi jin ciwon wannan abu.

"Am sorry" ya ce muryarsa a sha?e.

Ai kamar ya kunna famfo. Sabbin hawaye su ka sauko mata. Muryarta har ta soma dashewa ta ce,
"Mari na fa kayi."

"You hurt me with your words Hamdi. Munafuki, kuma ki ce ban haifu ba?"

Cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login