Showing 60001 words to 63000 words out of 182745 words

Chapter 21 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

98

Wan jinkirta tashi kallonsa tayi.

"Tura ce ta kai bango Alhaji. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan baka sassautawa Abu ba to wannan fito na fito Win yana nufin ta gaji da aurenka. Muma kuma ?ofa ta buWe mana na daina shanye mulkin mallakar da kake mana. Ah to."

"Wai ni Gambo anya ba sauya ku aka yi ba?" Ya faWi da gaske.

Hajiya tayi dariya "ai na faWa maka tura ce ta kai bango. Ka bar gani na shiru shiru. Wallahi da Kamal ka yiwa abin da kake yiwa Taj da gidan nan ba zai Waukemu ba. Ita kanta Abu har gulmar yakana irin tata muke yi da su A'i. Akan korar Taj da kayi kuma ta cigaba da zaman gidan nan akwai yayunta biyu da su ka fita harkarta. Kafi kowa sanin tana da gata. Mace tilo cikin maza shida! Babu yadda su Alh. Lurwanu basu yi ba akan za su Wauko Taj daga wajen Jamila ta?i. Kawai don ta faranta maka. Amma kullum sakayyar da kake yi mata ba mai daWi bace."

Ita ma ficewarta tayi ta barshi da tulin tunani da fargaba. Ba zai yaudari kansa ba. Tsoro ya mamaye shi da abin da ya faru yanzu. Idan ya matsa matansa za su iya barinsa babu waige. Idan kuma yayi sakaci gidan zai fi ?arfinsa. Abu Waya ya rage. Ya dinga cizawa yana busawa. A yau dai dole ya busa don yana cizawar Abunsa za ta Salle. Matar da zuciya ta kasa tsufa daga yi mata soyayya tamkar yau ya aurota.
RAYUWA DA GI?I 18



Batul Mamman=ؖ?






***

Snacks lodi guda jere akan trays Zahra da Salwa su ka dinga shiga dasu falo. Komai da zafinsa saboda yanzu aka soya. Sai sassanyan zoSo da kunun aya sun sha ?an?ara a cikin jugs.

"Zahra mun tayar dake tsaye ba notice ko? Da ba ki wahalar da kan ki ba. Yanzu mu ke shirin watsewa." Cewar Ya Zulaiha.

Zahra tayi murmushi "ko yaya dai ya kamata ku ci. Abinci na so Worawa sai Salwa ta bani shawarar sayen frozen snacks daga Happy Taj."

Zahra ta nuna Salwa ta sha mayafi "kin ganta nan tana dawowa ko zama bata yi ba ta hau suya. Da kun tafi ma sai an bi ku dashi har gida."

Kowa dariya ya yi banda Ahmad da ya maka mata harara. Sai kuma Kamal da Taj da su ka kalli juna. Kamal ya yi dariyar tsokana don ya san ran Taj bai so ba.

Ya Hajiyayye tana shan zoSo ta ce "Mungode sosai. Sai ku fara shiri ku ma. Ba?on gidanku ya yi aure yau."

Kallon neman ba'asi Zahra ta yiwa Ahmad. Shi kuwa Salwa da ta tsaya cak yake kallo. Rawar kanta da baya so tayi yawa. Amma duk da haka sai yaji tausayinta ya tsirgs masa kafin ya iya bawa matarsa amsa.

"Taj aka Waurawa aure bayan sallar juma'a."

Ita ma Zahran da yake ta gama harbo jirgin Salwa sai da gabanta ya faWi. Ta waiga gefenta da sauri amma bata ga Salwan ba.

Ashe Ahmad na ambaton auren Taj ta bar wajen a guje.

"Me ya sami Salwa?" Wajen mutum uku su ka tambaya a tare.

Zahra sai ta faWi abin da ya fara zuwa bakinta "ai kuwa samosa ta bari akan wuta."

Da sauri tabi bayanta har Waki. Da shigar Salwan ta banko ?ofar da sauri ta murWa mu?ulli. Kan gado ta faWa ta ri?e ?irji. Kukan da take tunanin yi ya?i zuwa. Sai ajiyar zuciya kawai da wani irin zafi a ?irji.

"Ana wata ga wata" Zahra ta faWi tana juyawa.

Ahmad ta gani a bayanta. Fuskar nan tasa babu salama. Tare gabansa tayi kafin ya fara buga ?ofar.

"Don Allah ka barta taji da abu Waya."

"Wane irin rashin aji ne wannan Zahra? Ke haka kika yi?"

Bayansa ta kalla "Rage muryarka don Allah kada a ji."

Kamar bai ji me ta ce ba ya cigaba da faWa.
"Duk ta bi ta dami kanta akan wanda bai ma san tana yi ba. Da ta san da yadda yayi wannan auren ma sai ta godewa Allah. Na riga na faWa mata da wuya Alhaji ya yarda Wansa ya auri ?ar Mami."

Tura shi Zahra tayi don maganganun ta tabbata za su ?arawa Salwa zafi akan abin da take ji. Duk soyayyar da bata sami haWin kan zuciyar da take muradi ba, abar a tausayawa ce. Lokacin da tayi ta dakon son Ahmad ta sha wuya. Allah ne Ya taimaketa ashe shima yana sonta. Ranar da ya faWa mata sai da tayi sadaka mai kyau saboda farinciki.

?anana cikin matan ne su ka wanke duk abin da su ka Sata sannan aka gyara falon kafin su tafi. Zahra ta so su bari domin dai ?an uwan mijin nata in baka yi bani wuri ne. Kowacce tana ji da boko da gayu. Don ko kina gama secondary aka aurar dake to fa Alhaji zai yi da wajewa da mijin. ?arsa dole tayi karatu kamar yadda ya yi. Aiki ko kasuwanci ko zaman gida kuma zaSin mijin ne idan ta gama.

Yadda su ka zo haka su ka tattara su ka tafi gida domin ganawa da iyayensu. Taj kawai aka bari ya shige Wakinsa ya kwanta. Addu'a kawai yake yi Allah Ya basu ikon yi masa uzuri kada laifinsa ya yi yawa. Zuwa Abuja already ya kama shi. Ya ma ?udurce a ransa ba zai Wauki wayar Amma ba ko ta kira. Gara su haWu kawai ayi ta ido da ido.

Abin farinciki shi ne irin tarbar da iyayen su ka yiwa zancen.

"Nan da ku ka taho a ayari kun zo yi mana kwarjini ne? Alhaji ya riga ku fasa ?wan. Har mun fara shirin biki." Umma ta faWi tana dariya.

Kamal ya ce "Tunda baku yi fushi ba mu ai Alhamdulillah."

Kafin su watse Hajiyayye ta sake tado maganar lefe bayan iyayen sun tashi.

"Bishir kai zan bawa aikin buWe mana sabon group a whatsapp. Sai a sake maganar a gaban waWanda basu zo yau ba. Kada ka sako mana Taj dai kaji ko?"

Murmushi ya yi akan maganarta ta?arshe
"Zan kiyaye. Yanzu mece ce shawararki yadda idan na buWe kawai zan rubuta inda aka kwana sai kowa ya faWi ra'ayinsa." Kowa ya yi na'am suna saurarenta.

"A nawa ganin ko sisi kada Taj ya kashe da sunan lefe. Na sani cikin gidan nan babu wanda bai mori arzi?in Taj ba tun baya gari. Mu da ?a?anmu kullum cikin hidima yake damu. To lokaci ya yi da za a ramawa kura aniyarta. So nake ayi lefe na kece raini amma babu kuWin ango. Ya ji da muhalli da sauran abubuwan da su ka sauwa?a kawai."

Abinka da gidan yawa. Amincewar tasu kaWai sai da ta kawo amsa kuwwa a falon. ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Wai a haka ma don mata sun fi yawa. Sun tsayar da shawarar yadda Bishir zai tsara jawabin. Sai kuma a bawa kowa damar faWin me zai kawo daidai ?arfi.

Wasu don zumuWi tun kafin a tashi su ka fara faWin nasu. HaWin kansu gwanin ban sha'awa. ?akin Mama yafi kusa da inda suke zaune saboda haka taji duk abin da su ke cewa. A zuciyarta ta raya lallai wannan zaman lafiya da ?ullewar zumunci tsakanin matan gida da ?a?a shi ne mafi girman arzi?in Alhaji. Ba don haka ba da tuni gidan yafi ?arfin duk wani zafin rai da tsare girarsa.

***

Yawan mutane ?an Allah Ya sanya alkhairi a gidan ya mantar da Abba damuwar da ya tsinci kansa Wazu a dalilin Alhaji. Murna ake taya shi da zuciya Waya. Cikin hikima ta Allah ya aurar da duka ?a?ansa ba tare da tsumi ko dabararsa ba.

Amaren ne ma dai Sajida ce kawai take walwala. Zee kuka, Hamdi kuwa ba a cewa komai. Tana can Wakin Halifa ta rufe ?ofa tana fama da ciwon kai saboda uban tunani. Dukan ne goma da Wari ba ma ashirin ba. Ita ta sani sarai cewa haWuwar farko ta kamu da son Taj. Irin son nan mai shigar farat Waya. A haWuwarsu ta biyu lokacin ta tabbatar da gaske zuciyarta take. Sai gashi haWuwa ta uku da ya dace su yi musayar zu?ata ya zo ba a yadda take so ba. Tarin ?aunar da take masa take ta bi iska saboda sana'arsa. Kuma don abin haushi bai tsaya a nan ba shi ne harda sake dulmiya mata uba cikin sana'ar da tafi tsana. Me namiji zai yi da girki don Allah? Ita mace da tun ?uruciya ake horata da ayyukan gidan miji da girki ake farawa. Komai manya za su ce game da aure da maganar Wa'ami suke farawa ko su ?are. Sai dai kaji ana kiran tsafta, iya kwalliya, ladabi da biyayya...sannan uwa uba girki. Shi fa girkin nan sai an ?ara masa UWA UBA saboda mahimmancinsa. Shi ne zai zo ya koya har ma ya fita iyawa. Don tayi imani girkinsa da nata zai sha bambam. Ya riga ya ?wace abin tin?ahon da ta?amar. To ita me za ta yi? Shara da wanke-wanke?

Muskutawa tayi tana sauke numfashi da ta tuna rashin kunyar da tayi masa rannan da irin abubuwan da ya ce mata shima. Ba shiri ta tashi ta zauna tana sakin murmushi.

"Da kansa ma zai sakeni tunda ba sona yake ba." Ta faWawa zuciyarta.

Da wannan tunanin taji wani irin kuzari na shigarta. Tunda Sajida tayi aure ai nata ba dole bane. Salin alin za su rabu. Haka kawai ba za ta iya rayuwar uba girki, miji girki ba. Duniya ma sai tayi mata dariya. Abin da tafi gudu da ?i ace shi ne a tare da ita muddin rai? Inaaaa!

Kamar ba ita ba ta fito tsakar gida. Ana ta taron yinin Sajida. Ita da Zee taji ana cewa tunda ko kamu ba ayi musu ba, za a jira mazajensu su faWi lokacin da su ke so su tare. A zuci tayi dariyar sai dai su kai Zee ita kaWai. Sai ta kalli Zee Win. Idanunta luhu luhu sun kumbura. Tayi zuru zuru ba a bu?atar likita wurin gane bata da lafiya. Tausayin ?anwar ya kama ta. Gashi tana ganin wannan auren mai raba shi sai Allah. Irin amincin gidajen nasu biyu da soyayyar da aka ce Baballe na yiwa Zee bata hango mata fitowa ba.

Da su ka shiga Waki, dafa ta tayi cikin rarrashi ta ce "Allah Sarki Zee. Allah Ya sanya soyayyar Baballe a ranki. Na kula yana da mutumci da sanin darajar mutane."

Zee ta sake fashewa da kuka "kema kin ga babu alamun auren nan zai rabu ko? Yaya zan yi?"

"Ki kwantar da hankalinki. Bawa bai isa ya ?etare ?addararsa ba. Wani ba ya auren matar wani. Yanayin yadda aka yi auren kaWai ya ishe ki ishara."

Kasa?e Zee tayi tana sauraron nasihar Hamdi kafin tayi magana.

"Ke baki da matsala kenan da auren? Kodayake me zai sa ki ?i Taj? Nima ba don abin da Ummi ta yiwa Abba a school Winku ba da na ha?ura." Wayarta ta mi?awa Hamdi "kin gani. Tun Wazu yake ta turo min message."

Sa?onnin har guda shida duk abu guda biyu su ke Wauke da shi. Na farko ha?uri Baballe yake bata akan rashin sanar da ita da neman yardarta. Na biyu kuma yana jaddada mata ba auren alfarma bane tsakaninsu. Sonta yake. Kuma yana fata za ta bashi dama ya koyar da ita son shi ita ma.

Murmushi sosai Hamdi tayi. Bata taSa sanin soyayya za ta burgeta ba a zahiri sai yanzu. Da alama Baballe zai yi saurin siye zuciyar Zee ta ce a ranta. Tsarin kalaman sun taho da rarrashin da mai karatu zai ji a jikinsa. Ai dole ma ta rabu da Taj. Ko don rashin irin wannan text Win na Zee da wayar da Safwan ya yiwa Sajida Wazu yana ?ara bata ha?urin abin da ya faru.

"Allah Zee kada ki tada hankali da yawa. Na san irin auren nan babu daWi. Amma ki godewa Allah da mai sonki aka haWaki. Kuma kina ganin yadda Abba da Yaya ke ta murna. Yawan kukan zai sa su ji babu daWi."

Sajida ce ta shiga Wakin a lokacin. Ta kalli ?annen nata tana murmushi.

"Su Hamdi malaman aure. Irin wannan huWuba haka? Ko dai dama soyayya ku ke da Ya Taj bamu sani ba?"

Idanun Hamdi hango mata Taj su ka yi a gaban tukunya sai taji tsigar jikinta na tashi. Wannan aure ba da ita ba. Ba dai za ta iya labartawa ?an uwanta niyyarta bane saboda kada yanzun nan su kaita gaban iyayensu.

"Gani nayi an riga an Waura. Gara mu ha?ura kawai. Kukan ciwo zai sa mata."

"Da gaskiyarki. Amma ni ke ce damuwata. Jiya da baki san da naki auren ba sam baki da damuwa sai tamu. Yau kuma an Waura naga kin yi saurin ha?ura kamar ba ke ce ki ka suma ba Wazu... Don Allah mene ne tsakaninki da shi?"

Da Sajida da tayi tambayar, da Zee idanu su ka zuba mata. Tana son gilla musu ?arya amma ta rasa wadda za ta fi dacewa. Allah ne Ya taimaketa ?an matan danginsu su ka shigo Wakin ana tsokanar amare. A dalilin Abba dukkaninsu basu da wasu ?awayen kurkusa da su ke shawara dasu. Su ne dai ?awayen juna sai cousins Winsu.

Gabanin Magriba da ba?i su ka sarara ne Hamdi ta shige ?uryar Wakinta da wayar Sajida da tata a hannu. Numbar Taj ta kwafa ta gama karanto addu'o'in neman nasara ta kira shi.

***

"Happy kana ganin ka kyauta kuwa? Duk fa irin yadda Yaya ya damu da mu ita ma Salwa jininsa ce."

Kamal ne yake yi masa wannan tambayar a yayinda yake shiryawa zai je Waukan Abba su je wurin Alhaji. Yadi ne ya saka mara nauyi ruwan bula mai kyau. Rigar tasa kaWan ya rage ta ?arasa gwiwa. Hannunta kuma ya Wan zarce gwiwar hannu kaWan. Aikin wuyan da aljihu da aka yi ruwan madara ba mai yawa bane. Hula ya Wora a kansa lokaci guda ya zama kamar ba shi ba. Ya yi kyau sosai. Sai da ya gama fesa turare sannan ya juya ya fuskanci Kamal.

"Ya kake so nayi da ita? Me ma nayi mata? Banda na bi shawararka ka san Allah da ko text Win da take yawan yi min ba zan kula ba."

"Na sani. Amma yanzu da ta shige Waki tun Wazu ya dace ka kirata ka Wan rarrasheta."

Taj ya ware idanu "in yi me? So ka ke tayi zaton aurenta zan yi? Gaskiya Happiness ka rage sau?in kai. Zai iya kai ka ya baro."

"To ko Yayan ka Wan yiwa magana mana. Sharewa kamar baka san komai ba fa ba daidai bane. Please." Kamal ya ce da damuwa. Baya son rigima irin wannan ta cikin gida. Su duka ?annen Ahmad ne. Amma ana iya samun dalilin da zai sa Ahmad Win ya zaSi Sangare guda ya ?untatawa Wayan.

"Yanzu dai bani key mu je. In na dawo zan yi masa magana in sha Allah."

Da murmushi Kamal ya ce "ko kai fa." Sai kuma ya sako wani zancen "Goben dai za ka tafi Abuja?"

"In sha Allahu. In Amma ta tsine min tas za ta bini. Gara naje na daidaita da uwata."

"Ba ka yi fushi ba dai da na ce ba zani ba ko?" Kamal ya faWi yana sosa ?eya.

?wafa Taj ya yi "Kaf Winku na san zaman da nake da ku. In matan suna da mazaje ai ku za ku iya zuwa. Amma har Naja da Rukky dake Abuja duk sun zame wai babu mai zuwa rakani."

"Naja fa ta ce za ta turo a Waukoka daga airport."

"Wannan ma laifi zai zama a wajen Amma. Cewa za ta yi wato har na fara neman ?an uwana na barta."

"Allah Ya fito da kai lafiya. Daga nan zan taya ka addu'a. In kaje dai ka gaishe da Anisa." Yana dariya ya yi maganar.

Wata kwafar Taj yayi don ya san tsokanarsa yake. Shi ya tu?a motar. Suna hanya yaji wayarsa tana ta ringing. Idan kiran ya katse a sake binsa da wani. Bai Wauka ba sai da ya tsaya a danja kafin a bada hannu. Ba?uwar lamba ya gani. Kira har huWu a jere dole ya bi.

Hamdi na ganin sunansa da hasken waya ko ringing bata fara ba ta Wauka.

"Assalam alaikum wa rahmatullah" ta faWi da ladabin da ya bawa Taj mamaki. Shi da ya sa rai da tsiwa da rashin kunya. Har ya gama tanadin yadda zai Sullo mata. Sai gashi tana yi masa gaisuwa irin wannan. Haka kawai zuciyarsa ta hana shi soma murna. Gara yaji da me ta zo. Hamdi ce fa. Wadda ta faWa masa ?iri ?iri bata son sana'arsa.

Basarwa ya yi ya ce "Wa alaikum salam. Wa ke magana?"

"Ya Taj ni ce. Hamdi ce. Don Allah magana nake so mu yi" Ta wani ?ara sauke murya ita a dole mutuniyar kirki.

"Ina tu?i yanzu. Idan na tsaya zan kira ki in sha Allah." Duk da idan ya so zai iya sanya earpod Winsa ya amsa wayar, jikinsa ya bashi dalilinta na nemansa. Shi yasa ya katse mata hanzari.

"To babu komai. Nagode. Nagode. Zan jira ka don Allah."

Jira ya yi ta kashe wayar kafin ya soma dariya. Ya labartawa Kamal rigimarsu ta ranar buWe Happy Taj da kuma randa ya koma gidan.

"To dai mata sai da lallaSawa. In kana son shawo kanta sai ka ajiye taka rigimar."

"Ashe ba za mu daidaita ba. Kallo Waya nayi mata na gane rigimammiya ce. Tana yi min zan rama don gidan abin ta zo."

Da takaici Kamal ya kalle shi "Kai Happy. Matarka ce fa kuma yarinya ba abokiyar faWa ba. Ko ina sai ka nuna hali ne?"

"Take takenta kamar cewa za ta yi na saketa. Haka jikina yake bani. Ni kuma wallahi sonta nake kamar babu sauran mata a duniya." Ya ?are magana yana kanne ido.

Shi ma Kamal da sha?iyanci ya ce "Shege...mutumin ya fola tsundum. Allah Yasa kada Alhaji ya kawo cikas dai kafin mu kwashi ?a?an love."

"Za ka yi bayani. Bari dai hankalina ya dawo jikina in mun shirya da Amma. Ko da duka ne sai ka faa min sunan budurwarka. In kuma babu sai muje wajen Baba Malam (yayan Inna) ayi maka ru?iyya. In ma wata jinnu ce ta ?yasa ayi waje da ita."

"Aljana sai dai a kanka. Ni kam ?alau nake."

"To in ba tsoro ba ka faWa min. Idan kuma kasa ka aka yi ne gara na sani. Sai na baka tips na shawo kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login