Showing 132001 words to 135000 words out of 182745 words

Chapter 45 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

106

wani naka bai zama silar ?unci ko zubar hawaye ko jinin wani ba. Sannan kaima kada Wan kowa ya yiwa naka. Ko babu komai akwai baki da ido kuma su Win gaskiya ne. Allah Ya kyauta."

Amsarta a lokacin ita ce tunda suna zaune a waje irin wannan ba za ta so yaranta su zama lusarai ba. Wannan mata kuwa ta nuna mata cewa duk runtsi ai gara idan an je gaban Allah ka zama mai kai ?ara da a kai ?ararka. Za ta koyawa yaranta su ?waci kansu amma kada su zama silar rigima kuma banda zalunci da wuce gona da iri. Manzon Tsira SAW cewa yayi kada mu cutar kuma kada mu bari a cucemu.

Hawaye ya zubowa Iyaa. Ta Wauki laifin ta Worawa kanta. Cin zalin da Ummin da dinga yiwa Siyama ne yasa ta canja tsarin tarbiyar lokacin. To amma Wan wannan guntun sakacin da kuma halayyar fiWrar da aka haifeta sun riga sun yi tasiri.

"Allah na tuba. Allah Ka duba min."

Wata walwala da jindaWinta duk sai su ka kau a lokacin. Ciwon kai ta Worawa laifin hakan da Yaya ta tambayeta game da sauyin da ta gani a tare da ita.

*
"Kai Happiness me ya same ka haka ka kumbura?"

A madadin sallama abin da Taj ya fara cewa kenan da ya shiga Wakin Kamal.

Son faWawa Happy gaskiya yayi sai dai kuma a ganinsa faWa a yau ba ?aramin rashin adalci bane. Babu yadda za ayi Taj ya san gaskiya kuma ya tare a gidansa a yau. In ya yi haka kuwa ya cutar da Hamdi.

"Wai ashe kifi ne jikina baya so yanzu ni ban sani ba? Jiya da ka kula tun a wajen dinner bani da kuzari. Kifi na ci last kafin mu tafi."

"Subhanallahi. Kuma Alhamdulillah tunda an gano. We'll just avoid it don a zauna lafiya."

"We? Kai kuma me zai sa ka daina ci?" Kamal ya tambaye shi.

"Ai ka sanni da kirki. Ba zan so na dinga ci a gabanka ba."

Da dabara Kamal ya sauya zancen da dai yaga Taj ya yarda.

"Wai ni ya na ganka haka kamar ba wanda ya kwana gida Waya da Hamdi ba?"

"Akwai ?ura fa Happiness. Alhaji ya Sallo min ruwa jiya." Ya faWa masa abin da ya faru.

"TabWijam ake cewa ko cabWijan...yanzu kana nufin ni da kai yau duk pillow za mu runguma?"

Bugu Taj ya kai masa ya goce "ta Allah ba taka ba. In sha Allahu gadona da naka yau sai an sami bambanci."

"Salman Khan na Hamdiyya wato ana yi maka kallon salihi ashe ashe ba haka bane." Kamal ya faWi yana yi masa dariya.

"Aure dai nayi...idan mutum yaji haushi wata asabar Win mu kai shi Wakin doctor"

"Maimakon ka zo mu zanta yadda za ayi a shawo kanta tun kafin ?an kai amarya su watse ka zauna tsokana."

"On a serious note kana ganin abin da take so zai samu yanzu? Alhaji fa take so ya canja yadda yake yiwa Abba. Bata san na fita son hakan ba ta Wauki fushi dani."

Shawarwari Kamal ya soma bashi sai dai a yau ko kusa zancen ba shigarsa yake ba. Ya riga ya san da me zai kama Hamdi a hannu. Damuwarsa yanzu canjin da ya gani tattare da Kamal mai yawa tsakanin jiya da yau. Happiness is hiding something. Yana ji har cikin Sargonsa. Ko maganganun da suke yanzu yana hango pain Win da Wan uwansa yake ?o?arin Soye masa. Dole zai yi wani abu a kai. Kamal bai fi shi wayo ba.

*
Wannan asabar ta kafa tarihi mai girma a gidan Alh. Hayatu. Yinin bikin Taj da aka shirya yi a gidan wan Inna sai ya dawo gidan mahaifinsa. ?an uwa na kurkusa da su ka san me ya wakana tsakanin uba da Wa sun taho harda maza irinsu dattijon arzi?i Yaya Babba su ka yi fatan alkhairi su ka tafi tare da Alhaji. Aka dinga kiran ?an biki cewa venue ya canja last minute. ?a?a, surukai da jokokin Marigayi Alh. Sule Maitakalmi sun gwangwaje cikin farinciki. Inna da ?an uwanta su Hajiya anko su ka yi da Amma uwar goyon Taj. Ango ya fito tsakiyar dangi babu shayi ko tararrabi gwanin ban sha'awa.

Wai aka ce taSa kiWi taSa karatu. Da yake a gida suke matashin Wan Yaya Kubra ne yayi musu DJ. Ba kunya ita da kanta ta ce masa ya kunna musu wa?ar da ta faWa masa tun a gida. Ta sanya autar Alhaji Surayya tayi coordinating komai. Layi aka yi a jere tun daga Yaya Hajiyayye har ita Surayyan. Dukkaninsu sanye da anko iri Waya na shadda light brown. ?inkin mata irin Waya, haka ma na mazan. Daga kan Yaya Hajiyayye kuma ta jere Inna, Umma, Mama da Hajiya a gefe da gefen juna.

DJ ya saki wa?a su ka dinga bi.
Hurry hurry come carry your baby go
Come and see my mother ahh....

Kowa sai ya bar abin da yake yi ana kallon zugar gidan Alh. Hayatu. Babu wanda bai yi rawa ba idan an zo kansa, har Ahmad da tun safe yake cikin ?unci. Sai yanzu da yaga Kamal yana walwala har yafi Taj rawar ma ya sake. Bayan sun gama matsawa su suka koma gefe suna nuna uwayensu ana ta dariya.

Wani abin burgewa shi ne da Taj ya taka har gaban Amma yana nunata da hannuwansa biyu yana faWin come and see my mother. Bata san lokacin da ?wala ta zubo mata ba. Ya rungumeta a wurin yana Wan dukan bayanta.

A wurin kowa har angon wannan wunin is the best event. Kowa yaji daWi. Ana la'asar Mama ta ce ayi haramar Wauko amarya a kaita gidanta.

*

?arfe biyar da rabi motocin kai amarya su ka cika layin gidan Abba Habibu. Motoci na alfarma da kece raini. Taj bashi da wasu abokai na a zo a gani sai cikin ?an uwansa. Su ne kuma su ka cika wurin ?wai da kwarkwata. Kowa ya zo Waukar amaryar Taj.

Su ma biki suka yi sosai. Gidan Abba Habibu babu masaka tsinke. Abinci da abin sha sai mutum ya ture.

?arfe uku aka shige ciki da amarya. Kayan gyaran jikin da Amina Meens_insense take yi Hairat matar Halliru ta saya domin yau. Ba don nisa ba da ita da kanta za ta sake yiwa Hamdi gyaran nan kafin a kaita. Sake scrubbing jikin tayi ta turarata sosai. Bayan an gama ta sanyata ta tashe jikinta da kwalacca Win meens Win. Sannan tabi gaSoSi da oil Win scentmania. Ita kanta Hamdi duk kukan rabuwa da gida da ta fara sai da ta dakata ta sha?i ?amshin sosai.

"Hamdi kada ki yi wasa da ?amshi. A jikinki da gidanki. Rahama ne shi babba kuma abokin ya?i da nasarar kamo zuciyar maigida. Mace mai wayo bata bari mijinta yaji wari a jikinta."

"Ba za ki amsa ba uwar miskilanci? Ana baki darasi kin wani haWe rai." Cewar Sajida tana harararta da gefen ido.

"Idan na amsa ace bani da kunya. Nayi shirun kuma ban tsira ba. Me ya hanaki yi min kara ki ce to?" Hamdi ta rama hararar.

"Ba laifinki bane. Gidan miji za ki kwana yau, dole ki min rashin kunya."
Sajida ta faWa da rawar murya.

"Kinga kin saka ta kuka ko?" Zee ta matsa jikin Sajida ganin har ta soma zubar da hawaye.

Jiki a sanyaye Hamdi ta matsa kusa dasu "ni me na ce don Allah. In ranki ya Saci ki faWa min mana. Meye na kuka?" Ita ma sai ?walla.

"To ni wa zan rarrasa cikin ku?" Zee ma ta kama kuka.

Rungume juna su ka yi suka kama kuka hai?an. Ta tabbata yau su uku kowa makwancinta daban. Aure abin so kuma abin alkhairi ya rabasu.

Hairat fita tayi ta basu wuri. Ana ganinta a waje aka fara tambayar ko Hamdi ta gama shiri.

"Yaya le?a Wakin." Ta ce da Yaya.

"Ga iyayensu nan..." Yaya ta faWi cikin kunya.

Hairat kuwa ta ce ita ya dace taje. ?an uwan nasu ma su ka goyi baya. Tana shiga ta samesu su uku suna sharSar hawaye. Da su ka ganta wajenta su ka ?arasa kowacce kukanta ya ?aru. Ta fara yi musu nasiha sai gashi tabi sahu. Sai da aka ji shiru aka biyo bayansu. Inna Luba da kanta da sanya Hamdi a gaba ta saka kaya. Riga da zani na leshi mai Wan karen laushi. Fuskarta babu makeup sai hoda da kwalli da Wan pink lipstick sama sama. A haka ma tayi kyau sosai.

"Har a fita ban yarda ki sake sanya min ?a kuka ba. Ki daure ki ri?e hawayenki don Allah."

"Haba Inna? Ba ma ta ni kike yi ba sai Yaya?" Hamdi ta kyaSe fuska.

"So so ne Hamdiyya..." cewar Inna Luba tana dariyar tsokanar jikar tata.

"Amma son kai yafi ko? Naji da ana cewa wai mutane sun fi son jikokinsu akan ?a?a."

Inna Luba ta kaWa baki ta ce "Duk ?arya ne."

"Ai kuwa sai na faWawa Yaya ta daina jin babu daWi idan kina shareta."

"Zo nan don ?aniyarki" Inna Luba ta yafito ta ta gudu.

Matar Kawu Abdu?adir ?anin Abba Habibu ce ta zauna da Hamdi bayan ta gama shirin ta bata kayan gyara ba mata da sati guda kenan ana bata ta shanye.

"Ki kula da abincin da kike ci da tsafta. Wannan sinadari ne. Kada ki dinga yi musu shan ?oshi don Allah. Komai saisa-saisa yafi"

Sunkuyar da kai tayi har ta gama yi mata bayani ta tashi. Daga nan gida ya kaure da guWar shigowar dangin Taj. Cikin Hamdi ya yamutsa da wata irin fargaba. Kukansu ita da su Zee ya dawo sabo fil. Aka fita da ita ko Abbanta da taci burin gani bata sanya a ido ba. Yadda ya bar gidan ranar kai Sajida ita ma haka yayi mata. Ba zai iya ganin fitarsu ba.

A motar Kamal aka sanya amarya. Mummy matar Yaya Babba da uwargidan Alh. Lurwanu wan Inna su ka saka ta a tsakiya. A gaba kuma wata Anti Zinatu ce.

Rantsuwa kala kala Kamal ya yiwa Yaya Kubra akan lafiyarsa kafin ta bari ya fito. Tana barazanar za ta tona masa asiri yayi dariya.

"Ni za ki lallaSa kafin na tona naki asirin. Alhaji da Yaya Ahmad sun san da ciwon. Na rufa miki asiri ne dai kawai..."

"Alhaji ya sani? Kamal ka kyauta kenan? Idan ya san nima na Soye ka san me zai min?" Ta katse shi a tsorace.

"Shi yasa nace ki barni na fita kada na janyo miki" dariya ya yi mata ta bashi hanya da zai fita ya ce "ba maganarki ce bana ji ba, sai dai ina so ki min ha?uri don ban sani ba ko wannan ne abu na ?arshe da zan yiwa Taj."

Haka ya fita ya barta tana share hawaye. Ta gama ?arar da duk basirarta da waWanda za ta nema amma ba a dace ba.

***

Gidan amarya ko yaya yake sai kaji ana son barka. Balle kuma gidan Tajuddin da Hamdiyya. Duk wanda ya shiga da santin gidan yake fita. Kayan ?awa da ?yale ?yale an saka amma masu aji wanda basu cika waje sannan basu fiye ?yal?yali ba. Harkar girma da girma kawai. Inna da masoyanta waWanda su ka goya mata baya sun yi rawar gani sosai. Haka zalika Abba Habibu da Yaya. Basu kwanta anyi musu komai ko don gudun raini da wula?anci.

Da sunan Allah a baki da zuci iyaye su ka kai Hamdi Wakin aurenta. Aka kuma umarci ?an uwanta da su bar kuka haka nan saboda ta sami nutsuwa. A gidan aka yi sallar magariba sannan aka soma tafiya. Yan matan dangin amarya da ango kowa da irin salon nasiha da sha?iyancin da yake yiwa amarya a kunne. Da aka watse ya rage Sajida da Zee sai Siyama da sa'aninsu daga ?a?an ?an uwan Abba Habibu. Sun zage sun sake gyare komai kafin shigowar angwaye. Iyaa bata bari Ummi ta bi su ba.

*

Taj ya haWuwa da Alhaji kafin su fita. So yayi su gana su kaWai ya ?ara yi masa godiyar dawo dashi cikin ahalinsa da yayi. Sannan yana so ya faWa masa yanayin Kamal da baya yi masa daWi. A ?arshe ya ro?e shi ya matsawa Kamal Win ya sanar dashi damuwarsa. Tunda ya san ba zai kalli idon Alhaji ya yi masa ?arya ba.

Da Ahmad su ka shiga wajensu Hajiya. Kowanne Waki idan yaje sai anyi masa addu'a. Sisters Winsa su ka kama koke koke. Ahmad ya haWasu manya da yara ya dinga faWa.

"Auren ku ke yiwa kuka?"

"Kwanansa Waya a gida fa zai sake tafiya."

"Sai ka koma basu gaji da ganinka ba" cewar Ahmad yana haWe rai don baya son Sata lokacin da ake yi.

Taj ya kanne ido Waya ya kawar da kai gefe "ni dai Hamdi"

"Lahhhh"

Suna tsokamarsa wai bashi da kunya da ya faWi haka a gaban iyaye ya ce su ma basu da ita da su ka kawo zancen ya sake kwana. Aka gama wasa da dariya su ka fito. A hanya ya fara faWawa Ahmad damuwarsa akan Kamal.

"Gabana har faWuwa yake yi idan ya faWo min a rai. Gani nake kamar ba wani ciwon allery."

Ahmad yayi ta maza sosai da ya iya daurewa ya cije yadda Taj ba zai gane ba.

"Ka tambaye shi?"

"Ina Wauko maganar yake neman hanyar canjata."

"Kada ka sa komai a ranka. Zan binciko maka."

Ajiyar zuciya Taj yayi "nagode Yaya."

Shiru su ka Wanyi kafin Ahmad ya Wauko zancen Salwa.

"Naji duk abin da tayi. Kayi ha?uri. Yau na so ta koma Bauchi amma ban sami zama ba."

Katse shi yayi "Yaya Ahmad don Allah mu bar zancen. ?anwarka ce. Nima kuma ?aninka ne. Na san babu sani ko goyon bayanka saboda haka kada ka ja zancen nan ko ka bani ha?uri. Ita ce ma zan bawa saboda ?in karSar tayinta da nayi."

Samun gidan yawa irin na Alh. Hayatu mai tattare da haWin kan iyali ba abu ne mai wahala ba. Na farko mutum ya zaSo mata nagari sannan ya tafiyar da mu'amalar gidansa a bisa tsarin shari'ar musulunci. Na ?arshe kuma ya dage da addua. SaSani a yau da kullum dole ne. Amma a ?alla wasu abubuwan da dama sai dai kaji ana faWi ba dai a gidanka ba.

A farfajiyar gidan su ka haWu da sauran ?an uwansu da tsiraran abokai. Sai Safwan da Baballe. Ahmad ya ce ba zai shiga ba a matsayinsa na wan ango. Su Kamal ne su ka raka shi ciki.

"Ya Taj ina ledar kazar amarya? Ko tana mota?"

Abba ne ya yi tambayar kafin su bar bakin motocin. Taj ya tsaya turus, wallahi ya manta ana wannan siyayyar. Bai taSa raka ango ba amma Kamal ya faWa masa.

"Subhanallahi...zo ka siyo min." Ya zira hannu a aljihu.

"Gashi na siyo" Kamal ya Wago ledoji biyu daga gaban motarsa.

Rungume shi Taj yaje ya yi.
"What will I ever do without you?"

"Sake ni dalla kada ka sani kuka" Kamal ya ture shi. Taj ya?i saki. Bishir da wani cousin Winsu harda ?ar ?walla.

"Ya aka yi ka san ban saya ba?"

"Wallahi jiki na ne kawai ya bani."

Murmushi suka yi sannan Taj ma ya karanto addu'a kafin ya shiga gidansa karo na farko a matsayin mijin aure.

A falo su ka sami ?an matan amarya da amaryarsu a tsakiya an lulluSeta da laffayar jikinta. Tana ji ana gaishe gaishe an barta da faWuwar gaba. Ta kama hannun Sajida tayi masa kyakkyawan ri?o kamar za ta tsinke mata shi.

Addu'a da fatan alkhairi aka yi musu a mutumce. Babu wannan rashin kunyar rungume rungumen sabbin aure da ake a gaban mutane. Ko kuma maganganu na rashin Wa'a tsakanin angwaye da amare. Da aka gama Safwan ya ce ya kamata su tashi haka nan. WaWanda za a kai gida su fito a kai su.

"Ni dai ina da abin cewa guda Waya kacal. Happy..." Taj ya kalli Kamal.

"Mrs Happy..." Hamdi ma ta Waga kai a hankali amma bata buWe fuska ba.

"Duk abin da za ku yi, ku ji tsoron Allah. Ku yiwa juna uzuri kuma ku kyautatawa juna zato."

Yanzu dai bata yi kuka sosai ba da zasu tafi sai hawaye. Taj ya fita ya raka su sannan ya rufo ?ofa ya dawo.

Hamdi tana nan bata motsa ba. Ya yi murmushi ya ?arasa kusa da ita ya zauna. Gabanta ya kama dukan tara tara. Yau da anyi an gama. Inda take yanzu gidansu ne ita da Taj. Magana take jira ya yi ko wani motsi duk taji shiru. Ba zato taji saukar abu a gefenta. Ta Waga kai da sauri, kafin ta buWe fuskar Taj yasa hannu ya haWe gaban laffar ta saitin fuskarta.

"Ni zan buWe. Kada ki Sata min tafiyar tarihin wannan daren."

Komawa tayi jiki babu kuzari ta zauna da ta gane babbar rigarsa ce ya ajiye a kusa da ita.

Rage tsayi yayi a gabanta ya ce "Zan taSaki Hamdi. Kin bani dama?"

"Na'am?" Hamdi taji wata ba?uwar murya ta fito daga bakinta ma'abociyar tsoro.

"Na fahimci a tsorace kike ne shi yasa na faWa miki."

Kafin ta sake yin magana taji hannuwansa a duka kafaWunta ya tayar da ita. Sannan ya kama laffayar ya soma warwareta????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? har ta ?are. Ya kalleta daga sama har ?asa ya godewa Allah a ransa.

Babu zato daga gareta kawai taji ya janyota jikinsa ya sanya hannuwanta a gefe da gefen cikinsa sannan ya rungumeta. Sun Wauki lokaci a haka kowa yana fama da yanayin da ya shiga kafin ya Wago haSarta yana kallon idanunta.

"Mun shirya Hamdi? Kin daina fushin?"

"Ba fushi nake ba."

"Har akan maganar Wazu?"

"?azu gaskiyata na faWa maka ai" ta Wan kawar da kai.

"Kina nufin yau ni da gwaurayen da su ka fita daga gidan nan bamu da bambanci?"

So tayi ta haWe fuska don ya san mahimmancin abin da ta faWa amma wannan maganar sai da tasa ta yin murmushi.

Sannan ta ce "Haka ne."

Hannunta ya ri?e su ka zauna "su rungumi pillow nima na runguma kenan fa?"

"Uhmm" ta amsa kunya na kamata.

Taj ya kalleta da kyau ya Sata rai "ke Allah kuwa da sake. Sadaki fa na biya."

Da dabara ta Wora hannu a kan bakinta don kada yaga dariyar da take neman yi.

"Aka biya maka dai." maganar ta fito kamar ba daga bakinta ba.

?ayataccen murmushi ya yi "Lallai, kin ce wani abu. Zan tuna miki a lokacin da baki zato." Ledojin da Kamal ya ajiye akan centre table ya buWe "zo mu ci abinci. Kuma kada ki ce kin ?oshi."

"?oshi kuma? Yunwa fa nake ji."

?asa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login