Showing 111001 words to 114000 words out of 182745 words

Chapter 38 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

103

jiya komai da iyayen Taj aka yi. Yau ma su ne ?irjin biki. Sai ace babu mahaifiyarta? Saboda miskiniya ce.

"Ya Hamdi meye haka ne? Ji idonki har ya soma caSewa fa." Cewar Zee ta ?ara mi?awa mai kwalliyar tissue domin a gyara idon.

Sajida wayarta ta shiga dannawa tana cewa "bar ni da ita."

Sai ji su ka yi tana gaishe da Taj. Ta kuma faWa masa kukan da Hamdi take yi da dalilinsa.

"Saka mata wayar a kunne."

Da canjin numfashin da yaji ya gane ta saka mata Win. Da rarrashi ya yi mata magana.

"Zan kawo miki Yaya in sha Allahu. Ki daina kuka idan ba haka ba kuma yau sai mun yi kuch kuch hota hai a gaban mutane. Mu yi ta rangwaWa kai kamar ?adangaru."

Dariya ce ta kama Hamdi. Sajida, Zee da maikwalliya su ka saki baki suna kallon ikon Allah.

"Wa?ar bata da hayaniya sai na taya ka."

"Haka ki ka ce?" Ya tambayeta yana murmushi "Wayarki na kusa?"

"Eh"

"To ki dubo wa?ar I am a disco dancer a youtube. Ni kuma idan baki daina wannan kukan shagwaSar ba in baki mamaki a gaban mutane. Ita zan yi. Kin kuma san zan iya. 80s aka yi ta ba ta zamaninku bace."

"To Baba Happy. Na ma share hawayen" ta goge idonta da kanta don barazanar Taj ba abin da za ta share bane.

"Wannan ladabin ba na gaske bane. Sai na tambayi Sajida naji ko kin ?ara yin kuka."

"Allah na daina."

"Hamdiyya" ya kirata a tausashe.

Kasa buWe baki ta amsa tayi saboda kiran nasa na daban ne.
"Uhmm"

"I'll see you later."

"Bye" ta mi?awa Sajida wayar.

"Iiiiiikon Allah" Sajida ta faWi baki buWe "me zan gani ni Sajida ?ar Habibu? Hamdi? Dama rashin jin muryar mijinki ne yasa ki kuka? Shi ne ki ka Worawa baiwar Allah Yaya. Ai kuwa bari nace mata tayi zamanta."

Da sauri Hamdi ta mi?e tana kici kicin karSe wayar "Waukota fa zai je ya yi. Shi yasa ki ka ga nayi dariya."

Zee tayi dariya "anya kuwa? Naji fa kina zancen wata wa?a wai bata da hayaniya."

"Ke, kira Ya Baballe ku gaisa kema ki ji daWi."

"Baballen lafiya? Sunansa Sadiq" ta faWa tana kallon yayyen nata.

A tare su ka bushe da dariya sannan Hamdi ta koma ta zauna aka gyare fuskarta kamar bata yi kuka ba. Ana gamawa ta koma gefe ta buWe youtube. Hannunta yana ?ai?ayin ganin wa?ar da Taj yake cewa zai yi. Da ta kunna Waya tayi kama da ta 80s Win daga Waukan ma. ?ayar kuwa Waukan zamani ne. Bata ma Sata lokacin kallon ta zamanin ba wadda ta kasance remake Win tsohuwar. Danna tsohuwar tayi inda kunya ta kusa sumar da ita da rawar da Mithun yake yi. Saboda raye raye nan ta?i jinin wa?e-wa?e. Idan Taj ya yi wannan girgizar da karya jikin tabbas a wurin dinar za ta tafi ta barshi.

Su Zee dai kallonta kawai suke yi. Tana duban waya da ido Waya tana kawar da kai.

"Ta fa ci kai wannan." Sajida ta faWi su ka yi dariya ko kula su bata yi ba duk da taji.

*

Da Taj ya gama wayar, ji ya yi an ture shi. Sai lokacin ya ankara ashe a jikin Kamal ya jingina da shau?i na Wibarsa. Ya rasa me yasa shi da Hamdi basa iya yiwa juna ba?unta. Kamar ba jiya jiyan nan da sauran ?ar rigimarsu ba. Yau kam komai ya wuce!

?aure fuska Kamal ya yi "Na ma rasa abin da zan ce maka Happy? Wato haka ake soyayyar ni ka barni ina fama da instagram da daddare?"

Taj ya kama dariya "ba dai ka tsaya wasa ba? So kake sai Dr. Mubina ta kawo maka katin aurenta ka zo ka ce min zuciyarka za ta fashe ko?"

"Allah ma Ya kiyaye. In sha Allah ba zan ga aurenta ba." Cewar Kamal yana mantawa da wa yake magana.

Wata irin juyowa Taj ya yi yana kallonsa "saboda kai za ka aureta ko kuwa ?asar za ka bari idan ta tashi auren wani a dalilin nauyin bakinka?"

Wayancewa Kamal ya yi "likitoci na auren ?an kasuwa ne? Idan rabon wani ce sai in tafi China odar kaya kafin a gama bikin."

Tsaki Taj ya yi "ta nan kuma ka Sullo? Hmmm, kai ka san yanayin aurena da matsalar Alhaji ne su ka shige min gaba. Ba don haka ba da yanzu kai ma kana kwanciya kamar gasara a ruwa idan kuna waya."

"Wannan karin magana ne ko me?" Kamal yana dariya ya tambaye shi.

"A bakin ?ar Ficikar nan naji."

Dariya su ka yi sannan Kamal ya ce zai fita waje ya tada mota kafin Taj ya fito sai su Wauko Yaya. ?ata lokacinsu faWan iyaye zai jawo musu.

Yana fita Taj ya bishi da ido. Jikinsa yana bashi tabbas akwai abin da Wan uwan nasa yake Soyewa. Kwana biyu ma tunda ya dawo ya gan shi a rame. Yanzu ne ma ya Wan ciko. Zuciyarsa ta bashi ko ma mene ne ya shafi Dr. Mubina. Kuma yafi tunanin ?ila soyayyar Happiness ce bata karSa ba. Da an gama bikin nan zai je ya sameta har asibiti ko ya nemi gidansu. Indai ba wani aka bawa ita ba zai nuna mata cewa rashin karSar Kamal asararta ce. Happiness is a rare gem. Ko shi da ya same shi a matsayin Wan uwa ba ?aramin dace ya yi ba.

?arasa shirinsa ya yi su ka fice daga gidan. A daidai bakin layin su ka ga motar Ahmad wanda dawowarsa kenan daga Bauchi. Horn su ka yiwa juna. Basu kula da Salwa a gaban motar da kuma Mami dake kwance a baya ba.

Kiran wayarsa Kamal ya yi yana sanar dashi kayansa wanda duka ?an mazan gidan zasu saka banda ango suna Wakinsa. Sun bawa Anti Zahra ta ajiye masa kafin ta tafi.

"Zan Wan makara amma. A gajiye nake."

"Wai ina ka je ne? Ance tun safe ka fita."

Ahmad ya kalli bayan motarsa ya sauke numfashi.

"Sai mun haWu dai."

Da taimakon Salwa su ka shigar da Mami cikin gidan. GabaWaya ta rikirkice saboda ?amshin turaren Taj da hancinta yake iya bambancewa duk inda ta ji shi. ?akin da take zama Ahmad ya ce su shiga da Mami.

"Bari nayi wanka naje wajen dinner Winnan. Ba zan jima ba in sha Allah. Gobe da safe sai mu tafi asibitin."

Da azama ta mi?e ita ma bayan ta kwantar da Mami "Nima bari na shirya kafin ka fito."

HaWe fuska Ahmad ya yi "Salwa."

"Na'am." Sai kuma tayi murmushi "wallahi sauri zan yi Yaya."

"Ba ki da hankali ashe." Ya nuna kansa yana juya Wan manunin yatsansa cikin Sacin rai "wa za ki barwa Mamin da kike zancen zuwa dinner?"

Murmushi tayi "lahh, Ya Ahmad ai kai ma ka san ba zan tafi haka kawai ba. Tun a hanya nayi magana da Anti Zabba'u (?anwar Mami). Tana hanya ma don na faWa mata mun shigo gari."

"Yaushe ku ka yi maganar ban sani ba?" Ahmad ya tuhume ta.

"Tun jiya ne bayan mun yi waya da kai."

Zama ya yi a gefen gadon yana matse gaban goshinsa kafin ya Waga kai ya kalleta da takaici.

"Dama shirinki kenan shi yasa ki ka yi min ?aryar Alhajinku ba ya kula da lafiyarta?"

"Wallahi Yaya..."

A harzu?e ya tashi kamar zai kifa mata mari "Shut up Salwa. You are very stupid."

"Don na ce zan je bikin ?aninka kake zagina Ya Ahmad?"

"Ba za ki ba! Ko ?alau Mami take babu inda zaki. Haba! Yarinya kin bi kin haukace kuma kina neman haukata kowa. Taj baya son ki, kuma ko yana so ina cikin masu hana shi aurenki saboda baki san bambancin so da obcession ba."

Kuka ta fashe masa dashi. Tana jin saukar maganganunsa tamkar sukar mashi. Sai ta mallaki Taj a matsayin miji kuma akan idonsa ta ?udurta a ranta.

Mami tana daga kwance tana Waga lafiyayyen hannunta akan su yi shiru. Kallonta Ahmad ya yi ya fice kawai domin dai ba a canjawa tuwo suna. Alh. Mukhtar ya faWa masa komai da yaje Waukarta. Ya kuma sanar dashi cewa ya saketa sannan idan sun tafi to ta tafi kenan daga rayuwarsa. Har abada baya son sake ganinta. ?annen Salwa mazan suna wajensa. Ita kuma ya ce idan sun gama zaman asibiti ya dawo masa da ita domin aurar da ita zai yi. Sun gama magana da wanda zai aureta ma.

Wannan ne dalilin da yasa ya taho da ita. Ba wai ?aryar da tayi masa ba. Don tabbas komai na bu?ata Ahmad yaje ya samu suna dashi. Kawai mijin nata ne dai ya fita harkarta.

"Zan jira Anti Zabba'u ta iso kafin na tafi." Ta ce da Mami.

"Uhmm uhmm Salwa" Mami ta ce da ?yar.

"Mami zani fa. Na san da lafiyarki ?alau za ki bani goyon baya."

BanWaki ta shiga ta sillo wanka. Ta fito tana cikin shiri Anti Zabba'u tayi mata waya cewa tana bakin gate. Garin saurin ta buWe mata abu ya faWo daga jikinta bata sani ba. Yun?urawa Mami tayi ta le?a abin. Sai da jikinta ya kama rawa. Sabuwar laya ce don zaren fari ne tas irin wadda take taunawa idan za ta yiwa Alh. Mukhtar magana. Zarginta akan Salwa ya tabbata. A asibiti Salwan tayi zaton bacci take ta Wauki wayarta ta kwafi lamba. Kuma taji bu?atar da ta faWa...tana son mallake wani. Sai yanzu ta gane malamin tsibbunta ne Salwan ta Wauki lambarsa. Kenan duk abin da take yi ?ar na lura? Bata son inda tabi har rayuwa tayi mata wannan atishawar ?an tsakin ita ma Salwa ta bi. Da ?alau take duk inda ake takawa zata je domin farincikin ?arta, amma bata so ?a?an su yi wannan rayuwar.

Bakin Salwa kasa rufuwa ya yi da ta buWe ?aramar ?ofar gate su Anti Zabba'u su ka shigo. Don ma babu motar Ahmad ta san ya tafi. Gayya guda har su shida. Ita da ?an matan ?a?anta guda uku. Sai babbar bazawara da goyo. Kowacce ta bawa shabiyar baya. Ita ma Anti Zabba'un ta gaji da aure aure ta ha?ura. Dama kuma ta jima tana ro?on Mami ta tilasta Ahmad auren guda cikin ?a?an nata amma ta?i yarda saboda kar ta san kar ne. Sai gashi Salwa ta faWa mata halin da Mamin take ciki. Da murna ta kwaso jiki. Ko Ahmad yana so ko baya so sai ya auri Waya kuma ya saki wannan mai dara daran idanuwan.

Ita dai Salwa bata san Mami taga layarta ba. ?aukewa tayi ta tura a jaka. Ta gama shirinta tsaf ta haWa da turaren wajen su Ummi ta fita. A rashin sani turaren aikin Alh. Usaini ta Wauka tunda shi ne aka ce mata zai kawo soyayya tsakaninsu.
A daidaita sahu ta samu har event centre Win. Motoci ko ta ina. Ta zo bakin gate tayi turus don babu kati!

***

Shafawa ido toka Taj ya yi da ya shiga ciki ya ce da Abba ya ro?i da Yaya ta fito su tafi saboda abin da Hamdi ta ce. Yayan da Inna Luba suna zaune a wajen.

"Ayi haka Taj? Muna da gefe bai fi ba?"

"To nima dai idan bata fito ba tabbas babu inda zani tunda amaryar tayi rantsuwar ba za ta fito ba."

"Barni da ita. Yanzu zan kira in yi mata faWa." Cewar Abba yana ?ara kaurara murya don ya ?ara mata kwarjini.

Taj ya ce "Abba me Soyon zai ?ara ko ya rage? Waye bai san ?arka nake aure ba? Wa kuma kuke son Soyewa kanku? Kuna jin gata ne kuke yi musu? Mushirikai da fasi?an iyaye ake gudun nunawa. Amma idan kuna yin haka nan gaba sai sun fi ku jin kunyar a ganku tare. Kunga sai ayi ta rubuta musu zunubin rashin kyautatawa iyaye."

"Kai Tajo, me yayi zafi?" Inna Luba ta ce a tsorace "ke tashi ki shirya ku tafi."

"Ke fa Inna?" Taj ya Waga mata gira "nawa kakannin babu. Ki zo ki wakilci kowa."

"Ja'iri, to bari nasa kaya. Dama wannan ?ar ce ta hana ni zuwa amma na so bin su wallahi" ta mi?e da murnarta.

Murmushi Abba ya yi. Yaya da Inna Luba su ka shiga Waki. Basu daWe ba kowacce ta fito cikin shiga mai kyau. Yaya lace Win da Mama ta aiko ta ce mata ankon manya ne ta saka. Kai kana ganinta banda lalurar ?afa da ba ?aramar mace za ayi ba. Fuska dai kam Masha Allah. Akwai kyau irin na Katsinawa wanda ?a?anta su ka haWa da na Simagade su ka fito gwanin ban sha'awa.

***

?arfe bakwai da minti arba'in da biyar daidai Amma ta kira Taj ya ce mata suna wajen parking.

"Bari a sauko da amaryar sai ku shigo."

"Amma tare muke da Yaya."

"Tun Wazu nake lalubenta cikin ba?i. Gani nan fitowa."

Da kanta taje wajen motar ta ri?o Yaya su ka shigo. Mama na hangota daga wajen zaman iyaye ta tada Umma su ka ?arasa. Hajiya ma ta ce da Inna lallai ta tashi. Tunda aka ce Taj ne ya kawota ta san tana tattare da jin nauyin shiga jama'a ne. Mutane sun fara kallon Yaya ana ?us?us da faWin uwar amarya ce sai aka ga matan Alh. Hayatu Sule masu aji sun je inda take suna yi mata maraba. Kayansu ita da matan da Amma iri Waya. Sannan su duka har ?asa su ka gaishe da Inna Luba. Wannan abu yasa duk mai abin faWa ta haWiye kayanta. Dukkan alamu sun nuna su Win suna cikin farinciki da son juna. Gutsiri tsomar ?an gayya bata da tasiri.

A Sangaren amarya kuma ?a?an Amma wato Ihsan da Amira da kuma Anisa sun haWu da masu ?ananun shekaru cikin ?an gidansu Taj da Anti Zahra sai kuma Sajida da Zee wajen rako amarya. GabaWaya matan doguwar riga su ka saka ta wani yadi sky blue da Wigon fari da pale yellow wadda aka yiwa wani irin Winkin bubu mai kyau. Umarnin Hajiya Gambo kenan. Duk wata jininsu da tayi Winki mai fitar da shape a gida zata ci bikinta. Babu head sai rolling da su ka yi da pale yellow Win yadi mai santsi. Babu yadda za ayi ka gansu basu burgeka ba. Modesty and elegance at its peak!

Amarya Hamdiyya kuwa gown Winta fara mai dogon hannu kuma wadatacciya. Bata bi jikinta ta tona sirrin wanda ya bada sadaki a gaban kowa da kowa ba. A kanta anyi mata Wauri da net silver wanda aka Worawa wani abin ado mai duwatsu sky blue na gashi ya kwanta ta Sari Waya. Daga tsakiyar Waurin inda gashinta yake a suturce aka Wora farin net dogo har ?asa. Wuyanta sar?ar farin gwal ce. Sai clutch bag Winta da takalmi mai tsini sky blue. Tayi kyau har ta gaji.

?asa suka sauko sannan aka zo bakin ?ofa aka jera yadda za a shigo. Kallo Waya Anisa ta yiwa Hamdi tunda sai yau su ka iso ta ganeta.

"Mai kukan uber?" Ta faWa ba tare da wani tunani ba.

Hamdi ta Wago su ka haWa ido. Ta saki murmushi mai ban sha'awa. Haka kawai sai Anisa taji ?uncin zuciyarta ya kau. Ta matsa kusa da ita tayi musu selfie sannan aka ce su tsaya kamar yadda aka tsara musu.

Matan layi layi suka yi hagu da dama har layi shida. Sai Hamdi a tsaye. A bayanta kuma Bishir da Abba. Sai kuma Kamal da Ahmad a bayansu. Sanye su ke da yadi pale yellow da aka yiwa Winki ma hannu da ya wuce gwiwar hannu da kaWan. Daga hula har zuwa takalmi komai nasu iri Waya in banda agogo. Hamdi tayi zaton tafiya za su fara yi don hankalinta a tashe yake tun a nan ga hasken flash ana ta Waukar hoto. ?ofar hall Win aka buWe ta soma jin sanyi da ?amshin wajen na buso ta sai ji tayi hannuwa sun kama nata da gentle ri?o. Tsigar jikinta tashi tayi da tsoro da kuma gane hannun waye. Tsayuwarsa kaWai a kusa da ita ta sanya sanyin nan ya ragu don kansa. Ta Waga kai su ka haWa ido.

Kayan jikinsa sky blue ne harda babbar riga irin wadda ake yi ta zamani ba burum-burum Winnan ba. Shi ma hannun rigarsa ta ciki ?arami ne kamar na ?an uwansa. Ya sanya hula da takalmi cover shoe navy blue mai duhu sosai. Gashin baki da gemunsa da basu cika yawa ba sun sha gyara.

"Ya Rabbi, har na fara tsoron ko ni kaWai zan shiga" Hamdi ta faWi a hankali tana kawar da kai don kallon nasa babu rissina a ciki.

"Ina tare dake kowanne taku. Ki daina jin tsoro." Ya bata amsa a kunnenta.

Hannunta zai saki yaji ta kuma dam?e nasa.

"Don Allah ka ri?eni har mu zauna. Zan iya faWuwa da takalmin nan." Ta marairaice masa idanu har lokacin tana magana a hankali don kada na gabansu ko baya su ji.

"Awwwnnnn, zuciyata" Taj ya dafe ?irji kuma da gaske yadda tayi Win ya shige shi ne sosai.

Fari tayi da ido tana harararsa "A nan Win ma sai kayi?"

"Kin gama dani ne Mrs Ha..."

Wani abu su ka ji kamar harbin bindiga da ya katse masa magana. Sai kuma muryar MC yana sanar da shigowar ango da amarya da umarnin kada kowa ya bar wurin zamansa da sunan Waukar hoto. Wani irin kiWan taushi ne yake tashi babu wa?a a yayinda suke shigowa wajen cikin nutsuwa. Matan dake gaba basu mai rawa sai Wan kwanon hannunsu mai fulawoyi masu kyau da su ke ta watsawa sama.

Da su ka iso gaba Yaya ta ?yallara idanu ta hango ?an matanta, bata san lokacin da idanunta su ka tara ?walla ba. Ta dinga hamdala a zuciyarta. Ashe Inna Luba ma hakan take a wajenta. Sai dai ita bata iya Soye nata hawayen ba. Jikokin kenan sai Halifa cikon na huWu. Sai kuwa na yayarta abar alfaharinta har kullum. Amma dai jininta da take da cikakken iko dasu waWannan ne. Da kanta ta dinga bin ?an uwan Yaya wato ?q?an abokiyar zamanta mazansu da matansu a samu mai zuwa bikin nan amma yadda su ka ?i zuwa na Sajida wannan ma ?i su ka yi. Ta ro?i maigidanta ko sau Waya ne ya yi musu magana ko ya zo ?arsa taji daWi ya ce ba zai taSa murna don ?a?an Wan daudu sun yi aure ba. Su je can su ?arata. Godiya kawai take ga Allah domin bai haWa mata zuri'a da lalatattun mutane ba. Dukiyar bata tsole mata ido ba. Girmamawar daga surukan ?a?an shi ne komai a wajenta.

A teburin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login