Showing 21001 words to 24000 words out of 182745 words

Chapter 8 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

76

ya yi mugun tashi. Balle da aka zo sulhun nan ta fahimci ashe su Hajiya ma dake gidan sun daina girki. Wannan dalilin yasa ta sauke dukkanin tijarar da ta tanadarwa Alhaji. Domin tana da tabbacin muddin ya sallameta akan Taj su ma za su gwada masa rashin goyon baya. ?arshenta cikin fushi aurensu ya sami matsala. Indai ba butulci ba kuwa irin zaman da su ke yi a gidan bata jin ya kamata ta yi musu sakayya irin wannan.

Zafin da taga sun Wauka ne ya bats damar yi musu wancan bayani yadda za su fahimceta.

"Kuna ganin rayuwar Taj za ta yi albarka idan sanadinsa gidan nan ya wargaje? Fushi irin na Alhaji nayi imanin sallamarmu duka lokaci guda ba zai yi masa wahala ba. Sai dai ya yi nadama daga baya. Sannan gabaWaya yaran gidan nan da wuya su sake yiwa Wan uwansu kallon mutumci. Da farin gashinmu a ka ace muna zawarci."

Allah Sarki. Tana rufe baki Umma ta rungumota.

"Ki yi ha?uri Abullen Alh. Hayatu. ShaiWan yaso amfani da Sacin raina ya haddasa mana fitina."

"Sunan da ki ka kira ni dashi na mene ne kuma?"

"Na ?aunar rigimammen tsohon nan mana."

Dariya su ka ji an kwashe da ita. Shaf sun manta da ?a?ansu dake wajen a tsaye. Kowa da jan ido an sha kuka suke dariyar daidaitawar iyayen nasu. Da wannan kuma babbar ?ar gidan Yaya Bintu ta sanar da ?an uwanta cewa babu masifa da za su bari ta shiga gidan sama da rabuwar kawunansu. Don haka kowa ya shirya abin da zai iya domin taimakawa Taj. HaWin kansu kaWai zai iya sassautawa mahaifinsu ha??in Wansa da yake Wauka.

Zaman lafiya aka ce yafi zama Wan sarki. Alhaji bai san cewa duk cikim alkhairansa na duniya yadda ya gina gidansa shi ne mafi girman arzi?insa ba. Gashi yana neman Sata abin sa da hannunsa.

Motar Ahmad su ka shiga ya kaisu gidansa. Sai ga Taj ya manta da dukkanin damuwarsa da ya ganshi tsakanin uwayensa.

***

Abba ya maimaita zancen da yaji daga Vice Principal yafi a ?irga a zuciyarsa bayan sun gama waya. Abin ne bambarakwai wai namiji da suna Hajara. Ta yaya ma za a ce Hamdi tayi dambe har ta kai rashin zuwansa akan matsalar zai iya jawo mata kora? Hamdi ce fa. Yarinyar da ko a cikin ?an uwanta lokacin ?uruciya da wuya a kawo ?ararta.

Damuwar da su ke ciki shi da Yaya akan matsalar tashinsa da aka yi daga wurin sana'a sai ta zama ba komai ba. Fatan wayewar gari kawai yake domin yaje ya ji me yake faruwa. Sai dai kuma hantsi na soma le?owa yaji wani irin tashin hankali. Da hankalinsa ya riga ya san yadda yaran ke kunyar nuna shi musamman ita Hamdi. Shin za ta yi maraba da amsa kiran nasa ko kuwa?
RAYUWA DA GI?I 8




Batul Mamman=ؖ?




***

ZazzaSin gaske ne ya kama Ummi tun bayan ta saurari wayar Vice principal da mahaifinta. Aikin gama ya riga ya gama. Bayan ya ajiye wayar wani irin kallo ya yi mata ya jinjina ?arfin halinta. Sannan ya ?ara tabbatarwa mace abar tsoro ce komai ?an?antarta.

"Wannan mutumin shi ne mahaifinki Ummi?"

Kai a ?asa ta ce "eh."

"Wanda yake zuwa kuma ya kuke da shi? Kuma me yasa ki ka zaSi faWin gaskiya yanzu?"

Shiru tayi babu amsa tunda Hamdi ma ta?i magana me zai sa ta fara?

Rai a Sace ya ce "To kuwa ki kwana da sanin cewa yau ce ranarki ta ?arshe a makarantar nan. Don ban ga wani dalili da zai hana a kore ki gobe ba ko da kece mai gaskiya. Sannan dole zan kira shi domin a warware komai gaban mahaifin naki."

Yanzu ma kasa cewa komai tayi sai faman sa?e-sa?en neman mafita. Sannan a gefe guda babu irin ashar Win da bata saukewa Hamdi ba. Da farko ta san kawai jindaWin samun mai yi mata bauta a makaranta tayi da sanin sirrin Hamdi. Yanzu kuwa wata irin tsana ce da za ka ji komai ma za ka iya yiwa mutum take ji akanta. Har lokacin bata saduda ba don tana jin da Hamdi tayi mata biyayya ta bata ruwan nan da bata ga wannan lokacin ba. HaWuwarta da Baba Maje gobe ba ?aramar tarzoma zai tayar ba.

"Ki tashi ki fice min daga office nace."

Tsawar VP ta dawo da tunaninta inda take. Ta mi?e za ta fita sai kawai wani tunani ya zo mata. Guntun murmushi ta saki wanda har ga Allah sai da ya VP Win tsoro da shakku akanta.

Wurin ?awarta konace babbar ?ar korarta Widad taje da saurinta. Sun gama nasu punishment Win na yau sai kuma washegari da ake sa ran samun ruwa. Za su wanke banWakunan makarantar kaf har na malamai. Ga kuma sharar harabar makaranta da cire ciyayi.

Widad na ganinta ta tashi zaune daga kwanciyar gajiyar da tayi. Ummi ko kallon arzi?i bata yiwa ciwon dake babban yatsan Widad na ?afa wanda taji a wurin faWan Wazu ba. Kuma ta gan shi sarai amma ba shi ne a gabanta ba.

"Bani wayarki in kira Uncle B"

"Kuna can aka zo inspection Win bazata tun bayan an nuna wayarki a wajen principal. Yau wayar da aka fitar daga Wakin nan tafi ashirin."

Muguwar harara Ummi ta jefeta da ita sannan ta yatsina fuska ta ce mata "banza, me yasa ko a pant baki Soye ba?"

"Korarmu aka yi waje bamu san dalili ba. Sannan aka yi searching Winmu da Wai-Wai." Widad ta amsa tana mai Soye zafin zagin da halin ko in kula da Ummin ta saba nuna mata.

Plan Winta na farko ya faWi tun kafin ta aiwatar. Dama niyarta ta faWawa sugar daddy Win nata da take kira Uncle B idan an nemi numbarsa kada ya yarda ya zo. Shawara ta biyu kawai za ta Wauka. Idan an zauna gobe kawai ta tada aljanu kuma duk yadda za ayi da ita kar ta yadda ta dawo daidai sai an koma gida. In ya so ko kasheta za ayi gara ayi a can.

***

A hanyarsa ta zuwa tasha cikin adaidaita sahu Abba ya kira ?aninsa a waya. Hankalinsa ne sam bai kwanta da zuwa makarantarsu Hamdi ba. Yana son kare martabar ?a?ansa daga dukkan abin da zai iya janyo musu raini daga mutane. Ya tuna wani lokaci da Yaya Hayatu kamar yadda yake kiran Alhaji yayi masa wata magana a baya.

"Habibu gaba nake jiye maka. Lokacin da za ka ji kunyar nuna kanka a wasu wuraren saboda kana ganin kamar darajarka bata kai ba. A lokacin ilimi ko rashinsa, talauci ko arzi?i ba su ne za su zame maka shamaki ba. Wannan mazantakar da kake gudu da Allah Ya karramaka da ita ce za ka so a baka aro ko na awa guda ne."

Bai manta yadda ya murguWa baki bayan wucewar Alh. Hayatu ba. Ya doka cinya harda tofar da yawu.

"Aniyarka ta bika. Sa idawa, ana ruwa kuna ?irgawa." Ya nuna ?afarsa "wannan sayyara da Allah Ya bani babu inda ba za ta shiga ba sha Allahu."

Ga ire iren ranakun sun zo. Ina ma ana mayar da hannun agogo baya. Da ya juya lokaci ya canja komai banda auren Jinjin. Matar da ta rufa masa asiri ta kuma bashi ?a?a mafi soyuwa a gare shi.

Gaisawa su ka yi da ?anin nasa da girmamawa sannan ya faWa masa halin da yake ciki a kunyace.

"Wallahi Yaya Habibu ka ganni a asibiti wani ma?ocina ne babu lafiya. Daga shi sai matarsa ga yara ?ananu ta taho dasu. Basu da kowa a nan sai mu ma?ota. Yanzu haka yayansa dake Zaria yana hanya. Tun asuba nake nan."

"Ahhh, yi zamanka Abdul?adir. Bari kawai naje."

"Ka daina Soye kanka daga rayuwar yaran nan. Yau in dukkaninmu babu sai kai kaWai shikenan sai ace zuri'armu basu da uba saboda abin da ya wuce?"

Yayi maganar ne saboda ya saba ji daga yaransa cewa ?a?an yayan nasa suna kunyar ala?arsu da shi. Bai ga laifinsu ba Fisabilillah. Amma kuma Allah da Ya haWa ala?ar Shi Ya san yadda zai tafiyar da al'amura. Tayasu Soye kansa ba dabara bace tunda duk lalacewa da uba ake ado.

Abba bai sake neman kowa ba ya tafi makarantar. Anyi sa'a yau shadda ya sanya ruwan madara, riga da wando harda hula. Da ya shiga makarantar bayan tafiyar minti arba'in tafiyarsa ya fara ?o?arin gyarawa. Sannan da zai tambayi masu gadi ofishin principal ya daddage ya kumbura murya. Amma kunne da idanu masu lafiya babu yadda za ayi su kasa fahimtar me ake son Soye musu. Basu dai nuna a fuska ba guda ya nuna masa hanyar office Win. A can gefe inda ake ajiye motoci ya ga wata kamar ta Baba Maje. Amma da yake baya tare da nutsuwa bai tsaya ?are mata kallo ba.

***

A rayuwa babu abin da yafi tashin hankali kamar a samu wani ya san sirri a kanka wanda baka so a sani. Kuma in anyi rashin sa'a ya dinga amfani da wannan damar wurin cusgunawa rayuwarka. A shekara shidan da Hamdi tayi a makarantar nan bata taSa shiga matsanancin hali ba sai da Ummi ta fara blackmailing Winta. A jiya da abu ya fito fili waWanda su ka sami ganin bidiyon nan su ka labartawa waWanda basu gani ba, sai taji zuciyarta wasai. Abin ya matu?ar bata mamaki. Tayi zaton in an sani an tsokaneta za ta iya yin kuka. Sai gashi babu wanda ya tunkareta tunda aka ga abin da ta yiwa Ummi da kuma maganar da ta yaSawa wata Metiron bayan ta dawo Waki.

Da yake wasu manyan hankalinsu a ?wauri yake, matar a gaban mutane ta tambayeta.

"Hamdiyya da gaske ne babanki Wan daudu ne?"

A fusace ta amsa da "Eh, amma yafi uban wasu da yake zaman prison."

Matar tayi matu?ar mamaki domin kuwa ba kowa ne ma ya san cewa mijinta yana prison ba saboda sata. La?was tayi don babu halin sake magana saboda ?an kallo sun sami sabon abin tattaunawa.

?arfe goma aka aiko kiransu. Tana zuwa ta sami Ummi tayi kneel down a gaban teburin Principal. Ga Baba Maje zaune akan kujera. Yana ganinta ya saki fuska sosai yana magana da Principal Win.

"Yauwa ita ce kuwa."

Principal ta dube shi da Wan sakin fuska don taga sam bai fahimci zancen ba ta ce "Nima ita nake nufi Alh. Maje. Wannan Hamdiyyan ce dai su ka yi faWa da Ummi jiya su ka yi sanadin hargitsa makarantar nan."

"Na gane bayanin naki Hajiya. Dama abin da nake son fahimtar dake shi ne ina ganin Waya daga cikinsu ce ta shigar wa ?ar uwarta. Ba wai a junansu su ka yi faWan ba." Ya yi mata bayani dalla dalla a ?o?arinsa na son ta gane.

Murmushi tayi masa don yanzu bata jin za su fahimci komai sai yaran sun yi magana.

"Ko me yasa ka yi wannan tunanin?"

?ar dariya ya yi gami da gyara hannun rigarsa "mahaifin Hamdiyya abokina ne tun kafin a haifesu kin gansu nan. Shi yasa nake tunanin ko karewa juna suka yi. Ba kuma wai goyon bayansu nake ba. In sun yiwa makaranta laifi zan bada goyon baya Wari bisa Wari a hukunta su."

Abin da ya faa ya bawa Principal Win mamaki sai dai bata ce komai ba sakamakon sallamar sakatarenta da mutane biyu. ?aya wani ?osasshen Alhaji ne ya sha babbar riga yana fama da kayan tumbi. ?ayan kuwa Abban Hamdi ne. Su na shigowa VP da wasu manya cikin malaman su ka shigo su ma.

Abba na ganin Baba Maje ya ce "da na san za ka zo ai da nayi zamana a gida."

"Ko kuma da ni na zauna ba."

Dariya su ka yi sannan aka yi musabaha tsakanin duka mazan wajen.

Murya da yanayin mahaifin Hamdi kaWai yasa malaman kallon kallo a junansu. Principal ta bu?aci a buWe zaman da addu'a sannan ta Wauko wayar Ummi ta mi?a mata.

"BuWe min wayar nan don na sami labarin ita ta fara janyo rigimar."

Kai Alhaji mai Wan tumbi wato Uncle B da baka gane Baba Maje ba tunda Ummin bata kama dashi sai ya kama faWan bogi.

"Ban hanaki zuwa da waya makaranta ba? Ke kenan kullum rigima ta tashi sunanki ne a sahun gaba."

Baba Maje buWe baki yayi don maganar ba tsoro ta bashi ba illa ruWa masa tunani. VP na ganin haka sai ya taso har inda yake ya ja shi waje.

"Duk abin da za ka ji ko ka gani kada kace komai don Allah har ka gama fahimtar inda zancen ya dosa."

"To amma..."

"Mu koma ciki. Komai zai warware kansa."

Ha?uri ya bawa Principal na katse su sannan su ka jira Ummi ta buWe wayar da rawar hannu. Jikinta babu inda baya Sari. So take tayi aljanun ?aryan tun yanzu amma bata da ?warin gwiwar pretending. Hamdi da bata san bada?alar dake kwance ba kuwa ko a jikinta. Jikin kujerar da Abba ke zaune ta raSa tayi kneel down abinta.

"Kunna min abin da ki ka kunnawa Walibai a jiya."

Nan fa Waya. Kasa kunnawa tayi. Displine master ya daka mata tsawa amma ko gezau.

"Kin cika umarnin da aka baki ko sai na tashi?"

Muryar Baba Maje ta fito da kaushi. Uncle B duk ya zata malami ne da ake tsoro shi yasa bai ji komai ba da yaga ta cika umarni da rawar jiki.

Ofishin karaWewa yayi da muryar Abba. Kunya tayi masifar kama shi. Idanunsa su ka yi jawur lokaci guda. Hamdi taji wani irin tausayinsa wanda yasa ta kuka. Baba Maje ya rasa me yake yi masa daWi.

Principal ta mi?awa kowa wayar ya gani da idonsa sannan ta umarci Hamdi da tayi magana. Ba tare da coge ba ta faWi abin da ya faru tun ranar da su Baba Maje su ka zo gidansu har abin da ya faru jiyan. Irin cin zarafin da Ummi ke yi mata da takura kawai don ta mallaki sirrin mahaifinta. Kallon takaici kala kala ya dinga sauka akan Ummin bayan ra gama magana.

"Ummi haka aka yi? A ina ki ka sami bidiyon?" Uncle B ya tambayeta har yana kai hannu zai Waga haSarta domin kanta a ?asa yake tana zubar da zafafan ?wallar tsanar Hamdi.

"Wai kai Win uban waye a makarantar nan da za ka taSa baligar mace?" Baba Maje ya tambaye shi a harzu?e bayan ya doke masa hannu.

"Kai zan yi wa wannan tambayar." Ya kalli Principal Win "ya kamata malamanki su san aikinsu in ba haka ba zan cireta daga makarantar nan."

Baba Maje ya ce "Kai a wa?"

"Ni a mari?inta" Uncle B ya bada amsa kai tsaye.

VP gaban kujera ya dawo don yaga an zo inda yake jira. Cikin zafin rai kuwa Baba Maje ya Wago Ummi tsaye ya dubeta.

"Kalli ?wayar idona ki faWa min waye wannan."

Numfashi ta fara ja tana shirin yin suman ?arya taji Baban nata ya yi mata wata irin wawiyar jijjiga. Muryarsa tana rawa har wajen office Win kuma ana ji ya ce,

"Idan ki ka ce za ki yi min ?aryarku ta Walibai zan sabauta miki halitta a wajen nan. Ki faWa min waye shi."

"Saurayi na ne."

Tasss, tass, tas ya Wauketa da wasu gigitattun maruka. Abba ya yi saurin finciketa daga hannunsa ya tsaya a tsakani.

"Haba Maje..."

"Matsa min Habibu." Ya furta yana huci.

Uncle B na ganin haka ya tashi zai sulale ya gudu sai dai babu dama. VP ya sanya securities Win makaranta a bakin ?ofa. Hasashen haka zai iya faruwa tun a jiya yasa ya Wauki matakin da ya dace.

Da ?yar da suWin goshi aka samu Baba Maje ya zauna. Abba ya dubi Principal Win ya yi magana.

"Da farko zan fara da baku ha?uri akan Sarnar da yaran nan su ka janyo muku. Ummi tayi kuskure sannan ita ma Hamdi tayi na Waukar doka a hannunta. Amma fa duka abin da ya faru laifina ne..." ya sunkuyar da kansa.

Principal ta kalle shi da tausayawa "bari na Wan ce wani abu a nan." Ta kalli Hamdi "mu iyayenku da ku ke gani muma haifarmu aka yi ba da wayo muka zo duniya ba. Shekarunmu na hawa ne muna daWa hankali. Duk wani kuskure da kuke yi a yanzu muma mun yi ?ila ma fiye da haka a lokacin tamu ?uruciyar. Yanzu mun girma mun san illar abin shi ne dalilin da yake sa muke muku faWa ma idan kun yi. Abin nufi a nan shi ne ?uruciya da raunin hankali a baya yasa mahaifinki yin kuskuren bin rayuwar da kowa yake ?yama. Gashi ita aba ce da ko ka daina da wahala abi'unta su barka Wari bisa Wari. Amma tunda Allah Ya baki shi a uba ki rungume kayanki da godiya. Da baki ji kunya kin Soye shi ba, babu wanda ya isa ya Waga miki hankali akan shi. Ki nuna godiyarki ga Allah ta hanyar appreciating Win duk abin da Ya baki."

GyaWa kai tayi tana goge hawaye "Abba don Allah ka yafe min."

Da ?ar muryarsa ya ce "Allah Ya yi miki albarka Hamdiyya. Ki bawa iyayenki na makaranta ha?uri su ma."

Ta kuwa bi umarninsa ta bawa kowa ha?urin abin da su ka yi jiya. Cike da kunya da jin nauyi Baba Maje ya bawa Abba ha?uri.

Abba ya yi murmushi "Don Allah ka bar wannan zance."

"Ta yaya zan bari? Bayan shekara sama da ashirin da rabuwarmu ace ?ar cikina ce tayi maka irin wannan tozarcin?"

"Magana ni dai ta wuce don Allah." Abba ya sake maimaitawa.

VP ya ce "yallaSai ina ganin sanin ala?ar Ummi da mutumin nan shi ne abu mafi mahimmanci yanzu tunda an kashe wancan case Win."

A lokacin aka fito da file na fitinannun makaranta inda sunan Ummi ya bayyana a kowanne term tun zuwanta a JS3. Bata fara laifin da ta cancanci a kira iyaye ba sai a SS2 da ta zama cikakkiyar senior. Kuma a lokacin ne duk sanda aka bu?aci iyayenta sai wannan mutumi dake zazzare idanu ya zo a matsayin kawunta. Ita ma aka bata dama ta faWi yadda suke biyan maigadi su haura katanga ita da wasu. Samarinsu su kai su gari a sha?ata a sha ice cream da su shawarma a dawo. A rantsuwarta dai ta ce babu abin da ya taSa haWasu na fasi?anci. Baba Maje kasa jurar jin maganganun ya yi ya finciki bulalar hannun wani malami ya shiga lafta mata. Da taron dangi aka raba shi da bulalar

"Kanki ki ka cuta Ummi. Nan duka Waliban da ki ka zalinta in basu yafe ba sai kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login