Showing 156001 words to 159000 words out of 182745 words

Chapter 53 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

116

yadda ya bawa Yaya. Harda cewa kada ta damu tunda Abba zai tafi zai rage wasu kayan.

Yanayinta ya dami Taj sosai amma kuma bashi da kuzarin yawaita magana. Ya rasa mene ne yake ci masa rai ya hana shi walwala. Haka su ka kwana a gidan kowa da abin da yake kai komo a ?irjinsa. Da safe su ka haWu ?arfe tara a harabar gidan Alh. Hayatu. Wata luxury bus Win gidan mai Waukan mutum talatin suka shiga direba ya kai su airport. Jirgin Abba Habibu sai uku. Su zasu shiga Qatar Airways, shi kuma zai shiga Ethiopia.

*
SaSanin abin da ?an uwan Taj suka yi zato na cewa zai dage sai Hamdi ta zauna kusa dashi kamar yadda tsarin boarding pass Winsu ya nuna, sai suka ga akasi. Daga zolaya a ka ce ta zauna seat Waya da ?annensa sai suka ga ta tafi ko a jikinta. Zama tayi ta rufe idanunta tun kafin jirgin ya fara motsi. Taj kuma bai yi cigiyarta ba. Da Yaya Hajiyayye ta kula ne ta zo da kanta ta kamo hannunta.

"Ina yi miki kallon wayayyiya za ki wani bari ?an uwan miji su shigar miki hanci? Zaman me zaki yi a cikinsu bayan ga mijinki?"

"Nan Win ma duk Waya ne." Hamdi ta amsa da sanyin murya.

"Duk biyu dai." Cewar Yaya Hajiyayye. Ta kaita inda Taj yake. ?anwarsu dake zaune a wajen ta harara ba shiri ta tashi tana dariya.

"Mu fa rigima muka so haWawa. Muce sai ya biya zata dawo nan. Amma sun manna mana hauka ko magana babu wanda yayi." Ta faWi tana dariya.

"Sun san me suka taka ne. Gashi nan babbar yaya ta shigar musu. To mu dai duk da haka sai an biya mu. Abaya za ka saya mana dukkanin mu."

Sai a lokacin Taj ya magantu bayan Hamdi ta zauna.
"Dama ku biyun nan akan ku Alhaji ya fitar da zakka. ?an 419 kawai. Yahoo girls."

Ai kuwa me zasu yi banda dariya. Har Hamdi sai da tayi. Da aka yi sanarwar kowa ya zauna Taj ya saka mata seat belt sannan ya kama hannunta ya sar?e da nasa. A lokacin taji komai ya kwance mata. Raunin zuciyarta ya ninku sosai. ?walla ta taru ta cika idanun fal.

"Happy" ta kira Taj da murya a sha?e.

Ya gyara zama "Uhmm."

"Me yasa na daina Wokin tafiyar nan?"
Bata jira yayi magana ba ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

"Shhhh. Please...." ya Wago haSarta.

Abin da ya gani bai yi masa daWi ba. She looked so confused. Ya buWe hannuwansa ya yi mata kyakkyawar runguma. Tayi kukan mai isarta amma bata ji sau?i ba. Suna wannan yanayin har jirgin ya gama taxi ya tashi. Ri?on da tayi masa ne kawai ya ?ara ?arfi amma bata yarda da Wago kanta ba. Jim kaWan bayan jirgin ya daidaita a iska Taj yaji ri?on yayi sako-sako. Ya Wan girgizata bata motsa ba, sai ma kwanciya da ta gyara a jikinsa tana bacci.

Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasul ya karanta ya tofa mata sannan ya ran?wafa ya kwantar mata da kujerarta. Baccin mai nauyi ne ya kama ta. Yaji daWi domin jiya shi da ita marathon Win juye juye kawai suka dinga yi. Ba ita ta farka ba sai da ya rage bai fi minti talatin su sauka a Doha ba. Za su yi transit na awa biyu sannan su kama hanyar Saudiyya.

Kowa watsewa yayi an tafi window shopping. Masu ra'ayi kuma idan sun ga abin da suke sha'awa za su saya. Hamdi da Taj kaWai aka bari. Suna zaune gadin kaya sannan ba hira suke yi ba.

Yaya Hajiyayye tana ankare dasu. Bata jima ba ta dawo ta sanya su a gaba.

"Wai har kun fara faWa ne daga aure?"

"Tuf, tuf, tufff" Taj ya kama tofi da baki.

Kama ?ugu tayi ta harare shi
"Ni kake tofewa Tajo?"

"Kece ana zaman lafiya zaki kawo abin da babu."

"Ai naga sai wani basarwa kuke yi. Ko laulayi kika fara ne Hamdiyya?"

Yadda ta sako maganar kai tsaye sai da Hamdi ta zabura ta hau rantse-rantsen ita bata da komai.

Shi kuma Taj sai cewa yayi "ki ka sani ko akwai?"

Wata uwar harara Hamdi ta watsa masa ba shiri.
"Ni wallahi ?alau nake."

Yaya Hajiyayye ta kallesu tayi dariya. Kunya duk ta kama Hamdi. Taj ya tashi yace ta taso su zaga su ma.

"Indai da matsala Hamdi ki faWa min. Ko baki yi karatu da Firdaus ba kinsan dai na haifeki. Taj Win ma..."

Da sauri Taj ya katse Yaya Hajiyayye kafin ta gama bayar dashi a gaban matarsa.
"Haba, haba Yaya Hajiyayye. A lissafin waWanda kika haifa ai kinsan dai babu ni. Sai da na zama mutum fa aka yi miki aure."

"Wai ka zama mutum. Taj kaji tsoron Allah. Lokacin da kuke zuwa gidana fa ko tsar..."

Da wani irin sauri Taj ya tashi yana dan dukan laSSansa a gabanta don tayi shiru. Tuni ta gano ashe ta Wauko hanyar bada maza. Ita da Hamdi suka ?yal?yale da dariya.

Ya harari Hamdi "Ke kuma meye abin dariya?"

"Ba dariya nake ba ciwon kumatu ne ya kamani." Ta bashi amsa tana gimtse wata dariyar.

A haka Yaya Hajiyayye tayi amfani da hikimar manya ta mantar dasu damuwarsu. Su ka rankaya da ita wajen ?an uwansu ana ta raha har lokacin boarding Winsu yayi.

A gefe guda ta tsaya tana kallon ?annenta lokacin da suke ta hayaniya ta saki murmushin da ya tsaya a fatar bakinta kaWai. Jikinta a mace yake da nauyin tunani kala-kala. Zuwa yanzu ta riga ta tabbatar ko me zasu tarar idan sun haWu da ?an uwansu ba mai daWi bane. Fatanta kawai Allah Yasa yazo da sau?i.

***

JEDDAH

A cikin ?a?an Alh. Hayatu ashirin da takwas, mutum biyar ne basu sami damar zuwa Umrar da aka fake musu da ita ba. Daga mai haihuwa ko yau ko gobe sai uku a ?asashen ?etare, Wayar kuma an saka mata ranar defence na Masters a Sokoto.

Da suka sauka daga jirgi sun yi zaton Umra zasu fara yi. Dama Abba ya yiwa Taj kwatancen inda zasu same shi idan sun fito. Basu wahala ba kuwa suka hango shi a jikin wata farar bus mai girma. Direbanta yana ciki a zaune. Da murnarsu suka nufi motar sai dai Abba sam babu wani kuzarin kirki a tare dashi sai ya?e.

Tambayar da Taj ya fara yi masa da ya mi?a masa hannu ita ce

"Ina Happiness?"

"Suna hotel. Motar zata yi kaWan idan dukkanmu muka taho."

"Ka san kuwa ni bana ?aunar takura."

Kowa ya yiwa kanwarsu da tayi maganar dariya saboda ?ibarta sannan suka fara tafiya.

Taj da Hamdi wuri Waya suka zauna. Tana jikin taga shi kuma yana gefenta. Duk motsinsa tana karanta yadda walwalarsa ta sake Waukewa.

"Kamar kana cikin damuwa."

?an guntun tsaki ya fara yi na frustration.
"Kin san irin abin nan da mutum yake gane akwai matsala amma ya kasa pin pointing Winta?"

Hamdi ta gyaWa kai.

"To haka nake ji."

"In sha Allahu ma babu komai."

Suka sar?e hannuwansu waje guda har zuwa lokacin da motar ta fara slow. Nan fa hankalin kowa yayi mugun tashi. Sunan asibiti suke gani Saro-Saro. Daga jerin kujerun baya mafi kusa da direba Yaya Hajiyayye ta zura hannu ta kaiwa Abba duka a kafaWa. Jikinta yana wata irin rawa.

"Abba waye a asibiti? WAYE?" Da muryar kuka ta ?ara da cewa "Dama jikina ya bani wallahi"

"Yaya ki bari mu shiga don Allah."
Abba ya bata amsa da sanyin jiki.

Motar kuwa ta ruWe da hayaniyar fargabar ?an uwan. Direban na tsayawa suka dinga fita da sauri. Taj ne kaWai bai fita ba kuma ya hana Hamdi tashi sai da kowa ya fita.

"Ka tashi mu fita don Allah."
Ita kanta a gigice take.

"Happiness ne fa bashi da lafiya. Ina jin ma babu shi gabaWaya."

Tafin hannu Hamdi tasa ta rufe masa baki. Sai ga hawaye ya sauko daga idanunsa. Hamdi ta rungume shi ita ma ta soma nata kukan. Tayar da ita yayi suka fita gaba na faWuwa. Suna sauka daga motar suka ga Ahmad da Mubina.

"Hamdi ban so maganata ta tabbata ba. Kinga Dr. Mubina" ya nuno mata su "dalilin Kamal ta zo na tabbata."

Jikinta ya sake yin sanyi ?alau har suka isa inda suke. Ahmad ya Wan bugawa Taj kafaWa. Mubina kuma ta rungumo Hamdi jikinta suka shiga lift kamar tana so ta rarrasheta. Mamakin hakan ya kama Hamdi. Ba wai bata damu da Kamal ba, amma a ganinta akwai waWanda suka fita bu?atar rarrashi akan sa ko me ya same shi.

Tamkar wanda bashi da laka Taj ya dinga tafiya da ?ofar lift Win ta buWe. Suna yin kwanar farko ya hango zugar gidansu harda iyayen a corridor ana ta koke-koke. Taj ya kalli sama inda aka rubuta 'Room 7' sai yaji hankalinsa ya sake tashi. Wani zafi ya mamaye jikinsa. Bai san yadda aka yi ya isa gaban Alh. Hayatu ya tsaya ba.

"Alhaji me ya same shi?"

"Kidney transplant aka yi masa."
Ya bashi amsa amma hankalinsa yana kan Hamdi. Wani irin nauyinta yake ji.

Taj yayi gaba da sauri zai shiga Wakin idanunsa sun yi wani irin ja mara misali. Bishir ya ri?e shi da ?arfi ya janye shi daga wajen. Umarnin likitocin Kamal ne suka ce kada a shiga Wakin duk da ya farfaWo. Yana bu?atar hutu sosai. Ita Hamdi bata kula da abin da ya faru ba. Hankalinta yana kan su Inna. Ta rasa me zata yi saboda kowa hankalinsa a tashe yake. Kawai sai ta du?a da nufin gaishesu. Umma tayi saurin tareta a jikinta.

"Tashi Hamdi. Zo mu ?arasa can ki zauna."

Ta girgiza kai.
"A'a zan zauna a nan nima."

Ga mamakinta da na sauran Alhaji da kansa yace ta bi Umma.

"Ku je Hamdi."

Bata da zaSi sama da bin Umman. Kallo duka sai ya dawo kanta. Haka ta bisu cike da tsarguwa. Me yasa za a ce ita kaWai ta tafi? Ko sirri zasu yi? Ko dai Kamal Win ya...

"Hamdiyya"

Muryar Hajiya ce ta fito da yanayi mai ban tausayi. Hamdi ta juya ta ganta a tsaye. Hajiyan ta da ta sani da wannan dake gabanta da bambanci. Ramar da alamun rashin kwanciyar hankali sun yi yawa sosai.

"Hajiya yaya mai jikin?"

Hannuwanta Hajiya ta kama ta rufe da nata yatsun. Hamdi ta Waga kai taga Inna, Mama da Umma duka suna kallonta da wani irin yanayi na tausayi. Idanuwansu sun nuna alamun an sha kuka. A take jikinta ya soma rawa. A take taji gwiwoyinta sun saki ba za su iya Waukar nauyinta ba. Bata san jikinta ?asa yake yi yana neman wajen zubewa ba sai da Hajiya ta rungumeta a jikinta.

Da kuka Hajiya tayi mata magana suna wannan yanayin.
"Hamdiyya na rasa me zan fara ce miki. Godiya zanyi ko ha?uri zan baki?"

"Hajiya ku faWa min abin da yake faruwa. Wallahi ji nake kamar zuciyata za ta buga don fargaba."

Jin haka sai Hajiya ta ja hannunta har gaban Inna ta haWa hannuwansu.

"Kai ta."

Gaba na matsananciyar faWuwa Inna ta ri?e Hamdi har ICU Win mata. Ta jikin gilas Win ?ofa Inna ta nuna mata gadon da Yaya take kwance.

"Wwwwaaaa..yyyyeee?"

Ta matse hannuwan Inna ba tare da ta sani ba tana kuka. Jikinta kuwa tamkar mazari yana ta rawa.

"Rage sautin muryarki kada ace mu bar wajen."

"Na rage. Nayi shiru...."

Hamdi ta soma faWi sai ta kasa ?arasawa. Wani abu ta lura dashi daga yanayin kwanciyar mara lafiyan duk da bata ganin fuskar. Ta saki hannun Inna ta sanya duka hannuwanta ta dafa gilas Win ta sake kara fuskarta da kyau. Realization hit her kamar an jefeta da dutse.

"Yaya?" Ta juya da sauri "Inna, Yaya ce a kwance?" Sai hawaye kamar famfo.

Inna ta gyaWa kai, itama wani sabon hawayen yana zubo mata.

Kokawa Hamdi ta fara yi da ?ofar Wakin sai dai ko gezau ta?i motsi. Inna tayi saurin ri?e mata hannuwa tana turjewa.

"Yaya ce Inna. Ku barni na shiga."

"Ba za su bari ba Hamdi. Zo mu je nayi miki bayani."

Hamdi ta?i tashi sai kuka kawai da take yi tana ro?onsu da su faWa mata gaskiyar halin da Yaya take ciki. Mubina ce ta tafi da niyyar kiran Taj suka haWu a hanya. Muryar Hamdi ya jiyo shi ne ya taho da sauri.

"Me ya same ta? Me aka yi mata take wannan kukan?"

Mubina ta haWiyi yawu. Ganin bata da niyyar faWa masa sai ya ?ara sauri ya zagaya ta inda suke.

Inna na ganinsa ta fara cewa "Taj kama min ita mu bar wurin nan kafin..."

Ri?e hannunta yayi zai janyeta duk da cewa hankalinsa yayi masifar tashi sai yaji ta turje. Maimakon ta bishi sai ta janyo shi jikin ?ofar ta nuna masa Yaya ta gilas Win da ake hangota. Da sanyin murya mai tsinka zuciya Hamdi tayi masa magana.

"Yaya ce. ICU aka rubuta kuma Yaya tana ciki. Ji nake duniyar ta tsaya min. Ka taimakeni..." ta juya tana kallon su Inna "ku taimaka min. Ku taimaka mata."

Ta sulale a ?asa a hankali tana ajiyar zuciya. Kukan ma ya Wauke mata. Taj kasa taSata yayi saboda maganganunta tamkar almara yaji su. A kiWime ya koma jikin gilas Win ya sake kallon wadda take kwance. Ya dawo ya ri?o hannayen Inna jikinsa yana tsuma

"Inna da gaske Yaya ce?"

Hannunsa da na Hamdi ta kama ta nufi hanyar lift. Su biyun a take suka nuna ba zasu fita ba.

"Zaman ku babu abin da zai ?ara musu. Addu'a suke bu?ata. Ku zo muje mu samu wuri nayi muku bayani."

Tana rufe bakinta Mal. Salisu mai shara ya iso wajen. Idanuwansa akan Hamdi suka tsaya. Inna ta lura da haka. Sai ta ce,

"?arta ce."

Mal. Salisu ya jinjina kai "wannan ne mijin nata Wan uwan Kamal?"

Inna ta gyaWa kai.

"To ku zo muje. Alhaji yayi magana da Dr. Hadifi ya sama muku inda zaku keSe ku yi magana."

A baya su ka bi Mal. Salisu har zuwa bakin wata ?ofa ta wani ?aramin Wakin taro. A nan suka tarar da Alhaji, su Hajiya da Yaya Hajiyayye, Yaya Kubra da Dr. Mubina. Hamdi bata san da yaya ta ?arasa shiga ciki ba. Ta dai ganta zaune a kusa da kujerar Alhaji. Kwantar da kai da murya yayi sosai babu isa da Wagawa wajen yi mata bayani.

"Dashen ?oda aka yiwa Kamal. Ciwo yayi masa tsanani..."

Hamdi bata tuna da wata surukuta ba ta katse masa hanzari a firgice tana kallonsa da dara-daran idanunta.
"Ta Yaya aka dasa masa?"

"Ki yi ha?uri Hamdi." Mama ta ce cikin kuka.

Tashin hankalin da ya sake bayyana a fuskar Hamdi har yafi na farko. Tana so tayi ihu, kuka ko ?orafi amma duka ta kasa. Zuciyarta ce kawai take harbawa fiye da ?a'ida. Taj du?ar da kai yayi ?asa don bai ma san me yake ji ba a lokacin.

Sai shiru ya mamaye wajen na ?an da?i?u sannan Hamdi ta iya samun damar yin magana da dashashiyar murya.

"Da izininta aka Wauka?"

Umma tayi gaggawar amsawa
"Sosai. Mu bamu ma san ita ce donor Win ba sai da aka yi."

A hankali Hamdi ta Waga kai ta kalli Alhaji. Yayi mata kwarjini amma dole tayi masa tambayar dake ranta.

"Alhaji don Allah ba tursasata aka yi ba?"

Raunin muryar Hamdi a yayin da take kwaWayin samun amsar da zata sassauta raWaWin zuciyarta ya shiga jikin kowa. Taj kam gabansa faWuwa yayi. Idan amsar bata yi daWi ba me zai ce da Hamdi?

"Baiwar Allah ni nafi cancanta ki yiwa wannan tambayar."

Kowa ya kalli Mal. Salisu. Cikin tausasan kalamai ya sanar dasu yadda komai ya kasance har aka yi aikin. Abu na ?arshe kuwa shi ne kunna musu audio Win Yaya. Kuka kuwa har su Inna da ba yanzu su ka fara ji ba. Ita dai Hamdi zuciyarta kusan tsayuwa tayi ma. Kukan kuma ya ?i zuwa balle ta sami salama.

"Idan kuna son sake tabbatarwa zan iya kai ku a nuna muku CCTV. Jiya sai da muka kalla tare da Dr. Hadifi wanda ya jagoranci aikin." Ya ?ar?are da cewa " Malama Khadija ita ta kawo kanta asibitin nan da ikon Allah."

"Ya Allah. Ya Allah Ka basu lafiya. Allah Yasa anyi aikin a sa'a." Hamdi ta shiga furtawa.

Mamaki ya turnu?e Alhaji da sauran mutanen. Ji wani irin tawakkali a tattare da ?aramar yarinya. Domin ta Wan sami sau?i ya sanar da ita tahowar Abba Habibu wanda bata da masaniya. Ko a lokacin da ya faWawa su Zee hanasu sanar da ita yayi. Ya san halinta. Bagarar da ita akan kada ta tsawaita tambaya zai fi wahalar da shi fiye da ?an uwanta.

Abin da kawai ta ce shi ne "Allah Ya kawo shi lafiya. Mungode."

Daga nan bata ?ara magana ba kuma bata yarda ta haWa ido da kowa ba. Bata so ainihin damuwarta ta bayyana. Cike take da fargabar me zai faru da Yaya. Me ya hanata farfaWowa? Idan gudan ?odar ta sami matsala yaya zata yi?

Hanyar banWaki ta tambayi Yaya Kubra ta nuna mata. Taj yayi saurin tashi zai bita sai Ahmad ya sha gabansa har ta fara nisa.

"Kuka zata je ta kuma yi" ya faWi yana ?o?arin kaucewa Ahmad Win dake tare duk hanyar da ya bi.

Tausayi Taj ya bashi sai dai a ganinsa Hamdi tana bu?atar Wan lokaci ita kaWai a wannan yanayin tunda babu kowa daga gidansu a kusa. A tausashe ya yi masa magana.

"Allow her Taj. Let her cry."

Taj ya girgiza kai "she needs me. Don Allah ka bari na bita."

"?an uwanka aka sakawa ?odar mahaifiyarta fa Taj. Kamal ya farfaWo amma ita tunda aka fito bata buWe ido ba. So kake tayi ta murmushin Wan uwanka zai tashi ko kuwa tayi kukan mamanta a gabanka? Give her that space ko na minti goma ne to sort her feelings please."

"Amma.." ya soma cewa cikin damuwa.

Alhaji ya Wora hannu a kafaWarsa sai yayi shiru ya juya yana kallonsa
"ka bi umarnin yayanka."

Ha?ura yayi ba don ya so ba.

***

A cikin banWakin, Hamdi ?ulle kanta tayi ta fashe da kuka mai matu?ar ban tausayi. Tana yi jikinta yana rawa. Idan Yaya bata tashi ba ina zata saka kanta? Me ta taSa yiwa iyayenta na kyautatawa da zata iya dogara dashi taji salama a bayan su? Wai ma wace magana suka yi ?arshe? Wane hali Abbansu zai shiga? Tambayoyi birjik a ?o?on kanta. Tayi kuka sosai har sai da taji kamar hawayen ya daina fitowa sannan ta buWe ?ofar ta fito.

A inda take tsaye daga bayanta ?ofofi ne na toilet guda takwas. Gabanta kuwa dogon sink ne da kawonan famfo da madubi. A gaban madubin ne taga wata mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login