Showing 81001 words to 84000 words out of 182745 words

Chapter 28 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

127

Salwa. Don duk abin da ake hankalinta bai bar kallon ?ofa ba.

"Gidan nan kowa nada kirki Firdaus. Da ina shigowa na haWu da wata ?ar uwar taku ma a bakin gate mu ka gaisa. Naga kamar ta tafi."

"Kai anya kuwa. Kowa na nan fa."

Ba don bata ri?e sunan ba ta ce "sunanta Salma ina jin."

"Salwa ko?" Sai kuma ta kalli matan dake zaune ta ce "Ina Anti Salwa ne? Sai yanzu na lura bata nan."

Cigiyarta aka fara yi ana kiran Anti Zahra ko ta san inda ta tafi saboda bata cewa kowa za ta fita ba. Ita dai jikinta sanyi ma ya yi. Dama tun a gida da ta rangaWa wannan uwar kwalliyar hankalinta bai kwanta ba.

"To ku kira ta mana. An duba banWakuna? Ko bacci ya Wauketa a wani Wakin?" Cewar Hajiya.

Hamdi ta tabbata ko ma mene ne babu hannun ?an gidan nan, duba da yadda su ka shiga ruWanin ina ta shiga. Firdaus ta ce musu ai Hamdi ta ce taga fitarta.

"Tambayata sunan wadda su ka gaisa a waje tayi shi ne na kula ita ce bata nan."

"Da shirin fita ki ka ganta?" Anti Zahra ta tambayi Hamdi.

Murmushi tayi don tambayar da take jira kenan dama.
"A'a, cewa tayi za ta je wajen shi..."

Yaya Hajiyayye ta ce "shi wa?"

"Ke kuma komai sai anyi miki gwari gwari ne? Taj take nufi ko Hamdiyya?" Yaya Zulaiha ta tambayeta.

Ta sake yin murmushi kawai. Kunyar inda take ba za ta sa ta bari Salwa ta sami biyan bu?ata ba. Tayi kaWan! A yadda tazo mata da raini da isa shi yasa za ta hana ruwa gudu matsawar da igiyar Taj a kanta. Ko sun rabu Salwa ta aure shi ba za ta ce ita ce sila har taji daWi ba.

"Ku kira min ita. Ko Kamal. Ta dawo ciki" Anti Zahra ta faWi hankalinta a tashe.

Yadda tayi yasa kowa kallonta da ayar tambaya. Sai ta wayance wai taga Salwan daga tafiya ta dawo ko abinci bata ci ba su ka fito. Nan kuwa tsoronta kada taje tayi abin da zai zubar musu da mutumci. Domin duk abin da Salwa za ta yi dole a danganta ta da Ahmad. Ita kuwa bata son abin da zai taSa mutumcin mijinta akan wata shirmen soyayyar da babu aji a ciki.

Kamal Win aka kira ya ce sun fita da ita da Taj amma ba jimawa za su dawo.

"Ya za ku fita da ita babu wanda ya sani?" Umma da ta kira wayar ta tambaye shi.

"Gamu nan Umma. Mun kusa gida ba in sha Allahu."

Sallah aka tafi yi. Wasu kuma suna ta aikin kwashe kwanuka. Masu aikin gidan dai za su aikatu da wanke wanke. Don ma ba da plate suke ci ba, haWawa ake yi.

Hamdi ta auro alwala ta tada sallarta a inda aka shimfiWa mata abin sallah.

Shigarta ta kamala ta burge Mama. Ta?i jinin lokacin sallah ya yiwa mata a waje su dinga aron mayafi ko hijabi saboda nasu bai dace da tsayuwa gaban Allah ba. A ganinta rashin daraja addini ne yake sa mata fita da suturar da ba za ta musu sallah ba. Su kansu sun san hakan bai dace da tarbiyya da ma Wa'a ga addini ba.

Da ta idar sake gaishe da Mama tayi bayan ita ma ta idar.

"Hamdiyya ina son mu yi magana. Matso kinji."

Gaban Hamdi ya Wan faWi. Ko faWa mata zata yi ta fara shirin zama bazawara?

"Ina fata kin san komai game da Taj yanzu da ala?arsa da mahaifinsa?"

"Na sani" ta amsa kai a ?asa.

Mama ta numfasa ta ce
"Kullum burinmu shi ne ?ila idan ya tashi aure su daidaita. Sai Allah Ya ?addara masa aurenki. Wannan ma ya ishi mai hankali tunani." Ta kamo hannunta ta ri?e "a halin yanzu mutumci da martabar mahaifinki da ta mijinki suna hannunki Hamdiyya. Hali da Wabi'ar da za ki nuna mana ita za ta tabbatar da Worewar rigimar Alhaji ko kashe gobarar da ta tashi babu gaira babu dalili."

Jin an taSo Abbanta ne yasa ?walla cika mata ido. Wani Sangare na zuciyarta yana ?ara tunatar da ita laifin mahaifinsu ne da su ke fuskantar wannan abu daga ita har shi. Yayinda wani Sangaren kuma yake kare Abba a matsayin an Adam ma'asumi wanda ya cancanci duniya tayi masa uzuri idan ya bayyana tubansa.

Da ?aramar murya ta ce "Me ya kamata na yi?"

"Na san ke yarinya ce amma tunda na ganki naji bani ds haufi akan zaSin da Allah Ya yiwa Taj." Mama ta faWi tana yi mata murmushi "Alhaji yana son mutane jajirtattu. In kin kula yaran gidan nan kowa baki gare shi. To ?uruciya su ke samun wannan ?warin gwiwa ta rashin gazawa daga gare shi. Saboda haka kada ki yarda ki zama sokuwa. Ko laifi aka yi miki yafi son ki gwada ?watarwa kanki ?anci. Sai abin yafi ?arfinki ya amince ki nemi wani. Abu na biyu kuma ki kasance a kodayaushe cikin nuna hali na kyakkyawar tarbiyya. Zan so ya gani kuma ya shaida cewa ?a?an Habibun da yake ganin ya kauce hanya ya sun cika ?a?a ta kowacce fuska. Na ?arshe kuma ki so mahaifinki da mijinki. Ki nuna masa ke kina ?aunarsu dasu da sana'ar da Allah bai haramta musu ba. Kina alfahari dasu kuma hakan bai rageki da zama ?ar da shi ko wani zai kasa ?auna a matsayin suruka ba."

A rayuwa akan ce wanin hanin daga Allah baiwa ne. Hamdi ta fahimci haka a yau. A shekaru irin nata ko ma fi wata ba za ta gane mene ne ainihin abin da Mama take so ba. Saboda duka maganar a Wan dun?ule take fita. Amma yau da gobe saboda tashi a gaban Abba yasa ta gane. Magana da iya zuba zance a wajen cikakken Wan daudu yana daga cikin alamomin da ake ganesu ma. Ya rage nasa ne nesa ba kusa ba da ya gane yana daga cikin abubuwan dake saurin saka a gane tsohuwar rayuwarsa.

A ta?aice Mama so take ita Hamdi ta saye zuciyar Alhaji da halaye masu kyau ta yadda zai gane Habibun da ya raina bai gaza ba wurin tarbiyyar ?a?ansa. Sannan sana'ar Taj bata cikin dalilan da mutum zai yi fushi da Wansa.

Godiya tayi mata da al?awarin kamantawa da yardar Allah.

"In kin kula gidan nan babu ?an ubanci tsakanin ?a?anmu. Duk da Alhaji ne ya Wora mu akan turbar zaman lafiya to amma fa akwai ?o?ari matu?a daga Hajiya. Daga cikin irin zaman ne alhakin kula da kuma tarbiyar ?a?a maza ta dawo hannuna. Ba don Allah Ya tsare ba da tuni a sanadiyar korar Taj komai ya rikice mana. Ni kaina ina Worawa kaina laifi domin kuwa ni na ?arfafa masa gwiwar girki. Fatana da raina da lafiyata in ga lokacin da Alhaji zai shigo da Taj ya dam?awa mahaifiyarsa."

Kowane gida akwai nasu kalar damuwar. Tana ganin kamar duk duniya sun fi kowa sai gashi gidan da tun shigowarta komai na jama'ar ciki yake burgeta su ma da nasu.

?akin Umma, Mama ta kaita. A nan ma babu kowa sai Umman ita kaWai zaune akan abin sallah. Suna shiga Mama ta fita ta barta. Umma ta Waga hannuwa tana addu'a, Hamdi sai ta Waga ita ma har Umma ta kammala ta ce Amin.

Umma ta zolayeta da cewa "Wato kin ji ina ro?a muku ?an bibbiyu sau biyu a shekara shi ne ki ke ta cewa amin ko?"

Kunya kamar ta nutse "Allah ban san ita kike yi ba."

"Janye Amin Win za ki yi?"

"Eh" Hamdi ta faWi da sauri, kunya duk ta ishe ta.

"Yanzu addu'ar tawa ce ba kya so?"

Sake daburcewa tayi ta ce "A'a ban janye ba. Yi ha?uri don Allah"

Umma tayi dariya sosai.
"Wasa nake miki kinji Hamdiyya. Zo ki zauna."

Ita ma kamar Mama da yi mata bayani akan gidansu babu Saraka ts fannin zamantakewa ta fara. Sai abin da ba a rasawa na zaman tare. Ko a cikin ?a?a tunda ba a raba siblings da ?an rigingimunsu. Amma dai duk inda aka je aka dawo su Win tsintsiya ne masu maWauri guda.

"Hamdiyya don Allah ki ri?e mijinki ri?on da Allah Ya umarci bayinSa kinji. Ki bawa maraWa kunya."

"In sha Allahu Umma."

"Na tambaye shi ya min rantsuwar ba taimako da rufin asiri kaWai ya so yiwa mahaifinki ba. Auren yake so kuma ke ya zaSa a matsayin abokiyar rayuwa. Saboda haka don Allah ki ji, ki ?i ji. Ki gani, ki ?i gani. Babu wata rayuwar auren da take Wari bisa Wari. Amma indai kun ri?e juna amana za a sami nutsuwa da rahamar da Allah Ya sanya a cikin aure."

Wani tunani ne ya Warsu a zuciyar Hamdi da Umma ta kaita Wakin Hajiya. Shin matan gidan nan sun san shirin da mijinsu yake yi a kanta na raba aurenta da Taj ne? Amsar a bakin Hajiyan ta samo ta ba tare da ta tambaya ba. Ita ma kamar ?an uwanta zancen da ta fara akan zaman lafiyar iyalinsu ne. Shekaru arba'in da Woriya suna gina ?a?ansu akan turba mai Sullewa. Ba za su taSa maraba da abin da zai kawo rabuwar kai tsakaninsu ba.

"Nayi imanin kin ji daga bakin mahaifinki cewa Alhaji ya bashi wata uku ya san yadda ya yi Taj ya sake ki. Haka ne?"

Taurin zuciya irin na Hamdi sai ta kasa kuka. Idanunta ne kawai su ka yi jazur kamar gauta. Ta gyaWa a hankali.

Hajiya ta dafa kafaWarta da kulawa "Inna ce kaWai cikinmu bata sani ba sai kuma ?an uwanku da shi Taj Win. Ko kin faWa masa?"

"A'a."

"Da kyau. Don Allah ki bar zancen a cikinki. Abin da nake so shi ne ki ginawa kanki matsugunin da babu wanda ya isa ya rabaki da shi. Kina ganin yadda ?an uwansa su ka karSeki hannu bibbiyu. Innarsa da danginta kuwa ..." ta kasa ?arasawa. Ha?i?a wannan karon akan Taj yayyen Inna da ?annenta da su ke duk maza sai Sarin kuWi suke yi.

Takanas babban wan ya turo matarsa ta sanar da Hajiya cewa su za su yi komai na bikin. Kayan gida da Inna ta ce za ta yiwa Hamdi duk an Wauke musu. Lefen da ?an uwansa ke haWawa kawai aka bar musu. Shi ma kuma akwai gudunmawa gagaruma daga garesu. Yadda Taj yake kyautatawa a gidansu da dangin babansa haka su ma can yake yi musu.

Ita dai Hamdi zuciyarta tsinkewa ta sake yi. Bata yi ?asa a gwiwa ba ta ce
"Hajiya maganar mahaifi ba abar wasa bace. Musamman shi da suke da wannan matsalar."

"Hamdiyya addu'a nake so ki yi. Ki ro?i Allah ki kuma yi taki bajintar saboda muddin Taj ya fara sakin aure a tsukin lokaci irin wannan wallahi sunansa zai Saci. Alhaji bai san wannan hukuncin duka gidan nan zai shafa ba. Za a ce da gaske tunda ubansa ya kore shi ba mutumin arzi?i bane. Sannan ina mai tabbatar miki Innarsa ba za ta zauna ba. Don wannan karon a shirye take. Dama can wa'adin zaman ne bai ?are ba amma da tabi ta ?an uwanta da ta daWe a gida."

"Subhanallahi" Hamdi ta faWi cike da tsoro.

"?warai kuwa. Idan Inna ta tafi kuma Mama...Haj. A'i da ki yi sallah a Wakinta ma tafiya za ta yi. Saboda kullum gani take laifinta ne Taj ya tashi da son girki." Ya dubi Hamdi da kyau "a yadda ki ka fuskanci gidan nan kina ganin ni da Umma za mu zauna? In kuma duka mu ka tafi yaya makomar shekarun da muka Sata muna gina ?a?anmu akan soyayyar juna da zumunci?"

Murya na rawa Hamdi ta ce "Hajiya aikin ya yi min nauyi."

"Ke fa mace ce. Kada ki bari na kuma jin wannan kalmar ta gazawa."

"Abbana...Yaya ma tana da lalura. Waye zai mutunta abin da zan yi?"

"Ubangijin da Ya tayar dake a cikin zuri'arsu, Ya kuma kawoki cikin tamu, Shi zai dafa miki."

"To amma ta yaya zan yi abin da aka yi shekaru ba a samu ba?" Har a lokacin zuciyarta ta kasa ganin me su ke so ta?amaimai.

"Mace na juya miji Hamdiyya. Mu dai namu ina jin a kan shi aka ?are kafiya da taurin kai" Hajiya ta faWi tana dariya. Hamdi ma murmushi tayi.

"Duk ya bi ya Sata mana yara da halin. Sai dai kawai na wani yafi na wani. Tunda Taj ya hana shigo masa gida ba iyalin Taj ba ina ganin yau da gobe yana ganinki da kyawawan halayenki zai gane Wansa da baban naki da yake ?i basu ragu da komai ba akan sana'arsu. Allah Yasa kin fahimceni."

"Na gane Hajiya. Amma..."

"Za ki iya Hamdiyya. Wallahi ina jiye mana ranar da Abu za ta botsare a gidan nan. Mai ha?uri bai iya fushi ba. Komai na zaman lafiyarmu zai tashi a banza. ?a?a ashirin da takwas idan kansu ya rabu yaya zamu yi?"

Yau dai bata sani ba kuka ya kamata tayi ko dariya. Duk inda ta shiga magana Waya su ke yi mata. Ina ita ina Waukar wannan nauyin? Alhajin da ya raina mahaifinta bata jin za ta taSa yi masa abin da zai burge shi har ya yafewa wani.

Hajiya tashi tayi ta ce mata su je Wakin Inna. Sun sameta da yawancin ?an matan jikokin nasu. Zolayarta su ke son rai tana biye musu.

"Ku zo ku fita." Hajiya ta nuna musu ?ofa. Babu wadda tayi gardama sai Hayat Win Ahmad da ya dage ba zai fita ba.

"?yale shi Hajiya" Inna ta kalli Hamdi tayi murmushi "iyayenki na san duka sun gama yi miki nasiha. Nawa kawai tuni ne akan ki ri?e maganganunsu domin su ne iyayen Taj. Sai Amma dake Abuja. Ya taSa haWaku kuwa?"

"A'a" Hamdi ta bata amsa

"Ai ta ce tana tafe jibi. Ita ma ba za ta bari su yi haWuwar wajen biki ba tunda an riga an Waura." Ta nunawa Hamdi kujera "Zauna ba a rasa abin faWa miki ba. Sai dai in kuma kara ce ba za ki yiwa Mama ba." Cewar Hajiya ga Inna.

Bayan ta fita Hamdi taji kunyar da tafi ta sauran Wakunan. Innar Taj tana da wani irin kwarjini da cika ido.

"Kina da zaSin kalar kayan Wakin da ki ke so?"

Tambayar a bazata ta zo mata. Ta Waga kai daga sunkuyon da tayi.

"A'a."

"Taso ki gani" Inna ta nuna mata waje kusa da ita akan makeken gadonta da tun shigowar Hamdi take santinsa a zuciyarta.

Kasa tashi tayi sai da Inna ta maimaita maganar tare da umarnin lallai ta taso. A Wofane ta zauna. Inna ta buWe catalogue ta Wora mata a cinya.

"BuWe ki zaSi wanda ya yi miki. Sai kuma ki zaSarwa mijinki."

Yawu ta haWiya. Jikinta har wani rawa yake tana jin sanyi sanyi na ratsa ?asusuwanta. Wannan fa ita ta haifi Taj. Da Yaya za ta ga zaman da tayi kusa da ita irin wannan ?arshenta sai ta Sallata.

"Hamdi"

Ita kaWai ta kirata da sunan da ake kiranta a gida. Wannan yasa taji ranta ya an sake.

Inna ta cigaba da magana "kin shiga Wakuna uku na surukai. Nan kuma Wakin na mamanki ne. Don Allah ki Waukeni a matsayinta domin hakan ne kaWai zai bani damar yi miki ri?on ?ar cikina."

Cikin rashin jindaWi Hamdi ta ce "Ki yi ha?uri."

"Ba fushi nayi ba. So nake ki ajiye komai ki saurareni da kyau."

Hamdi ta mi?a mata hankalinta kacokan. Inna ta fara da yiwa Abba da Yaya addu'a da su ka haifi matar da ta auri Taj. Saboda ta jima tana tsoron kada aurensa ya tashi iyayen ?ar su fasa saboda korarsa da mahaifins ya yi. Abu na biyu kuwa fito mata tayi a mutum. So take Hamdi ta amsa sunanta na matar Taj ba tare da taji War a zuciyarta ba.

"Indai mijinki ne to ki manta da matsayinsa ki kama abinki a hannu. Na san komai da ?an uwana su ke Soyewa game da sharaWin da Alhaji ya bawa mahaifinki. Ni kuma in Allah Yaso Ya yarda kin shigo kenan. Allah ba zai bawa kowa damar ganin ?arshen auren ba ballantana su cigaba da Wora zarginsu. Hatta ?an uwanki ina yi musu fatan samun nasarar zaman gidajensu. Abu ?an?ani ne zai faru a Worawa babanku laifi. Idan kuwa ta Sangarenki ne to da uba da miji duka a kunnuwanki za ki ji ana cin zarafinsu."

Darasi mai girma Inna ta Wora mata, saSanin su Hajiya da aikin da su ka bata ne mai girman. Akan shekarunta taji kamar an ?ara mata ashirin saboda yadda take ganin ba za ta iya ba. Amma kuma ta sami ?warin gwiwa sosai.

"Taj yana son ki. Ki sa ya ?ara ?aunarki Hamdi. Ki hana zuciyarsa sakat ta yadda aurenku ba zai sami tangarWa daga yinsa ba don Allah."

Bayan ta gama Waukar karatun mai girma sannan Inna ta kira Firdaus ta ce su koma falo. A can aka cigaba da hira wadda ita dai amsarta bata wuce murmushi sai eh ko a'a. Tunanin da aka barta dashi yafi ?arfinta. Abu guda ta fahimta shi ne matan gidan duka basa son auren nan ya mutu. Gashi Abbanta ya tsorata da barazanar Alhaji yana ta yi mata tuni.

Cikin dabara aka sa Firdaus ta tambayeta size Win da ta?i turawa Taj. Da ?yar ita ma Win ta sanar da ita. Sannan cikin ?anen Taj wata ta aunata gwajin riga da siket da na doguwar riga. Sai gashi kafin magrib ta soma sakewa dasu. Na?asun da aka samu bai wuce na rashin shigowar Kamal ko Salwa ba. Sannan ko sau Waya Taj bai kirata ba. Ta sha?a tayi fam tana jiran ya tsikareta ta fashe.

Ita ma Anti Zahra har fargabar zuwan Ahmad Waukarsu take yi. Ta san shi sarai. Laifinta zai fara gani kafin ya saukewa ?anwar tasa kwandon masifa.

***

Ikon Allah Taj da Kamal su ka gani yayinda Salwa ta soma kuka tun a bakin gate wai Taj yana wula?anta ta. Aka yi ta rarrashinta ta?i shiru saboda makirci. A dole Kamal ya ce ta shiga motar. Shi ne su ka tafi Happy Taj. Office Win Kamal dake cikin boutique Winsa su ka shiga. Ta sami wuri ta zauna tana goge ?walla.

"Salwa tunda ku ke da Taj ya taSa cewa yana son ki?"

Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta. Taj yaji a duniya yanzu babu abin da ya tsana kamar mace ta dinga wasa da yatsunta. Tsaki ya ja ta dubi Kamal.

"Kana ganin abin da yake yi min? Meye laifina don na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login