Showing 90001 words to 93000 words out of 182745 words

Chapter 31 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

105

zuwan Yaya Kubra. Wannan yasa da ta shiga office Win ta ce ,

"Allah Yasa ban Sata miki lokaci ba. Naga kamar jirana kike."

"Na san yanayin aikin. Ina da niyyar jira har zuwa dare ko za ki zo." Ita ce amsar da bata sannan su ka gaisa.

Yaya Kubra ta Wora ledar kwalin maganin akan tebur tana fuskantarta.

"Na sami sa?onki. Amma mene ne dalilinki na breaking doctor-patient confidentiality? Laifi ne babba kin sani."

Murmushi Mubina tayi "domin mu ceci Kamal kamar yadda ki ke tunani. Sannan ban karya doka ba. Magungunan ba a same su a nan ba shi ne nayi masa order daga India. Da su ka iso ni bana nan ina wajen conference a Ghana. Za ki iya duba date Win. Na kira shi bana samu. Kuma ban san numbar kowa nasa ba, sai sunanki da na asibitinki. Shi yasa na tura."

"Kema kin san dai ba zan yarda da wannan zancen ba."

Mubina ta dage ta?i bari fuskarta ta nuna ta san bata kyauta ba. Dags ?arshe dai ta ce,

"Tura miki kawai nayi. Ban san za ki buWe ba."

Dariya Yaya Kubra tayi. Da alama babu yadda za ayi ta kama wannan matashiyar likitar da laifi.

"Ki yi min bayanin ciwon Kamal baki da baki ba abin da nake zargi daga magani ba."

"?oda ce. Duka biyun. Idan ciwon ya sake tashi sai dai mu fara dialysis. Shekara guda kenan yana fama. Kusan duk wani magani da na sani mun gwada. Amma they are barely functioning." Mubina ta faWi da rawar murya.

Jikinta har yafi na Mubina rawa Yaya Kubra ta ce "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Doctor kun taSa shawarta yi masa transplant?"

"A nan matsalar take. Ya ce min shi kaWai ne mai rhesus negative blood group a gidan. Dalilin da yasa ya?i sanar da kowa kenan."

"Wannan ai ba dalili bane. Ya ma aka yi shi kaWai yake da negative? Wane blood group ne?"

Yaya Kubra tayi maganar cikin hawayen da bata san ya sauko ba. Ita da ta zo da niyyar jin ko kidney stone ko wani infection. Bata zata abin ya kai haka ba. Kamal, Happiness Winsu da ciwon ?oda wadda take gab da daina aiki gabaWaya.

Kukan da ita Mubina tayi a lokacin da ta hanga taga kamar mafita ta ?arewa masoyinta, shi yayarsa take yi.

Abin da yake faruwa babba ne. ?oda ba abar sayarwa bace. Sannan ko a cikin gidan su mutum ba fa kowa ne zai iya yarda a cire tasa a bawa wani ba. Duk da tana da ya?inin da wuya aje da maganar gida ba a sami kaso fiye da saba'in a shirye da su bayar ba. A ina za su sami ?oda? A dangi?...abin da kamar wuya. Sannan zancen cigiya ma bai taso ba. Hukumomin tsaro da na lafiya basu yarda wani ya saka kuWi ya sayi wani Sangare na jiki ba. Faruwar haka zai sa mutane su dinga sayar da organs Winsu da zarar sun shiga matsala da ma abubuwa daban daban marasa daWi da za su iya biyo baya.

"Ki kwantar da hankalinki mu yi magana doctor."

A gigice Yaya Kubra ta ce "ta ina hankalina zai kwanta? Iyayenmu duka na tabbata jininsu positive ne. A ina ya sami negative don Allah?"

Bayanin wannan ruWani Mubina tayi mata kamar ba likita ba don hankalinta na neman gushewa. Da gaske likitoci kamar kowa in lalura ta waji nasu ce su ma ba sa ji, basa gani. Group Win jini daban kamar yadda ta sani guda huWu. A, B, AB da O. Sannan yana Wauke da wani sinadari da ake kira rhesus. Idan akwai sai wannan blood group Win ya zama positive (+), idan kuma babu sai ace negative (-). Abin mamakin shi ne da group Win jinin da rhesus Win duka a wajen iyaye ake gada. Uwa za ta iya zama A+, uba kuma O-, sai su haifi Wa O+. Ya gaji group a wajen uba, rhesus a wajen uwa. Wannan shi ne normal. To a case Win Kamal an wayi gari shi kaWai ne yake Wauke da jini rhesus negative. Wannan yana nufin Waya daga cikin iyayensa yana Wauke da alamun rhesus negative Win a Soye. Tunda kowanne abu na jikin Wan Adam ana samu daga uwa da uba a tare, wanda yafi ?arfi ya nuna kansa (domimant gene). ?ayan kuma ya zama a Soye (recessive gene). To wannan Soyayyen zai iya bayyana a jikin ?a?an da za su haifa a matsayin mai ?arfi. A ta?aice dai Waya daga cikin iyayen Alhaji ko Hajiya suna Wauke da rhesus negative gene. (Batul ba likita bace. Wannan bayani na samu shi ne bisa bincike da nayi. Idan yaci ?aro da ?a'idar likitanci don Allah ayi min uzuri. Littafin fiction ne dama.)

"Allah Sarki Kamal. Nagode Doctor. In sha Allah zan yi cigiya a family Win Hajiya. Don da ace daga Sangaren Alhaji ne tabbas Kamal ba zai kasance shi kaWai ne mai wannan blood group Win ba."

"Cigiya kuma? Doctor Kubra please ki duba abin a matsayin likita. Anya ya kamata ki fara bin dangi kina neman mai bashi ?oda?"

"Zuba ido zan yi ciwo ya cinye shi? Me yasa ki ka faWa min in ba don haka ba?"

"Saboda mu nemi mafita amma ba da garaje ba. Cigiya zata iya zama laifi a shari'ance. Musamman idan mai bayarwar ya nemi a biya shi."

Duk ta inda Yaya Kubra ta Sullo sai Mubina tayi mata nuni da illar hakan. Iyayensa ya kamata su sani. Shi kuma Kamal ya?i amincewa saboda a ganinsa tayar musu da hankali zai yi. Ga ciwo, ga kuWi amma babu mai iya taimakawa. Damuwar da za su shiga sai ta ninka ciwon nasa.

"Da na sani Taj na faWawa." Mubina ta ce da taga Yaya Kubra ta manta da dokokin aikin nasu. Yadda zai sami lafiya kawai take nema.

"Rufa mana asiri. Gara kowa yaji akan Taj. Ina miki rantsuwa da sai yafi Kamal jinya. Those two are like one soul in two bodies."

Da ?yar Mubina ta sami kan Yaya Kubra. Sun tsayar da magana akan cewa za ta zo ranar next appointnent Winsa. Daga nan sai su san abin yi kuma.

***

Yadda Mami ta so ko ana muzuru ana shaho haka Alh. Mukhtar maigidanta kuma uba ga Salwa yake yi. Ta zauna ta kalallame shi da ?arya da gaskiya aka son da Salwa take yiwa Taj.

"Mu ne da alhakin sama mata farincikinta. Idan ba haka ba Allah muna gab da rasata."

"Ni uban mace ki ke so in kira tsohon mijinki in ro?i ya sa Wansa auren ?ata? Da hankalina fa."

?aure fuska tayi "to sai ka barta ciwon so ya kasheta ai."

"Ki gaggauta kiranta ta dawo gida kafin ranta ya Saci wallahi." Har wani haki yake don Sacin rai. Rainin hankalin Mami ya yi yawa.

Juyawa ya yi zai fita tayi saurin jefa layarta ta biyan bu?ata a baki ta tauna. Kamar an tsayar da ?afafunsa ya tsaya cak.

"Nace ka kira Alh. Hayatu ka san yadda za ka yi dashi ya amince a aurawa Wansa Taj Salwa." Ta faWi da izza.

"To. Yanzu ko yaushe?"

"Zauna ka kira yanzu."

Zaman ya yi ya Wauko waya. Ta mi?a masa wayarta mai Wauke da numbar Alh. Hayatu ya kwafa ya yi dialing.

"Assalamu alaikum"

Ta jiyo muryar tsohon masoyinta abin begenta har yau. Sake tauna layar tayi ta zarewa Alh. Mukhtar idanu. Jiki na rawa ya amsa sallamar tare da gabatar da kansa.
RAYUWA DA GI?I 24




Batul Mamman=ؖ?







Lallai Alh. Mukhtar Winnan ya gamu da sharrin Mami shi ne abin da Alhaji ya fara rayawa a ransa bayan sun gama waya. Yadda ya dinga koro bayani akan irin son da ?arsa take yiwa Taj da fatan amincewar Alhajin don ayi aurensu kai ka san kan ba ?alau ba. Shi dai yana son ?a?ansa, amma fa yana ganin babu ?ar da ta isa ta saka shi zubar da mutumci haka a gaban tsohon mijin matarsa. Irin waWannan abubuwan ya fara gani da burinta na fin kowacce mace matsayi ta kowacce hanya yasa shi sakinta. Yana da labarin yadda matan Alh. Mukhtar biyu su ka fita bayan an aurota. Kuma duk wadda ya ?aro bata jimawa za ta yi waje ita ma.

Zama ya gyara da ya tuna yadda ya ce masa ya amince kai tsaye. Fakewa zai yi da guzuma ya harbi karsana. Ya san a taurin kai irin na Taj akan ya auri Salwa ya faranta masa gara ya saki Hamdi. Ana yin sakin da kansa zai ce masa ya janye batun auren. Duk da a iya saninsa Salwa yarinya ce mai saukin hali. Babu mamaki sirrin zuciyarta ta sanar da Mamin ita kuma tayi amfani da raunin ?ar ta Worata akan hanya mara Sullewa irin wannan. Tsigar jikinsa har wanu tashi tayi da ya yi addu'ar Allah Ya tsare shi surukuta da Mami da lusarin mijinta kamar yadda ya la?aba masa suna.

Bai ga alamun Habibu Simagade zai iya wani kataSus wurin raba yaran ba. Yanzu da ya sami dama shine zai yi amfani da ita. ?ansa yake muradi ya dawo gida. Amma ba tare da iri ko jinin Wan daudu a tare dashi ba. Saboda rashin son ganin Hamdi ranar da aka ce za ta zo gidan zamansa ya yi a kasuwa har ?arfe tara. Shi ba abin ya ce kada ta zo ba matan gidan su soma tijara. Ya fahimci yanzu kamar ma jira suke ya ce kule su ce masa cass.

Ahmad ya nema da yazo gida yana son ganinsa da daddare. Bayan ya taso daga office kai tsaye can ya wuce. Alhaji ya keSe dashi yana tambayarsa ala?ar Taj da Salwa tunda duka a gidansa su ke.

Tsoro ne ya bayyana a fuskar Ahmad.
"Alhaji wata maganar ka ji?"

"Ya zan yi maka tambaya ka amsa min da tambaya?"

Da sauri ya bashi ha?uri tare da amsa tambayar da ya yi masa.
"Babu komai a tsakaninsu amma kuma ba faWa su ke yi ba. Shi Taj ma bai fiye zaman gida ba ai saboda kullum su ke buWewa."

"Babanta, Alh. Mukhtar sunansa ko?" Alhaji ya faWi da irin rashin damuwar nan.

Ahmad baya jindaWin yadda ake magana akan Salwa yanzu. Rannan ?an uwansa ne su ka yi ana ta dariya. Yau kuma Alhaji ke tambayar sunan babanta kamar wani abin gudu.

"Sunansa kenan."

"Ya kirani yana ro?on na amince Taj ya aureta."

Maganar ta dake shi sosai "Ro?o kuma Alhaji?"

"Ro?o mana. Ya tabbatar min ita take son sa. Kaima yanzu ka ce babu komai tsakaninsu. To me zai sa ita babar taku ta amince harma mijinta ya kirani?"

"Zan yi mata magana Alhaji." Ya girgiza kai "Gobe in sha Allah zan ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????mayar da ita Bauchin. Idan ma mijin ne su sama mata a can." Tashi ya yi zai tafi. Alhaji ya ce ya dawo.

"Babu daWi mutum ya nemeka akan wata alfarma ka nuna masa baka so. Saboda haka na faWa masa na amince. Sa?on da nake son baka shi ne ka sanar dasu cewa bana so komai ya wuce wata Waya indai da gaske su ke."

Yana magana ne yana kallon yanayin Ahmad. A ransa kuma yana addu'ar Allah Yasa Wan nasa ya yafe masa. Da gangan yake maganar a haka saboda yana so idan Ahmad ya tashi kai sa?on ya nuna musu shi fa bai Wauki maganar da mahimmanci ba. Sannan baya Wokin haWa zuri'a da ?arsu. Ya sami wannan canjin ra'ayin ne bayan wani nazari da ya yi. A matsayinsa na uba sai hankalinsa bai kwanta da ya yi amfani da ?ar wani domin biyan bu?atarsa ba. Idan komai ya tafi yadda yake so ya dawo ya ce da Taj kada ya auri Salwa me kenan ya yi? Shi mai ?a?a da jikoki mata ya dace ya tozarta ?ar wani haka? Gashi saboda sanin halin babarta ya tabbatar idan ya yi sake ta auri Taj sai sun mayar masa Wa abin wasan yara.

Ba a raba hanta da jini. Hakan da yake yi ya san duka Ahmad zai faWawa Mami. Kuma tunda yaro ne hankali zai yi ?o?arin nusar da ita illar bari a yiwa ?arta irin wannan auren. Da bakinsa ne dai akwai nauyi bayan ya aminci Wazu ya dawo ya ce ya fasa. Abin zai zama cin fuska sosai. Fatansa yanzu dai Allah Yasa iyayen suna da hankalin gane manufarsa.

Da wannan damuwar Anti Zahra ta tarbi Ahmad. Juyin duniya tayi ta tambayarsa amma ya?i faWa mata abin da yake faruwa. Abinci ma kasa ci ya yi saboda ba?incikin yadda Salwa take zubar da darajarta ta ?a mace. Gashi yanzu ta sa iyayenta biye mata. Don ma su Hajiya akwai kawaici. Babu mai zancen Mami a gidan ko a aibata ta. Amma yanzu da sun ji maganar auren nan babu abin da zai hanasu fitowa ?iri?iri su ?i.

Salwan ya kira tana Waki tana chatting da Ummi. Cikin sigar wayon da Alh. Usaini ya koya mata take ta jan Salwa tana dukan cikinta. Rai bai so ba ta katse hirar ta fita wajen Ahmad. ?akinsa ya kirata ba ma falo ba.

"Kun yi maganar Taj ne da Mami?"

"Eh" ta amsa masa babu wannan girmamawar da ya santa da ita.

Yadda su ka yi da Alhaji ya faWa mata. Babu kunya ta kama murmushi. Baki har kunne.

"Da ni ne ke Salwa da na ha?ura da mutumin da bai damu dani ba. Wane irin aure za ku yi yanzu? Shi baya so kuma na tabbata da wahala ?an gidanmu su so."

"Ai ba da su zan zauna ba." Ta ce da tsiwar da bai santa da ita ba. Wai duk so ne ya canjata ko kuwa dama can halinta ne da bai sani ba?

"Shikenan. Zan kira Mami na faWa mata. Duk abin da ya biyo baya kada ki ce ban yi warning Win ki ba."

Da ?un?uni ta tashi tana cewa "alkhairi zan gani."

Daina bashi mamaki tayi. Ya ce mata ta haWa kayanta gobe za ta koma gida. ?arfe tara za su kama hanya. Tana fita ya kira Mami ta rangaWa uwar shewa. Mantawa tayi da wa take magana ta ce,

"In ya san wata ai bai san wata ba. Har ni zai wula?antawa ?a saboda yaci sa'a tana son shi?"

"Mami ana dole ne? Aurensa duka-duka sati ne fa da ?an kwanaki. Ni dai da za ku Wauki shawarata da kin ce mata ta ha?ura."

Da faWa Mami ta ce "to mai halin ubansa. Wanda baya kishina da na ?a?ana. Idan ta ha?ura kai za ka aureta?"

"Allah Ya baki ha?uri." Kawai ya ce.

"Amin. Kuma ka tanadi abin da za ka bani don a wata guda ko babanta ba zai iya haWa abin da ya dace ba."

Allah Ya sani bashi da irin kuWin da ya san idan ya bata ba za ta raina ba a yanzu. Sabon wata ne kuma farkon term an koma makaranta. ?a Waya amma Wawainiyar karatu sai dai kawai a dinga yiwa iyaye addu'a. A bisa tsarin gidansu kuma tunda su ka soma kawo ?arfi sun Waukewa Alhaji abubuwa da dama. Ba kuma don bashi da kuWin ba. Ko a danginsa babu kamar shi har yanzu. Suna yi ne don neman albarka. Kayan abinci, kayan bu?ata na gida irin su sabulu da kuWin kashewa ga iyayensu. Duk masu aiki da masu kasuwanci suna contributing. A matsayinsa na babban namiji duk da cikin matan akwai waWanda samunsu yafi nashi, amma yana ?o?arin ganin ya yi bajinta. A haka kuma yake bawa Mamin dubu talatin duk wata.

"Kai, Ahmad. Baka ce komai ba."

Ya ma manta waya yake.
"Allah Ya hore. Sai da safe."

Ko minti goma basu yi da gama wayar ba ta sake kira. Ya san zancen ba zai wuce na kada ya dawo da Salwa ba. Shi yasa ya?i Wauka. Zai kaita gida gobe in sha Allahu.

?arfe bakwai da rabi Anti Zahra ta same shi a Waki wai Salwa ta fita.

"Bangane ba. Ina ta tafi?"

"Ina ta tambayarta tana kuka. Da alama bata son tafiyar. Da ka ?yaleta."

A harzu?e ya tashi yana ta faWa. Sai a lokacin Anti Zahra taji me yake faruwa. Ta ma kasa comprehending wannan al'amari.

"Don Allah kayi shiru kada Taj ya ji. Kwanansa biyu yana fama da zazzaSin nan mai zafi. Sannan ko babu komai ka haWa uwa da ita. Mutumcinta abin karewa ne a wajenka komai rashin daWin da abin ya yi maka."

"Gidan wa zata da safiyar nan? Idan tana tunanin zan bita ne wallahi tayi kuskure."

"Naji. Ka san ba za ta wuce gidan ?anwar babanta ba ta Sheka. In ba nan ba kuma ?ila ta wuce Bauchin."

"Ita ta sani."

Sai dare ya Wauki wayar Mami. Ta ?are masa tanadi kuwa. Shi kuma ya tsaya akan bakansa na cewa indai Salwa ta dawo gidansa to Bauchi zai maidota. Ba zai zauna da mara kunyar da bai isa ya faWa mata taji ba. Mami da taga ya?i tan?waruwa ta ha?ura.

"Shegen yaro mai halin ubansa."

***

A kwana biyun nan kullum Hamdi sai ta kira Taj. ZazzaSi ne irin wanda ya kan zo gama gari mai shiga gida gida. Ita kanta tana mamakin yadda ta damu da ciwon nasa da kuma rashin ganinsa. Da Zee ta tsegumtawa Sajida halin da take ciki haWuwa su ka yi suna tsokanarta.

Zee ta ce "Salman Khan ya sallame zuciyar Hamdi."

Ita kuma Sajida tana dariya ta tuna mata tsohon ?udurinta.

"Ta dai gama cika bakin bata son namiji mai girki. Yanzu gashi nan mai gidan abinci ya hanata sukuni."

Da yake a wayar Zee ake ta bidirin, gajiya tayi da kare kanta ta tsuke bakin nan.
"Aljannar mace dai tana ?ar?ashin ?afar mijinta. In kuma kuna ba?incikin kada na samu ne sai in ji."

Sajida da Zee me za su yi kuwa banda dariya. Ashe rana irin wannan za ta zo musu a kurkusa haka basu sani ba.

?yalesu tayi ta koma kitchen wajen girkinta. Tana aiki tana tunaninsa. Yau ce rana ta uku tun zuwan da ya yi ta kira masa Kamal. Wayar ma idan sun yi ba wani jimawa su ke ba. Gaisuwa ce da jin yaya jikin nasa. ?an wasan nan duk ya daina.

"Ke!"

A firgice ta kalli Yaya. Bata san tun yaushe take tsaye tana yi mata magana ba.

"Jikin nasa ne har yanzu?"

Wayancewa tayi kamar bata gane ba "wa?"

"Garinku in kin san shi. Wa ma za ki ce min?"

?asa ta kalla a kunyace. Fuskarta babu walwala. Yaya ta fahimci har yanzu a kwance yake.

"Jiya dama Abbanku yake zancen zuwa a dubo shi. Zan sake yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login