Showing 72001 words to 75000 words out of 182745 words

Chapter 25 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

84

Abin mamaki yana zama ya kira sunan Kamal sai yaji shiru. ?aga kansa ke da wuya yaga ashe bacci ne ya Wauke shi. Saurin bacci ba Wabi'ar Kamal bace. Kuma bai fi minti biyar da raka ?an uwansa waje ba don ya tabbatar sun tafi. Ya yi tsammanin zai dawo su yi hira ma tunda yaga kamar jikin da sau?i. Hankalinsa sai bai kwanta ba. Anya allergy ne kawai? To ko kuma allurar bacci aka yi masa? Shi kaWai ya dinga sa?e sa?e a ransa har Mubina ta shigo.

HaWuwar farko ta jinjinawa soyayyar dake tsakanin ?an uwan biyu. Lokacin Kamal ya tashi har Taj ya bashi labarin yadda su ka yi a Abuja. Ya Wora da mitar me yasa ya zama na ?arshen sanin bashi da lafiya. Cacar bakinsu su ka yi aka daidaita. Sai ga Kamal kamar ba shi ba. Jikinsa ma yayi ?wari sannan kumburin duk ya sauka.

"Zan sallameka amma akwai magunguna da zan sabunta maka. Don Allah kada kayi wasa dasu."

Tashi Taj ya yi ya ce "Idan akwai a pharmacy Winku ki bani na siyo kafin mu tafi."

"A'a ka barshi kawai" in ji Kamal

"Ba duka za a samu ba." Ita kuma ta ce da sauri.

Murmushi Taj ya yi, amma a zuciyarsa yaji rashin yarda dasu. Zargin nasa bai sami Worewa ba da yaga da gaske Mubina wata kulawa ta musamman take bawa Kamal. DaWi ya kama shi. Wannan karon da alama za a dace, Kamal zai daina gudun matan da yaga yana yi.

"Bari na baku wuri ku ?arasa maganan. Na san ba komai na patient ya kamata wasu su ji ba."

"Har akwai abin da ya shafeni wanda bai kamata kaji ba?" Kamal ya faWi yana Wauke kai daga hararar da Mubina take masa.

"In ta faWa ka sanar dani. Bari na duba ko Bishir ya zo."

Ficewa ya yi ya barsu. Mubina ta sami sakewar ?ara sanar dashi dokokin da ya kamata ya kiyaye.

"Me yasa ya fita?"

"Ya zata akwai wani abu tsakaninmu. Bai san ni yanzu soyayya ko sadakarta aka bani zan mayarwa mai ita ba."

Murmushin zuci kawai Mubina tayi. In zai Soyewa kowa ita ba zai yaudareta ba. Tana da saurin karantar mutane. Tun farkon zuwan Kamal asibitin ta fahimci ya kamu da sonta. Sai dai bayan ya gama faWa mata alamomin ciwonsa da aka yi gwaji ta sanar dashi lalurar shikenan komai nasa ya sauya. Soyayyar da take gani ?uru?uru ta koma ya?in neman lafiya. Da ya gane da wuya lafiyar ta samu sai ya zama mai mugun sadaukarwa ga duk wanda yake mu'amala dasu. Musamman wannan Wan uwan nasa Taj. A halin da ake ciki za ta cigaba da adana soyayyarta ta mayar da hankali wurin ganin ya sami lafiya. Bata son ta bari komai ya shiga tsakanin aikinta a kan samun sau?insa.

***

Bayan kwana biyu da sallamar Kamal ya wartsake har ya koma shagonsa. Sai lokacin Taj ya sami sukuni da nutsuwa a ransa. Kullum yana tunanin Hamdi amma damuwar Kamal ta ishe shi. DaWinsa Waya da ya koma gidan Ahmad Salwa ta tafi Bauchi. Hankalinsa kwance ya soma fafutukar neman gida don Inna ta faWa masa bikinsa ba zai Wauki lokaci ba. Yawancin fitar da Abba su ke yi ko Bishir. Bai fiye neman Kamal Win ba saboda yana ganin hutu ya kamace shi ba taya shi neman gida ba. A cikin kwanakin kullum yana waya da Abba. Abban ya so zuwa duba Kamal amma da ta tuna yadda su ka yi Alhaji sai ya ha?ura kawai ya kira shi. Yaya har fushi tayi. Ta nuna masa rashin dacewar hakan. Shi dai ha?uri ya bata da ?an dabarun wayo har ta daina zancen.

Yau alhamis ta kama kwana shida da Waurin aurensa. Ya sami sabon gida a sharaWa self-contain daidai me sabon aure. Mama ce ta bashi shawarar kada ya ce sai ?aton gida. Gara ya mayar da hankali wajen gina filin da su ka saya shi da Kamal shekara biyu da su ka wuce.

Shirye shiryen biki yana ta kankama. Iyayen basu saka rana ba sai sun ci ?arfin shirinsu. Masu haWa lefe su Yaya Hajiyayye kuma an taso Taj a gaba ya kawo size Win underwear Win Hamdi. Ya gama zille zillensa ta biyo shi har office a Happy Taj ta saka shi a gaba.

"Kirawota a gabana ka tambaya."

"Na ce miki fa zan tambaya yau Winnan na turo miki."

"Ai na gaji da gafara sa. Kai ko irin abinnan na angwaye da an Waura aure su fara damun amarya da fitina da alama baka iya ba"

Kunya kamar ya fice ya bar mata office Win.
"Haba Yaya Hajiyayye. Sai kace wani Wan is**. Kunyarki ma ta kama ni."

Dariya tayi sannan ta ce "Ka kira yanzu nima jirana ake yi in faWa."

Ido ya zaro "wa da wa za ki faWawa? Wannan ai tonon silili ne. Kowa sai ya san girmanta saboda Allah? Sirri ne fa." Ya yi kicin kicin da fuska.

Yaya Hajiyayye me zata yi kuwa banda dariya.
"Sirri manya. Ba dai naji ance weekend za ka kaiwa su Hajiya ita ba? Tana cire mayafi zan aunata tas da ido wallahi."

"Zan fasa kawota."

"Ka ma isa?"

"To umarnin zan bata kada ta yarda ta cire mayafi...kai, hijab ma za ta saka."

"Kayi ka gama. Telan da zai yi mata Winkunan biki ma ranar zai zo aunata." Ta ce tana kallon idanunsa.

"Tela kuma?" Ya ambata kamar yau ya fara jin kalmar "Dama har yanzu ana wannan jahilcin Yaya? Na zata yanzu mata ke auna kansu su bawa telan idan ma namiji ne."

Ganin ta same shi a hannu ta cigaba da kunna shi.

"?inkunan maza ai sun fi na mata kyau. Sun san duk wani lungu da sa?o da za su auna saboda shape ya fito."

Abu ya yi tsamari. Taj harda gumi don takaicin yadda idanunsa ke nuna masa Hamdi a gaban wani ?ato yana gwadata. Mantawa ya yi da girman yayar tasa ya ce,

"Wannan dai kafurci ne ?aWa'an. Kamar ba a zuwa islamiyya a garin nan?"

Ta gimtse dariyarta da ?yar "mu ne kafiran kuma yau Taj?"

"Allah Ya baki ha?uri" ya ce yana kumbure kumbure.

Dariyar da take dannewa sai da ta fito. Tayi mai isarta ta ce to lallai a yau Winnan take so ya tura mata kafin ?anwarsu da ta tafi UK da mijinta ta dawo nan da kwana uku.

Tunda ta tafi yake tunanin yadda zai tambayi Hamdi. A ganinsa mai baki amma yana da kunya. Ga amaryar tasa ita ma gwanar tsiwa. ?arshenta daga tambaya ta fassara shi.

*

A unguwar tasu ya yi Isha tare da Abba. Ya jira shi ya sanar da Yaya zuwansa sannan ya shiga su ka gaisa.

"Kwana biyu mun tada kai tsaye. Naji kana ta yawon neman gida."

"Yiwa kai ne Yaya."

Abba ta kalla don bata daina fushin zuwa dubiya ba "Kamal bai yi fushi damu ba ko?"

Shi da ya san komai a bakin Zee ya riga ya fahimci Abba tsoron zuwa yake kada su haWu da Alhaji. Nuna mata ya yi babu komai tunda ba jimawa ya yi ba. Kwana Waya ne.

"Allah Ya ?ara masa lafiya." Ta tashi ta ce "Me za ka ci a Wora maka? Yau abincin ana magariba da kowa ya ci aka bayar saboda zafi. Abbanku kuma ya ce a ?oshe yake bamu ajiye masa ba."

Shi da ba wata surukuta yake yi da su ba sai cewa ya yi zai ci indomie. Abba ya mi?e saboda sabo zai tafi kitchen Win.

"Girkin matarsa zai ci. Don Allah zo ka tafi ka watsa ruwa ka huta."

"Au...haka ne fa" ya furta yana jin kamar ya faWawa Yaya gaskiya. Baya son su fara jindaWin kasancewa tare bayan ya san auren ba mai Worewa bane.

Dariya su ka bawa Taj. Yaya ta ce ya jira yanzu za ta turo Hamdi.

*

Tana jin takun Yaya ta gyara filo ta kwanta. Dama tunda taji muryarsa ta san sai an nemeta. Ba kuma son ganinsa take yi ba. Abubuwa uku ke damunta. Haushin abin da Alhajinsa ya yiwa mahaifinta da wa'adin da ya basu, sai kuma rashin nemanta da ya yi na tsayin kwanakin nan. Na ?arshe kuwa kewarsa ce da ta mantar da ita rashin son girkin da yake yi. Ranar da taji Kamal ne babu lafiya dai tayi masa uzuri amma sai ta?i kiransa ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? kira Kamal Win.

"Tashi kafin ranki ya Saci." Yaya ta kai mata duka a cinya. Ta tashi tana sosa wurin.

"Kina fa da zafin hannu Yaya."

"Wuce ki Wan gyara fuskarki ki je ki dafawa Taj indomie."

"Indomie kuma? Ba ya iya dafawa ba? Ya tafi gidansu mana." Ta turo baki.

Hannu Yaya ta kai za ta Walle bakin ta gudu.

"Bana son rashin Wa'a Hamdi. Kuma saura idan kin je ki kasa gaishe shi. Mara kunya kawai."

Yaya na fita tayi saurin cire kayanta ta saka riga da wando na bacci ta Wora hijabin da ya wuce gwiwarta kaWan. Fita ta zo yi Zee ta kama kiran Yaya.

"Zo kiga a yadda za ta fita."

Saurin rufe mata baki tayi "gulma dai haramun. Ina ruwanki?"

"Babu ruwana amma dai a matsayina na mai jin maganar iyaye zan so ?ar uwata ma tayi hakan."

Harara kawai ta gallawa Zee Win. Ta koma gaban Wan madubinsu ta fesa body spray sannan ta shafa hoda da man leSe. Dama niya tayi taje masa tana hamma ta ce bacci take ji.

"To uwar iya...haka yayi ko kuwa sai na cire hijabin?"

"Da yafi bada citta don wallahi har laSe sai nayi muku."

Hamdi ta tafa hannuwa "gulmawiya, shi yasa naga kin yi saving sunan Baballe da Sadiq a wayarki? Wato Wan zuwan nan da yake yawan yi har ya kwance miki hadda. Kin manta kukan bakya so Win da ki ke yi."

Zee taji kunya sosai. Sai ta cije don Hamdi ba za ta rabu da ita da wuri ba.

"So muke mu rigaku haihuwar da Ya Taj ya ce ku za ku fara yi."

"Na shiga uku. Zee zancen haihuwa yayi miki? Da wa zai haihun?"

Zee ta ?yal?yale da dariya "Hamdiyya Habib mana"

Tana faWin haka ta fice daga Wakin. Hamdi ta gama jimamin maganar ta fito da ?udurin fara cika umarnin Abba. Za ta cigaba da nunawa Taj bata son girki da ma wasu abubuwan da take jin za su taimaka wurin Sata masa rai.

*

Danna waya yake su na chatting da abokinsa Wakili da su ka yi karatu tare a Indiya ta shigo. Sallamar nan ciki-ciki da gaisuwar.

Taj ya yi kamar bai ji ba ya?i amsawa. Sai da ta shigo cikin falon ya Waga kai ya kalleta.

"A dinga sallama ?an mata."

Ta juya idanu "Ai nayi."

"Banji ba." Ya faWi lokaci guda ya shagala da kallonta. A garajen fitowarta hijabi ruwan madara ta saka mara kauri. Da kaWan ya wuce babu a jikinta. Rikita masa lissafi yaga tana neman yi ya wayance da cewa "ba za ki iya sallamar bane in tafi?"

Ta turo bakin nan "to Assalam alaikum."

"To wa alaikum salam."

"Guda nawa kake ci?"

"Me?"

"Indomie Win mana."

"Oh, ki kimanta." Ya gyara zama abinsa.

Tana son tambayarsa ko me da me za ta saka a ciki amma bata son yawaita yi masa magana. Fita tayi ya ajiye wayar da dama amfaninta rage masa kallon ?urillar da yake yi mata.

Ita kaWai ta kama tsaki da ta tuna yanzu ?ila fa duk yadda za ta dafa zai ji bata yi ba saboda sabo da girki. Yanke shawarar yinta normal kawai tayi. Ta Wauko attaruhu da albasa za tayi grating amma bata san gejin cin yajinsa ba. ?arshe dai guda biyu ta saka da ?aramar albasa. Ta raba jajjagen biyu sai taga kamar yayi yawa. KaWan ta saka ta dafa indomie Win dashi. Sai ta kuma soya wani da curry da Wan maggi cikin mai daidai suyar ?wai. Yana fara ?amshi ta juye ?wai uku da ta kaWa a kai. ?amshinsa har falo. Ta kawo cucumber ta yanka rabi a zagaye ta jera a gefen plate Win mai Wan zurfi kaWan ta tsakiya. Indomie Win tana ?arasawa da sauran ruwa mara yawa ta juye sannan ta rufe kanta da ?wan. Yadda bata son ci da sanyi shi yasa tayi gaggawar kai masa.

Tana ajiye tray Win ana Wauke wuta. Taj ya kunna torchlight Win wayarsa ya hasketa tayi saurin rufe ido.

"Hamdi da zuciya Waya kika dafa min dai ko?"

"Me ka gani?"

"Wuta aka Wauke. Kin san mu a India yanzun nan sai mu fassara abu."

Murmushi tayi don ta fara gano tsokanarta yake da zancen Indiyan nan.

"To Shah Rukh Khan. Da me ka fassara Wauke wutar?"

Taj ya haWiye abincin da ya kai bakinsa ya ce "Da lokacin wa?a cikin duhun dare mana. Muna bin bango muna rawa."

Toshe bakinta tayi ta kama dariya. Abin nasa azimun. Wai bin bango. Ganin ya tsura mata idanu amma bai fasa cin abincin ba shi ne ta ce.

"Bin bango kamar wasu ?adangaru."

"Kin ci sa'a yunwa nake ji da na tashi na gwada miki yadda ake yi."

"Bana ma son sani" ta zare wayar fitila daga inda aka jona chaji ta kunna. A take haske ya wadata a falon. Ta buWe fridge ta Wauko ruwan sanyi ta Wauko da kunun ayan da Yaya ta haWa da rana.

Ta kawo gabansa ta ajiye a gefen tray Win sannan taje ta kawo kofuna guda biyu ta dire masa. Kujerar nesa dashi taje ta zauna

"Nagode" ya ce bayan ya gama. Abincin kaWan ya rage.

Hamdi ta kalle shi da wutsiyar ido "banlbu daWi ko? Ba irin haka ka saba dafawa ba?"

"Ke dai ki ce kina son in yaba miki. To nayi. Yayi min daWi sosai."

Bata yarda dashi ba "duk iya girkinka?"

"Girkina daban, na matata Hamdiyya ma daban. Zan dinga taimaka miki a kitchen amma ba kullum ba. Ina son in dawo gida kamar kowane namiji in ci abincin da matar gidan ta dafa."

Yana lura da yadda maganarsa tayi mata daWi. Ba dai ta son nunawa ne. Shi kuwa indai tana da kunnuwa to ba zai fasa faWin maganganun da za su yi tasiri a zuciyarta ba. Tashi yayi ita ma ta mi?e.

"Bari na ?arasa gida na huta kuma."

Tray Win ta du?a ta Wauka ya ce "na faWawa Yaya ranar asabar zan zo mu je gidanmu."

"Gidanmu ko gidanku?" Ta ce a tsorace.

"Saurin me kike yi? Gidan iyayena ba gidana ni da ke da ?a?anmu ba"
Ya ?are maganar yana kashe mata ido.

"Sai da safe" tayi masa fuskar shanu. Hira dashi tana yi mata daWi amma biyewa zuciya ganganci ne.

"Oh, don Allah Wauko min underwear Winki na sama da na ?asa ana son ganin size."

Tray Win hannunta ta kusa saki da taji me ya ce. Bata ankara ba taji hannuwansa sun dam?i nata. A karo na biyu su ka ji wannan yanayin da ya bambanta da in sun taSa kowa. Zame nata hannun tayi ta bar masa tray Win.

Taj ya ce "yauwa yi sauri. Kuma don Allah wankakku."

Wata uwar harara da ta banka masa ba shiri ya ajiye tray Win a inda ta Wauka.

"Ai gaskiya ce. Naji an ce ?an mata maimaici su ke na sati biyu ko ma fi kafin su wanke."

Kamar za tayi kuka ta ce "Don sharri? To ba zan bayar ba. Idan ma bokanka ne yake so kace masa na hana. Ya turo aljanu su satar masa."

"Dare ne dai kuma babu wuta. Ki cigaba da kiraye kirayen abubuwa. In su ka zo..." ya faWi a hankali yadda zancen zai shigeta.

Ai kuwa bayanta ta kalla da sauri ta Wan matso kusa dashi. Tausayi ta bashi. Duk tayi wi?i wi?i da idanu.

"Yayata ce ta ce na tambayeki fa."

"Size ake tambaya ai. Ya za ka ce in baka?" Hamdi ta ce da mamakin irin nasa tunanin.

"Don kada ki faWa min ba daidai ba. Nafi son komai accurate."

"To ba zan bayar ba. Ka kamanta yadda ya dace." Ta Wora hannuwa a ?ugu.

Taj ya san bata da masaniyar shigar da tayi. Da bata yi wannan tsayuwar a gabansa ba.

"Don't dare me Hamdi. In ki ka yi wasa da hannuna zan kamanta."

Da sauri ta koma bakin ?ofar falon har tana tuntuSe saboda gigitar kalamansa.

"Matsoraciya."

"Naji."

"Za ki turo size Win ko in sa Zee ta Wauko min na tafi dasu?"

Zai aika ta sani yanzu. Tunda ya iya faWa mata zasu riga haihuwa ai komai ma is possible yanzu.

"Zan turo." Ta ce a hankali.

"Good girl. Sai jibin ko?"

Kada azo tafiya ya ce su biyu kaWai shi yasa ta ce masa da Zee za su je. Shi kuma ya ce a'a don yanzu matar aure ce. Sai ta ce to da Halifa.

"Haka kawai sai in Wauke ki da ?ato a mota?"

Hamdi ta Sata rai "Halifan ne ?ato?"

"Yanzu duk duniya daga Abba sai ni sai Alhajina ne kaWai normal maza a wajenki. Sauran kowa ?ato ne."

"Kaima ?aton ne kuwa."

"Mijin ?atuwa ba."

Dariya yake yi da yayi maganar. Sai gata tana murmushi. Fushi dashi ma da alama Sacin lokaci ne. Sai da safe ya yi mata ya tafi. Ta tattare kwanukan ta tafi kitchen tana wankewa hirarsu na dawo mata. Da ta gama gidan tsit yayi mata. Yau ko inji Halifa bai fito ya kunna ba da aka Wauke wuta. Bata san Yaya ce ta hana ba. Wai ?arar za ta dami Taj.

?aramin table Win da ta Wora masa tray taje Waukewa sai taga wayarsa. Ta Waga ta juyata a hannunta. Dole masu iphone su ke jin kansu. Wayar a hannu ma daban take. Abba ta yanke shawarar bawa da safe don da alama yau sun yi baccin wuri.

Kimanin rabin awa da tafiyarsa taga kira daga wani suna an sa Anti Zahra. Sai da aka kira na biyu sannan ta Wauka. Muryarsa taji ta saki ranta. Ya ce ta ajiye wayar zai zo ya karSa washegari.

"Zan bawa Abba ya taho maka da ita."

"To nagode. Goodnight."

*

Famfo iya famfo Mami ta yiwa Salwa. Tunda ta koma gida da ramar kwana biyu amma kamar tayi jinya hankalin Mamin ya tashi. Ta kira Ahmad ta ?are masa tanadi. Harda kiransa wanda baya kishinta.

"Aure kuma tunda tana so ko uban naku bai isa ya hana ba."

"Mami kin fi so ta kai kanta inda ba a sonta? A ?arshe ta dinga fuskantar wula?anci."

"Rufe min baki. Matan gidanku sun gama cinye maka zuciya baka iya taSuka komai. Arzi?in Taj kai kana da rabinsa ne?"

"Kowa rabonsa yake ci Mami. Don Allah ki daina biyewa Salwa."

Cikin faWa tayi masa tsawa "Salwa za ta dawo. Ina so ka yiwa Alhajin naku maganarta don na san yana ?aunarta. Ita wadda Taj Win ya aura na riga na samu bayani akanta. Bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login