Showing 84001 words to 87000 words out of 182745 words

Chapter 29 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

113

ce ina son shi? Ba fa cewa nayi ya saki yarinyar da ya aura ba."

"Ki dinga gyara kalamanki akan matata. Sannan kin fi kowa sanin cewa ba zan juyo ba. Ba yaudararki nayi ba so don't give me that crap wai in haWaku."

"HaWamu ma bai taso ba tunda Alhaji ya ce..."

"A wurin wa ki ka ji wannan maganar?" Ya tambayeta muryarsa a sama.

"A wurin Yaya mana." Ta bashi amsa tana tura baki.

Kallonsu Kamal ya yi don bai gane komai ba ya ce "wace magana ce Happy?"

A ta?aice Taj ya yi masa bayanin da bai yi ba saboda rashin lafiyarsa.

"Bana jin Yaya zai faWa mata." Kamal ya faWi yana kallonta "a ina ki ka ji?"

Rigimar da Mami ta ce ta haddasa tsakanin Taj da duk wanda zai goyi bayan ya?i aurenta ta tuna. Ta kuwa taSe baki cike da raini.

"Ina ruwanka? Kai dai burinka ba ya saki Hamdi ka aura ba?"

Duka su biyu zabura su ka yi cikin Sacin rai.

"Salwa!" Kamal ya yi mata tsawar da a tunaninta ba zai taSa iyawa ba saboda yafi Taj sanyin hali.
"Ki kiyayeni wallahi."

"Idan na?i fa? Ya Kamal na fa san kana son yarinyar nan. Ko ba abin da ya kwantar da kai ba kenan? Me yasa baka taSa yin wani ciwon allergy ba sai da Ya Taj ya aureta? Wallahi zan iya dafa izu sittin baka da wani allergy."

"Kinga Salwa, kalleni nan" Taj ya yi mata magana yana cijewa don ta riga ta kai shi matakin da yake son taSa lafiyarta. Wani abu da bai taSa yi ba ko da wasa.

Idanunta a bushe ta kalle shi. Bai san bata tunkari wannan rigimar ba sai da ta shirya mata daga gida.
"Ina jin ka"

"Zo ki tafi kafin wani cikinmu ya yi miki rauni."

"Please Taj kada ka biye mata. Ka bar zancen raunin nan kada wani ma yaji." Kamal ya yi maganar da kana gani za ka gane yadda yake ?o?arin danne Sacin ransa.

"Za ka aureni Ya Taj. Allah kuwa..."

Kawai ta sa kai ta fita. Bayan tafiyarta Kamal ya zo zai yi masa rantsuwar zancenta ?arya ne Taj ya dakatar dashi.

"Idan kana tunanin na yarda da zancenta har ina bu?atar ka wanke kanka to gaskiya akwai matsala tsakaninmu."

Murmushi Kamal ya yi "Allah Ya huci zuciyarka."

"Amma wane irin ciwo gareka Happiness?"

Koda Kamal ya juya ya kalli Taj sai yaga babu alamun wasa a tare dashi. Allah Ya taimake shi ya fara ajiye magungunan allergy su antihistamine saboda rana irin wannan. Durowar magungunan ya buWe ya fiddosu duka.

"Ka ce baka yarda da zancenta ba."

"Daga cikin addu'ar da nake yawan yi mana harda kada Allah Ya haWamu son abu guda da mutum biyu basa tarayya a kansa. Zancen ciwo kuwa ai rantsuwa tayi. Tunda tana sa gaba gabas zancenta zai iya zama gaskiya."

?aya bayan Waya yabi magungunan ya dudduba. Pain relievers ne da wanda su ka danganci kwantar da abin da ya shafi allergy.

"Allah Ya baka lafiya Happiness."

"Amin."

***

Tafiyar minti biyar a mota za ta kai mutum wani babban mall da ya yi shura a titin kafin a gina Happy Taj. ?an Kano da son sabon abu na yayi kusan kowa ka taSa zai ce maka ya yi siyayya a Glory Mall. Wurin sha?e yake da kaya na alfarma. Sannan akwai snacks irinsu shawarma, small chops, popcorn, ice cream da sauransu. Har event centre garesu a ciki. Wurin mallakar wani hamsha?in Wan kasuwa ne da ya dam?awa babban Wansa alhakin kula da shi. Kuma a shekara biyu da rabin farko uban ya yi alfahari da Wansa. Ciniki ake yi na bugawa a jarida.

Komai ya soma taSarSare musu cikin abin da bai fi sati guda da buWe Happy Taj ba. Idan kaya ake so boutique Win Kamal yana da na kowanne jinsi manya da yara. Abin da ya shafi abinci kuwa harda wanda mutane basu sani ba akwai a Sangaren Taj.

Kamar wasa su ka dinga tunanin ko irin abin nan ne na Wokin sabon waje. Idan an kwana biyu abu zai koma normal. Sai aka yi rashin sa'a kasuwa da gaske take damawa da su Taj cikin albarkar Allah. Haka kawai mutane su ka fara janye jiki. Ciniki ya yi wani irin ja da baya mara daWi. Alh. Usaini ya shiga gagarumar matsala da mahaifinsa. Inda rashin tawakkali yasa uban ya taso shi a gaba da muggan kalamai da tsoratarwa. Indai ciniki bai daidaita ba to ya kwana da sanin zai karSe mall Winsa ne ya bawa wani daban cikin ?a?ansa. Wannan abu ya yi matu?ar tayar masa da hankali. Ya shiga faWi tashin hanyar dawo da martabar mall Winsu amma abu yaci tura. Har an kai wasu masu kai musu kaya sun fara janye jiki.

A irin wannan yanayin na neman hanya kowacce iri ce Allah Ya haWa Alh. Usaini da Ummi. Cutar hassada tayi mata lulluSi tun daga kai har tafin ?afa a lokacin da taji labarin auren Hamdi da mamallakin Happy Taj. Ranar harda kuka sai da tayi. Zuciyarta a cunkushe tana fama da takaicin yadda ?ar Wan daudu ta sami miji irin Taj. Ta taSa zuwa wajen da wani saurayinta. Yadda taga Taj ta san wadda ta fita ma bata isa ta aure shi ba, balle kuma Hamdin da bata kama ?afarta a gayu da rufin asiri ba.

Wani abin kayan haushin kuma jan kunne da gargaWin iyayenta da yayanta akan ?anwar Hamdi da ya aura. Ko kallon banza ta yiwa Zee ya yi al?awarin canja mata kamanni.

Ranar da ta haWu da Alh. Usaini, cikin jin zafin auren Hamdi ta fito ds niyyar zuwa Happy Taj ta Sata ta a gaban Taj. Sai da ta iso kuma ta rasa me ya kawo mata tsoro ta kasa ?arasawa. Haka kawai ?afafunta su ka kaita Glory mall. Ta je wurin snacks ta sayi meatpie da lemo ta sami wuri tana ci. Amma hankalinta gabaWaya yana kan ginin Happy Taj.

"Ki tafi can mana idan nan bai yi miki ba."

Kallonsa Ummi tayi za ta faWi ba?ar sai ta adana. Mutumin zai yi shekara arba'in da biyar. Ya sha shadda ?ar ubansu da Winki na alhazawan birni. Ga ?amshi na waWanda naira ta tsaga jikinsu ta zauna da kyau.

Murmushi tayi masa "ba kallon son zuwa nake ba. Fatan abin da zai zo ya tayar da wurin gabaWaya koda gobara ce nake yi." Ta kashe masa ido.

"Ko zan san dalili?" Amsarta tasa ya sami interest akanta.

"Kaji daWin kaini gaba? Allah Ya kiyaye." Ta tashi tsaye.

"Ko kusa. Nima burina kenan.." ya kashe mata ido yadda tayi masa.

"Dalili?"

"Sun kashe min kasuwar mall Wina mana."

Zama ta koma tayi "nan wurinka ne?"

"Eh. Amma yana fuskantar barazanar rufewa saboda su."

Dariyar mugunta Ummi tayi a zuci. Daga ranar su ka ?ulla ita da Alh. Usaini. Suna neman hanyar da za su nakasa Taj domin su gurgunta masa sana'a.

A wannan rana ta asabar da Salwa ta fito daga Happy Taj cikin Sacin rai, ta faWa Glory Mall saboda akwai mai POS daga bakin gate Winsu. Tana jiran mutumin ya idar daga sallar la'sar a gefen ?ar container Winsa take waya da Mami. A ciki take zayyane mata duk fa abin da ta ce tayi ta gwada amma ?arshe Taj yaci mutumcinta.

"Ni dai Mami da kin barni naje masa a yadda nake. Na tabbata idan ina kwantar da kai zai dube ni."

Zaginta Mamin tayi ta ce mata kuma ta kwantar da hankalinta. Ta sanar da mahaifinsu ya ce zai kira Alhajin su yi magana. Tana da ya?inin yadda Alhaji yake ragawa Salwa don mutumcin babanta da yake gani nw. Duk taurin kansa ba zai ?i tayin ?a ba. Musamman tunda ba son wadda Taj Win ya aura yake yi ba.

"Kin nuna musu kin san baya son auren?"

"Eh, kuma ban faWa musu cewa waya naji Yaya Ahmad yana yi da matan gidansu yana sanar dasu ba. Har wani cewa yake su yi wani abu kada a raba Taj da wadda yake so. Ni ko oho."

"Ki daina yin komai. Da kansu za su nemi ki idan babanki ya yi masa magana."

Wayarta duka a kunnuwan Ummi da Alh. Usaini waWanda su ka yiwa juna wani irin kallo gami da murmushi. Tana gama wayar Ummi ta matsa kusa da ita su ka gaisa. Sai ta nuna kamar ita ma mai POS Win take jira. Abin ka da mata in an haWu. Hira a taSa nan a taSa can sai gashi sun yi exchanging number.

Bayan Salwa ta ciri kuWin ne ta fito Kamal ya kirata. Babu ja in ja ta faWa masa inda take. Shi ne su ka Wauketa don darajar Ahmad kawai. A hanya harda basu ha?uri wai ranta ne ya Saci. Babu wanda ya kulata a cikinsu har su ka isa gidan. Taj ya yi zamansa a mota.

"Happiness ka turo min ita in kaita gida kafin magrib."

Salwa bata ce musu komai ba tayi wucewarta ciki. Ganin Kamal bai shigo ba ta tsaya ta goga hoda da lipgloss kafin ta shiga ciki. Hayaniyar mutan gidan taji daga Wan korido Win da ake ajiye takalma kafin a shiga falon. Ta ?ara yin tsaki. Bata san za ta ?i mutanen nan ba sai da taga yadda aka dinga kai kawo akan zuwan Hamdi. Yanzu kuma da alama hirar ma da ita suke yi.

Sallama tayi ta shiga da wani irin farinciki a fuskarta. Bata sha wahalar haWa ido da Hamdi ba don ita ma Win sallamar tasa ta Waga kai ta kalli ?ofa. Murmushin nasara ta sakar mata. Hamdi ta mayar mata. Daga ita har Taj Win sai ta fanshe wannan Sacin ran da su ka sa ta wuni cikinsa.

"Salwa ina ki ka je?"

?an firgita tayi domin kuwa Ahmad ne ya yi tambayar da kakkausar murya.

"Da Ya Taj muka fita. Cewa ya yi na raka shi Happy Taj. Shi ne mu kaje harda Ya Kamal"

"Bangane ba? Ya zai kawo matarsa kuma ya yi wani wajen. To da izinin wa ma???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ki ka fita?"

Kafin ta bawa Yaya Zulaiha amsa Kamal ya shigo. Sai ta canja akalar tambayar.

"Ko dai soyayya ku ke da Kamal?"

Da wani irin sauri ya ce "Allah Ya kiyaye. Ina da wadda nake so."

Jama'ar falon su ka kama ihun murna. Harda masu cewa ko a dakatar da bikin Taj saboda dama indai da amana tare ya kamata su yi aure.

Wannan amsa ta Kamal ta Sakanta ran Salwa. Yadda ya faWa tamkar wata abar ?yama. Ahmad kansa sai da yaji babu daWi. Anti Zahra ta kallesu su biyun. Idan Salwa ta cigaba da zama dasu za a iya samun matsala tsakaninsa da ?an uwansa. Ko me za ta yi ita ma jininsa ce.

"Ku tashi mu tafi" ya ce da Anti Zahra, bana son Magariba tayi min.

"Kai Ahmad, kamar kana dawa? Don Allah ka zauna."

"Ai mun gaisa da ?anwar tawa ko?" Ya yiwa Hamdi murmushi.

"An kusa kira Yaya. So kake Ya Taj ya yi sallah shi kaWai?" Bishir ya ce.

Fin ?arfi aka yiwa Ahmad. So yake kawai su shiga mota ya gamu da Salwa. A dole ya bi ?annensa waje su ka tare cikin motar Taj abin tausayi suna hira.

Aka sake tashi yin sallah. Hamdi ta koma Wakin Mama. Salwa sai ta faki ido ta bi bayanta. Su Mama suna Wakin Umma ana ta shirye shirye.

"Washhh. Wannan zirga zirga Ya Taj duk ya tara min gajiya."

?in kulata Hamdi tayi. Kowa yaci tuwo da ita ai miya ya sha. Darajar inda su ke yanzu yasa ta kama kanta. Amma ramuwa kam zata yi gwargadon abin da aka yi mata!

***

Gayya guda aka rako Hamdi bakin gate da sha tara ta arzi?i. Har ta dinga jin wani iri saboda bata kawo musu komai ba. Yawancin kowa a bayan mota ya ajiye kyautarsa. Banda likitar gidan. Yaya Kubra a hannu ta dam?a mata wata ba?ar pepper bag da aka rubuta Scentmania a jiki. ?amshi a take ya cika gaban motar tun ba a buWe ba. Ya haWe da sanyin AC sai ya bada wani irin ni'imtaccen yanayi.

"Zamu yi waya in miki bayanin turarukan kinji. Mun kuma gode da wannan ziyara."

"Nima nagode sosai. Allah Ya saka muku da alkhairi."

Suna ta Wagawa juna hannu aka rabu a mutumce. Daga nan kuma motar ta koma ta kurame. Taga ta zubawa idanu tana kallon gilmawar ababen hawa da fitilunsu. Taj ya kalleta yafi a ?irga ya tabbatar da gaske shi ne bata son kulawa. Murmushi ya yi. Ya taSa wayarsa wanda Hamdi ta gani da wutsiyar ido amma ta share.

"Hello, Salwa..."

Iya abin da taji ya ce kenan ta juya a fusace su ka haWa ido. Wayar a gefe ya ajiyeta. Babu kuma wani abu da zai nuna mata wayar yake yi. Dariyar kamata ya fara sai yaga babu fuska sam. Ta tsuke baki kawai ta sake juyawa. Har wani numfashi mai nauyi ya kula tana saukewa. GabaWaya sai yaji ya kasa sukuni. Dama ya san za ta ji haushi. Amma ya yi zaton za ta jira bayani daga gare shi.

"Mrs Happy"

Shiru.

"Hamdi" sunan nan har tafin ?afarta take jinsa idan ya faWa amma ko motsi bata yi ba.

"Please ki juyo.." nan ma biris tayi dashi " to kada ki ga laifina duk abin da ya biyo baya."

Gyaran murya taji ya fara ta taSe baki. Wato zai fara yi mata daWin bakin maza da take ji ....katse mata zancen zucin ya yi.

"Dil ne yeh kaha hain dil se (my heart has said this to your heart)"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Banda wa?ar India don Allah. Wallahi kunya ma nake ji. Bana son namiji yana..."

"Mohabbat ho gayi hai tumse (I have fallen in love with you)"

"Na shiga uku" Hamdi ta sanya hannuwanta biyu ta toshe kunnuwanta "ka bari don Allah zan saurareka."

"Meri jaan, mere dilbar (my life, my love)."

"Ya Taj wasa nake. Ba ma fushi nayi ba..."

"Mere aitbaar karlo (have faith in me)"

"Happyyy" ta faWi kamar tayi kuka wai yau ita ce miji yake yiwa wa?ar india.

"Jitna beqarar hoon main (how much restless I am)"

Titi yake kallo abinsa yana sakin baiti. Ta rasa yadda zata yi dashi. Kawai sai ta kai hannuwanta ta cupping fuskarsa wanda ya sanya shi Wauke wuta na wucin gadi.

"Allah na ha?ura." Ta fada a hankali.

Gefen titi ya gangara da motar ya Waga handbrake tare da canja giya zuwa 'P'. Ya juyo su ka haWa ido har lokacin bata cire hannuwanta daga fuskarsa ba.

Shan kunu ya yi "Ki barni in ?arasa. Ba ke nake yiwa ba."

Ita kuma ta marairaice masa
"Don Allah kayi ha?uri to sai na fita."

?wayar idanunta yake kallo sai ta rufe idon.
"Can I have that kiss now?"

Zame hannuwanta ta soma yi daga fuskarsa ya janyota gabaWaya. Garin ya Worata a cinyarsa handbrake ya sauka. Motar ta Wan yi gaba amma ba da sauri ba saboda giyar da ya canja. Rungume shi tayi ?am?am tana salati ta sanya fuskarta a tsakiyar ?irjin shi.

"Wayyo Allah Abbana...Yaya..."

Bata san lokacin da ya sake tsayar da motar ba. Hannunsa aya kawai taji a ?asan haSarta ya Wago kanta sama.

"Salwa bata da matsayi ko kaWan a wajena kinji." Kai ta gyaWa a hankali.

"Fitar da muka yi ba abin da kike tunani bane. Happiness ne yake ?o?arin fahimtar da ita ta ha?ura."

"Ai na yarda."

"Akwai wa?a da ta dace da irin wannan yanayin." Ya Wage gira.

"Kada kayi don Allah."

"Ke dai???"

"Bana so." Ta turo baki.

"Hamdi."

"Na'am." Ta ce tana mai jin nauyinsa don ya?i sakinta balle ta koma mazauninta.

"I love you."

?asa ta so yi da fuskarta don kunyar yanzu tafi ko yaushe. Sai dai Taj yaci alwashin yau sai ya rage wani abu a kunyar nan ya tafi dashi gida. Shammatarta ya yi kamar zai yi magana taji saukar leSensa akan nata. He was so gentle amma ya kashe mata jiki har ta sake narkewa a jikinsa bata sani ba. Rungumeta yayi a haka kanta a gefen kafaWarsa kamar mai bacci. Shi kuwa wani irin contentment ya samu ds nutsuwa a zuciyarsa.

Basu yi aune ba su ka ji ana ?wan?wasa gilas
in motar. Mutanen dake waje suna cewa ko lalacewa tayi ko kuma mai ita wani abu ya same shi. Kamar ?ifta ido Hamdi ta koma wurinta tana raba idanu. Taj ya kalli mutanen ya ga da wuya su fahimci matarsa ce idan su ka gan shi da mace. Kawai sai ya canja giya ya yi gaba. Shi da Hamdi su ka haWa ido su ka kama dariya.





_Uwargida....I see you! SonSo Sis Juwairiyya_
RAYUWA DA GI?I 23




Batul Mamman






Har su ka ?arasa gida idan sun kalli juna sai sun yi murmushi. Abin da ya Waurewa Hamdi kai shi ne yadda Taj har wani kawar da kai gefe yake irin na masu jin kunya. To ai ita ma kunyar take ji. Kuma ita ya dace ta dinga yin haka. Sai gashi kafin tayi yake yi. Gajiya tayi lokacin sun iso layinsu ta kalle shi.

"Wai mene ne?"

Gefe ya kaWa kai yana wani rufe ido "Awwnnnnn, ni ki daina tambayata. Kin fi ni sanin ko mene ne."

Murmushin fuskar Hamdi Waukewa yayi. Ta soma harararsa.

"Banda wa?a kuma harda irin haka kake yi?"

"Irin yaya?" Ya tambaya kamar bai gane manufarta ba.

"Meye wani awwnnn don Allah?"

Hannu ya kai ya shafa kumatunta "Saboda ina son ganin wannan hararar da juya idanun naki. You always look cute."

Murmushi ta soma yi ya kuwa sake cewa "awwnnnn" yana dafa saitin zuciyarsa.

Wannan karon dariya tayi. Irin dariyar da bai taSa gani daga gareta ba. Zuciyarta tayi fari kamar auduga.

"Kin san wani abu? Zo mu shiga ciki kafin ha?urin Abba ya ?are."

Bakin ?ofar gidansu ta kalla. Ai kuwa Abbanta ne yake Wan le?owa. Bai yi zaton za su yi dare ba. Kuma sun iso Win ma ta?i fitowa. Shi ne ya kasa sukuni. Kada fa ta biyewa Taj al'amari ya kwaSe a gaba.

"Zan kira ki idan naje gida. I hope ba da wuri ki ke bacci ba."

Bata iya bashi amsa ba da ta hango inuwar Abban da gaske. Kamar an tsikareta ta fito da sauri. Tana hango shi ya koma cikin gida ta bi bayansa. Taj ya yi murmushi kawai. Ya juya baya zai yi ribas ya yi arba da ledojin da ?an uwansa su ka ajiye mata. Parking ya gyara ya Webi yadda hannuwansa za su iya Wauka ya je ?ofar gidan yana sallama.

Caraf yaji Abba yana yiwa Hamdi faWan kada ta manta da maganarsu. Shi ba zai iya ja da Alh. Hayatu ba. Jin sallamarsa yasa shi yin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login