Showing 123001 words to 126000 words out of 182745 words

Chapter 42 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

125

kiyaye kawai."

Ita ma ha?urin ta shiga bayarwa ba ji ba gani.

Da dai Kamal yaga tarkonsa ya kama sai ya cigaba a haka. Ya karSi laifin da bai yi ba ya cigaba da bada ha?uri. Sai da komai ya lafa ya tambayi waye babu lafiya. Da yaji Taj ne ai sai ya ture nasa ciwon ya fita. Mubina ma sallama tayi masa ta koma ciki.

"Alhaji mu je mana" ya dawo da ya ankara shi kaWai ya fita.

"Jeka. Likitan da ya duba shi zan tambaya game da wani bayani da ya yi min."

Da sauri Kamal ya wuce. Alhaji ya bi shi da kallo har ya fita sannan ya koma reception jiki babu ?wari. GabaWaya Kamal Win ya sauya sosai. Tun rashin lafiyar kwanaki da aka ce allergy ne ya lura yaron nasa ba yadda ya saba yake ba. Ya dai ha?ura da yawan tambayarsa ya jiki ne da yaga yana harkokinsa na yau da gobe babu fashi.

"Doctor Winnan da muka gama magana gobe ?arfe nawa za ta tashi? Akwai patient da nake son ta duba min na manta ban faWa mata ba."

Wani Wan littafi mutumin ya duba ya ce "yau bata da night (call), sai 3 na yamma kuma za ta shigo goben. Yanzu ma na san alfarma kawai ta yi masa tunda ya saba zuwa amma she is off."

"Shi wa kenan?" Alhaji ya Soye matsanancin tashin hankalin da ya kama shi.

"Wanda ka gansu tare."

"To nagode"

Wani irin sanyi mai farawa daga cikin ?ashi ne ya dirarwa Alh. Hayatu. Kamal bashi da lafiya kuma yana Soye masa.

Fargabar da ya dawo mota da ita ce ta hana shi sakar musu fuska yadda ya yi niyya.

"Alhaji ko su dawo motata?" Kamal ya tambaye shi bayan ya zauna mazauninsa.

Ba tare da ya kalli inda Kamal Win yake tsaye da Taj ba ya ce "Tunda cinyesu zanyi ko?"

"Tuba nake." Kamal ya faWi yana dariya "Happy mu haWu a gidal"

Motarsu Alhajin ya koma shi kuma Kamal ya ja tasa shi kaWai. Yana murna da Alhaji ya hana su biyo shi domin da sun ?ara lokaci a tsaye Taj zai cigaba da yi masa tambayar ?ure.

A motar ma duk da ba hira suke ba amma Alhaji sai da ya tambayi Taj ko Kamal ya faWa masa me yake yi a asibiti cikin dare. Amsar bata sauya daga irin wadda ya bashi ba da kansa ba.

Daga nan kuma motar ta koma ta kurame. Kowa ya yi shiru har aka isa gidan. Da su ka isa tsayuwa su ka yi a bakin motar don basu san ina za su nufa ba kuma. Alhaji da ya san jiransa suke yi sai lokacin ya Wan saki fuska bayan isowar Kamal. Wayar Inna ya kira kuma bai yi mamakin da bata yi bacci ba ta Wauka. Ya ce mata ta fito akwai ba?uwa.

Inna ta taso da hijabinta don dama sallah kawai take yi tana addu'o'i. Da ta buWe ?ofar sakin baki tayi kafin kuma ta fito waje sosai inda suke ta rungumo Hamdi.

"Alhaji lafiya dai ko?"

"Lafiya ?alau. Kawai dai naga bai dace ta koma gida a daren nan ba tunda matar aure ce."

"Haka ne" Inna ta gyaWa kawai cike da mamakin da ya?i ?arewa "shi kuma wannan gidan Ahmad za a kai shi ko?"

"A'a" Alhaji ya amsa mata da wani irin murmushi a fuskarsa. Haka kawai yake jin son kyautata mata ko don yadda hankalinta ya tashi Wazu "a gidan nan zai kwana."

Wani irin farinciki mara misali ya sake mamaye Taj. Kamal kam rungume shi ya yi yana faWin "mun gode Alhaji. Allah Ya ?ara girma. Ya ja kwana. Mun gode"

Ya dafa kafaWar Taj Win "Happy zo mu je ka kwanta."

Sake basu mamaki ya yi da cewa "Kada ku takura, ya kwana a Wakin ?asa na Sangare na."

Wai kuma sai ya juya zai shige ciki. Inna har lokacin tana ri?e da hannun Hamdi ta juya ita ma da sauri tana mai danne kukan da take shirin yi. Taj kawai ta kalla taga yadda furucin mahaifinsa na ?arshe ya kawo wani irin hasken annuri ya shifiWe masa a fuska. Sai hamdala da take ta karanta daga laSSansa. Abin da ake jira kuma ake ganin kamar ba zai yiwu ba ne ya faru a lokacin da ba a zato.

"Allah Ya faranta maka fiye da yadda kayi min. Ina ro?on Allah Ya kawo maka Wauki ta inda ba ka zato akan duk masifa ko rashin kwanciyar hankalin da zai tunkaroka. Na gode Yaya Hayatu."

Yau ake kira farar rana. Rabon da Zainabu Abu ta kira Alhaji da sunan da ta saba kiransa a matsayinsa na Wan uwanta ya manta. Yana son ya juyo ya bata amsa daidai da addu'ar da tayi masa amma ga ?a?a da suruka a wajen. Don kada ya bada kansa sai ya gyaWa kai kawai.

Hamdi ta ajiye fushinta a gefe domin wannan abu ma?iyi ne kaWai ba zai taya Taj murna ba. Ita da bata cika son magana ba sai take jin ya kamata ta ?ara nunawa Alhaji cewa mahaifinta ya horar dasu da kyakkyawar tarbiyya. Da wannan tunanin a du?a har ?asa a gefen Inna. Muryarta a hankali cikin nutsuwa ta ce,

"Allah Ya saka da alkhairi Alhaji. Allah Ya bamu ikon faranta maka fiye da yadda kayi mana. Mun gode."

Sai yanzu ya yi magana "babu komai. Ku shige ku kwanta."

Inna dama jira take ta sami damar yin kukan farinciki. Da sauri ta wuce ciki. Tana ri?e da hannun Hamdi har Wakinta. ?an kwanan kowa ya kwanta banda mutum biyu Badi'a da Sadiya da su ka san Taj babu lafiya. Basu tashi matan gidan ba su ka zauna jiran su Alhaji. Suna ganinta da Hamdi ta yi musu bayani kafin ma su tambaya.

"Aikin babanku ne ya taho da ita daga asibiti wai dare yayi."

Badi'a ta ce "to ina Taj Win?"

Da wata irin murna ta wanda yake cikin za?uwar bada labari ta sake cewa "Alhaji ya dawo dashi gida"

Sai kuma ta faWi cikin sujjada tana yiwa Allah kirari. Hanyar fita Sadiya tabi za ta fita ta fesawa ?an uwanta Inna ta dakatar da ita. Ta nuna mata dare yayi ga gajiyar da aka kwaso. Da ?yar Sadiya ta haWiye zancen ta ha?ura sai asuba.

"Hamdi akwai ruwa a heater. Ki Wan watsa ruwa don jikinki yayi daWi sai ki kwanta."

Babu musu ta tashi za ta shiga banWakin da Inna ta nuna mata. Jikinta tayi tsamin gajiya sosai. Innar ta bata wata doguwar riga da ?ar hula ta shige dasu. Kafin baWakin akwai wani Wan wuri da aka saka shoe rack da wani Wan tabur inda aka ajiye mai da turaren jiki irin oils Winnan na Scentmania irin nata. Nan ne wurin shafa mai sannan mutum ya shiga Waki ya ?arasa shafe shafensa. Wanka tayi ta Wauro alwala. Tana fitowa ta samu su Sadiya sun kwanta. Sai Inna dake sallah. Dama tana kunyar yadda za ta kwanta Waki Waya da mahaifiyar Taj. Da taga tana sallah kawai sai ta zauna. Ita kuma Inna da ta idar ta tambayeta me ya hanata kwanciya.

"Nima sallar zan yi Inna."

Wani murmushin farinciki da Inna tayi ya nuna tsantsar jindaWinta. Ta bata hijab su ka yi raka'a shida sannan Hamdi ta soma hamma. Sai tayi kamar ta idar. Ai kuwa akan abin sallar Hamdi tayi bacci. Wannan qiyamul laili da tayi tare da Inna kuwa ta saya mata wajen da babu wata mace da za ta taSa auren Taj ta mallaki wannan gurbi. KaWan daga sirrin Tahajjud!

A Sangaren Alhaji kuma Kamal, Bishir da Abba da ya dawo daga baya duk Waki guda su ka kwana da Taj. Alhaji yana jiyo hayaniyar murnarsu kamar ba dare ba. Sai ya tuna ?uruciyarsu da kuma samartakarsu da ya katse na tsayin shekaru. Rashin jindaWin abin da yayi gami da tunanin wane ciwo ke damun Kamal sai su ka hana shi baccin kirki.

Wuraren huWu da rabi yaji alamun an buWe ?ofar Sangaren nasa. Dama baccin babu nauyi. Da sauri ya le?a domin ya gani ko jikin Taj ne ya tashi. Fitowarsa tayi daidai da fitar Kamal. Nan jikinsa ya sake mutuwa. Ya koma bakin gado ya zauna. Baccin da bai koma ba kenan sai kawai ya ta da nafila. Yana ji aka soma kiraye kirayen assalatu. A zuciyarsa ya ?udurta sauka ya tashi su Taj nan da minti talatin sai su yi alwala su tafi masallaci.

Ko minti goma ba ayi ba yaji ana buWe gate a hankali. Ya sake tashi ya le?a sai ya hango motar Kamal ce ta fita. Bai yi wata wata ba ya sauka ?asa da mu?ullin wata sabuwar motarsa. Da kansa ya ja hankalinsa a matu?ar tashe. Rabonsa da tu?i ya ma manta. Cikin sa'a da yabi hanyar asibitin sai ya hangi motar Kamal tunda titi fayau yake dai motoci jifa jifa.

Haka ya bishi har asibitin ba tare da ya sani ba. Yana parking bayan shigar Kamal ciki sai ga Mubina. Da sauri ta shiga asibitin tana magana a waya. Bayanta Alh. Hayatu yabi da sauri. Tana shiga cikin asibitin tayi hanyar emergency inda ya ga fitowarsu Wazu ya kirata da kakkausar murya.

"Dr. Mubina"

Cikinta ya ba da wani mahaukacin sauti domin ta riga ta gane muryarsa. Ta juyo kamar mara laka a tsorace.

"Kai ni wajen yarona."

Gaba tayi ya bita a baya har Wakin. Ta buWe da sallama. Nos Win da ya taya ta aiki da daddare yana tsaye akan Kamal dake kwance babu riga. Juyawar nan da Kamal ya yi da yaji motsinta sai idanuwansa su ka sauka a cikin na Alh. Hayatu Sule Maitakalmi.
RAYUWA DA GI?I 30






Batul Mamman=ؖ?





Kuna neman reliable data ba cuta va cutarwa? Ku saya a baku na kowane layi cikin aminci da rahusa?
Look no further. Contact MKdataservices for your data, airtime, tv subscription and nepa bills.

08038258489

https://www.mkdatasarvices.com.ng

Sayen nagari....mayar da data gida!

~~~~~








Ya yun?ura zai tashi ba shiri don ya san yau Win abin da zai fuskanta sai ya gwammace kiWa da karatu. Alhaji ya yi masa alama da ya koma. Ya sake yun?urawa dai sai Alhajin ya kalle shi yana mai buWe masa idanu. Dolensa ya koma ya tada kai da filo.

Mubina dake tsaye da tasar allura tayi wi?i-wi?i da idanu ya duba "?arasa ki duba min shi mana."

Tayi sauri ta isa gaban gadon. Ido Kamal ya rufe don allurar akwai zafi. Alhaji yaji wani irin tausayinsa ya tsirga masa. Kujerar gaban gadon yaje ya zauna. Ya kama hannun Kamal na dama ya ri?e. Irin ri?on ?arfafa gwiwa da rarrashi.

Dama yaya lafiyar kura? Duk wani emotion na rauni da Kamal yake adanawa tun farkon rashin lafiyar a lokaci guda ya fashe. Ya ?ara ?arfin ri?on hannun mahaifinsa yana kuka mara sauti. Tsananin tausayinsa yasa Mubina taya shi. Nos Win ma kawar da kai gefe yayi. Shi kuwa Alhaji dakewa ya yi duk irin yadda hankalinsa ya tashi.

"Kuka a gaban mace Kamal kamar wani mace? Ni fa ka san ba shiri nake da rago ba."

Hawayen ?aruwa su ka yi. Ya dawo da kansa saitin Alhaji kawai ya cigaba da abinsa.

Alhaji yayi murmushi "matana basu taSa ganin hawayena ba duk shekarun nan. Kai kuwa ka saka mace a gaba kana abin kunya. Ko batun ala?ar taku shi ma ?arya ku ka yi min?"

Girgiza kai Kamal ya yi. Alhaji ya dubi Mubina da allura a hannu tana kallon ?asa. Allurar ya ce tayi tunda da alama akan lokaci ake bu?atarta. Ba don haka ba ya san Kamal ba zai fito da asuba ba. Bayan anyi allurar wadda yadda yaga an soka ta ciki ya ?ara kiWima shi sai ya tambayi Nos Winnan abin sallah. Gari har ya soma haske basu yi asuba ba. Daga kan gadon Kamal ya bi shi sallar. Bayan sun idar suna zaune su biyu, Alhaji yana zaune akan abin sallah ya tambaye shi game da ciwon.

"Lalurar dake damunka a hanyar fasi?anci ka same ta ne?"

"A'a Alhaji" ita ce amsarsa.

Muryar Alhaji ta karye domin a tsorace yake Allah Ya sani. Kamar kada ya idar da sallah ya yi tambayar tun farko.

"To me yasa? Mene ne dalilin Soyewar?"

"Saboda maganin ba mai samuwa bane Alhaji. ?oda nake bu?ata kuma ..."

Yana son yin faWa amma ya san cewa abin da zai sa Kamal yi masa Soyon ciwo ba ?aramin abu bane.

"Gani, ga ?an uwanka mutum ashirin da bakwai amma ka kasa faWa? Bayan na san karamcin da Allah Ya yi min a gidana. Yau ko babu ni babu mahaifiyarka ina da ya?inin cewa sauran uwayenka za su tsaya maka ka samu a jikin ?an uwanka ko da kuwa ?a?an cikinsu ne."

Nan dai Kamal ya yi masa bayani akan matsalar da aka samu. Bai gamsu ba sai da Mubina tayi masa fashin ba?i. Amma duk da haka zuciyarsa fafur ta?i amincewa. Ana bayanin yana jin zufa a duka jikinsa. Gabansa kuwa faWuwa kawai yake yi.
Yayi salati yafi a ?irga. Kamal ya yi mamaki domin faWa yasa rai zai yi masa.

"Alhaji baka yi min faWa ba."

"Wane irin faWa kuma Kamal? Ta yaya ma za ka yi tunanin zan maka faWa? Halin da zuciyarka take ciki na firgicin ciwon ma da ina da iko wallahi zan raba ka dashi. Da ace akwai yadda zanyi cikin ku babu mai yin atishawar da zai ji a jikinsa. Baka ganin dalilin ciwo na dawo da Wan uwanka? Ta yaya kai kuma zan yi fushi da kai?"

"Kayi ha?uri."

Tare su ka fito bayan allurar ta saki Kamal. Alhaji ya dage sai dai ya bishi a motarsa. Zai turo a Waukar masa tasa.

"Kawo mu?ullin to.." ya mi?a hannu zai karSa. Alhaji ya hana.

"Da ?a?ana da jikoki kake tunanin zan yarda kana rabin mutum ka ja ni?"

Suka yi dariya sannan su ka shiga Alhaji ya ja su. Jifa jifa su kalli juna su yi murmushi don su kwantarwa juna hankali.

"Alhaji don Allah maganar nan.." Kamal ya fara ro?onsa da su ka isa gida.

"Shiga ciki Kamaluddeen" Alhaji ya katse magiyar da ya so yi masa akan ya yi shiru da maganar.

Bayan Kamal Win yabi ya same shi yana yiwa su Taj ?aryar abin da ya fitar da shi da asuba. Murmushi yayi musu bayan ya amsa gaisuwarsu. Su huWu yau su ka kwana a Waki guda kamar wasu yara ?anana.

"Yaya kan naka?"

Abba ya wani turo Taj gaba "taSa shi kaji Alhaji. Jikin da sau?i. Ai jiya bamu yi bacci ba saboda yi maka gadinsa."

"Nagode Sulaiman. Yau ni ne abin tsokana ko? Ko da yake girmanka ne baban Hayatu."

Aka saka dariya sannan ya haye sama ya kira Ahmad. Taj ne kawai ba ya sakin jiki ya yi dariyar saboda har yanzu zuciyarsa ta kasa gaskata wai shi ne a gida.

***

Rabon da Abba Habibu yaga rigimar Yaya irin wadda ya gani tun bayan dawowarsa a daren jiya ya manta. Ta nuna masa rashin jindaWinta sosai. Da mitar ta kwana ta tashi.

"Amma dai kin san ba dawa taje ta kwana ba."

"To mene ne maraba? Gidan surukan da bata riga ta tare ba saboda Allah. Salon a sami abin goranta mata nan gaba."

Kwanciya Abba ya gyara don bacci sam bai ishe shi ba. Ya yi dare a waje sannan rikici ya hanasu bacci sosai.

Yaya ta haWe rai "kwanciya ma za ka yi?"

"Da fa? So ki ke muyi ta Waga murya a sami abin goranta mata da yawa?"

Saukowa tayi don kanta da taji me yace "amma ka san damuwata. Ina gudun kada ace bamu saya mata mutumci ba."

"Akwai mutumcin da ya wuce auren da aka Waura mata? Kuma na nanata miki cewa ba Taj bane ya ce ta zo su tafi. Yaya Hayatu ne ya ce ta bi mijinta."

"Zancen nawa dai ya fito. Ya ce ta bi shi saboda yana ganin ya isa. Ni bana son wani ya rainaka ne." Ta faWi da ?an?anuwar murya.

"Nayi zaton kin yi min sanin hagu da dama ashe ba haka bane? Wallahi kuWi ko mu?ami ba zai sa na wula?anta ?ata ba. An riga an Waura aure. Bai kamata na nuna mata bijerewa umarnin mahaifin mijinta garesu daidai bane. Ko har kin manta matsayin da muka haWu da Taj tsakaninsa da babansa?"

Jikinta sai ya sake yin la'asar. Ta kama bakinta bayan ta bashi ha?uri. Bawan Allah dama ba ri?o gare shi ba. Nan da nan ya kashe wancan zancen ya sako maganar kai amarya tunda ya san dole za a dawo da Hamdi daga gidan Alh. Hayatu. Sai da su ka gama tsara komai ya koma ya kwanta ita kuma ta fito falo.

A firgice ta sami Zee tana kai kawo. Zee Win na ganinta tayi maza ta rufe ?ofar falon kada kowa ya ji.

"Yaya kada ki tada hankali idan ki ka ji me zan faWa."

"Allah Yasa dai lafiya Zee."

"Jiya Hamdi bata dawo gidan nan ba."

Da gangan Yaya ta ce "kai haba?"

Zee ta sake kwantar da murya "Wallahi kuwa. Nayi ta kiran wayarta bata Wauka. Sai da asuba tayi min message wai tana gidan su Ya Taj."

"Indai haka ne ai babu damuwa."

Zee kasa Soye mamakinta tayi. Da tsammanin faWa ta zo sai ta samu ba haka ba. Yaya ta gama tsokanarta sannan ta taimaka tayi mata bayanin me yake faruwa. Su ka gama dariya da tunanin me za su ce da mutanen da suka kwana idan aka fara cigiyar amarya.

***
Hajiya, Umma da Mama sai da safe Inna ta sanar dasu duka abubuwan da su ka faru a gidan da daddare, har ma da ba?uwarsu. Murna a wurinsu ba a cewa komai. Dawowar Taj abin farinciki ne da shi kaWai ya cancanci ayi ?warya ?waryar walima saboda farinciki.

"Amma banda abin Alhaji me zai sa ya taho da Hamdiyya bayan tare da mahaifinta su ke?" Umma ta faWi bayan sun Wan nutsu da murnar.

"Kema dai Jamila kamar baki san halin mijin naki ba. ?arshenta gani ya yi kamar Taj ya damu shi ne zai taho masa da ita don ya kwantar masa da hankali. Son ?a?a kuma a wajen mutumin nan ai ba a magana." In ji Mama.

Wata uwar guWa su ka ji daga falo. Dama suna Wakin Mama ne. Inna ta sallami kowa ta bar Hamdi saboda baccin da ya sake Wauketa bayan tayi sallar asuba.

Fitowa su ka yi iyaye, ?a?a da jikoki. Ashe Amma ce tayi fitowar sassafe ko wanka bata yi ba. Hijabi kawai ta Wora akan rigar baccinta ta fito. Tana ganin matan gidan, musamman Inna sai ta kama kuka.

"In da na san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login