Showing 18001 words to 21000 words out of 182745 words

Chapter 7 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

75

ita take mata. Su Webo ruwa da kwafar note dama tuni ta daina saka wasu. Kuma ko da wasa Hamdi bata taSa faWin wata kalmar neman sau?i ba. Komai Ummi ta ce 'to' ce amsar. Ita dai burinta ta bar makarantar ba tare da kowa ya san ko waye mahaifinta ba.

Da yake a cikin hutun da su ka aka yi jarabawar JAMB, yanzu ?an kwanaki su ka rage kafin a fara WAEC. Kowa ya du?ufa da karatu ba ji ba gani. WaWanda basu Wauki karatun a bakin komai ba irinsu Ummi kuwa shagalinsu suke yi.

Ranar wata laraba da safe aka tashi makarantar babu ruwa. Abin ka da lokacin zafi. Tsakanin April da May a garin Kano dama ba a cewa komai. Rijiyar makarantar mai dama dama ba a samun komai sai wani ruwan dauWa wanda zai iya sati bai kwanta ba. Kowa ya shiga damuwa don ko darussan aji ba a shiga ba. Ga Wan karen zafi ana ta zufa. Principal tun safe ta fice sai wajajen shabiyu ta dawo da tankokin r??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????uwa har bakwai a bayanta. Yara sai murna. Aka umarci malamai da su kula da Waliban wajen bin layi ta yadda kowa zai samu. Sannan an ja musu kunne babu mai ?arSar ruwa sau biyu. Kuma bokiti biyu kaWai za a cika wa kowa saboda kada wasu su rasa.

Layi layi aka jera Waliban na ajujuwansu. A sammakon Hamdi ita ce ta talatin da huWu a layinsu. Kafin a zo kanta rana ta gama dafa ta. Ana zuba mata taji wani sanyi ya ratsata. Ta Wauki bokatan hagu da dama ta wuce Waki. Tun kafin ta isa bakin matattakalar hostel Win ta hango Ummi da ?awayenta a zaune kan dandamalin wurin suna ta hayaniya ana dariya. Fuska a haWe Ummin ta tarbeta da ta ?arasa.

"Kin daWe a layi gaskiya. Ke ko irin turereniyar nan baki iya bane?"

Take takenta Hamdi ta gane sai dai ta riga ta yiwa kanta al?awarin ko me zai faru ba za ta bata ruwan da ta wahala wurin samu ba. Jikinta gabaWaya ?ai?ayi yake yi mata. Ga ?ishi ga yunwa.

"Ban iya ba."

"Mtswww, wuce ki kai min ruwan in samu nayi wanka kafin a gama abinci."

Wata za?a?ura ta ce "Ummi kin ce fa nima za ki sa ta Webo min."

"Ki bari ta juye min mana." Ta cewa wadda tayi maganar a wula?ance.

Juyawa Ummi tayi taga Hamdi ta ajiye bokatan ta sar?e hannu a ?irji.

Rai a Sace ta ce mata "?auki mu tafi mana."

"Ki je ki bi layi don babu wanda za a zubawa sau biyu. Har ticking suna ake yi."

"To sai ki san yadda za ki yi. Ni ki wuce ki zuba min zafi nake ji."

Hamdi ta rasa daga ina take jin wani ?warin gwiwa kawai ta ce "naga kamar baki gane ba. Wannan ruwana ne. Ki je ki Webo naki."

Wata uwar shewa Ummi tayi tana dafa ?irji "dani kike? Har kin manta abin da zan iya yi miki idan ki ka Sata min rai?"

Tunawa da alamun mutumcin su Iyaa tayi sai take ganin kamar duk haukan Ummi ba za ta fitar da bidiyo Win ba.

"Kin daWe baki nunawa duk makarantar nan waye ubana ba."

"Kanbu, dani kike?" Ummi ta faWi cike da mamaki. Sai kuma ta fasa faWan ta ce ?awayenta su Wauko bokitin.

Suna kai hannu Hamdi ta tare kayanta ta hanyar dur?usawa a gaban bokatan ta tarosu da hannuwanta.

"Wallahi ba zan baki ruwan nan ba."

Mamakin me Hamdi ta taka a yau ne ya kama Ummi. Taga gara ta nuna mata idan tace za ta yi abu lallai babu fashi. Waya ta Wauko daga aljihun wandonta na kayan prep. Gaban Hamdi na faWuwa amma idonta yau ya ?e?ashe. Tana ji kamar kowa muryar Abbanta ta ?arade wurin. Kan kace meye wannan Walibai sun taru suna jin bayanin Ummi na cewa wannan zu?e?iyar muryar fa ta mahaifin Hamdiyya Habib ne wanda ya kasance Wan daudu. Aka dinga tururuwar le?a bidiyon ana cewa ga kama nan.

Kallon Hamdi aka fara ana zunWe tayi kamar bata jinsu duk yadda ranta ke suya ta du?a za ta Wauke ruwan sai taji Ummi tayi wata maganar da ranta ba zai iya Wauka ba.

"Mamanta kuwa cangal ce mai ?afa Waya da kwata" ta cilla ?afa Waya ta ban?aro ?irji Sari Waya "idan tana tafiya sai ka rantse Awilo ne zai yi rawar wa?arsa."

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Hamdi ta iya faWi don dariyar da aka tuntsire da ita a yayinda Ummi ke kwatanta tafiyar Yaya ta mugun ba?anta mata rai. Sakin bokiti guda tayi ta Waga Wayan da hannu biyu ta juye shi tas akan Ummi. Kowa kuma sai ya bar abin da yake yi aka tsaya kallo.

Ummi bata gama dawowa hayyacinta ba Hamdi ta cakumi wuyanta ta soma kai mata duka. Dambe sosai ya Sarke a tsakaninsu inda Hamdi ta dinga tumurmusata da ?asa. Tunda kayanta a ji?e suke sai jikin ya yi futu-futu kamar an tonota daga rami. ?awayen Ummi da suka ji ta fara neman ceto ne su ka ?waceta sannan su ka yiwa Hamdi taron dangi. Mutum uku ne su ka danneta a ?asa suna duka. ?an hostel Winsu na ganin haka su ma suka saka hannu wurin kai mata Wauki. Wurin ya hargitse aka dinga Sarin ruwa ana doke doke.

Prefects ma basu iya yin komai ba sai malamai da aka kira. Duk wadda take waje a lokacin da ?an kallo da ?an dambe aka tasa ?eyarsu sai ofishin Principal.

Baiwar Allah ji tayi kamar ta fasa ihu da taga yadda yaran nan su ka Sannatar da ruwan da ta wahala wurin nemowa. Ba'asi guda ta nema shi ne su waye su ka fara faWan. Aka nuna Hamdi da Ummi. Ta karSi bulala kuwa ta zane musu jiki ta zauna tana haki. Mataimakinta ne ya karSi shari'ar saboda abin mamaki yau Hamdi yake gani kuma wai ita ta fara faWan. Duk yadda aka yi a sanin da ya yiwa shaiWanci na Ummi ya san laifin ba zai wuce nata ba.

Masu tarar aradu da ka ya haWa da displine master sannan ya zauna sauraron abin da ya haWa yan matan. Ummi ta kitsa ?arya da gsskiyarta ita kuwa Hamdi ko tari bata yi ba. Mutumin nan ya kaWa ya raya amma ?ememe ta?i magana. Sai ajiyar zuciya kawai take saukewa. Waje ya tura su ya tattauna da malamai. Kowa ya riga ya san halin Ummi da Hamdi. Duk da haka tunda Principal tayi rantsuwa ya ce a dubo lambobin iyayensu a sanar dasu ana nemansu washegari Juma'a. Duk wanda bai zo ba ?arsa ba za ta yi jarabawar da za a fara ranar litinin ba.

Hamdi a yau ko a jikinta. Ta riga ta sanyawa zuciyarta Soyon uba bashi da wata fa'ida. Da tun farko ma an san shi Ummi bata isa tayi amfani da wannan damar akanta ba.

A Sangaren Ummi ne dai hankalinta ya nemi gushewa. ?aryarta ce za ta ?are nannda ?an awanni. Kiran iyayenta ba ba?on abu bane ko kaWan. Inda gizo ke sa?ar dai shi ne wani Sugar Daddy Winta ne yake zuwa a matsayin kawunta. Wai ita marainiya ce. Baba Maje da ke kawota kuma yaron kawun nata ne. Har ila yau baban nata yana karSar wayarta duk ranar komawa makaranta tun da aka bata wayar. Wadda take amfani da ita ba tare da sanin hukumar makarantar ba wata ?awarta take bawa ajiya. Babbar waya ce da wani saurayin daban ya saya mata. Tun kafin a dawo taje gidansu yarinyar ta tura wannan bidiyo Win da ta yiwa Abban Hamdi. Idan ta kuskura ta bari aka kira wani ba mahaifinta ba Hamdi za ta sami damar da ta zarce wadda ta samu ta cusguna mata. Gumin da ya tsatstsafo mata ta yarfe kafin ta tashi da rawar jiki taje ta sanar da Vice Principal numbar da zai kira a madadin wadda su ke da ita.

***

?okin da ya kama shi tunda aka yi sanarwar jirgi zai sauka nan da mintuna kaWan ya bashi mamaki. Belt Win da aka ce fasinjoji su Waura ya gyara gami da le?a tagar jirgin. Garin Kano yake gani da tsakar rana ?arfe biyu da rabi. Tsirarun bishiyoyi da yalwar ciyayin damina sai gine gine marasa tsayi ba kamar inda ya baro ba. Tayoyin jirgin na dira ?asa sabon yanayi ya ba?unce shi na farinciki da tarin fargaba. Uwayensa da ?an uwa tun a waya su ke nuna farincikinsu. Alhaji ne damuwarsa. Zai karSe shi ko kuwa yanzu ma zai cigaba da nuna masa ?yama kamar wanda yake aikin saSon Allah?

*

Kafin kowa ya kula wata matashiya dake tsaye tare da iyalan Alh. Hayatu Sule ta hango Taj ta cikin ?ofar gilas. Kyakkyawan saurayi ne wanda duk hangen mace indai ta same shi ta sake Waga ido neman wani dole a sanyata a sahun marasa wadatar zuci. Yana kama da ?an uwansa amma akwai wani abu dake tattare dashi wanda ya bambanta shi dasu da take iya gani. Ba hasken fata bane domin wasu cikin ?an uwan nasa sun fi shi haske. Haiba da cikar halittarsa su ne suka fi komai Waukar hankalinta. Tana can duniyar sa?e sa?e bata kula da yadda ?an uwan nasa da ?a?ansu su ka bar wurin ba domin tararsa sai daga baya.

Idanu kansu su ka dawo ganin yadda ake pasin-pasin wajen rungumar Taj. Gashi taron mata don Ahmad da Kamal ne kaWai maza in ka cire jikokin gidan da ba wani sabo suka yi dashi sama da waya ba. Bishir da Abba su na makaranta.

"Aunty Salwa mu je mana."

Wani yaro ne ya yi maganar yana jan hannun matashiyar budurwar da Taj ya sacewa zuciya farat Waya. Murmushin jin kunyar kanta tayi ta kama hannun yaron su ka matsa kusa dasu. Yaron ya saki hannunta ya koma wajen Ahmad yana cewa ya Waga shi zai ga Uncle Taj.

"Daddy ni bai ganni ba. ?aga ni sama."

Kamal ne ya Waga yaron ya mi?awa Taj. Ya karSe shi ya rungume yana sumbatar kumatunsa.

"Babana da kansa."

Yaron ya girgiza kai "Uncle Taj sunana Hayat."

"Ba Hayatu ba?" Taj ya ce da alamun mamakin da yasa yaron saurin cewa "Hayat yafi daWi."

Dariya kowa yayi sannan Ahmad ya Wan turo budurwar nan gaba.

"Ga Salwa ku gaisa."

Taj ya sakar mata murmushi domin kuwa ?anwar yayansa Ahmad ce da su ka haWa uwa. A yanzu haka sakamakon karatu da ya kawota Kano daga Bauchi garin da mahaifiyar tasa ta sake aure shi ne take zaune a gidansa. Shekararta ta biyu kenan a Kano kuma iyalin Alh. Hayatu har matansa basu nuna mata wani abu da zai sosa zuciyarta ba. ?anwar Wansu ita ma ?arsu ce.

Shi Ahmad matarsa Waya da yara biyu. Hayat da ake kira da sunansa bisa umarnin Alhaji sai jaririyar da ko arba'in Winta ba ayi ba mai sunan Mama wato Aisha.

?unguma su ka yi a motoci huWu su ka nufi gida. Mazan motarsu Waya su kaWai. Kamal ya yiwa Taj bayanin cewa sun canja shawara zai zauna a gidan Ahmad har lokacin komawarsa.

Jikinsa a sanyaye ya tambaye su "Alhaji ya ce kada na zauna masa a gida ne?"

"A'a" Ahmad ya faWi da sauri.

"Yaya ka faWa masa gaskiya mana." Cewar Kamal dake tu?i "Soyewar bata da wani amfani."

"FaWa min me ya ce Happiness."

Tiryan tiryan kuwa Kamal ya faWa masa yadda Alhaji yaje Sangarensu har Waki ya ce yaga sa?on Taj na tahowa buWe gidan abinci. Ba zai hanasu mu'amala da Wan uwansu ba amma indai da niyyar cigaba da saSa masa ya dawo ya nemi wurin kwana.

"Amma ya amince ka shiga gidan ka gaishe da su Hajiya. Kawai dai kada ka bari ku haWu."

"Zan zauna a hotel."

Dukkaninsu kallonsa su ka yi. Ba kuma don abin da ya ce ba, yadda muryarsa ta fito kai ka san ba ?aramar dauriya ya yi ba. A sha?e take da wani irin rauni daga zuciyarsa.

"A gidana za ka zauna. Tun jiya nasa Salwa ta gyara maka Waki." Ahmad dake baya ya zura hannu gaban motar ya Wan bubbuga masa kafaWa.

"Ba zan zauna na takura iyalinka ba. Infact mutumcina ma zai zube. Kawai bamu taSa haWuwa ba sai da aka koreni daga gida for the second time."

Dariya Kamal ya yi "zaman hotel Win ba matsala bane amma ba mutumcin aljihunka bane gaskiya a garin da kake da gidan ?an uwa sama da hamsin da za su so zamanka tare dasu."

Kamar shi ya kar zomon, Taj ya Waure fuska ya ce masa "kawai ka faWi abin da yake ranka. Kana tsoron kada naje ace na fara bin mata ko?"

"Ba a ji mutuwar sarki a bakina ba, amma dai kai da kake kan tsini idan ka ?ara da kwanan hotel ban san yaya za ku kwashe da Alhaji ba."

"Allah ni ba Wan isk* bane. Saboda tsoron kada Alhaji ya yi min baki watarana na lalace ko girlfriend na kasa yi." Taj ya amsa defensively.

"Daga budurwa sai lalacewa Taj?" Cewar Ahmad, shi da Kamal su na dariya.

Shi kuma Kamal ya ce "dama me za kayi da busassun turawan nan da ba su da gaba da baya?"

HaSa Taj ya ri?e yana kallonsa kafin ya ce "Yaya kaji irin zancen banzan da Happiness yake yi ko? He is long overdue for marriage."

"Da za ku yi auren maybe da ka samu daidaitawa da Alhaji."

Hirar tasu sai ta koma ta dacewar Kamal da Taj su nemi mata su yi aure haka nan. Da haka su ka isa gida. Sai dai kafin maigadi ya buWe musu gate motar Alhaji ta tsaya a bayan tasu.

"Alhaji ne" Ahmad ya faWawa Taj.

Zuciyarsa ya ?arfafa ya fita daga motar duk da tunin da yayunsa ke yi masa akan gargaWin Alhajin na baya son ganinsa. Da sassarfa ya isa bakin motar da gilasanta duka ba?a?e ne. Ba a sauke ko Waya ba a ciki amma ya tabbatar daga cikin ana ganinsa. Direba ke tu?in motar amma da dishi-dishi yana iya hango Alhaji zaune a baya. Ya taka har bakin tagar Sangaren nasa ya dur?usa cike da girmamawa.

"Sannu da zuwa Alhaji."

Tun a hanya jikinsa dama ya bashi zai ga Wan nasa. Tunaninsa ne ma ya hana shi gama uzurin da ya fitar dashi. Yanzu da yake ganinsa kewar Taj Win ta mamaye zuciyarsa. Idanunsa su ka tara ?wallar da yake jin abin kunya ne a ganshi da ita. Saboda haka bai Sata lokaci ba wurin umartar direbansa da ya yi ribas su bar wurin.

"Alhaji ka daure ka saurari yaron nan don Allah."

"Koma na ce!"

Direba ya so yin musu Alhajin ya manta da dattijantakar mutumin ya daka masa tsawa. Wannan yasa shi danna accelerator bayan yasa giya a ribas da ?arfi. ?ura kuwa ta tashi ta baWe Taj da yake dur?ushe har lokacin bai motsa ba.

Ba shi ya tashi ba duk da magiyar su Kamal da wasu cikin matan da su ka riga su dawowa daga airport. Anyi a idonsu ne saboda an buWe gate. Kuma dama Kamal na yin horn su ka firfito tare da iyayensu.

Ahmad ne ya Waga shi zai shiga dashi gidan ya cije ?afarsa.

"Mu je gidan naka."

"Kaga su Umma fa a tsaye. Mu ?arasa ku gaisa sai mu tafi."

Kai a sunkuye Taj ya girgiza kai.

"Wallahi ba zan shiga gidan nan ba sai ranar da mai shi ya kirani ciki da kansa."

Motar ya kama zai buWe Kamal yayi saurin danna lock da mu?ullin hannunsa.

"Kada kayi taurin kai. Don Allah ka shiga ciki."

Kai Taj ya Waga ya hango Salwa a tsaye tare da sauran. Bai yarda ya haWa ido da kowa cikin matan gidan ba ya ?wala mata kira.

"Salwa..."

Gabanta ya faWi, zuciyarta tayi wani irin bugu. Sai kuma wani irin Wumi mai daWi ya lulluSe mata jiki da ta tuna sunanta kaWai Taj ya ambata a wannan yanayin da yake ciki. ?afafunta kusan da ikon kansu su ka ?araso da ita gabansa.

"Kai ni gidan Yaya a rickshaw (haka ake kiran adaidaita sahu a India)."

Alamun rashin fahimta ya gani a tare da ita ya nuno mata guda da ya shigo layin nasu.

Kai Ahmad ya girgiza domin hanata sannan ya umarci Kamal da buWe motar. Da kansa ya tura Taj baya ganin ?anin nasa ?iris yake jira ya saki ?wallar da ta rufe masa idanu.

"Kai shi gida zan taho."

Haka kawai ya ce da Kamal ya buWe gaba ya ce da Salwa ta Wauki Hayat su bi shi. Suna tafiya shi da sauran suka koma ciki.

"Korarsa ya sake yi?" Umma ta tambaya da kukanta.

"A'a. Ku shirya mu je gidana ku gan shi."

"Me ya faru Ahmad?"

Mama da Hajiya duka kuka su ke yi. Inna kuwa jingina tayi da ?ofar shiga gidan ta runtse idanunta. Da yake duk da mayafi su ka fito Ahmad buWe motarsa da ya bari a gidan ya yi ya ce su shiga.

"Alhaji zai yi faWa Ahmad."

Da mamaki mai haWe da Wimbin takaici Mama ta kalli Inna da tayi maganar baki buWe.

"Sau tari damuwar uwa da jajircewarta na taimakawa wurin ragewa ?a?a raWaWin hukuncin uba. Kina tsammanin akwai riba idan duka ku biyun kun juya masa baya? Ko kuwa kina ganin yin hakan wata gwaninta ce da Alhaji zai yaba?"

Umma dama tafi kowa zafi kuma maganarta indai akan gaskiya ne ba kasafai take taunata ba.

Jiki ba ?wari Inna ta ce "ba haka bane."

Umma ta ce "to yaya ne? Sama da shekara goma rabon da Wanki ya sanya ki a ido zahiri. Banda ma Allah Yasa Takwara (da yake haka su ke kiran juna da Amma) jajirtacciya ce da tuni Wannan ya bi duniya. Uwa da uba a raye amma kun bar masa wawakeken giSi mai wuyar cikewa. Baku san ku yabi ?o?arinsa ko kuyi masa faWan kuskure ba."

"Kiyi ha?uri don Allah" Inna ta ce tana kuka sosai.

"Magana ce ta gaskiya. Kin goyi bayan miji kun mayar da yaro marayan ?arfi da yaji. Yau ko Wan kafin Fatiha ya kawo muku gida wannan hukuncin ya yi tsauri, balle girki. Mene ne aibun girkin nan ne? Har mamakin ki nake yi idan kina sha'anin gidan nan kamar babu abin da yake faruwa."

"Jamila ya isa haka don Allah. Na tabbata tana da dalilinta na yin duk abin da tayi tunda ita tayi na?udar Taj. Ta fi mu son sa." Hajiya ma ta gwaSa tata maganar.

Kukan Inna ya sake tsananta da wannan rashin fahimta da abokan zamanta su ka yi mata. Ita fa tun lokacin da taga auren Mama yana girgiWi a dalilin Taj hankalinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login