Showing 105001 words to 108000 words out of 182745 words

Chapter 36 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

130

buWe kamfanin robobin. A wurinsa ma su ka ranci kuWin. Shi ne ya basu shawarar Wauko wanda ya yi boko sosai wato Alh. Mukhtar aka yi masa MD. Yana fara samu Mami ta sakarwa Ahmad mara. Babu wanda ya san maganar nan har yau.

"Ku kaini ofishinsa. Ina son magana dashi."

Da rawar jiki su ka yi gaba. Har yanzu akwai wajen kaso talatin da biyar na kuWin da ya ranta musu da basu gama biya ba. Hankalinsu in ya yi dubu to a tashe yake.

Sun isa ofishin MD inda Alh. Mukhtar na ganinsu shi ma ya tashi da rawar jikin ganin iyayen gidansa. Aka gaisa su ka zauna. Ya mi?owa Alh. Hayatu hannu yaga babu fuska ko alamar zai karSa. Ba shiri ya ja da baya.

"Wurinka Alhaji ya zo. Ka gane shi ko?"

"A'a" Alh. Mukhtar ya faWi da gaskiyarsa "sai dai fuskar kamar na san mai irinta."

Muryar nan ta Alhaji a dake ta fito ya ce "?ana Ahmad Hayatu Sule Maitakalmi ko?"

Idanu Alh. Mukhtar ya zaro "Alh. Hayatu? Kai ne? Ikon Allah."

?aya daga cikin Alhazan da su ka zo tare Alhaji ya cewa ya yi bayanin matsayinsa a garesu. Tiryan tiryan kuwa ya yi duk da sun cika da mamaki. Bayan ya gama kana ganin Alh. Mukhtar ka san ya gama rikicewa don gumin da yake ko ruwan sama albarka. Alhaji ya ce waWancan biyun su Wan basu wuri. Su na fita ya soma faWa.

"A lokacin matarka ta so sabauta rayuwar Wana. Shi yasa na ajiyeka a nan domin in kare Ahmad. To yau kuma an wayi gari taje tayi abin da ta saba tana neman shiga tsakanin wani Wan nawa da matarsa." Ya yi maganar cikin Waga murya.

"Alhaji ban sani ba wallahi..."

"Ta yaya za ayi ka sani bayan kaima juyaka take yi?"

"Kada kasa su koreni. Ina da ?a?a wallahi." Ya ce hankalinsa na neman gushewa.

"Ka ce ni Hayatu na ce ta karya asirin. Ita ko wani nata sun yi kaWan su tarwatsa rayuwar zuri'ata. Taj ba Wanta bane. Idan na ?yaleta akan Ahmad saboda ha??in uwa ne. Amma muddin ta sake shiga rayuwar wani nawa wallahi sai ta WanWani kuWarta. Ni da kake gani kaza ne akan ?a?ana. Ina iya taka abuna idan sun min ba daidai ba domin su gyara. Amma idan wani ya kamanta zai sha tsatstsaga har sai anga jini. Ina fata ka fahimceni."

Jikin Alh. Mukhtar babu inda baya rawa. Bai taba ganin mutum mai ban tsoro da kwarjini kamar Alh. Hayatu ba.

"Na gane. Don Allah ka yi ha?uri."

Alh. Hayatu ya tashi "ina son ganin canji a tattare da Taj kafin sati mai zuwa. Ta karya koma me tayi don ta sanni farin sani. Akwai irin abin da bana yafewa. TaSa min ?a?a yana sahun gaba. Sannan ka tashi tsaye kamar kowanne magidanci ka nemi tsari daga sihirice sihircen marasa tsoron Allah."

Ko kallon Alh. Mukhtar bai sake yi ba ya fita. A waje ya yi sallama da alhazawan nan ya kama hanyar Kano ko ruwan garin bai sha ba. Sallah kawai su ka yi su ka tafi.

***

Abu na maza, babu wanda ya yi tunanin raini ko surutu akan gidan Abba Habibu. Irin abin da mata za su yi ta gutsiri tsoma ana cewa me ya kai shi auren wadda bata kama ?afar arzi?insa da na iyayensa ba. Ahmad da Kamal sun zo. Sai ?anin Inna da kuma ?annen Alhaji guda biyu. Irin tarbar arzi?in da Abba ya yi musu ba ?aramin daWi su ka ji ba. Sun riga sun san ko waye, ba a Soyewa kowa ba. Ga amininsa Baba Maje, sai ?aninsa Abdul?adir da wasu ?an uwansu maza da su ka lallabo su ka dawo rayuwarsa bayan ganin luWufin da yake samu.

Abinci ne na gani da faa su ?ar Ficika su ka yi. Kuma kamar yadda ya yi al?awari tuntuni ko hanyar gidan basu zo ba shi da yaransa. Baba Maje ya yi rawar gani ya kawo dubu ashirin a bayar tukwici. Abdul?adir ma ya kawo sha biyar. Abba ya cike ya zama hamsin. ?an kawo lefe kuma su ka ?i karSa. Sai da Abba ya ce rainawa su ka yi saboda sun gan shi a haka. Ba shiri su ka karSa aka rabu a mutumce.

Ko rabin awa basu yi da tafiya ba gidan ya soma cika da ?an kallon kaya. Gashi Zee bata nan. Sajida ce kaWai take ta fama. Sai ga Iyaa ta zo da Siyama da Ummi. Ta kuma umarcesu da taimakawa Sajida wajen saka ido akan kayan da kuma aikin buWewa mutane.

?iris ya rage Ummi ta haWiyi zuciya ta bar duniya. Dama Baballe ne ya taho dasu a motarsa. Dolenta ta taho. Yawan akwatunan da irin kayan da ta gani ya birkita mata lissafi. Zuwa yanzu ma dai sakin aure ya kamata su ji anyi. Maimakon haka sai wannan uban kaya kamar za a buWe shago. Dole ma ta kira Salwa idan sun koma gida.

Abin ba?inciki yadda Iyaa ta Wora mata aikin kula da wata ?aramar jaka da aka sha?are da sar?o?in gwal, awarwaraye, zobba da kuma sar?o?i na fashion masu matu?ar tsada. Sai da Iyaa ta ?irga komai harda sanya Siyama Wauka a hoto sannan ta mi?a mata.

"Ko kwali ne ya Sata to ku Sata tare. Ki kula dasu sosai. A nunawa mutane arzi?in Hamdi amma a kula da masu Wan hali da mahassada."

Ummi za ta iya rantsuwar maganar mahaifiyarta da harshen damo ta fito. Bata sani ba ko tsagwaron ba?incikin da take ji a zuciyarta Iyaa ta gani. Haka nan ta karSi jakar ba don tana so ba. Irin ba?incikin da take ji ba wai so take ta mallaki kayan ko ta sace ba. Ita da ace za su Sace ko su ?one ?urmus Hamdi ta rasa da ko miliyan biyar aka dam?a mata ba za ta yi farinciki kamar haka ba.

*
Bayan tafiyar Alh. Hayatu, karatun ta nutsu Alh. Mukhtar ya yiwa kansa. Ya dinga haWa Waya da biyu yana lissafin yadda yake aikata abubuwa da yawa bisa umarnin Mami kuma ba a son ransa ba. Ya yarda hannunka mai sanda Alhaji ya yi masa da zancensa na ?arshe. Ji dai maganar Taj Win da ta ce dole ya auri Salwa. Gashi takanas akan yaron mahaifinsa ya zo ya yanka masa gargaWi mai kyau.

Rasa tudun dafawa yayi ya kira babbar ?arsa da wani tunsni ya zo masa. A gidan take shekara talatin da huWu duk wanda ya zo da maganar aure da kansa yake gudu. Ita da duka sauran ?an matan gidan su huWu da samari biyu babu uwayensu mata biyu da yake aure kafin zuwan Mami sun fita ta ?arfin tsiya. ?a?an Mami a gidan huWu ne. Salwa da ?annenta maza biyu.

"Bushra ki ce da Mami wai na kira ban sameta ba. Kowa ya fita daga gidan zan turo mai feshin maganin sauro. Ke kuma ki zauna ki jirani. Idan akwai aikin yi ko share share bayan an gama sai ki yi."

Sa?on nasa ta faWawa Mamin da umarninsa na ta zauna tayi aiki. Mami ta saki murmushi. Yadda ta farra?a shi da ?a?an yana burgeta. Gashi yau ko tishin tauna layar bata yi ba amma ya aikata da kansa. Salwa ta kira su ka fita. Samarin dama basa nan. Ita kuma Bushra ta sanar da ?an uwanta duk su ka tafi ma?ota. Ba a jima ba Alh. Mukhtar ya dawo.

"FaWa min gaskiya Bushra, Mami tana da kayan asiri a gidan nan?"

Rawa jikinta ya fara. Idanunta su ka ?ara girma don tsoro da firgici.

A ?agauce ya ce "Ba mu da lokaci. Ki faWa min idan akwai."

Kai ta gyaWa. Ya ce idan ta san inda su ke maza ta nuna masa.

"Ban sani ba. Sai dai mu duba."

Babbar rigarsa ya ajiye a kan kujera ya ce ta saki jiki su yi aiki da sauri. Ai kuwa yaga zafin nama. Duk gidan sun gaji da rayuwar da Mami ta ?a?aba musu.

?akin Mamin suka fara zuwa. Yana karanto surorin neman tsari ya watso duka kayan cikin wardrobe Winta da kowacce durowa. Sun tsinci ?ulle ?ulle da wasu ?warya da tarkace guda biyar. Aka koma ?asan gado nan ma akwai. Daga nan sai Wakinsa. Abu ya ?azanta. Kansa har ciwo ya dinga yi saboda tashin hankali. A Wakin ?aran gidan ne dai ba a sami komai ba. Kitchen ma Bushra ta nuna wani ruwa da ta kan ga Mami ta tsiyaya musu a girki. Ya Wauka ya tuttular. Kit Winta inda take ajiye abubuwa masu mahimmanci ya Wauka ya mu?a da ?asa sai gashi ya buWe. A nan ya tsinci laya mai sunansa da ake taunawa. Sai kuma masu sunan duka ?a?ansa banda nata. Da kuma sababbi a leda Waya Taj, Waya Zainab (Inna).

"Wallahi Baba wannan take sakawa a baki ta ce kayi mana abu kuma sai kayi. Ko ranar da ka ce in na kuma fita zance za ka tsine min da ita tayi magana."

Ha?uri ya bawa ?ar tasa. Ya rasa matakin Wauka na gaba. Ita ta bashi shawarar su ?ona komai. Ya ce kada ta taSa. Da tsintsiya da abin kwasar shara ya tattara komai ya tara a tsakar gida. Ya kawo fetur ya zuba sannan ya kira Mami ya ce su dawo.

"Har maganin ya fita?"

"An fasa, sai gobe."

Masifa ta yi masa na katse mata baccin yamma sannan su ka taho gida. Ana buWe musu gate ta hango shi daga shi sai ?ar shara a jikinsa ya sanya wasu tarkace a gaba. Su ka fito daga mota ta taho inda yake. Jikinta ne ya saki lokaci guda da ta gane mene ne a gabansa.

"Alllll....hhhhajjii? Mmmmene nee wannnnan?"

HaWe rai ya yi sosai ya tura mata ashana da ?afarsa.

"?auki ki cinna musu wuta."

Jikinta rawa ya kama yi sosai. Tana ta gumi ta rasa abin yi.

"?auki mana!" Ya daka mata tsawa.

Ta kasa motsi sai ?ullewar ciki. Salwa da taga halin da babarta ta shiga ita ma tsorata tayi. Tunda bata san kayan mene ne ba dur?usawa tayi ta Wauki ashanar.

"Baba ni bari na ?ona."

Kafin Mami ta iya tare ta har ta ?yasta ashana. Tana cillawa kuwa kayan nan su ka yi wata mahaukaciyar ?ara tamkar tashin gurneti. Mami tayi zaman daSaro a ?asa tana ihu.

"Kin kashe ni. Salwa kin kashe gidan nan."

Da faWa Alh. Mukhtar ya ce "ta dai kashe ki ke kaWai banda gidana."

"Mami kayan meye?" Salwa ta tambayeta ganin kuka take hai?an. Bata sami amsa ba sai daga bakin babanta.

"Nagodewa Allah da Ya turo Alh. Hayatu gareni ya farkar dani mugun baccin da nake yi. Sai yau na gane ashe zaman waWannan abubuwan muke yi ba aure ba."

Mami kuka kawai take yi da gurnani. Hankalinta ya kai ?arshen tashi. Idan ya saketa bata da tudun dafawa. A zaune ta ja jiki zuwa inda yake za ta kama ?afarsa ya janye da sauri.

"Ka rufa min asiri."

"Ki rufawa kan ki dai" ya dubesu ita da Salwa dake tayata kuka "yauwa, Alh. Hayatu ya ce in faWa miki ki warware abin da ki ka yiwa Wansa har su ke rigima da matarsa. Idan ba haka ba kuma ki jira martani daga gare shi." Ya wuce ciki.

Mami ta zauna tana tumami da kuka kafin ta tashi ta bishi ciki da sauri.

"Wane Wan? Taj? Wallahi ban yi masa komai ba."

"Ki daina saurin kama sunan Allah tunda baki san shi ba. Da idona naga laya da sunansa."

Mami ta kwantar da murya "Ayyaaa Alhaji, bamu yi amfani da ita ba. Dama na ajiye ne sai sun yi aure da Salwa. Ai ban baki ba ko...."

Ta juya babu Salwa babu dalilinta.

"Salwa? Alhaji ina Salwa?" Tayi maganar kamar wata zararriya. Tsoro take ji kada ?ona kayan nan ya janyowa ?arta wani abu. Don dai tabbas malaminta ya sha yi mata kashedi akan kada ma wani ya gani balle a taSa.

?akunan gidan ta duba bata ganta ba. Tayi wajen gate tana faman kiranta ko kallon titi bata yi. Bata yi aune ba mota ta Webe ta tayi sama ta dawo. Maigadin Alh. Mukhtar da ya biyota yana son faWa mata Salwan ta fita ne ya koma ya sanar dashi abin da ya faru. Ya fito su ka wuce asibiti tare da mai motar da ya bugeta.

Salwa kuwa tunda taji sa?on babanta hankalinta ya tashi. Indai Alhajinsu Taj ne ya yi waccan maganar kenan asirin ya kama su. Matsalar kawai tunda ake zargin Mami a hankali zsi gano ita ce. In haka ta faru kuma zai hana Taj aurenta idan su ka fara soyayya. Tasha ta wuce tunda da atm a jikinta ta ciri kuWi sai Kano. Wurin Ummi za ta je ta taimaka mata da wanda za a rufe bakin Alhaji.

Motarsu ko fita gari bata yi ba Alh. Mukhtar ya kirata ya faWa mata abin da ya sami Mami. Don ba?inciki sai da tayi kuka. Haka ta sauka daga motar ta tafi asibiti.

***

Mai shawara aka ce aikinsa ba ya Saci. Duka abubuwan da Inna ta sa Taj yi ya rungumesu hannu bibbiyu. ?uncin zuciyarsa ya ragu sosai. Duk da ya kan ji haushin Hamdi yana taso masa lokaci zuwa lokaci tunda fitar asiri sai a hankali, amma a zuciyarsa ya sani cewa ba zai taSa iya rabuwa da ita ba kamar yadda ya dinga ji a kwanakin baya. Banda yawan addu'a, Inna ta sa yanzu ya ware plate goma na abinci kullum sai sun bayar sadaka. Ba wai ragowar na mutane ba. Mai kyau da an gama dafawa ake packaging. Ranar farko ma na mutum Wari biyu su ka yi aka kai asibitin gwamnati. Kusan zai rantse ma daga ranar ya fara jin canji sosai. Ciyar da mabu?ata ba ?aramin abu bane.

Duka wani jere da gyaran gidan amarya an gama shi a farkon sati. Duk wanda ya shiga kamar kada ya fito. Hatta kayan da za su saka Kamal ya kai wa Hamdi nata ana jibi fara biki. Bayan ta shiga gida ta gwaggwada ta dawo ta same shi. Ta faWa masa babu wanda yake bu?atar gyara. Sai kuma tayi godiya sosai.

"Yanzu yaya kike ji game da Wan uwana?"

Kai ta sunkuyar tana murmushi. Da ya sake yin tambayar ta ce "Alhamdulillah."

"Kina ganin faWa ya ?are? Za ku iya zama babu tashin hankali?"

"Ban sani ba ko daga wurin shi." Ita ce amsar da ta bayar da ?aramar murya.

"Nayi magana da shi. Ke nake tambaya kuma."

Kunya ce ta isheta ya ce gara ma ta daina domin tunda ta shigo danginsu ta sani cewa bayan shi yanzu ta sami ?arin ?an uwa. Kuma kowa zai tsaya mata idan Taj ya yi nufin cutar da ita.

"Zan iya in sha Allah."

"Alhamdulillah. Kamar yadda na faWa masa ku bi komai a sannu. Kada ku ce dole a yau ko gobe ku ke son ganin ala?arku ta dawo kamar da. Wannan zai janyo muku too much expectation, wanda kuma rashin samunsa zai sa ku zama disappointed."

"In sha Allah zan kiyaye."

"Hamdiyya"

Mrs Happy ya saba kiranta. Shi yasa Hamdiyyar ya faWar mata da gaba.

"Na'am Ya Kamal."

"Don Allah ki ri?e min Taj amana. Abubuwa da yawa sun same shi. Yana bu?atar inda zai sami kwanciyar hankali."

?an murmuhi tayi "ai kana nan Ya Kamal sai mu dinga shawara. Ka fini sanin abin da ya dace da shi."

Murmushin da Kamal ya mayar mata mai matu?ar rauni ne. Da ace idanunsa ma take kallo za ta ga sun kaWa.

"Yanzu ke ce mafi kusa dashi."

"Ba zan shiga tsakaninku ba in sha Allah" ta faWi da sauri.

"Rayuwa da yau da gobe za su iya shiga. Ni dai na baki amanar Happy. Please Hamdiyya, give him the happiness he deserves."

Har ya tafi tana juyayin maganganunsa masu kama da sallama. Anya lafiya kuwa?

***

Idan ka ji yara na wa?ar gobe Juma'a, kuturu dariya yake ko zai sami Wan kwabo to lallai ranar ta kama Alhamis. Ta wannan satin ita ce ranar Kamun amarya Hamdi wadda iyayen ango Taj su ka yi rawar gani wurin tsara taro na burgewa. Biki ne na ?an kasuwa kuma ?an boko. In baka yi bani wuri. Sun tsara abinsu na yau ma mata kawai. Mazan gidansu ko mutum Waya ba a yarje masa zuwa ba. Daga DJ Winsu kuwa har mai hoto da MC duka mata ne. Daga cikin wani katari da Alh. Hayatu ya sake yi a rayuwa harda dacewa da kyakkyawar tarbiyar ?a?ansa akan sunnar Fiyayyen halitta SAW. Ba dai a rasa nono a ruga, wani dole sai ya bauWe. To amma dai majority a gidan sun ginu da wannan tarbiyar ta iyayensu mata. Wannan yana daga cikin dalilan da su ka sa Alhaji ya kan kasa yiwa wanda ya kuskure uzuri. Shi fa kusan komai Allah Ya bashi. Bai san wani nau'i bane na gwajin rayuwa. Idan ya ?an?antar da kai ya yarda rahama ce daga cikin taskar Ubangijinsa sai Allah Ya ?ara masa da lada mai gwaSi. Idan kuwa girman kai da jin cewa isarsa da iyawarsa ne su ka bashi kamar yadda ya tsinci kansa yanzu, to dama Allah barin mutum yake da iyawar tasa.

?arfe Wayan rana mai kwalliya ta zo ta fara rangaWawa Hamdi bayan tayi sallar azahar. Jiki ya sha gyara na gaske saboda haka in ka ganta sai ka ?ara kallo. Ga ?amshi wanda da kanta ta ce a bar turara mata jiki haka nan saboda kada ta fara Waukar zunubi a cikin mutane.

Tana idar da sallar la'asar ta saka kaya aka Waura mata ashoke. Da ta fito daga Waki Yaya tashi tayi ta bar wajen. Bata son kowa yaga ?wallar da ta cika mata idanu. Yau ita ce Allah Ya nufi ?arta da auren gata irin wannan. Da bikin Sajida abin bai yi armashi sosai ba saboda tangal tangal da auren ya soma yi tun kafin a Waura shi.

Leshi ne haWaWWe mai laushi aka yi mata Winkin gargajiya wato buba da zani. Ado da kyan leshin kaWai sun wadata ba sai an Sata Winkin da tarkace ba. Ruwan toka ne da adon ja kaWan a jikin zare sai navy blue Win fulawoyi. Ta ri?o jar ?aramar jaka ta amare tana kuma sanye da jan takalmi mai tsini da maWauri. Ashokenta na ka da na kafaWa navy blue da silver. Sai wata dan?areriyar sar?a mai duwatsu navy blue su ma da ja. Make up Winta na hankali bata koma aljana a kwaba ba.

A tsakar gidan aka tsaya ana ta Wauke Wauken hotuna da ?an uwa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login