Showing 63001 words to 66000 words out of 182745 words

Chapter 22 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

90

?an mata. Ka san mu masu auren nan komai mun sani."

"Daga Waurawa? Ka rufa mana asiri dai kada ?ar mutane ta tare da ciki."

"Sai kace wani namamajo" Taj ya sha kunu.

"Da meye?"

Da irin wannan faWan nasu na wasa su ka isa gidan Abba. Idan ka kallesu sau Waya dole ka ?ara. Alhaji ya tara arzi?i a gidansa. Ba mazan ba, ba matan ba. Shi kan shi ya san wannan.

Waya Taj ya yiwa Abba bayan sun fito daga motar. Ba a jima ba kuwa ya fito da shirinsa harda babbar riga.

"Ko shigo ciki ku gaisa da mutan gidan mana. Dama can an zama Waya balle kuma yanzu. Kuma mazajen ?an uwanta ma sun zo. Sai ku san juna ko." Ya nuna ?ofar yana murmushi.

Bayansa su ka bi Taj yana sunne kai shi a dole ya shiga gidan surukai. Kamal ya faki ido ya Wauke shi a hoto ya adana domin duk ranar da ya bashi haushi ya tura group Winsu na gida.

*

Hamdi na zaune da waya a hannu tana jiran kiran Taj a Wakin Halifa ita kaWai. Falonsu kuma Safwan ne da abokansa biyu. Sai kuma Baballe da iyayensa. Ga Yaya da amare Sajida da Zee. Tsakar gidan kuwa ?an uwa ne na kurkusa su ke ta aikin kayan miya na girkin gobe saboda sun san dole a sake zuwa kafin ?an Waukar Sajida su zo. Musamman waWanda basu ji auren Hamdi da Zee da wuri ba.

Abba ya shiga falon da sallama aka amsa. Taj da Kamal su ma su ka yi. Yaya jan mayafi ta ?ara yi. Bakinta har kunne. Duk yadda take son nuna kunyar surukai abu ya gagara. Allah Ya gatance mata a lokacin da bata yi zato ba.

Musabaha su ka yi da duka mazan. Sannan su ka gaisa da Iyaa da Yaya. Abba ya sake gabatar musu da juna.

"Safwan ai ka san Taj ko?"

Safwan ya yi murmushi "sosai Abba. Tun kafin ya dawo ma ta haWa mu. Abokina ne ko in ce Wan uwa ma."

Sajida ta sunne kai tana murmushi. Safwan Win dama Wan ayi ne na gaske.

"To ina jin duka dai Baballe ne baku sani ba. Sunansa Abubakar kuma Wan amini na ne."

Baballe ya taso ya sake basu hannu.

"Ni ne dai Wan autanku. Ina fata zamu yi zumunci mai Worewa."

Iyaa taji daWin yadda Wan nata ya yi. Sai da ta yi dariya da Safwan da Taj su ka ce sun Wauki girman. Aka Wan yi raha sannan Baba Maje ya juya dama da hagu.

"Ina Hamdiyya ne? Mijinta ya zo ba za ta le?o su gaisa ba?"

"Yi maza ki kirata Zee." Iyaa ta faWi ganin Yaya ta sunkuyar da kai.

A Wakin Halifan ta sameta. Ta rasa gane zaman me take yi ita kaWai bayan ta nuna musu ita bata da damuwar auren.

"Ki zo ku gaisa da Ya Taj. Amma ki yi sauri don fita za su yi da Abba."

Kafin Zee ta gama magana ta fice da ?aton hijabin da tayi sallar magariba. Falon ta shiga da sallama. Idanunta Taj su ke nema. Shi ma kuma ?ofar yake kallo. Su ka haWa ido ta kasa yakice nata.

Tabbas Taj ne mafarkinta, amsar addu'arta kuma zaSin zuciyarta. A wannan Wan ta?aitaccen kallon makaman ya?in neman sakin su ka fara saukowa ?asa da kansu. BuWar bakin Inna Luba da shigarta falon kenan sai cewa tayi.

"Mu dai Tajo idan mun zo Wakin amarya ba girkinta za mu ci ba. Ranar zagewa za ka yi ka girka min don ni ce da gidan ba ita ba."

Dawowa daga duniyar da taso mantar da ita waye Taj tayi. Ta kuwa tura baki tana kumbure kumbure. Shi kuwa dariya ma ta so bashi. Yana ta lura da rikicikin yanayin dake bayyana a kyakkyawar fuskarta. Wani irin farinciki na shigarsa. Wannan yarinyar matarsa ce. Bai san lokacin da ya yi murmushi ba.

"Ku je daga soro ku gaisa mana kafin Habibun ya fito." Baba Maje ne ya yi maganar. Hamdi bata Sata lokacin bin umarninsa ba saboda son samun damar yiwa Taj magana.

Ita ta fara zuwa soron kafin ?amshin Taj ya yi masa iso. ?asa ta dur?usa da ya shigo don so take kawai a yita ta ?are yanzu.

"Ina wuni Ya Taj?" Ta furta cikin sabon salon ladabinta gare shi.

"Lafiya ?alau. Tashi mana."

?in motsawa tayi "dama ha?uri nake son baka akan rashin kunyar da nayi maka rannan. Don Allah ka yafe min. Wallahi ba hali na bane."

'Irin wannan ladabin na neman bu?ata ne' Taj ya ayyana a ransa. A fili kuwa cewa ya yi "ya wuce. Nima ki yi ha?urin abubuwan da na ce miki."

"Babu komai wallahi." Ta ce da murmushinta.

"Uhmmm, dama...na ce...dama...wai ko za ka...uhmmm" ta dinga in'ina saboda kalmomin sun ?i haWuwa.

Shi yasa ta so su yi maganar a waya. A haka duk yabi ya yi mata kwarjini. Kamal ne ya fito a lokacin.

"Happy ga Abba nan. Ya ce kada lokaci ya ?ure."

Taj ya dubeta. Duk tayi laushi. Fuskarta kuma tayi fayau da alama tayi kuka.

"Zan kira ki in sha Allah. Kamar ?arfe nawa ki ke kwanciya don kada na tashe ki?"

"Zan jira ka. Don Allah ka kira."

"Okay." Har zai fita yaji ya dace ya Wan bata assignment Win da zai sa tayi tunaninsa ko bata so "aapna khayal rakhna."

Ai kuwa a take ta Winke fuska. Taj ya kalleta ya saki murmushi. A babu yadda ta iya dole ta mayar masa tunda tana da bu?ata a wajensa. Da ta koma ciki maimaita kalmar kawai take yi tana addu'ar kada Allah Ya kawo ranar da zai zage ya yi rawa da wa?a kuma.

***

Kamal ne ya sanar da Alhaji zuwansu. Daga nan ya yi tafiyarsa Waki. A gajiye yake sosai. Ga wata yunwa da bai ma san yana jinta ba sai da ya shiga gida. Agogonsa ya kalla bayan ya cire. Ya san a ?alla yana da minti shabiyar kafin su gama tattaunawa. Don ba zai iya baccin ba tare da sanin me zai faru da ?aninsa ba.

Ledar wasu magunguna ya Wauko daga ?ar?ashin gadonsa. Ya Salli iya wanda yake bu?ata ya zuba a wata ?ar roba sannan ya fita zuwa cikin gidan domin samun abin da zai ci.

A waje kusa da gate inda Taj ya yi parking Alhaji ya zaSi ganawa dasu. Gashi dare ne. Kuma lokacin zafi. Sannan wurin akwai shuke shuke. Saboda haka sauro ya far musu. Abba ya lura Taj a takure yake.

"Da ka sani ka barni na taho ni kaWai Taj. Yanzu haka ma Alhaji yana iya jin babu daWi in ya ganmu tare."

"Idan ka Sata amaryata ba za ta yafe min ba." Salati ya kama a jejjere "Abba tuba nake. Ba da kai nake ba."

"Kaji nayi magana?" Dariya su ka yi tare.

"Abba ko mu koma mota ne? Sauron nan yanzu sai ya tayarwa mutum da maleriya."

"Kai Taj, maleriyar ma tashi take?"

Da gaskensa ya ce "ni dai tawa tashi take. Tunda na dawo bana jimawa ban yi zazzaSin nan ba."

Da damuwa Abba ya ce masa "kayi a hankali. Ba a sakaci da lafiya. Mataki za ka Wauka don shi dai sauro bai san mutumci ba."

Dariya su ka sake yi a lokacin da Alhaji ya doso inda su ke. Ya kuwa murtuke fuska saboda ba?inciki. Yaushe rabonsa da hira da Taj wadda za ta saka su dariya haka? Ya ma rasa da wanda zai yi sai Habibu.

Du?awa Abba ya so yi tunda ya fuskanci Alhaji na ?yamar taSa shi sai Taj ya taro shi da sauri.

"Ai kun gaisa Wazu."

"Yawan gaisuwa ai yafi yawan faa Taj." Abba ya ce sannan ya dubi Alhaji "barka da dare Yaya Hayatu."

"Hmm" kawai ya ce daga ma?oshi a matsayin amsa sannan ya ce Taj ya basu wuri.

Ba don ya so ba ya tafi. Zuciyarsa tana ta fama da wasiwasin kada ya barsu Alhaji ya sake yi masa abin da yafi na Wazu.

Gyaran murya ya yi bayan tafiyar Taj ya yiwa Abba duba na ?yama.

"Habibu!"

"Na'am" ya sadda kai yana sauraronsa.

"Ina son Tajuddin. A cikin ?a?ana ma ban haWa ?aunarsa da ta kowa ba. Abin da ya shiga tsakaninmu har na kore shi bai rage min son abuna ba."

Murmushin jindaWi Abba ya yi "Alhamdulillah. Allah Ya ?ara kawo muku daidaito."

"Daidaito kam ana gab da samu sai ka zo ka shiga tsakani."

Hankalin Abba tashi ya yi sosai. Taj bai Soye masa komai game da rabuwarsa da mahaifinsa ba. Da kuma burinsa na son ya dawo gida kamar kowa.

"Indai don ina aiki a gidan abincinsa ne wallahi zan ajiye...kai na ma ajiye. Ba zan so na zama sanadin sabunta Saraka tsakaninku ba."

Wani irin murmushi Alhaji ya yi "idan ka bar aikin ma zai maye gurbinka da na wani. Bani da matsala da aikinka."

Fahimta ce ta Warsu a zuciyar Abba. Ya dubi Alhaji a firgice.

"Hamdi? ?ata ce ba ka so tare da shi?"

"?warai." Ya amsa idanunsa na kallon sararin samaniya.

Auno halin da Yaya za ta shiga ya yi. Jikinsa ya soma rawa.
" Ka taimaka min Yaya Hayatu. Wallahi nayi musu tarbiyya bakin gwargwadon iyawata. Duk da ni na haifeta amma na sani bata da wani aibu na halayya sai abin da ba a rasa ba na ajizancin Wan Adam."

"Ita kuwa take da aibu tunda kai ne ubanta." Ya haWe rai "Habibu, na baka wata uku ka kashe auren nan. Cire zuri'arka daga jikina shi ne kaWai abin da zai sa na dawo da Taj gidana. In har da gaske ka damu da shi ba za ka bari rayuwarsa ta ?are a bin gidan ?an uwa idan yana son ganawa da mahaifiyarsa ba."

Duk dauriya sai da yaji ?walla na neman zubo masa.
"Me yasa ka yarda aka yi auren?"

"Saboda banga alamun idan na?i zai ha?ura ba. Ka riga kayi tasirin da maganarka tafi tawa a wajensa. Zai iya yin komai domin fitar da kai kunya a yadda ya zo min."

Gumi sosai Abba ya dinga yi. Allah Ya sani yafi jin Yaya akan Hamdi. Wannan tsananin farincikin da ta shiga idan ya koma ba?inciki kamar ba za ta iya Wauka ba. Mutane da yawa za su yi musu dariya. Wadda za ta fi yi mata ciwo kuwa ta ?an uwanta da su ka haWa uba ce da ta mahaifin nata da har yanzu yake aibata halittarta da aurenta da an daudu.

Ya sake kallon Alhaji sai dai babu wata fuska ta yin magana. Magana Waya Alhajin ya ?ara yi masa kafin ya koma ciki.

"Ina fata za ka nuna dattako ka ri?e maganar nan tsakaninmu. Dabarar kashe auren tana hannunka. Ni dai kawai nan da wata uku magana ta ?are."

"In sha Allahu."

Jikinsa rawa ya dinga yi shi yasa ya kasa komawa motar har sai da Taj ya fito. Kafin ya ?araso Abba ya yi composing kansa.

"Yau dai na shanyaka da yawa. Muje kada dare ya ?ara yi."

Kasa ha?uri yayi ya tambaye shi "Babu matsala ko Abba? Me ya ce maka?"

"Ban sanka da haka ba Taj. Tattaunawa ce dai ta yaushe gamo da kuma rashin jindaWinsa da bamu tuntuSe shi da maganar auren ba sai a makare."

Kallon rashin yarda Taj ya yi masa. Sai dai Abban ya toshe duk wata ?ofar da zai fahimci matsalar. Sun kama hanya za su koma motar Taj yaji Kamal na kiransa. Da ya juya sai yaga Inna tare da Kamal Win.

Fuskarsa ta haskaka da wani irin annuri. Ya ce da Abba "Innata ce."

Kamal juyawa ya yi bai biyota ba. Ta ?arasa kusa da gate Win. Idanunta cike da ?walla. Taj kuwa tuni ya yi laushi don ya kwana biyu sai dai su gaisa a waya.

"Baki kwanta ba?"

"Ina fa. Ina ta fakon shigowar Alhaji ne idan kun gama." Sai kuma tayi murmushi "ango ka sha ?amshi."

Dariya ya yi ya rungumo kafaWarta. Ba shiri ta ruWe tana fama ture shi gami da waigawa don kada a gansu.

"Ga Abba...surukinki."

Abinka da sabo. ?asa ya yi zai gaisheta.

"Subhanallahi. Haba don Allah. Tashi mu gaisa. Ai mun zama aya kuma."

Duk da bata so amma a mutumce su ka gaishe da juna. Yana ta bata girma.

"Da farko zan fara da baka ha?uri don nayi imanin ko me Alhaji ya faWa maka ba mai daWi bane. Sannan don Allah kada ka wahalar da kanka wajen yiwa ?ata komai. Tunda ka iya bawa yaron nan ?arka in sha Allahu ba zan bari ta kuka da komai ba. Nagode da karamcinka a garemu."

"Ikon Allah. Hajiya ai nine da godiya da Taj bai ?yamaci zuri'ata ba."

"Wanda ya baka ?a ai ya gama maka komai." Ta faWi tana murmushi "idan babu damuwa ina son ya kawo mana ita cikin sati mai zuwa. Zan karSi numbar mamanta mu yi magana kafin na zo. Ka san Alhajin naku sai da lallaSawa."

Murmushi ya yi shi ma "kada ki damu. Hamdi ?arki ce kuma ikonki. Ina ?ara godiya."

Taj ma godiyar ya yi mata. Abba ya dubi uwa da Wan su ka bashi tausayi. Me yafi wannan ciwo ace uwa tana son ganin Wanta amma sai dai ta saci hanya ta fito kamar mai laifi? Dole zai san yadda ya yi da Yaya da Hamdi a raba auren cikin lumana.

***

Har ?ofar gida Taj ya kai Abba. Su ka yi sallama ta girmamawa. Taj yana ta sake tambayarsa ko babu matsala game da ziyarar da su ka kaiwa Alhaji. Shi kuma ya tabbatar masa babu komai.

"Gobe in sha Allahu zan tafi Abuja. Idan komai ya tafi yadda nake so ba zan wuce kwana biyu ba in sha Allahu."

"Kada ka damu. Happy Taj zai tafi kamar kana nan da yardar Allah."

"Ba manufata ba kenan" Taj ya faWi yana sosa ?eya "dama akan ..."

Gira Abba ya Wage gira "matarka ko? In turo ta ku yi sallama ne?"

Da sauri Taj ya koma mota yana ta dariya shi ma Abban ita yake yi. Da gangan dama ya yi tsokanar don kawai ya kawar da damuwar da yake gani a tattare da shi tun a gidansu.

Hamdi na jin shigowar Abba ta le?o yi masa sannu da zuwa. Ya kalleta ya kalli Yaya da ita ma fitowar tayi da sauri.

"Suruka da matar Taj jiran me kuke yi min ne?"

"Jin inda magana ta kwana mana." Cewar Yaya.

Ita kuwa Hamdi wayancewa tayi ta gudu. ?akinsu ta koma amma akwai mutane. Sai ta zaga bayan gidan amma bata yi nisa ba. Ta zauna akan wani bulo ko tsoro bata ji ta kira Taj.

Murmushi ya yi da call Win nata ya shigo. Ko tada motar bai yi ba don ya tsaya duba wani sa?o a waya. Ya bari sai da ta gama ringing sannan ya kirata.

"Za mu iya magana yanzu?" Ta furta a hankali bayan ta kuma gaishe shi.

"Yes."

Raba kanta tayi da dogon tunani ta faWi abin da ya kamata duk da ba shi bane ranta yake so.

"Dama cewa nayi tunda Ya Sajida tayi aure namu ba dole bane ko? Kada ka takura kanka saboda gidanmu."

Kamar bai fahimceta ba ya ce "Ban gane ba. Wani abin ne ya faru?"

"Uhmmmm. Dama wai ko za ka sakeni" tayi saurin ?arawa da "tunda ba sona kake ba. In aka ce dole ka zauna dani za a shiga ha??inka. Kaga kuma hakan bai dace ba. Ace mun takura maka ta wannan hanyar bayan duk irin taimakon da kake yi mana."

Wannan yarinya da abin dariya take ya ayyana a zuci. Ji yadda take zuba zance kamar wadda ake karantowa.

Ita kuma kasa jurewa shirun nasa tayi ta ce "Baka ce komai ba."

"To me zan ce? Naga kin gama yanke hukunci ke kaWai."

Ha?uri tayi saurin bashi. Sam bata so ta Sata masa rai kada ya yi amfani da hakan a kanta.

"Wai dama tunda ba so ka ke ba..."

"Ni yaushe mu ka yi maganar nan dake har nace bana so?"

Gabanta ne ya faWi. Kada fa ya?i amincewa.

"Rannan Win nannnn. Ka tuna? Da nayi maka rashin kunya ka ce ai ba sona kake baaa." Ta marairaice masa.

"Anya kuwa nine? Ban tuna ba Hamdi." Ya danne dariyar da yake son yi.

"Allah kuwa ba ?arya nake ba."

Muryarta yaji ta fara rawa.
"Yanzu dai so kike a raba auren?"

"Eh."

"Amma bai yi wuri ba? Kada sunanki ya Saci a gari."

"Kaga bamu zauna tare ba. Ko mun rabu babu mai cewa don nayi wani abu ne. Za ma a fahimta sosai."

"Tun yaushe ki ka fara wannan tunanin?"

Hamdi ta fara murnar jin muryarsa a sake.
"Tun yamma. Wallahi har ciwon kai da zazzaSi sai da su ka kamani saboda neman mafita...au...saboda nema maka mafita. Bana son mutum ya takura saboda ni."

'Zan yi maganinki'
Lokaci ya duba a wayarsa. Tara da arba'in da biyu.
"Yaya jikin naki? In ba a rufe muku gida ba ki Wan fito mana."

Sai kuma taji faWuwar gaba "takardar za ka bani?"

"Ina jiranki" kawai ya ce.

Da sanWa ta fito tayi sa'a ?ofar soronsu mai ?ara idan an turata a buWe take har yanzu. ?ofar gidan ta buWe tana sako ?afa su ka kusa karo da Taj. Baya tayi za ta faWi ya yi saurin ri?o kafaWunta. Ita da shi duka wani sabon al'amari ya ba?uncesu lokaci guda. Sai da ta daidaita tsayuwarta ya ce,

"Sannu."

Ta amsa da ka. Yawun bakinta ne a bushe. Tana tare da fargabar ko har ta saku. Bata yi aune ba taji hannun Taj a goshinta.

"Mene ne?"

"ZazzaSin nake son ji. Da alama akwai saura. Zo mu je asibiti."

"Na'am?" Ta waro masa idanunta.

Wayarsa ya Wago "bari na kira Abba na faWa masa za mu fita."

"Dani Win?" Ta ce a gigice. Idanunta sun soma raina fata.

"Idan dare ya ?ara yi kafin mu dawo sai su rufe gidan kawai. Sai mu wuce gida mu kwana."

Hanjin cikinta ya wani cure waje guda don tsoro "Wai da ni?"

"Kada ki damu. Zai fahimta. Mata ta ce so babu wani abu" ya bata amsa kai tsaye.

"Don Allah kayi ha?uri."

"Ban yi wasa da ciwon wanda bashi da kusanci dani ba ballantana kuma naki."

"Na warke tun da rana."

Taj ya ?an?ance ido "ki ka ce kuma da yamma."

Da sauri ta ce "Eh, da yamman nake nufi. Kafin rana tayi sanyi."

"Hamdiyya kenan. In tambayeki mana."

"Ina ji."

"Kina so na?"

Tsareta yayi da kallo. Ta sunkuyar da kai.

"Kada ki cuci kanki. Da amsarki zan yi amfani."

"Ba za ka ji haushi ba?"

Taj ya yi murmushi "ko kusa."

"Zan fi so mu rabu."

"Ban yi miki ba kenan?"

Yau acting kamar daraktan kannywood ya bata training, ta marairaice masa.

"A'a, ba haka nake nufi ba. Naga kamar bamu dace ba. Ka fi ?arfin ?ar talakawa iri na."

"Zan sanar da Abba duk yadda mu ka yi...."

"Wane Abban? Nawa?" Ta Waga murya fiye da yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login