Showing 51001 words to 54000 words out of 182745 words

Chapter 18 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

81

daudu ne. Girkin ne kaWai idan ya yi sai an bishi an saya. Da shi kaWai yake tsaye a ?afafunsa. Banda wauta da ?uruciya me zai sa ta ?arsa ta zauna ta faWawa wanda ya killace mata uba daga gaban murhun da kowa yake ganinsa a da. Yanzu sai ya gama ya dawo iyakarsa kitchen. Ba a ganshi ba balle ma a aibata shi. Kuma saboda duka kitchen Win maza ne har ya fara ?o?arin gyara tafiyarsa.

"Kin bani kunya wallahi."

"Yaya..."

"Tashi ki bani wuri."

?akinsu ta shiga tana kuka kamar ranta zai fita. Soyayyar da take yiwa Taj ta Wauki sabon salo. Haushinsa kawai take ji. Ba ma ta son shi. Kuma ba za ta taSa son nashi ba.

"Aikin banza. Meye abin burgewa a namiji mai girki? To da me matarsa ma za ta burge shi?" Ta ayyana a ranta duk cikin kukan.

Shi a ranar kasa gane kansa aka yi a Happy Taj. Da yaga komai ?an?antar abu sai ya yi faWa sai ya koma office Winsa kawai ya rufe ?ofa. Kan 3 seater yaje zai kwanta ya tuna Hamdi ta taSa kwanciya a kai sai ya tashi yana tsaki.

"Ashe yarinyar nan bata da kunya? Na iya ha?ura ma da Alhaji ya koreni balle wata ?aramar yarinya?"

Daga inda suke kowannensu ya dage yana sauke fushinsa ta hanyar ?ara faWawa zuciyarsa girman laifin Wayan. Shi dai Taj baya son wadda ta kasa ganin ?o?arin mahaifinta a matsayin da Allah Ya ajiye shi. Ita kuma Hamdi gani take tsabar mugunta ce ma za ta sa ya cigaba da ingiza mata uba akan hanyar da babansa ya kore shi a kanta.

***

An yi Kamun Sajida ranar laraba cikin farinciki da taron dangi. Hamdi tuni ta ajiye wani Taj ana ta sha'ani. Wannan karon ko ciwon kai bata ce tana yi ba saboda tsananin farinciki. Sajida ta sami wanda take so kuma yake sonta ba tare da ya taSa goranta mata ba. Damuwar su Yaya da tsoron ?an matansu ba za su auro ba ta kau. Komai nasu na rufin asiri sun yi domin fitar da juna kai kunya.

Alhamis aka yi sisters' a wani event centre. Ranar dai har rawa Hamdi tayi tunda taron mata ne. Sai da Anti Labiba ma ta janyeta saboda ko gajiya bata yi. Ana canja kiWa take komawa.

"Wannan ko ke ce amaryar sai haka."

Wata ?ar uwarsu ta kare mata "barta tayi. Ranar nata auren ai ba yi za ta yi."

*

Ana can ana shagalin biki wasu motoci biyu masu kyau su ka yi parking a ?ofar gidan Abba. A tsaye yake da Kamal da Taj. Kamal ne ya zo bashi tashi gudunmawar wadda ta kasance ta kayan abinci. SaSanin ta Taj da ya bashi kuWi. Yana ta cewa sun yi yawa da almajirai na kaiwa cikin gidan waWannan motoci su ka tsaya.

?ar Ficika ne ya fara fitowa daga motar gaban yana murnar ganin Abba a ?ofar gida.

"WaWannan mutanen ne su ka zo nemanka nace musu ai ka tashi daga wurin. To sai..." ya juya ya nuna wani Alhaji da ya nufosu yana takawa kamar baya so "wannan Alhajin ya nemi in kawo shi wurinka. Har za mu je restoran Win sai na tuna Wazu ka ce min kana gida."

Abba ya yi murmushi "ai da ka sa wani ya rako shi ma."

"Yaran nawa duk basu san nan Win ba."

Abba ya mi?awa mutumin hannu domin su gaisa sai ya ?i Waga nasa. Kallon wula?anci kawai yake yiwa Abban. Shi da ragowar mazan da su ka firfito daga motocin har su biyar.

"Kai ne Habibu Simagade?"

Abba ya Wan murmusa "a da kenan." Ya kuma mi?a hannun mutumin bai karSa ba dai.

"Ni ne uban Safwan mahaifi."

Mamaki ya bayyana a fuskar Abba. Tabbas ga kama nan. To amma ba wani abu bane tunda da ana neman aure kawunnansa ne su ka zo.

"Allah Sarki. Bari nasa ayi shimfiWa a ciki."

"Barshi. Zuwa nayi na faWa maka cewa idan ka kuskura aka Waura aurensa da ?arka gobe sai na Waure duka mutanen gidan nan."

"Alhaji me ya faru?" Abba ya ce da fargaba. Taj da Kamal ma hankalinsu tashi ya yi.

"Meye ma bai faru ba? Ya faWa min yana son wata yarinya nasa aka bincika aka ce ubanta Wan daudu ne. A ranar na soke maganar. Shi ne ya haWa kai da wan uwarsa aka zo aka nemi aure da komai a bayan idona. Suna ta Soye Soye basu san na sani ba. Dama bari nayi sai goben in ci muku mutumci duka a wajen Waurin auren. Sai yayansa ya shiga maganar" ya nuna babban Wansa "shi yasa na zo yau. In kun je an Waura za ku ga abin da zai faru. Zuriata tafi ?arfin haWa jini da irinku. ?ata gari, lalatattun mutane"

Banda Innalillahi babu abinda Abba ke faWi. ?ar Ficika kuwa ihu ya saka kamar mace yana ta jan jallabiyarsa sama yana tumamin wai sun shiga uku.

Baban Safwan ya kalle shi cikin takaici da ba?incikin anyi asarar namiji. Ha?uri Abba ya fara bashi ya dakatar da shi. Kamal da Taj su ka saka baki ya ce babu ruwansu. Ba su yi aune ba Abba ya dire gwiwoyinsa a ?asa zai fara ro?o mutumin ya juya abinsa bayan ya yi tsaki.

"Alhaji ka yiwa Allah kada ka hana auren nan."

Da sauri Taj ya kama hannunsa zai Waga shi amma ya?i mi?ewa.

"Abba don Allah ka tashi."

"Idan auren nan bai yiwu ba gabaWaya gidana laifina za su gani. Sajida bata taSa saurayi ba sai akan shi. Sun saka rai Taj, kowa ya saka rai. Duniya za ta zage ni. Duniya za ta min dariya.."

Babu wani tunani ko hangen nesa Taj ya ce masa "Abba indai ka amince za ka bani Hamdiyya, in sha Allahu gobe za ka aurar da ?a."

"Taj?" Kamal ya kira shi gabansa na faWuwa.

"Ina son ta Abba. Saboda ita na zo gareka."

Abba Habibu rasa bakin magana ya yi. Ido kawai ya zubawa Taj har motar baban Safwan ta bar layinsu bai sani ba.
RAYUWA DA GI?I 16



Batul Mamman =ؖ?




_Ya Rabbi. Ya Zhuljalal wal Ikhram. Allah ?a?anmu sun koma makaranta. Ka duba mana su da dukkan abokan mu'amalarsu da sauran ?a?an bayinKa. Ya Allah Ka tsare su daga dukkan sharri. Ka kare su daga zamewa kowa sharri. Allah Kada a kai ?ararsu, kada su kai ?arar wani. Ka basu ilimi mai albarka da amfani. Kasa aci moriyar abin da ake nema na boko da addini. Ya Sami'ud du'a Ka fimu sanin mawuyacin halin da ?asarmu take ciki. Ka horewa iyaye abin da za su ciyar da iyalansu daga halali. Ka makantar damu akan haram. Duk uzurin da zai taso Ya Allahu kada Ka sa mu ro?i kowa. Ka buWa mana. Ka albarkaci nema da samun mu. Ya Rabbi Ka kawo mana sau?i da sassaucin rayuwa. Ka azurtamu daga taskarKa wadda bata da iyaka. Amin_




***

Kallon da Abba ya yiwa Taj na tsantsar ?auna da girmamawa ne bayan ya gama mamaki. Ya mi?e tsaye ya kama hannun daman Taj da hannayensa biyu.

"A duniya bayan iyayena da matata da kuma ?an uwana da ba su guje ni ba da kuma ?alilan cikin abokai, kai ne mutum na farko da jini bai haWamu ba amma kullum burinka ka sanya farinciki a rayuwata."

Kamal samun kansa ya yi da girgiza kai saboda tsoron kada ya amince da Wanyen aikin da Taj ya Sallo.

"Abba..."

Kallonsa Abban ya yi yana murmushin danne ciwon dake cin zuciyarsa.

"Kada ka damu Kamal. Ba zan taSa zama butulu gareku ba. Na san duka abin da kake gudu. In sha Allahu ni Habibu ba zan bari son zuciya yasa na zama mai ?ara nesanta uba da Wansa ba."

Daga Taj har Kamal ba ?aramin tausayi ya basu ba. Taj ya rufe ido ya ce,

"Abba, Alhaji ya daWe da zare hannunsa a kaina. Auren Hamdi ba zai ..."

Kamal ya katse shi da hanzari "wallahi zai ?ara girman fushinsa a kanka. Haba Happy, ba ka tunanin su Inna ne?" Ya mayar da idanunsa ga Abba "ni zan auri Sajidan in sha Allahu. Laifin ba zai tattare akan Taj ba."

Abba jinjina zumuncin ?an uwan yayi. Kuma bai bar zancen a cikinsa ba ya faWa musu.

"Lallai Yaya Hayatu ya iya haihuwa. Ko sha?i?an da su ka fito ciki guda ba lallai su yi zumunci irin naku ba. Amma ku tafi gida, nagode. Zan bawa Sajida ha?uri. Na san za ta yi min uzuri."

"Sai dai idan ni ne baka son bawa ?arka. Ba auren taimako zan yi ba. Allah na fi shekara ina sonta."

"Har a yaushe ka santa?" Kamal ya tambaye shi don bai yarda da zancensa ba ko kaWan.

"Duka wannan bai taso ba. Ku je gida. Nagode"

Abba zai shige gida ?ar Ficika ya kamo shi da sauri. Duk sun manta dashi. Kwarwar da yake da ihu ma ba sa ji saboda mahimmancin abin da su ke tattaunawa.

"Simagade....au Habibu ashe baka da hankali? Ya Allah zai kawo maka agaji a lokaci irin wannan ka nemi ka watsa mana ?asa a ido. Ina mai tabbatar maka da cewa Sajida kai za ta Worawa alhakin rabata da farincikinta. Daga nan kuma bamu san halin da za ta shiga ba. Ni a tawa shawarar kawai ka bari su aure su duka."

"A'a Balarabe. Baka san komai akan yaran nan ba. Son zuciya a yanzu ita ce ?iyayya mafi girma da zan nuna a madadin kyautatawar da su ke min."

?ofar gidansa ya ?arasa da sauri don ?irjinsa zafi yake. Sai dai ko rabin jikinsa bai samu shigewa ba ya faWi a wurin. ?ar Ficika aka sake samun abin yi. Ya Wora hannu a ka zai cigaba da ihu, Kamal ya daka masa tsawa.

"Kada ka kuskura ka sake tara mana jama'a. Yi sallama ciki ka yi min magana da Yaya."

"To, to" ya amsa kamar ba Wan cikinsa bane ya yi masa tsawar. Yadda mata ke ruWewa a irin wannan yanayin, haka nasa hankalin ya gushe.

Da Kamal ya juyo bai ga Taj ba. Ya fara tunanin ko cikin gidan ya shige, don yanzu komai aka ce ya yi ba zai yi mamaki ba. Ya lura yana da taurin kai irin na Alhajinsu, sai dai kuma shi Taj ya haWa da Wanyen kai kamar wani Wan ta kife. Idan ya san abu daidai ne to kawai damn the consequences.

Horn Win mota yaji daidai ?ofar gidan. Ya le?a Taj ya fito a lokacin.

"Mu kai shi asibiti."

"Ai ka bari a faWawa Yaya ko?"

Bai ma yi wannan tunanin ba. Amma da yake ya san mahimmancin yin hakan sai ya gyaWa kai. Salatin Yaya su ka ji su ka koma cikin soron.

"Damuwa ce Yaya. Kada ki Waga hankalinki musamman tunda da mutane a ciki. Za mu kai shi asibiti." ?aga shi su ka yi Kamal ya ?arasa dashi motar. Taj kuma ya tsaya sakamakon maganar da Yaya ta fara yi.

"?ar Ficika kuma ya ce..."

Taj ya gallawa ?ar Ficikan harara shi kuwa bawan Allah ya girgiza kai da sauri.

"Wallahi ban faWa mata komai ba."

"Me ku ke Soye min?" Ta tambaya hankalinta a tashe. Dama bata ga abin da zai Waga masa hankali ya faWi ba. Bayan bikin nan shi ne babban farinciki da cikar burinsu.

Gani su ka zasu Sata lokaci sai kawai Taj ya ce ?ar Ficika ya faWa mata in sun tafi.

"Amma don Allah ki bar maganar a wajenki kafin ya tashi mu san abin yi. Yanzu hankalin mutane ne kawai zai tashi."

"To, nagode. Idan kun je asibiti ka faWa min. Sai na kira ?aninsa ya taho."

Kana ganin yadda take magana sai ta baka tausayi. Da gani hankalinta ya kai ?ololuwar tashi. Tana dannewa ne kawai saboda mutanen cikin gidan.

*

Asibitin kuWi Kamal ya kai su amma ba wanda ?an gidansu su kw zuwa ba. Ana bu?atar file Taj ya buWe musu na family. Aka shiga dashi ciki aka duba shi. Jininsa ya hau sosai shi da bashi da bp. Dole aka bashi gado ana jiran jikin ya daidaita. Drip aka saka masa da allurai sannan ya sami bacci.

Zaman jiran Abdul?adir ?aninsa Taj da Kamal su ka yi a Wakin. Kamal ya dube shi a tsanake.

"Yanzu Happy duk abubuwanbda su ka faru da kai a gida ba su isheka ba? Kai da bakinka kake cewa za ka auri Hamdi. Auren ma gobe goben nan. Less than 24hrs. Har kana yiwa Abba ?aryar sonta kake kawai don kafi kowa iya rigima."

"Allah da gaske nake ina sonta Happiness."

"Kai Win? Ya aka yi ban sani ba?" Ya tambaya don bai gaskata shi ba.

Babu wani juya zance ya ce "Saboda nayi tunanin za ka ?aryata duk wata niyyata ta janyo Abba Happy Taj. Infact bana tunanin da ka sani ko zuwan farko ba za mu yi gidan ba in ka san waye babanta."

"Lallai ka iya ganganci. Banda Soye min da kayi da kuma kana can tayi saurayi fa?"

Taj ya yi murmushi "wallahi a next flight za ku ganni."

"Da ni na ce ina sonta fa?" Kamal ya yi tambayar idanunsa cikin na Wan uwansa.

"In sha Allahu ma Allah ba zai jarabcemu da son abu Waya wanda mutum Waya ya kamata ya so ba." Ya haWe kafaWunsa don tsigar jikinsa tashi tayi.

"Next time kada ka Soye min abin da ya kamata na sani."

Gira Taj ya Waga yana ?ar dariya ganin Kamal ya Wauki zafi da gsske.
"Bros, faWa min gaskiya. Ba ka ciki ko? Kaga matar yara ce irina."

Fuska Kamal ya Waure amma da gani ya sauko "Ji min mutumin nan. To meye marabata da kai?"

"Wata biyar mana. Kai fa kana cikin layin tuzurai."

"Baka da mutumci Taj. Ni ne tuzurun? Kai kuma teenager ko?"

Taj ya gyaWa kai yana dariya.

"Banda ?uruciya, teenager kamar ka ina zai kai budurwa kamar Hamdiyya?"

"Inda ake kai matan..."

"Ehemm. Ughhh" Abba ya yi gyaran murya da ?arfi don ya katse hirar tasu haka. Yaga an kusa zuwa wurin da bai kamata kunnuwan uba su ji ba.

Kan sa su ka yi suna tambayarsa jiki. Da sau?i kamar yadda idanuwansu su ke iya gani. Ya ?ara yi musu godiya sannan ya ro?esu da su bar maganar auren nan haka. Allah zai bashi yadda zai yi da iyalinsa.

"Idan Alhaji ya amince za ka yarda a Waura goben?" Taj ya tambaye shi kafin su fita. Shi ko a fuska bai nuna damuwa ba da Abba yake ta maganar su daina zancen.

Shi dai Abba ya gama gajiya da zancen. Sannan ya matsu su tafi saboda so yake ya fice ya koma gida su shawarta da Yaya.

"Me zai hana? Waye zai ?i jinin Yaya Hayatu ko ma in ce zuri'ar Alh. Sule?"

Jin wannan ya kwantarwa Taj hankali. Ya san Alhaji ba shi kaWai bane shamakinsa. Shi kan shi Abba za a sha fama da shi.

***

Salati Yaya ta fara yi kafin ta fashe da kuka. Zaune su ke a cikin wani Wan falo ?arami na Wakin Abba. Ita da shi da kuma Baba Maje, Inna Luba mahaifiyarta da kuma ?aninsa Abdul?adir.

FaWan kukan Inna Luba ta fara yi mata kafin ta koma tausarta.

"Indai ku ka nunawa yarinyar nan cewa kun karaya na tabbata ciwon da za ta ji sai yafi na fasa auren."

"Yaron nan ya cuce mu" cewar Abdul?adir.

"Na dai cuce mu. Rayuwar da na zaSa ce ta zo tana bibiyar ?a?ana" Abba ya faWi da raunin murya.

"In ka amince kuma kana jin Sajida ba za ta ?i ba, yanzu zan kira Baballe ya zo gidan nan a rufe magana. Gobe ya auri ?anwarsa bakin kowa alekum. Ko kuwa?"

Abba ya nuna farincikinsa da godiya.

"Zan so haka. Amma Maje ka tuna lallai akwai ha??i tsakaninmu da yaran nan. Aure ba a son yi masa shigar sauri. Yanzun nan sai ya jagwalgwala abin da ake son gyarawa."

Baba Maje ya dage harda cewa "indai ba kuma rowar ?ar za ka yi min ba ka amince kawai. Ba don ni na haife shi ba amma Allah yaro ne mai biyayya. Ina sa rai in Allah Ya so ba zai bamu kunya ba."

Yadda ya matsa Winnan sai Inna Luba ta ce a kira yaron. Ba a mayarda hannun kyauta. Kuma Allah kaWai Ya san dalilin faruwar wannan al'amari.

Cikin farinciki Baba Maje ya kira Baballe a gabansu. Allah Yasa baya nesa sosai ya ce gashi nan zuwa. Ita Iyaa da Siyama suna can wajen biki. Uwar ba?in hali kuma an tafi bikin ?awa kamar yadda ta shirgawa Iyaa ?arya.

Kowa ya yi zugum ana jiran isowar Baballe. Baba Maje ya takura masa da waya saboda basa son ?an biki su fara dawowa. An gargaWe su lallai kada su wuce takwas a waje har amaryar.

Baballe ya iso hankalinsa duk ya tashi. Irin wannan kira da wayar bai saba dasu daga mahaifinsa ba. Shi yasa ya dinga tunanin ko wani abu ne ya faru. Kafin ya iso sai da ya kira Iyaa yaji lafiyarta da ta Siyama. Ummi kuwa bata Wauki wayar ba don kada a ce ta dawo gida. Sam ba ya raga mata akan halayen da ta tsiro musu da su a gidan.

Tiryan tiryan haka Baba Maje ya labarta masa halin da ake ciki a gaban kowa. Wanda shi Abba ya so su keSe. Don idan Baballe zai ?i, ba zai ji nauyin idanuwansu ba.

"Baba don Allah ko za mu koma soro mu yi magana" abin da ya ce kenan da Baban nasa ya matsa masa akan ya bada amsa.

Gabansa sai da ya Wan faWi. Yaran yanzu ba a ci musu laya. Ya gama yabonsa shi ne yake son watsa masa ?asa a ido.

"Nan dukansu amsar da ka bani dole zan dawo musu da ita. Saboda haka gara ma kawai ka faWa a gabansu."

"Baba don Allah" ya faWi yana cije leSensa na ?asa. Shiru ba zai amfane shi ba a wannan lokacin. Shi yasa yake son faWa masa dalilin da ya sa ba zai iya auren Sajida ba.

"Ka je ka saurare shi don Allah. Share ire iren waWannan abubuwan fa don mun isa su ne su ke zama dalilan yaji ko mutuwar aure. Allah Ya kiyaye." Inna Luba ta faWi tana nuna musu ?ofa.

Ba don ya so ba ya tashi su ka fita. Ransa duk ya Saci don Baballe bai saba yi masa haka ba. Yaro ne shiru shiru mai sau?in kai. Tsayinsu kusan Waya don ma shi shekaru sun Wan dur?usar da shi. Fuskar Iyaa ma'abociyar fara'a ya Wauko. Ga shi kyakkyawan matashi mai zuciyar nema. Banda aikin da ya samu ?an watannin baya akwai shi da buga bugar neman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login