Showing 93001 words to 96000 words out of 182745 words

Chapter 32 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

114

masa magana yanzu in sha Allah a waya."

Fuska mai tona asirin zuciya. A take fuskar Hamdi ta washe. Yaya ta kama baki tana salati.

"Anya dama ba shirya maganar auren nan ku ka yi da Taj ba? Cikin ?an kwanaki kin zurma haka?"

"Ni ban zurma ba Yaya"

"Tsiwar ma ai naga ta ragu. Allah Ya yiwa aure albarka. Amma ki rage murna don ba dake zai je ba. Halifa zai Wauka."

"Kai Yaya, ni yaushe na ce zan je?"

Dariya tayi "nima wasa nake miki. Ai na san ko tayi aka yi miki za ki ce a'a."

Bata ?ara magana ba tunda ta gane Yayan ma tsokanarta take yi. To ita har me tayi da ake mata wannan fassara?

*

A Sangaren Taj abin da ya zata zazzaSin gajiya ne ashe combo ne na typhoid da maleriya. Ciwon da ya manta rabonsa da yi. Shi ne ya yi masa rubdugu irin wannan. Kuma da yake zafi ake yi sai ya haWu goma da ashirin. Dalilin zazzaSin ne ma su Mama su ka tsahirta da sanya lokacin biki. Shirye shirye dai sai abin da ba a rasa ba. So su ke amarya ta shiga Wakinta nan da sati uku ko wata guda. A nasu shirin idan ta tare da wuri za su Sata shirin Alhaji. A ganinsu dama wata ukun nan da ya bayar ya yi ne saboda sanin cewa da wahala ace Abba Habibu yana da abin da zai yi bikin wata ?ar nan kusa.

Sosai Ahmad yake bashi kulawa. Musamman bayan tafiyar Salwa. Fushin da ya fara akan yadda aka yi mata dole ya kau da ya gaskata ita ce ta janyowa kanta.

Kamal ne dai tun ranar da ya kai shi asibiti ya ?ir?iri tafiya washegari. Ciwo ke neman kayar dashi kuma baya son kowa ya sani. Haka ya tattara ya tafi asibiti. Mubina ta kwantar dashi. Magunguna tana iya bakin ?o?arinta. Bata so su fara dialysis domin ana kaiwa wannan matakin, transplant (dashe) shi ne best option Win da zai rage.

Ranar da ta kwantar dashi bayan ya zama stable ta kira Yaya Kubra. Dama kullum jiran wayarta take yi. Tana gani kuwa ta bar ayyukan gabanta ta tafi asibitin.

"Akwai shirin da ki ka fara yi ne Doctor saboda in san next course of action?"

Yaya Kubra ta gyaWa kai "na fara bincike ta bayan gida. Wata questionnaire na ?ir?ira a google form nace ta research Wina ce. Ita na tura a groups na family ake ta cike min. Harda families Win duka matan gidan mu. Kuma da yake da suna so far na sami mutum huWu that are rhesus negative."

Idanun Mubina harda ?walla ta ce "Masha Allah. Amma dangin kusa ne?"

"Surprisingly daga dangin Hajiya na sami uku. ?aya ne a dangin Umma. Ai jinsi baya hana bayarwa ko? Duka huWun mata ne."

Mubina ta ce gender baya hanawa.
"Amma fa Kamal A negative ne. Indai ba irin nasa ba kinsan sai dai O ko AB negative ko?"

"Dukkaninsu O negative ne. Yanzu su Alhaji ya rage su sani sai a tuntuSe su."

"Muje ki ganshi. Akwai Nephrologist da na fara magana dashi daga Port Harcourt. Idan an sami nasarar samun mai bayarwa sai naji yaushe zai iya zuwa."

Godiya Yaya Kubra tayi mata har ta rasa kalmar faWa. Mubina ta shige gaba zuwa Wakin da Kamal yake. A hanya tayi ta nanata mata don Allah ta daure zuciyarta idan ta ganshi. Wannan yasa zuciyar Yaya Kubra ga tsinke tun kafin su shiga.

Mubina ce ta fara shiga da sallama. Yana kwance gaSoSi da fuskarsa sun kumburo sosai. Shi kaWai ya san irin azabar ciwon da yake ji. Amsa sallamar ya fara da muryarsa can ?asa kawai sai ya yi tozali da Yaya Kubra. Ya yun?ura ya tashi zaune kafin ta ?araso.

Hannu ta Wora akan bakinta don kada tayi kuka mai haWe da ihu da taga yadda ya koma.

"Kamal?" Ta kira shi da rawar murya.

Ya mi?a mata hannu, kwarmin idanunsa yana ziraro hawaye ta ri?e. A gefen gadon ta zauna su ka rungume juna. For the first time tun bayan ciwon nan ya same shi ya fashe da kuka mai ban tausayi. Duk wani ciwo, ?unci da damuwa da yake Soyewa ya bari ya nuna kansa a wannan lokacin. Shi Wan dangi yana ta fama da damuwa shi kaWai. Abin da gidansu basu saba ba.

Yaya Kubra tana kuka tana shafa bayansa da lallashi. Mubina kuwa ficewa tayi don bata son karyar masa da zuciya fiye da halin da yake ciki. Mara lafiya baya son ganin rauni a tattare da likitansa.

Tsahon minti goma zuwa shabiyar kafin yaji sanyi a ransa ya daina kukan.

"Kiranki tayi ko?" Ya tambayeta yana nufin Mubina.

FaWa ta soma yi masa "Me yasa ka zaSi wannan rayuwar Kamal? Bamu da mahimmanci a wurinka? Ko kana ganin ba za mu damu da lalurarka ba?"

"Irin wannan kallon kamar kina yi min sallama shi ne bana son gani. Wannan kukan zamu dinga yi kullum har lokaci..."

"In sha Allahu za a dace. Ina nan ina bincike."

"Bata faWa miki cewa ko dialysis ba zai iya ri?eni na tsayin lokaci ba?"

"Na sani Kamal. You need a new kidney. And we'll find one in sha Allah" ta share masa hawaye da hannunta.

Al?awarin ri?e masa sirri ya ro?eta har zuwa lokacin da za ayi bikin Taj. Sannan ?anwarsu mai shirin haihuwa ko yau ko gobe ita ma ta sauke.

"Me yasa? Wallahi ka san ba za ka burge Taj ba. Infact ni ba zan so ganin ranar da zai sani ba. Za ku yi faWa Kamal. Za ku yi faWa sosai. Ko jiya da naje duba shi sai da yayi ta zancen wai ina duba maka magungunan allergy kuwa."

Jingina ya yi da pillow don ya gaji da zaman. Ya yi ajiyar zuciya.

"Na sani. Amma Happy zai tsayar da duka uzurin rayuwarsa ne. Zuwa yanzu kin san mutum ne mai sanya abu a rai. Amma kina gani saboda mu ya mayar da komai ba komai ba tsakaninsa da Alhaji. Kuma hakan fa ba ?aramin ciwo yake yi masa ba."

"Tsakanin uba da Wa ne wannan. Ina maganar Happy da Happiness. Sai ka shiryawa duk abin da zai biyo baya."

"In ya ganni a haka kina tunanin zai iya yi min mita? Kuka kawai za mu zauna mu sha abinmu."

Yadda yake maganar kai ka san akwai tsantsar tawakkali. Yaya Kubra a nan ta wuni har tara na dare sannan ta tafi. Ta amince za ta yi shiru amma ba don Kamal ba. So take ta samu cikin dangin wanda idan ta bijiro da bu?atar ba zai ?i ba. Maganar neman donor ta hanyar gwamnati ba zai yiwu ba. WaWanda su ke kan list sun yi yawa sosai.

Tsakanin Kamal da Taj a waya sai ta whtsapp. Kamal ya cire simcard da sunan baya ?asar. Wai ya tafi China odar takalma. Taj harda mitar me yasa bai faWa masa shirin tafiyar ba. Ya ce wanda ya bawa sautu ne ya sami matsala. Gashi kuma komai ya kammala. Ana bu?atar mai kaya. Abinka da rashin sabo da yi. Taj bai kawo komai ba ya yarda. Iyaka dai in suna waya ya dinga kiran wash wash kenan don kawai yaji Kamal yana sannu kamar ya ari baki. Bai san ciwon Kamal Win ya ninka nashi ba.

***

Kamar yadda Anti Zahra tayi hasashe, Salwa gidan ?anwar babanta ta tafi. Gidan da tun farkon karatunta baban ya so taje amma saboda Mami ta raina arzi?insu ta rufe ido ta ce bata san zance ba. Wannan tafiya da tayi sai ta sami lasisin fita yadda take so tana haWuwa da Ummi. Gwaggonta kuma bata iya yi mata magana saboda tsoron jarabar Mami.

Bayan bugun cikin da Ummi tayi mata sai ta nuna mata cewa tana jajanta mata rashin samun soyayyar Taj. Ta kuma yi mata al?awarin za ta taimaka mata ta sami biyan bu?ata indai tana so.

"Mamina ma ta gama komai har an fara maganar aurenmu" ta faWawa Ummi da farinciki.

TaSe baki Ummin tayi "in an Waura muku auren kina tunanin kin yi nasara ko me? Mutumin da baya sonki kuma igiyar auren tana hannunsa."

A tsorace Salwa ta ce "kuma fa haka ne. Amma ba sona bane baya yi. HaWuwarsa da matar da aka aura masa ?ar Wan daudu duk shi ya lalata komai. Da muna waya normal."

A zuci Ummi tayi tsaki. Wannan Salwan irin matan nan ne da sakarci ya rinjayi tunaninsu. Gashi dai ta san cewa ta girmeta amma irin shirmen da take yi da sunan soyayya ita ko da wasa ba za ta yi ba.

"Ni naga sharrin ?ar Wan daudu. Akanta aka koreni daga makaranta sannan aka fasa bikina. Gidanmu kowa ya tsaneni akansu. Wallahi da zan haWu da Hamdiyya Habib sai na rama abin da tayi min ko yaya ne."

Idanu Salwa ta zaro tana kallonta "Hamdiyya? Ai kuwa ita ma sunanta kenan. Babanta yana aiki a Happy Taj."

"Ni ban san a ina yake ba. Amma dai shi ma sana'ar girki yake yi. Kin ganta. A yadda suke matsiyata bana jin ko iskar da mai Happy Taj yake sha?a ita ma za ta sha?a wataran."

Hoton Hamdi ta nuna mata wanda ta samu ta Wauka daga wayar Siyama na ranar aurensu. Salwa ta dinga sallallami gami da rantsuwar ita ce. Ita ma Ummi ta nuna nata mamakin ?warai.

"Indai Hamdi ce nayi miki al?awarin zan bada nawa taimakon na raba su da masoyinki."

"Nagode. Ni kam alkhairi ne ashe ya kai ni Glory mall rannan."

Ummi sai dariyar ya?e kawai take yi. Ita kanta duk fitinarta abin da Alh. Usaini ya tanadarwa Taj ya yi mata hatsabibanci da yawa. Ta riga ta nuna masa tana tare dashi bata da hanyar guduwa. Haka kawai take tsoron mutane irinsa waWanda za su iya yin komai domin biyan bu?atarsu. Rashin kunyarta bata kai nan ba. Domin kuwa duk iya shegenta akwai abubuwan da take tsoron yi don kada su koma kunnen iyayenta. Tunda Allah Ya kawo Salwa sai ta bashi shawarar amfani da ita don ya cimma burinsa.

***
Jinyar sati guda Taj ya yi kafin ya farfaWo sosai. Har ya faWa kuwa. Abba yaje duba shi har gidan Ahmad. Kuma ya sami tarba ta mutumci daga gare shi. Wannan ya sake daWaWa ransa akan halin ?a?an Yaya Hayatu. Da zai tafi ne Taj ya yi masa maganar Hamdi.

"Abba don Allah ina neman alfarma a gareka."

"Indai zan iya in sha Allahu zan maka."

"Maganar rabani da Hamdi. Don Allah ka cire komai a ranka ka bimu da addu'a."

"Innalillahi..." Abba ya ri?e kai "faWa maka tayi? Ban san Hamdi da surutu ba wallahi."

Taj ya yi murmushi "ba ita ta faWa min ba." Ya tuna maganar da Salwa tayi ya ce "Yaya Ahmad ne ya faWa. Amma ya ce kada na damu in sha Allah su Inna ba za su bari ba."

"Lamari na iyaye..."

"Allah bai bawa iyayenmu damar kashe mana aure ba. Musamman idan raba auren cutarwa ne ba hanyar samun maslaha ba."

"Ina jiye maka yawan saSanin da kuke samu dashi. Hakan ba zai haifar da alkairi ba."

"Abba ina ?o?arin tsayuwa akan iyakar addini kan abin da ya shafi Alhaji. Duka abubuwan da yake fushu dani a kai shi yake nuna amincewarsa sannan ya zargeni da rashin kyautawa."

Shi dai Abba gani ya yi zai shiga tsaka mai wuya. Ya yi ta nunawa Taj illar dake tattare da zama cikin fushin iyaye.

"Don Allah ka nemi sulhu dashi kafin lokaci ya ?ure."

Muryar Taj a raunane ya ce "na jima ina wannan amma ya?i bani dama. Zan cigaba da ?o?ari amma Abba kada ka kuma sako aurena a ciki don Allah."

Tausayi ya bawa Abban "na daina. Allah Ya kiyaye mana Sacin rana."

"A sunnar Annabi SAW? Inaaa, Abba ai sai dai lada."

Nauyi Abba ya fara ji tun kafin Taj Win ya je inda bai dace ba ya ce "naga ka fara jin sau?i. Bari na tashi."

Taj ya dinga dariya kamar ba shi ne yake kwance kafin zuwan Abban ba.

***

Inna tana falonta ana yi mata kitso aka yi mata waya. Ba?uwar lamba ta gani. Ta Wauka da sallama su ka gaisa da matar da ta kira.

"Na san ba ki gane ni ba tunda bamu zauna tare ba. Mahaifiyar Ahmad ce. Ahmad babban Wa namiji wajen Alh. Hayatu nake nufi."

Murmushi Inna tayi. Wannan ?alau take kuwa? A take ta cire wayar daga kunnenta ta karanto Ayatul Kursiyyu. ?abi'arta ce haka. Duk abin da bata gamsu dashi ba koda bata aka yi sai ta tofe shi da Ayatul Kursiyyu kafin tayi amfani dashi. Yadda Mami ta gabatar da kanta sam bai yi mata ba.

Sai da ta gama sannan su ka gaisa da ita.

"Dama naji shiru ne ina ta sa rai da wayarki amma baki kira ba. Nace bari ni na neme ki naji me ake ciki."

"Wace magana kenan?" Tashi tayi daga wurin kitson ta koma Waki.

"Auren Taj da Salwa. Alhaji ya ce baya son a wuce wata guda. Naga har an cinye sati."

Azkar Win tunkarar shugaban da kake tsoron cutarwa daga gare shi Inna ta karanto wannan karon kafin tayi magana.

(Allahummak finihin bima shi'ta)

"Wane Taj Win wai? Nawa dai sati biyu kenan da aurensa. Bani kuma da labarin zai ?ara wani."

Mami tayi kwafa a hankali tana raya duk za su zo hannu ne. Da ta san haka za ta yi mata tun farko ma da ta karSo laya.

"To ki tambayi maigidan naki. Sai mu yi magana daga nan."

Inna ce ta fara kashe wayar. Ta dinga karanto addu'o'i. Me yasa duk wata rigimar gidan akan Taj take kunno kai? Istigfari tayi da sauri sannan ta fita ta tafi Sangaren Alhajin. Dama yana gida. Girkin Umma ne. Inna tayi sallama ta shiga falon bayan Umma ta amsa ta iske shi yana cin abinci.

"Alhaji me nake ji daga bakin tsohuwar matarka?"

Karo na biyu kenan da Inna tayi masa magana babu kyautata kafazi. Yana namiji sai da yaji wanibabu a ransa. Maganar Hajiya na neman tabbata da ta ce masa kada ya ?ure ha?urin Abu don mai ha?uri bai iya fushi ba.

"Wani abin ne ya faru?" Ya tambayeta kamar bai sani ba.

"Ka fini sani Alhaji. To amma ina so ka sani ka gama yi min hawan karkatacciyar kuka. Wannan juya min yaro da kake yi ya isa haka."

"Haba Inna. In ranki ya Saci kada ki bari hankalinki ya gushe mana. Da mijinki fa kike magana." Umma ta ankarar da ita don muryarta tashi take sosai.

"Me ya rage min? Yau ko agola ne Tajuddin ai iyakar abin da mijin uwa da baya sonsa zai yi masa kenan. Wai ni matar nan za ta kira ta ce ya maganar auren Taj da Salwa?"

"Me?" Umma ma ta Waga murya ba tare da tunani ba.

"Ah to, kema kya faWa. Wai da Alhaji su ka yi magana."

Ya fa manta da maganar nan. Duk a zatonsa idan Ahmad ya faWa mata yadda su ka yi za taji haushi ta ce basa so. Daga ranar da su ka yi maganar ko tunawa bai sake yi ba saboda rashin mahimmancin zancen a wajensa.

Umma ta dube shi "Alhaji wai haka?"

"Eh. Mun yi magana da mijinta ya bawa Taj Salwa. SharaWina kenan idan ba zai saki ?ar gidan Habibu ba. In ba haka ba kuwa..."

"Kana son ya saketa kafin auren ya wuce wata uku ko? Ahmad, Wan halak ya faWa mana" Inna ta ?arashe masa.

"Tunda kun sani sai ku sa ya zaSi Waya. Na gama magana."

"Ahaf. Ai babban kuskurenka da ka bari aka yi auren nan Alhaji. Shi ne mai wuyar. Ko yanzu ba abin mamaki bane ace Hamdi tana da juna biyu."

Ba Alhaji da ya kusa ?warewa da ruwan da yake sha ba, Inna ma zaro idanu tayi.

"Kai Umma?"

"Auren yanzu da ake yiwa yara bayan duk sun ?osa. Ko mu nan nawa ne ?a?anmu su ka haihu wata tara ko goma da aure? Indai an bada sadaki ai magana ta ?are. Don ma ba lafiya gare shi ba."

"Ai kuwa sati mai zuwa za ta tare." Inna ta faWi sannan ta dubi Alhaji "ka faWawa tsohuwar matarka ta nemarwa ?arta miji tun wuri."

Inna na fita Alhaji ya tsare Umma da tambaya. Shi fa daina gane komai ya yi daga inda ta ce bashi da lafiya.

"Ciwo ne da Taj Win?"

"Typhoid yake da maleriya. Satinsa guda ko aiki baya zuwa."

Ransa a Sace ya ce "Kuma shi ne aka rasa wanda zai faWa min?"

"Taj ne fa. Ka damu da ciwonsa ne dama?"

"Me kike nufi?"

"Wai abin da ido ya gani baki ke faWa."

Ta jima da fita daga Wakin ta bar Alhaji da tunani. Me yasa sai akan Taj iyalinsa su ke yi masa irin wannan? Sai kuma maganar Salwa. Bai san har yanzu Mami bata da cikakken hankali ba. Ai da maimakon hannunka mai sanda sai ya fito musu a mutum kawai.

Yana wannan lissafin tuni Mami ta garzaya wajen toshe Sarakar da take hangowa. Magana ta yiwa Alh. Mukhtar. Ya kuma aiwatar duk da baya so.

Alhaji sai waya kawai yaji. Ganin sunan mai kiran ya hanzarta Wauka domin ya kashe maganar Salwa. Sai dai kafin ya ce komai Alh. Mukhtar ya yi masa dabaibayi.

"Akwai wasu ?an uwana mazauna Kano da muka yi magana mutum biyar. ?aya ma ?anin mahaifina ne uwa Waya uba Waya."

"Wani abu ne ya same su?" Alhaji ya ?osa yaji ?arshen zancen ko ya sami damar yin nasa.

"Lafiya ?alau. Dama don a sama muku sau?i ba sai kun taho har nan ba. Shi Baffan namu na sanar dashi za ku zo neman aure da biyan sadaki. In kun saka rana sai ka sanar dani. Na tura musu lambarka ma dai."

Alh. Hayatu mai baki sai yaji yawun bakinsa ya ?afe. Ta ina zai fara cewa ya fasa? Abin da kamar wuya. Girmansa zubewa zai yi. Idan matansa su ka san halin da yake ciki ya tabbata dariya za su yi masa.

"Idan na saka ranar zan sanar da kai."

"Yauwa to nagode." Ya an numfasa "don Allah kada a ja lokacin. Nima na gama shiri."

"To"

Alhaji ya gyaWa kai. Kuma har zuciyarsa sai yaji yana tausayin Alh. Mukhtar Win. Shi da zai iya dafa littafi mai tsarki ya yi rantsuwar matansa basa biye biyen tsibbu ashe a aljanna yake. Gudun faWuwar girma ya janyo ya kasa kyautata musu akan abu guda da su ke bu?ata daga gare shi.

*

Inna na dawowa daga Sangarensa taci karo da wasu rantsattsun akwatuna manya manya guda huWu a tsakiyar falo. ?an gidan an haWu ana ta murnar yaushe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login