Showing 15001 words to 18000 words out of 182745 words

Chapter 6 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

88

bai kamata ka kira biyayyata gareka da rashin hankali ba." Ya cigaba da magana kai tsaye babu tauna lafuzza don yau dole ya amayar da Sacin ransa "saboda gudun shiga ha??i ban taSa yiwa kowa iko da Wansa ba. Amma sau biyu Yaya kana bawa yaron nan abin da nake son hanawa. Hakan ba komai zai janyo min ba illa ba?in jini daga gare shi. Koda yayi min biyayya zata zama bisa tursasawa ba don son rai ba. Maganin kar ayi, kar a soma. Tunda ka nuna masa za ka iya bashi abin da na hana sai ka ri?e shi na bar maka."

"Ni kake faWawa magana Hayatu? Ashe zumuncinmu bai kai nayi umarni ko hani ga tsatsonka ba tare da ka Waga kai ba?" Yaya Babba ya faWi yana mai jin ciwon maganganun da kunnuwansa ke ji.

Musayar yawun da suke ba ?aramin tadawa Taj hankali tayi ba. Ya dur?usa a ?asa yana kuka yake ro?onsu da su yi ha?uri.

"Wallahi ba zan sake tada zancen nan ba har abada. Ku yafe min don Allah."

"Baka isa ba! Karatu ko ba kyauta aka baka ba sai kayi shi. Tunda ka iya raina ?o?arina akanka ka haWani da Wan uwana dole ka cika burinka."

Taj na kuka ya ri?e ?afar mahaifinsa yana ro?on yafiyarsa. Yaya Babba ma idanunsa sun kaWa sun yi ja. A haka ya ja girmansa don gudun rigima ya bashi ha?uri.

"Kayi ha?uri. Ban yi zurfin tunani ba, da ban shiga huruminka ba. Don Allah ka Wauki Wanka ku tafi."

"Na gama magana. Wallahi daga yau Taj ya bar gidana..."

"Kada ka rantse." Ya yi nufin dakatar dashi sai dai ya makara.

Suna ji suna gani Alhaji ya juya ya shige motarsa yayi gaba. Taj ya bi motar a rikice kafin ya sami wuri kusa da akwatinsa ya zauna cikin wani irin yanayi na rashin kuzari. Zuciyarsa wani irin ?unci kawai ke yawo a cikinta. Bai san lokacin da aka kwashe kayansa ba. Sai hannuwa da yaji na Wan uwansa, ?aramin Wan Yaya Babba wanda ya kasance sakonsa ya tayar dashi. Da ?yar ya yarda ya shiga gidan. Mummy tana kuka tana bashi baki tare da al?awarin gobe Yaya Babba zai mayar da shi.

***

A wannan rana ko gyangyaWi Taj bai samu ba. Kuma haka ta kasance a Sangaren Baba Yaya da Alhaji da Inna. Don bayan ta dawo gida da ya sanar dasu hukuncin da ya Wauka har suma tayi. Gidan ya rikice da koke koke. Iyalin Alh. Hayatu su ka taru su ka juya masa baya daga matansa har ?a?ansu. Hakan kuwa bai yi masa komai ba face ?ara tsanar turbar da Taj yake son bi. Da kuma abin da Yaya Babba yayi masa.

Washegari duka ?a?an Marigayi Alh. Sule su ka taru a gidansu dake Soron Winki inda mata guda Waya da ta rage musu a matsayin uwa take. Ita ce mata ta uku cikin matansa. Zama irin na da yasa ita da ?a?an sauran abokan zamanta su ka cigaba da zumunci tamkar lokacin da mahaifinsu yake da rai.

Ita Yaya Babba ya kaiwa ?arar Alhaji tun a jiya. Tasa aka kira mata kowa dake kusa. Amma ma dake nesa dama ta iso kwana huWu da su ka wuce hutun shekara. Tana Abuja da niyar tahowa bayan sati guda. Amma kiran Gwaggo yasa ta biyo jirgin ?arfe tara na safe.

Bayan an zazzauna Yaya Babba ya mayar da iya abin da ya faru ta Sangarensa. Tun daga wayar da Mama ta yiwa Mummy da suna India har zuwa yadda ta kasance jiya. Aka tambayi Alhaji sai kaWa baki ya yi ya ce bashi da abin sake tofawa.

"Yanzu Hayatu har kayi girman da za ka nuna mana iko akan ?a?anka?" Yayarsa mace mai bin Yaya Babba wadda daga ita sai shi tayi maganar da ?walla a idonta "na zata za ka yi farinciki da zumuncin da muke dashi wanda mu ka Wora ?a?anmu da jikoki. Kai ba abin alfaharinka bane ace Wanka yaje neman sau?i a wajen Wan uwanka? Shi kuma bai bashi kunya ba ya share masa hawaye."

Ransa sosuwa ya yi da har suke ganin laifinsa.
"A cikinku akwai wanda zai bar Wansa namiji ya Sata lokaci a jami'a yana koyon girki da yadda ake sarrafa kayan abinci?"

"Me zai hana tunda ba haramun bane" wani ?aninsa ya amsa kai tsaye. Wasu duk su ka amsa da za su iya.

"Wallahi ?arya kuke yi. Ni ban taSa ganin namiji a arewa mai sana'ar abinci ba wanda baya abin mata."

"Saboda al'adar bahaushe ta mayar dashi aikin mata kaWai ba. Amma a kudu da sauran ?asashen duniya maza nawa ne su ka yi fice da girki kuma in ba faWa su ka yi ba sai ka rantse ma ?an dambe ne."

"Ni yanzu me kuke so daga gareni?"

Gwaggo ta dube shi. Ha?i?a akwai ciwo wurin iyaye idan ?a?ansu su ka ?i bin umarninsu. Gashi mutum mai a?ida wanda baya son ko yaya aga gazawar nasa. Kuma dole yanzu yaga kamar an haWe masa kai. Don ko ita idan zata yi rantsuwa ta san babu kaffara da matu?ar wahala in ka cire Yaya Babba da Amma a sami mai barin Wansa namiji ya yi wannan karatun.

"Hayatu kaje gidan Jafaru ka Wauko Wanka maganar nan ta mutu daga yau."

"Ai nayi rantsuwa Gwaggo. Akan Taj wallahi ba zan yi kaffara ba."

Cikin fushi Yaya Babba yace "Nima kuma wallahi ba zan zama silar raba Wa da iyayensa ba. Idan rashin albarka ya bishi a dalilinka duniya ni za ta zaga."

Gwaggo dai gajiya tayi da basu baki ta kama hawaye tana cewa don babansu baya duniya shi yasa su ke yi mata haka.

Amma da bata ce uffan ba tun farkon zamansu ce ta katse musayar yawun da suke.

"Gwaggo ki zama shaida. A gaban kowa duk sun yi rantsuwa ba za su zauna da Taj ba. To ni ina so kuma dashi zan koma. Zan ta?aita hutuna mu baku wuri ku sha iska."

Kallonta kowa ya kama yi kafin kuma mazan su nuna a gidansu zai zauna.

"Jamila zai bi domin babu amfanin ya zauna a nan kowa yana yi masa kallon wanda uba ya kora." Gwaggo ta kashe maganar.

"Gwaggo ina so ki min shaidar ?arshe. Yadda kowa baya son a shiga abin da ya shafe shi da ansa to nima kada wanda ya shigar min gonata. Zan yiwa Taj abin da zan yiwa Wan cikina tsakani da Allah."

Kafin kowa ya sake magana ta tashi ta fice daga gidan gabaWaya.

Kamar wasa ?aramar magana ta zama babba. Da kaWan da kaWan zance ya zaga zuri'ar gidan kowa ya san me yake faruwa. Wasu na goyon bayan Taj wasu na ganin laifinsa. Inna da Mama sun fi kowa shiga tashin hankali. Sai Kamal da ya kwanta ciwo sosai. Alhaji kuwa tunda Amma tace za ta Wauke shi ya san sai abin da Allah Yayi. Bai fasa ganin laifin Mama ba akan zama mutum ta farko wajen haWa shi da ?an uwansa da kuma raba shi da Wansa. Irin abubuwan da ya dinga yi mata sai da ya kaita ga yin yaji. Tana ficewa kuwa Inna ma ta kama gabanta. Butulci ne zai sa ta cigaba da mi?e ?afa a gidan da mai son Wanta ta kasa zama. Hajiya da Umma da basu tafi ba ba daWinsu Alhaji yake ji ba. Abu sai da ya kai anyi zama na musamman da dangin kowannensu. An sasanta dai amma tunda Taj ya bar gidan kaso mai yawa na walwalar gidan ya kau.

***

Tafiya Amerika yana bu?atar visa da dogon cike ciken takardu wanda Amma take ganin Sacin lokaci ne. Saboda haka ta nemi visar India da passport Winta na ?ar ?asa na Amerika. Nan da nan ta samu. Cikin sati biyu suka bar ?asar. Dama Abuja ta koma dashi. Ita ta kai shi makaranta ta jira komai ya kammala bisa tsari. Zai cigaba da aikinsa a wurin Paaji a duk ranar da bashi da lecture kamar yadda ya yi lokacin degree Winsa na farko.

Da za ta tafi ta kawo kuWi ta bashi.
"Kada ka kunyata ni. Kada kuma kayi abin da zai ?ara girmama rigimar Yaya Hayatu da Yaya Babba. Ka kiyayi duk wani abu da Allah baya so. Shi kuma ba zai bari ka taSe ba."

Rufe ido ya yi yana kuka. Ta dungure masa kai "meye haka? Da Yaya Hayatu zai ga wannan kukan ai cewa zai yi abin da yake gudu ya faru."

Dariyar dole Taj ya yi. Ta rungume shi tana rarrashi. Duk da yaji bambarakwai amma sai hakan ya sanyaya masa zuciya.

"Bana son ragwanta. In shagwaSa ce dai I will indulge you amma ragon namiji baya burgeni kaji ko?"

Murmushi yayi. A rayuwarsa zai iya ?irga sau nawa ya haWu da Amma. Ya san tana da kirki amma bai san halayenta irin waWanda yake gani yanzu ba. Uwa da uba ya samu a dunkule a tare da ita. Ta ?arfafa masa gwiwa sosai sannan ta faWa masa zata yi ?o?ari kafin lokacin hutu tayi duk abin da ya dace domin ya sami visa.

Wannan shi ne mafarin zaman Taj a Amerika. ?a?an Amma sun yi aure. Su suna Minnesota babbar Anisa kuma tana aure a Florida. Iman kuma a Lagos take zaune da mijinta. Yayinda maigidan yake yawo tsakanin Nigeria wurin amaryar da ya yi bayan ya yi ritaya da Amerika.

Sai ya kasance bayan Taj ya gama karatu shi da ita ne a gidan kodayaushe. Sun sha?u matu?a. Tana aikinta shima yana yi awani restaurant da ya yi fice a abincin Asia da Afrika. A wurin ma'aikatan wurin ya koyo nau'ikan abincin gargajiya na Nigeria na ?abilu daban daban. Cikin Wan lokaci ya yi suna sosai. Takanas aka zo aka gayyace shi gasar da ta ciwo masa wasu ma?udan kuWaWe bayan ya sami nasarar yin na biyu. Da kuWin da kuma tanadinsa tun na India yake son buWe mall a Kano.

Rashin zuwansa gida bai hana shi mu'amala da ?an uwansa da iyaye ba. Musamman yanzu da aka sami cigaban hanyoyin sadarwa. Suna yawan bidiyo call ana ganin juna musamman yayin aure da haihuwa. Alhaji ne kaWai baya Waukar wayarsa har yanzu. Amma ta tilasta masa tura masa sa?on gaisuwa kullum rana ta Allah na kar ta kwana. Sai dai da yake zuciya bata da ?ashi, ya ri?e uban a zuciyarsa. Ya Wora masa alhakin raba shi da ahalinsa. Da nesanta fuskarsa da ta mahaifiyarsa. Shi yasa ya ?udurcewa ransa ba zai sake taka gidansu ba sai Alhaji ya neme shi da kansa.

***

Hutu ya ?are lafiya. Ranar da ?an makarantar kwana za su koma Hamdi bata samu ta runtsa ba. Tana fama da tararrabin yadda Ummi za ta kwance mata zani a kasuwa. Duk siyayyar da Abbanta ya yi mata babu abin da ya burgeta. Rashin fara'arta ya dami Yaya har sai da ta kai ga yi mata magana kafin Abba ya kaita tasha.

"Sai da aski ya zo gaban goshi nake ganin alamun rashin son komawa a tare dake Hamdi."

Zee ma ta ce "Ya Hamdi ko kukan bodin za ki fara a term Win ?arshe? In faWawa Abba a dawo dake makarantarmu?"

Duka Hamdi ta kai mata da wasa a ?o?arinta na danne damuwarta. Bayan fitar Zee daga falon Yaya ta muskuta kusa da ita.

"Hamdiyya."

"Na'am" ta amsa a raunane.

"Na san baki so zuwan iyalin Maje gidan nan ba tunda aka zo da Ummi."

A zabure ta kalli Yayan da tsananin mamaki. Ita kuwa tayi murmushi.

"Kina mamakin yadda aka yi na sani?"

Ta gyaWa kai.

"Kin guji gida saboda kada a san waye mahaifinki. Yanzu kuma gashi an zo an ganshi har gidan kina tsoron kada asirinki ya tonu."

"Yaya..." ta soma faWi cike da kunya.

"Ki koyi son abin da Allah Ya baki sai Ya ninka miki da wanda baki zata ba."

Yawu ta haWiya "to."

Yaya ta cigaba da cewa "Ban taSa nadamar auren mahaifinku ba saboda bai bani wannan dalilin ba. Irin kulawar da muke samu daga gare shi wasu masu kuWin sai sun yi kishi da mu. Zaman lafiya yafi zama Wan sarki. Hamdi sandar hannunka da ita kake duka kin ji. Hangen ta hannun wani ba naki bane don baki sani ba ko duk ?aya ce ko bata ma da ?wari."

Numfashi ta sauke ta sadda kai ?asa ta bawa Yaya ha?uri. Ita kuwa da yake ba mace bace mai ri?o ko son ayi ta nanata zance sai cewa tayi a bar maganar.

To a haka Abba ya dawo shabiyun rana ya sanar dasu Baba Maje na nan tafe zai kai su makaranta tare da Ummi. Ya ?are da faWin,

"Tare zamu tafi."

Albarkacin Yaya dake zaune a wurin da nasihar da tayi mata Wazu ne kawai ya hanata fasa ihu. Ta rasa inda zata tsoma ranta taji daWi. Addu'a kawai ta kama yi Allah Ya kawo sanadin da zai fasa binsu don gudun kada ya dinga sakin baki a gaban Ummi.

Addu'arta ta ?arbu domin an fara zuba kayanta a motar Baba Maje sai ga wani dattijo yana sallama da Abba. Kana ganinsa baka bu?atar ?arin bayani za ka gane ba mutumin kirki bane. Shadda ce yellow shar a jikinsa tana uban ?yalli ga hula ya harbo gaban goshi irin na tsofaffin ?an duniya. Taunar cingam yake cakakal-cakakal yana karkaWa mu?ullin mota. Ga wata uwar yatsina yana faman yi a yayinda idanunsa ke ?arewa layin gidan kallo.

"Maje anya ba za ku tafi ba kuwa? Ban san me ya kawo shi ba amma ina jin ba abu bane da zamu ?are da wuri."

"Ba dai abokin sana'arka bane ko?" Baba Maje ya tambaya don yanayin mutumin babu sha'awar son kusanci da shi.

"Agent Win wanda nake hayar gidan abincina ne."

"To ko dai mu jira?" Baba Maje ya sake cewa da ?ar damuwar yadda yaga abokin nasa kamar baya cikin nutsuwa.

"A'a, ku tafi kawai."

Godiya ya yi masa akan biyowa Waukar Hamdi sannan ya juya wajen mutumin su kuma su ka shiga mota.

Akan hanyarsu Baba Maje yayi ta ?o?arin haWa hira tsakanin Ummi da Hamdi. Da yake Ummi akwai wayo sai ta fishi jan Hamdin a jiki. Ya kuwa ji daWin hakan sosai.

Abba da ba?onsa kuwa ba komai su ka tattauna ba illa ?arin kuWin haya da aka yiwa gidan abincin nasa. KuWin ya yi biyun abin da yake biya. Ya fara ro?on alfarma mutumin ya ce sai dai ya tashi. Dama kuma ya samo mai biyan wannan farashin ne. Ya kuma san babu yadda za ayi Abba ya biya. Shi ne ya zo masa da dabara.

"Idan na tashi yaya zan yi da iyalina? Don Allah ka rage min wani abu."

"Sati biyu zan iya baka ka tattare komatsanka ka tashi. Idan kuma kuWin sun samu kafin nan sai ka kawo a sabunta kwantiragi."

Yana gama faWin haka ya shige motarsa ya tada ?ura ya bar unguwar. Abba ya koma gida da sanyin jiki ya labartawa Yaya halin da ake ciki.

***

"Ki fara kai min nawa kayan Waki don akwai abin da nake bu?ata yanzu a ciki."

Ko minti biyar Baba Maje bai yi da barinsu da kayansu da za su kwashe su kai hostel ba Ummi ta rikiWa ta koma annobar ?an FGC.

Wani irin kallon mamaki Hamdi ta bita da shi "ban gane ba."

"Au...kin daina jin hausa ne saboda mun shigo school? To jirani a nan. Zan aiko miki da yaren da za ki fahimta." Da tafiyarta ta ?asaita ta wuce ta bar Hamdi a tsaye.

Ita kuma ganin ta tafi ta fara Waukar kayanta ta nufi hostel Winsu. Tana ajiyewa ta koma da sauri domin Webo sauran sakamakon garin da hadari saboda damina da ta tsaya sosai. Da isarta ta iske wata yarinya da ta tabbatar cikin ?an koran Ummi take. Wata tsadaddiyar waya ta fito da ita daga ?asan hijab ta yafito Hamdi da hannu. Da taga bata matso ba kawai sai ta danna wayar. Nan da nan wurin ya karaWe da muryar Abba inda yake cewa (Altine kece haka? Ikon Allah) da muryar nan tasa da ko ita ?arsa bata so.

Hankalinta ya yi masifar tashi. A take ta ji?e da wani irin gumi. Ta mi?a hannu a firgice za ta karSe wayar sai yarinyar ta ja da baya.

"Ummi ta ce ki kwaso mata kayanta idan ba haka ba duk makarantar nan kowa sai ya gani"

"To" ta amsa da sauri tare da du?awa ta fara Waukar kayan.

Yarinyar ta yatsina fuska "no, ta ce da Wai-Wai za ki Wauka."

"To" Hamdi ta sake amsawa da rawar jiki.

Banda akwatuna biyu akwai manyan ledoji uku. Haka tayi sawu biyar tana zuwa hostel Win su Ummi. Bata ganta ba sai da ta kai ledar ?arshe ta sameta zaune akan gadonta.

"Ina za ki baki jera min ba?"

Cak ta tsaya ta dawo da sauri ta jera kayan a kwanar Ummin. ?an Wakin su ka zuba musu ido suna ganin ikon Allah. Bayan ta gama a gadarance Ummi ta ce mata gobe ta zo da wuri ta Webo mata ruwa. Ta amsa kawai ta fita.

Da ta fita ko ganin hanya bata yi saboda hawayen da ya cika mata idanu. Da haWa hanya ta isa inda sauran kayanta su ke ta kwaso. An soma yayyafi ga iska mai ?arfi. Saboda haka akwatin da jakar sun yi buWu-buWu. Zuciyarta a ?untace ta tafi nasu hostel Win. Ajiye kayan kawai tayi ta hau gado ta dun?ule jikinta tana kuka. Nan da nan wurin ya cika da mutane ana tambayarta me yake faruwa amma ko Wago kai bata yi ba. Sai wata ce da taga yadda ta dinga Wiban kayan Ummi ta basu amsa.

"Wannan hutun da alama ita Ummi Maje za ta takurawa."

Alhini da tausayi su ka dinga nunawa bayan ta faWa musu me ta gani. Abin bai yi musu daWi ba domin kuwa Hamdi bata rigima.

"Lallai Ummi bata da sauran rabo don ko mu masu baki da take zalinta bamu yafe ba balle mara baki irin Hamdiyya."

Wadda tayi maganar tana rufe baki wata ma ta kama. Su ka taru su ka gama Webe mata albarka (mu guji irin waWannan laifukan da bama Waukarsu a bakin komai. Babu wani ha??i abin rainawa) sannan su ka watse.
RAYUWA DA GI?I 7




Batul Mamman=ؖ?


Sanarwa
In sha Allah post zai dinga zuwa ranakun Litinin zuwa Juma'a.





***

Ummi dai baje kolin rashin mutumcinta tayi akan Hamdi har ya kasance sauran Walibai suna samun sararawa. Kowanne aiki Hamdi, kowacce bola da shara ma ita Win dai take nema. Wanki harda na su pant

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login