Showing 117001 words to 120000 words out of 182745 words

Chapter 40 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

121

kunnuwansa ranar da Zabba'u ta kawo mata tana cewa sunanta Ra?umi da akala. Har tana yi mata rantsuwar idan ta tauna ko me ta umarce shi zai aikata. Burinta a lokacin tunda ta haifi Ahmad yana ?arami ta fitar da su Hajiya.

?in nuna musu ya gani ya yi. Ya kuma bari tayi amfani da ita. Ranar ta yiwa Hajiya Wiban albarka ajin ?arshe duk yana jinsu daga Waki. Zuciyarsa kamar ta fito ta baki amma ya kasa fitowa saboda a kan idonsa ta saka a bakin ba tare da ta san yana gani ba. Ta tauna ta umarce shi da ya zauna a Waki kada ya fito ko me zai faru.

Haka kuwa aka yi. Rigima ta kaure amma duk yadda yaso haka ya zauna a Waki. Don ba?inciki har hawaye sai da ya yi. Sai kuma ya shiga karanto addu'o'in tsari tunda ya gama gano illar layar. Lallai idan ya zauna da ita rayuwarsa za ta zama mara amfani.

Shigowa Mami tayi da aka gama faWan tana kumbure kumbure.

"So nake ka saki Haj. Gambo yanzu yanzun nan."

Ko Waga kai ya kalleta bai yi ba ta sake maimaita umarnin amma shiru. Dama layar na hannunta sai ta Waga ta juya masa baya za ta mayar cikin bakin. Bata yi aune ba taji ya dam?e hannun ya zare layar.

"Ki je gida na sake ki saki uku."

Farat Waya ya faWi maganar don kada a sami matsala. Ta kuwa dafe ?irji a gigice.

"Haj. Gambo nace..."

?arfin gwiwarsa ya dawo gare shi ya ce "ni kuma ke nace."

"Wallahi baka isa ba...wayyo Allah. Na shiga uku. Alhaji ina zani? Ina kake so nayi da Ahmad bayan ka san ni marainiya ce?"

GabaWaya kamanninta sauyawa suka yi a take. Tana wannan hargagin ya kira Mama ya ce ta Wauko Ahmad duk inda yake a gidan ta goya shi.

"Idan ba ni ba kada ki bawa kowa har uwar da ta haife shi."

Mafarin da goyon Ahmad ya koma hannun Mama kenan. Ba a raba Wa da uwa amma bai san sunan da za a kira shi ba idan ya bari jininsa ya tashi a gidan shirka. Haka ya nunawa iyalinsa cewa faWan da ta takali Hajiya ne yasa shi sallamarta. Ya kuma yi ne don kyautata ?imar Wansa a gidan. Daga lokacin bai sake shiga harkarta ba sai da ta fara Worawa Ahmad Win bu?atun da su ka fi ?arfinsa yaje ya samawa mijinta aiki. Baya son haWa inuwa da mushiriki kuma wanda yake tu'ammali da tsibbu. Shi yasa ya nesanta kansa daga gareta. Baya bari komai ya haWasu. To amma yau dai tura ta kai bango. Idan tana cin ?asa lallai ta kiyayi ta shuri. ?arta ko ita ce autar mata kuma masoyiya ga Taj ba zai taSa sahale masa aurenta ba.

Wayarsa ya Waga da sauri ya kira Taj...abin da rabonsa da yi har ya manta.

***

?irjin Anti Zahra dukan tara tara ya kama yi da ganin wannan rashin hankali da ake yi mata a gida. Inda su ka sami ?arfin halin iya shigar mata kitchen su ka yi binciken kayan abinci da girki shi ne babban abin mamaki. Gashi an zuzzubar da shinkafa akan kafet. Yaran babbar ?ar Anti Zabba'u sun tattake wata a wurin. ?arnin kifi kuwa ba a magana. Mai?on duk an shafe a kujeru da centre table don ?eta. Wata ma remote ne a hannunta na daman. A hagu kuma tana ri?e da kofin da aka keSe domin maigidan ta cika shi da juice.

Shi kuwa Ahmad Anti Zabba'u da Salwa yake kallo yana neman wadda za ta yi masa bayani. Saboda yadda ransa ya Saci kuwa Adam's apple Winsa hawa da sauka kawai yake yi ya kasa magana. Gani yake duk kalmar da za ta fito bata da ?arfin nuna yadda yake ji a zuciyarsa.

Anti Zabba'u ko a jikinta domin da shirinta ta fito. Ta saki rai tayi musu maraba kuma bata damu ba da basu amsa ba. Sai ma kaWa baki da tayi ta ?walawa ?arta da ta tafi kitchen ?aro musu juice tayi. Ita ce ake so Ahmad ya aura yanzu.

"Habitti (Habibty take kiranta saboda tafi ?an uwanta kyau, sunan sai ya bita) fito ga yayan naki ya dawo." Ta kalle shi "tun Wazu take damunmu da mitar ka ?i dawowa."

Daga cikin kitchen Win aka ?wala ihu duk wai na murna sannan wata ?ar tsumburburar budurwa ta fito da sassarfa cikin farinciki. Sanye take da matsatsen wando skin tight wanda daga gani a can ?asan dilar gwanjo aka samo shi. Ta Wora masa wata yarbatsulan riga mai rawa a jiki da wasu irin igiyoyi. Sai da ta tabbatar ta haWa ido da Anti Zahra sannan ta buWe hannuwa.

"Yaya Ahmet oyoyo."

Saurin shiga tsakaninsu Anti Zahra tayi don ta kula Ahmad bashi da niyar kaucewa.

"A gabana? Baki da hankali da alama." Cewar Anti Zahra cikin fushi "nayi miki kama da matan da za su Wauki wannan Wabi'ar ta wasan banza tsakanin cousins?"

Da wani salon shagwaSa Habitti ta ce "Ya Ahmet kana jin matarka ko?"

Ko kallonta bai yi ba balle tasa ran yaji ?orafinta. Hankalinsa ya tattara ya dubi matarsa.

"Me yasa ki ka shiga tsakaninmu Zahra? Da kin barta ta ?arasa abin da tayi niyya."

Anti Zahra taji wani abu ya soki zuciyarta. Ita kuwa Anti Zabba'u har ta fara murmushin ?eta sai taji ya cigaba da magana.

"...ni kuma sai na nuna mata idan tana ta?ama ta sha nonon hauka to nima na tsotsa tunda duk tushenmu Waya."

SiWe hannu Anti Zabba'u tayi da sauri ta mi?e tana taro zanin da ta kwance domin taji daWin yin lodi.

"Ahmad ni ce mahaukaciya?"

"Kin ji na ambaci sunanki?!"
Yayi magana muryarsa a sama. Yau da yarinya ce tayi masa haka da wahala idan bai zane ta ba.

Ita da ?an matan duka jikinsa sanyi ya yi don ba haka su ka zata ba.
"Rashin kunya za ka yi min don na zo gidanka jinyar mahaifiyarka?"

"Jinya ki ka zo? Wa ya kira ki?" Ya buWe mata wuta.

Anti Zahra sai da taji babu daWi ta Wan taSa hannunsa "?anwar Mami ce fa. Ka sassauta harshenka a kanta."

"Kin fini saninta ne?" Ta girgiza kai da sauri don bata taSa ganin fushinsa irin wannan ba. Anti Zabba'un ya sake kallo "cikin waannan ?a?an naki babu wadda za ki je gidan aurenta ki yi wannan abin ba tare da mijinta ya yi muku kallon rashin nutsuwa ba. Kin kuma sani amma shi ne ni ki ka yi min saboda ga karkatacciyar kuka mai daWin hawa ko?"

Hankalinta sake tashi ya yi don yau tv ta sayar daga lokacin da Salwa ta kirata ta haWa kuWin aikin da aka yiwa Habitti.
"Saboda uwarka tana kwance shi ne za ka ci min mutumci?"

"Idan da ?alau take ba ki isa ki shigo gidan nan ba wallahi. Yau nayi aure? ?a?ana biyu fa! amma ko sau Waya babu ke babu waWannan abubuwan..." ya nuna matan da jikinsu ya gama la?was sama da ?asa.

Babbar ce ma Hansatu ta Wan taSuka abin kirki ta tashi tsaye "idan ka cigaba da faWawa mamanmu magana fa ba za mu yarda ba."

Da wutsiyar ido ya kalleta sai gata tayi tsit ita ma. Ya juya ga Salwa da ko tari bata yi ba tun shigowarsu. Babu shiri tayi ?asa da kanta ta kama hanyar Waki za ta wuce sumsum.

"Idan kin wuce ciki wane mahaukacin ne zai yi min bayanin me yake faruwa da gidana? Ban soke batun zuwan nasu kafin na fita ba?"

"Yaya..."

"Ina raga miki ne kawai saboda ke mace ce, ba don haka ba da tuni na sauke miki abin da yake damun ?wa?walwarki. Shashasha wadda bata san ciwon kanta ba."

Rasa da me za ta ji tayi. Da Sacin ran Ahmad wanda bata saba gani ba, ko kuwa da ganin da Innar Taj tayi mata dumu-dumu a wajen dinner akan abin da take shirin yi? Ha?uri ta buWe baki za ta bashi ya Waga hannu ya dakatar da ita.

"Ku haWu ke da su ku kwana a Wakin da ki ke. Gobe da safe..." ya ciro dubu goma daga aljihunsa ya ajiye akan centre table yana kallon su Anti Zabba'u "ku Wauki wannan ku yi kuWin mota kuma a gyara min gida kafin a fita." Ita kuma Salwa ya ce "ke kuma zan kira babanki ya turo mai Waukarki ki koma gida. Kuma wallahi kin ji na rantse idan ki ka fita daga gidan nan kafin lokacin tafiyarki sai na baki mamaki."

Yana gama magana ya shige Wakin Salwan ya Wauko Mami kamar jinjira don duk ta zuge. Kai tsaye Wakin Zahra ya wuce da ita kowa yana ganin hawaye shaSe shaSe da su ka ji?a fuskarta. Duk abin da aka yi tana ji. Tafi kowa sanin dole ?anwarta ta zo da wata manufa. Takaicinta da ko magana bata iyawa sosai yanzu sai dalalar yawu. Da ko zama a gidan Zabba'u bata isa tayi ba. Sai kuma murnar Ahmad ya nunawa duniya ya haifu. Wannan sau?in kan nasa da take ganin za a iya cutarsa yasa ?afa ya ture. Ya nuna mata shi Win jinin Alh. Hayatu ne babu ?arya.

Sai da ya kwantar da ita sannan ya ce da Anti Zahra ta Wauko duk abin bu?atarta da na yaran su koma Wakinsa.

"Idan tana bu?atar wani abu fa?"

"Zan dinga le?awa."

Bai amince ta kwana ba don ya sani akwai cin zali ma idan yace sai ta kula da Mamin da ta Wora mata karan tsana tun kafin aurensu.

*

Mummunar sha?a Salwa taji a wuyanta. Gashi bata san ko wace ce ba domin ta bada baya tana shirin cire kaya.

"Sakar min wuya" ta ce da ri?on ya yi ?arfi ta tabbatar ba na wasa bane.

"Mu za ki yiwa shigo-shigo ba zurfi ki sa a ci mana mutumci?"

Da mamakin muryar ta ce "Anti ni za ki sha?ewa wuya?"

"Haifarki nayi da ba zan sha?e ki ba?"

Da zafin nama Salwa ta juyo ta doke hannun nata. Ganin ta buWe baki tana shirin yi mata magana yasa ta ce "tunda baki haife ni ba nima ba zan kasa doke miki hannu ba."

"Wato na kula shiri ku ka yi da Ahmet ki ka taso mu don ku wula?anta mu." Cewar Habitti tana hura hanci.

Ba su san ran Salwa yafi nasu Saci ba saboda disappointments Win da ta kwasa. Shi yasa bata ji nauyin ramawa ba.

"KwaWayi dai ya kawo ku tunda uwarku na kira ba ku ba..."

Kiffff, taji saukar marin da yafi kama da gwaSe baki don sai da laSSanta su ka amsa. A take kuma idanunta su ka kaWa da ?wallar azaba. A makance ta kai hannu domin ramawa akan Hansatu da tayi marin sai hannun ya sauka a kuncin Anti Zabba'u.

Ita kanta Salwa sai da gabanta ya faWi da taga wa ta mara, sai dai kafin ta gama sanin me za ta yi ?a?an gwaggon tasu su ka yi mata rubdugu. Kowa na kai hannu aka lillisa mata jiki. Ihun ma da za ta yi don Ahmad yaji ya kawo mata Wauki an toshe bakin. Sai da su ka tabbatar tayi laushi su ka barta da ta daina ?o?arin kare kanta. Abinka da waWanda su ka saba da damben gidan haya.

Kukan da take fitarwa a hankali ga jini yana ta zuba daga hancinta ne ya sanya Anti Zabba'u cewa "Yanzu idan Ahmad ya ganta ya zamu yi?"

"Ba ma zai ganta ba. Kafin su tashi zamu kama gabanmu. Banda dare ai da babu abin da zai sa mu kwana" Habitti ta faWi tana sake dungure mata kai.

***

Shiru motar ba ka jin komai sai hawa da saukar numfashin Hamdi dake baccin gajiya. Musu su ke da Taj yana tsokanarta da cewa yau shi ya haskata tana cewa ita ta haska shi. Can sai ji ya yi ta koma uhm da uhm-uhm idan yayi magana. Yana juyawa yaga Waurinta ya karkace saboda yadda ta kwantar da kai a jikin kujera. Mamaki da haushin ta rusa masa plans Winsa su ka kama shi.

"Lallai ma yarinyar nan. Bacci ma kike yi a irin wannan lokacin?"

KafaWarta ya girgiza a hankali ta Wan buWe ido ta kuma rufewa.

"Ko ki tashi ko in wuce gidanmu dake" ya faWi yana karantar fuskarta.

Ko gezau bata yi ba wanda yasa shi tunanin tabbas bacci take yi. Don da ido biyu take ba za ta yi shiru ba. ?wafa ya yi ya kaWa kai.

"Allah Ya kaimu gobe nima sai na rama. Idan an kawo ki a kwance ina bacci za a ganni akan gadon amarya."

Nauyin baccin da ya rufeta bai hanata jin abin da ya ce ba. Murmushi tayi a Soye ta gyara kwanciyarta. Baccin kwanakin nan da bata samu ne ya yi mata kamun kazar kuku.

Taj cigaba ya yi da tu?in yana yi yana kallonta. A baccin ma tayi masa kyau. Sai da ya kusa shiga unguwarsu ciwon kan da ya soma ji bayan Salwa ta taSa shi ya dawo masa da ?arfi. Abu kamar wasa sai gashi yana gumi. Da ?yar ya iya ?arasawa ya tsayar da motar amma bai kashe ba. Sai da ciwon ya lafa ya fita ya zagaya gefenta ya buWe sannan ya ran?wafa yana kallonta sosai.

?amshin turarensa da numfashin da yake yi daf da ita ne yasa tsigar jikinta tashi tun kafin ta buWe ido. Yun?urawar da za ta yi yayi daidai da sake matsowar Taj. Kawunansu su ka haWu da ?arfi.

"Ya Salam" Taj ya dafa kansa da hannu Waya, ya kuma Wora Wayan a goshinta inda yake tunanin ta nan su ka buge.

"Fasa min kai za ka...." Hamdi ta fara cewa sai ta kula idanunsa sun yi ja da taimakon fitilar waje ta gidansu.

"Kuka kake yi? Kan nawa da zafi ne?" Ta tambaye shi ganin yana runtse ido. Bata san fami ta yiwa ciwon kan nasa ba.

Yadda tayi tambayar sai da yasa shi yin murmushi.
"Abu kamar auduga ina zafi a nan?"

"Awwnnnn" ta ce tana yi masa murmushi da fari da idanu "wai irin abin nan ace tsabar soyayya ka buge ma baka ji zafi ba."

Taj kasa jira ta gama magana ya yi. Tunda ta rangwaWa kai ta ce awwnnn Winnan ya daina gane komai. ?an yatsansa ya Wora akan bakinta yana zana leSen wanda ya sanyata shirun dole. Sannan ya zame hannun a hankali ya kawo kansa daidai fuskarta.

" I realy tried to be a gentleman tonight Mrs Happy amma kin hana."

"Me kuma nayi?" Hamdi tayi tambayar cikin faWuwar gaba don ta fara tsorata. So take ta ganta a cikin gida kawai.

"Baki yi komai ba sai taSa zuciyar Tajuddin."

Wayancewa tayi saboda take takensa da take gani ta ce "Wai ka san ma'anar sunanka kuwa?"

Shi ma da gatse ya bata amsa "Ta yaya zan sani baki faWa min ba?"

"Taj yana nufin crown, kaga Tajuddin yana nufin..." ta fara cewa ya katseta.

"Ina son ki Hamdiyya Habib Umar"

Sannan ya turo kanta ta hanyar turo kanta gaba da hannunsa da ya sanya a bayan kan. Sauran maganganun da su ke bakunansu basu sami damar shiga kunne ba saboda sabon al'amarin da Taj ya kawo musu. Tun hankalin Hamdi na kan ?ofar gidansu har ta manta a ina take. Sunan Taj ne kaWai yake tafiya tare da bugun zuciyarta.

Kamar ba za su rabu ba. Taj ne ya yi ta maza ya Waga kai yana kallonta da murmushi.

"It seems like zama dani ya fara shafarki fa yarinyar nan. Haka ake so. Wani abin ma sai gobe ko?"

"Kai da ka ce bacci za ka yi kafin mu ci kaz..." kasa ?arasawa tayi ta kama laSSanta ta Same da ta ankara da katoSarar da take shirin yi. Ba za ta so ya fassarata da rashin kunya ba. Ta sunkuyar da kai tana faman matsa hannuwa kamar mai tausar gajiya. Sai dai ta makaro!

HaSarta Taj ya Wago a hankali ta kawar da kai gefe ido a rufe. Yana murmushi ya ce,

"Kalle ni nan." Ya Wage gira

"Ni fa ba haka nake nufi ba." Hamdi ta ce kamar tayi kuka don wani kallon kya yi kya gama Taj yake yi mata.

"Me ki ka ji na ce?"

Cikin shagwaSa Hamdi ta ce "to ka daina yi min irin wannan kallon."

Amsar da ya tanada don ya cigaba da tsokanarta ya fasa faWi da yaji kamar an kwaWa masa guduma a ka. Haka kawai lokaci Waya abin ya ta'azzara.

Numfashi ya ja da ?arfi sannan ya ce "Kira min Abba don Allah."

"?ara ta za ka kai?"

Jikinsa nauyi ya yiwa ?afafunsa sai gashi ya yo kanta gabaWaya. Da fari ta zaci wasa ne sai da taji ya sakar mata nauyi yana jan hailala a hankali. RuWewa ajin ?arshe Hamdi tayi. Ta tattaSa shi tana kiransa bata ji ya amsa ba. Kansa ta Wago ta sanya hannunta Waya ta dafa kumatunsa.

"Don Girman Allah ka tashi. Wannan ba wasa bane wallahi."

Nan ma shiru sai numfashinsa da yake fita da sauri sauri. Da ?yar ta yun?ura ta Wauko jakarta ta zaro waya. Abba ta kira ya fito da gaggawa da yaji yanayin muryarta.

Da farko da ya hango ?afafun Taj ta ?ofar gaba inda take zaune har zai koma. Kunya ta kama shi sai yaji Hamdi na kiransa da ?arfi.

"Abba zo ka gani."

Ko da ya ?arasa bai san lokacin da ya kai hannu ya Wago Taj Win daga jikinta ba. Yadda duka gaSSanta su ke karkarwa haka nasa su ka fara. Da rawar baki Hamdi ta iya faWa masa iya abin da ta san ya faru.

Ido Taj Win ya buWe a hankali da yaji an Waga shi. Hamdi ta buWe bayan motar Abba ya taimaka masa ya shiga.

"Bari na duba waye yake gida tsakanin yaran Mal. Ba?o da Halliru sai mu kai shi asibiti."

Da sauri ya yi gaba zuwa gidan ma?otansa da su ka iya tu?in mota. Tafiyarsa ke da wuya kiran Alhaji ya shigo wayar Taj. Da kansa ya zaro ta daga aljihu ya mi?awa Hamdi. Cike da dauriya da cije baki ya ce mata idan Kamal ne kada ta sanar dashi don baya son tayar masa da hankali. In sun je asibiti sai a faWa masa.

Screen Win ta kalla lokacin kiran farko ya katse ta Waga kai domin faWa masa sunan da ta gani sai kawai ya kwantar da nasa kan a cinyarta ya rufe idon.

"?auki ko ki kashe. ?arar tana damuna."

RuWanin ciwon nasa da wata fargaba da ta shigeta saboda tsoron mai kiran ne su ka sa ta kiransa da sunan da taga Taj

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login