Showing 42001 words to 45000 words out of 182745 words

Chapter 15 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

97

ake zai iya canja mata WanWanonsa idan ta haWa. Sai Abban ya kira ya ce ko da yamma ne idan tayi Halifa ya kawo saboda ana so. Sai aka yi rashin sa'a Haiifan bai dawo daga makaranta da wuri ba. Ita kuma tana tsoron yin kwantai.

"Yaya zan kai masa da kaina."

Izinin tafiyar tayi mata sannan tayi mata kwatance yadda za ta gane. s
Sau Waya ta taSa zuwa tun dawowarta. Adaidata ta samu har can. Shagon a bakin titi yake a gefen wata plaza. Tana sauka ta matsar da kayanta gefe sosai ta kira Abba kamar yadda Yaya ta ce tayi idan ta iso. Kira huWu, wayar tana ta ringing babu amsa. Gashi ta?i jinin a dinga kallonta. Madaidaiciyar cooler Win da ta sako meatpie Win mai hannu biyu ta kinkima ta ?arasa.

Wurin a cike yake Masha Allah. Mutane suna ta kai kawo ana ta sayen abinci. A bakin ?ofa ta kuma tsayawa ta kira Abba. Wayar ko shiga bata yi ba wani ya fito ya ganta.

"Ahhh, wannan dai duk yadda aka yi Wiyarmu ce don ga kama nan. ?an mata shigo daga ciki. Aunty Simagade yau ana ta fama da ba?i."

Gaban Hamdi ya yanke ya faWi. Da ganin mutumin Abba zai girme shi. Duk da dai bleaching ya caSalSala masa fuska fiye da ta Abban. Ya wani sha jallabiya da Waurin ?irji. Kansa kuma ya yi Waurin ture ka ga tsiya da Wankwali irin zanin.

'Me ya kawo Wan daudu wajen nan?' Ta yi wa kanta tambayar cikin yanayin ?uncin rai.

Ashe kallo yana ciki. Tana sanya ?afafunta wani irin ba?inciki ya turnu?eta. Akwai kwastomomi da yawa a ciki. Amma fa a yau dandazon ?an daudu sama da huWu ne su ke ta karakaina wajen Waukar odarsu da kawo musu abinci. Muryoyinsu da ta?i jini sun cika ko ina. Sai shewa ake ana yiwa juna sha?iyanci. Ita kuwa waige ta kama yi tana son hango mahaifinta.

*

Ubangidan Abba a birnin Jedda lokacin da yake ganiyar daudancinsa ne ya zo Kano. ?ar Ficika ake kiransa saboda ?an?anta da ?warewa a iya shege. Duk wani mai ji da haya?insa idan ya gamu da ?ar Ficika a Saudiyya dai sai ya sauke kai. Clicks da connections na fitina babu irin wanda baya haWawa. A lokacin da suke tare da Abba ya so ?warai ya sanya shi a hanyar da kowa yake bi ya yi kuWi. Sai ya fahimci Habibu ba komai ne a gabansa ba illa girki. Shi dai a tura shi gaban murhu ya haWa abinci. ?aryar mutum ya ce ya taSa ganinsa a wani waje sama da wurin girki ko cin abinci. ?ar Ficika sai ya tsaya masa. Ko a bayan idonsa wani ya nemi yiwa Abba wayo ya sanya shi a gurguwar turba sai ya ci mutumcin mutum. Lokacin da Baba ma yaje wurinsa, da Abba zai dawo ?ar Ficika ne ya biya masa rabin kuWin jirgi.

Bayan dawowarsa gida babu abin da ya sake haWa shi da kowa cikinsu. Ya tattare wannan shafin rayuwar tasa ya watsa a shara. Yaran da suke aiki a ?ar?ashinsa kaf babu Wan daudu. Maza ne kawai masu ra'ayin girki a dalilin rashin wata sana'ar. To yau kwana uku kenan da ?ar Ficika ya nemo Abba. A kamen takari aka watso su gida shi da wasu yaransa. Gashi girma ya kama shi amma zuciyar nema bata mutu ba. A nan gida Najeriya kuma bashi da ido da ?afa kamar Saudiyya. Yana neman abin yi ne ya haWu da wanda ya san inda Abba Habibu yake. Shi ne aka kawo shi har gidan abincinsa.

Abba bai Soye masa sabuwar rayuwar da yake yi ba. ?ar Ficika yaji ya kwaWaitu da samun darajar da ya rasa a wajen danginsa. Shi da yaransa babu wanda baya fuskantar ?yama daga ahalinsa. Godiya ya yiwa Abba ya ce kuma zai buWe gidan abinci. Yana fata zai taimaka ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????masa.

"?an halak baya manta alkhairi. In sha Allahu zan maka iya ?o?arina."

"Idan babu damuwa zan so ganin yadda salon kasuwar take a nan. In zai yiwu ma kawai lokacin tafiyarka sabon restoran Win sai na karSi wurin nan."

Abba bai yi ?asa a gwiwa ba ya kira Taj ya sanar dashi. Shi kuma jin ta?aitaccen tarihin ?ar Ficika da tsoron da Abba yake na kada ya komawa rayuwarsa ta gidan jiya sai ya amince.

"Idan mai laifi ya so tuba yana da kyau a bashi dama. Rashin yin hakan na taimakawa wajen sake dulmiyar dasu cikin ayyuka marasa kyau."

Taj ya ce "haka ne Abba. In ya rasa samun aikin da zai bashi halal zai koma ya nema daga haram ko yaya take."

Da wannan shawarar Abba ya amince masa. Shi kuma saboda jindaWi ya ce zasu dinga tayasu aiki duk lokacin da su ka sami lokaci tunda ba su da abin yi. Shi ne fa su ka zo yau. Girki harda wanda Abba ya manta. Yaji daWi domin yau kasuwar ta buWe fiye da kullum. Ya ala?anta nasarar da kyakkyawar niyyarsa ta taimako. Don bai manta wula?ancin da ya sha ba sanda ya dawo. Da wanda ya gani a dalilin neman wurin kafa sana'a da ya rasa wancan.

*

"Kai, kai, kai...Tabarakallah."

Hamdi ta waiga baya ta haWa ido da wani ?armasasshen mutum da ita kanta ta fi shi tsayi. Kanta ya yi yana murmushi kamar zai rungumeta. Kafin tayi baya Abbanta ya janyeta gefensa. ?ar Ficika ya cigaba da murmushi yana kallonta.

"Wannan ma taka ce?"

Yaronsa da ta haWu dashi a waje ne ya bada amsa.

"Aiwa, baka ga kama ba? Anti Simagade an dasa kyakkyawar shuka tayi fure mai ?amshi." Ya faWi yana lan?waya hannu da juya idanu.

Wani irin Waci ya dinga kai komo a wuyan Hamdi. Da ?yar ta yiwa Abba biyayya ta gaishe da mutanen da ya gabatar a matsayin abokan sana'arsa a Saudiyya.

"Cewa za ka yi mu iyayenta ne. An riga an zama Waya. Za ku yi ta ganinmu har sai mun saba."

"To" ta ce da gatsali ta kuma juya ko coolar bata ajiye ba tayi waje.

Tana fita hawaye ya wanke mata fuska. Wannan wace irin rayuwa ce? Ta Wauka Abba girki da abubuwa na siffar mata kawai yake yi. Me zai sa ya mu'amalanci mutane irin waWannan? Don sai da ta gansu ne ma ta gane me ake nufi da asalin Wan daudu.

"Hamdi"

Sarai taji kiran da yake mata amma ta ?ara sauri. Kafin ta ?arasa titi ta dire coolar a gabanta ta Wagawa wani adaidaita sahu hannu. Kafin ya gama tsayawa ta faWa ciki su ka yi gaba.

Abba ya kalleta ya juya ya kalli ?ar Ficika da ya biyo shi.

"Ba dai ganinmu bane ya Sata mata rai ba?"

Murmushi ya ?a?alo "ahh haba dai. Sauri take yi."

?ar Ficika ya murmusa "ko kai a gabana ka ?arasa girma fa Habibu. Ta yaya zan kasa gane abin da na saba gani?"

Cike da jin nauyi Abba ya faWa masa yadda a baya bata ma son nuna shi a matsayin uba. Yana ganin babu mamaki yanzu wannan abin da tayi yana da nasaba da tunaninta na komawarsa ga Wabi'ar baya.

"To ko mu daina zuwa? In ya so lokacin da ka bar nan Win sai mu dawo?"

Allah Ya sani kamar ya ce eh, to amma nauyi da tunanin me zai je ya dawo a rayuwar su ?ar Ficika sai ya ce a'a. Yau kaWai da ya haWu dasu ya ga wani irin farinciki da annashuwa a tare dasu. Sun sake suna ta aikin abin da su ka fi ?warewa wato girki. Har sai da ya yi tunanin me yiwuwa tun dawowarsu babu wanda ya sami tarba mai kyau da mutuntawa sai yau.

***

Hamdi tayi kuka tun daga hanya har gida. Da ?yar ta iya labartawa Yaya abin da ta gani. Abba na dawowa kuwa Yaya ta kawo zancen ita ma nata ran a Sace.

"Yaya Habibu ka sani cewa bahaushe na cewa abokin Sarawo shi ma Sarawo ne. Yanzu duk wanda ya ganka da mutanen nan zai yi maka kallon irinsu."

Da laluma ya dubeta "Jinjin juya baya ba nawa bane ga wanda ya nemi taimakona. Duka duka yaushe muka sami wannan rayuwar bayan haWuwa da yaron nan Taj? Ko har kin manta cin zarafin da aka dinga yi min akan neman shago? Duk unguwar da naje sai su ce kada yaransu su yi koyi dani basa so."

"Naji kuma duk na fahimta. Amma hanyoyin samun lada ai suna da yawa. Shigowar mutanen nan rayuwarka a wannan lokacin da kake neman tada ?imarka a cikin mutane gaskiya ba zai haifi Wa mai ido ba."

Ta sake faWi cikin fushi. Duk yadda ya so Sullo mata ta?i amincewa. Tsayuwa ya yi akan bakansa shi ma. Yau dai Waya zai yi abin da yake jin ya dace ko ba zai faranta ran iyalinsa ba.

"A bar maganar nan. Indai ?ar Ficika ne, ba zan kore shi ba."

"To ai shikenan. Allah Ya kyauta Sacin rana."

***

Yadda Salwa ta matsawa Taj da waya da messages a duk wata kafar da zai gani, haka Anisa ma take yi. Gashi dai basu san da zaman juna ba amma kowacce ta matsa lamba.

Ita Salwa banda ?awa har Maminsu ta san irin soyayyar da take yiwa Taj. Da fari ta nuna rashin goyon baya saboda Wan tsohon miji ne. Sai da taji ta kuma ga waye Taj a wani bidiyon girkinsa a youtube da Salwan ta nuna mata tayi mubaya'a. Matashi ne mafarkin duk wata budurwa. Burin duk wata uwa da take son ?arta da arzi?i. Ko da wasa girkinsa bai zo ranta ba balle ya dameta. Yana da kuWi kuma ta san asalinsa. To me ya rage?

"Kada ki yarda ya manta dake. In ya tafi ki dasa kanki a cikin rayuwarsa."

"Ta yaya? Ko sau Waya bai taSa nemana ba da kansa."

Mami tayi dariyar manya "wannan ai duk ba wata matsala bace. Ke ki dinga bibiyarsa. Gaisuwa safe, rana da dare. ?an abubuwan nan namu na mata ku baku iya ba. Sai a zauna sakato ana jiran namiji ya yi komai."

Salwa ta sunkuyar da kai "Mami idan mace tana bin namiji fa wula?anta ta yake yi."

Taf...taji saukar duka a kafaWa. Rai a Sace Mami ta ce "banda shashanci dama ai ba da soyayya za ki bishi ba. Kulawa kawai. Ko kissar ma sai na koya miki?" Ta harari ?arta.

"Na fahimta Mami."

"Ko ke fa."

Da haka Salwa ta kafa masa ?ahon zu?a. Waya da sa?wanninta babu wani abu da zai bada ita har yasa Taj gudunta. Yayana sama Yayana ?asa ne dai. Gaisuwa, bibiyar ayyukansa da yi masa fatan alkhairi. Tun yana sharewa har dai bisa shawarar Kamal ya soma amsa mata a mutumce.

"Ba'a san inda rana za ta faWi ba. Ka daina wula?anta duk mai nuna damuwarsa a kanka."

"Kada ta sa rai ne Happiness."

Dariya Kamal ya yi "kai ma kamar wani Wan yaro in kayi wani abin. Ai yadda ta zo maka a ?anwa haka za ka je a matsayin yaya. Tunda baka so ta bijiro da zancen soyayya sai ka toshe ?ofar."

"Kamar ya?"

"Ka dinga bata labarin wata a matsayin budurwarka. Wataran ka ce ma tana gaisheta."

Girgiza kai Taj yayi kamar yana gaban Kamal Win "ba zai zama cin fuska ba kuwa?"

"A ?anwa fa tazo maka. Kuma dai kayi mata hannunka mai sanda ta?i Waukar haske. Ba sai ka bita ba kawai a tafi a haka. Ya dai fi akan ka dinga shareta wanda za ta fassara a matsayin wula?anci."

A haka suke ta tafiya. Ya Taj da ?anwarsa Salwa.

A Sangaren Anisa kuma bai san wane tudu wane kwarin aka bi ba sai ji ya yi Amma ta tado masa da zancen ko za su fara haWa lefe kafin su koma gida.

"Lefe kuma? Na wa?" Ya tambayeta kai tsaye babu mamaki a tare dashi.

"Kada ka raina min wayo Taj. Ya ku ka yi da Anisa?"

"Anisa kuma?"

Amma ta Waure fuska "Allah idan na sake magana ka ce min 'kaza kuma?' Sai ranka ya Saci."

"Yi ha?uri Ammana." Ya yi mata murmushi.

Mayar masa tayi sai kuma ta sake shan kunu.

"Ka san sau nawa Daddy yana yi min maganarku? Sai dai nayi ta kame kame saboda ka ?i cewa komai."

Yadda su ka yi da Anisa da Hajjo ya faWa mata.

"Ni na zata mun gama magana tunda ta fahimceni."

Yanayin Amma duk babu wani kuzari ta ce "Maganar da aka fara daga sama ai a can ya dace a ?are ta. Me yasa ba ka faWa min ba?"

Ya yi shiru. Ba zai iya ce mata yaga kamar tana so ba shi yasa ya kasa sanar da ita ba.

Anti da kanta tayi mata waya tana cewa wai ta kira tayi mata murna ?arta ta sami miji. Anisa da Taj sun daidaita.

Da murna Amma amsa mata da "cewa zaki yi na cigaba da tari. Allah Yasa damu za ayi."

"Amin amin" Anti ta amsa da farinciki.

Da su ka yi waya da Daddy ma zancen kenan. Har yana cewa idan su ka dawo da kansa zai yiwa Alhaji magana. ?udurin Taj na aure bayan ya koma gida ba abin a kawo ido a zuba masa bane. Dole su za su yi nasu ?o?arin a yanzu da Taj ya zama successful su mayar dashi gaban mahaifinsa.

Ya gama tsare tsaren hanyoyin da zai bi domin bawa Alhaji ha?uri ya janye fushinsa. Wanda hakan ya yiwa Amma daWi sosai. Shi ne ta tayar masa zancen shi kuma ya nuna ba haka aka yi ba.

"Ni yanzu ya kake so in yi Taj?"

Ta ma rasa ta inda za ta Sullowa lamarin. Idan ta nuna bata so a yanzu da maganar ta fito daga bakin kishiyarta da mijinta kowa ita zai zarga. Za a ce ita ce bata so. Sannan ga dukkan alamu ma dai gadar zare Hajjo take neman ko ma a ce ta ?ulla mata. Kuskure guda zai sa a ce tana gudun ?ar kishiya. Ko kuma a gorantawa Taj rufin asirin da aka yi masa. Ta san Hajjo sarai. Idan abu bai tafi yadda take so ba to mutum ya shiga Wari ba ma uku ba.

"Kasan me nake so da kai?"

Ya girgiza kai "ko mene ne zan yi miki Amma."

"Kada ka nuna musu komai ta waya yanzu. Don Allah ko da wasa kada kayi abin da Anisa za ta sami maganar da za ta kaiwa Hajjo. Idan mun koma gida sai ayi maganar a gaban kowa. Yanzu ko me zamu yi a waya babu mai fahimta."

Ko da Daddy ya zo lokacin da za ayi mata send-off party na retirement basu nuna komai ba ita da Taj. Lafiya lafiya yake waya da Anisa su gaisa. Idan bata kira ba sai ayi sati biyu bai nemeta ba. Bisa shawarar Anti da Hajjo da su ka kitsa wancan zance na amincewarsa duk da Anisan bata so haka ba take yawan kiransa ko ta tura sa?o ta whatsapp.

Wata gomq sun ?are kamar ?ifta ido da buWewa. Duk wani shiri na komawarsu gida ya kammala. Catering services Winsa na Happy Taj ne dai bai rufe ba. Duk lokacin da bu?ata ta tashi zai iya komawa ya yi aikinsa ya dawo gida.

Zuciyarsa a ranar da za su tafi tana cike da Wokin sake ganin Hamdi. Ba tare da saninta ba, duk wasu abubuwa musamman wanda su ka shafi samari yana sani a wajen ?an uwanta. Zee akwai surutu. Ita ke faWa masa irin abin da Hamdi take yiwa samari idan sun zo.

"Ni fa ina ganin kamar akwai wanda take so" ta taSa faWa masa watarana.

Murmushi yayi shi kaWai da ya ji muryar Hamdi tana cewa Zee "gulmammiya, yau kuma faifaina aka buWewa Salman Khan? Ki gama Yaya tayi mana shari'a don ba yarda zanyi ba."

Zee ta diririce, wayar da bata gama ba kenan ta tashi tana bata ha?uri.
Ita kuwa kaza huce kan dami tayi. Mutumin nan na Abuja da bata san sunan shi ba ta riga ta cire shi a rai, tana kuma jin haushin yadda ya jirgata ta hanyar nuna kamar ya damu da ita.

***

Dogon tsaki mai madda da gunna Ummi ta saki a lokacin da Iyaa take duba katunan bikin Sajida da Yaya ta kawo da kanta.

"Allah Ya shiryeki Ummi. In Allah Ya so ba zan taSa aibata ki da bakina ba balle ki fi haka."

"Me kuma nayi? Yanzu mutum bai isa ya yi tsaki ba sai an fassara shi?"

Tashi Iyaa tayi ta bar falon. Idan ta zauna tabbas za ta ?are da dukan Ummi da duk abin da ya zo hannunta. Haka su ke ta fama tun bayan dawowarta daga makaranta. Ummi ta kangare fiye da tunaninsu. Maganar aurenta da aka sa ran yi da ta gama makaranta tabi ruwa. Mijin dama na gida ne. Duk shaiWancinta tana masifar son sa kamar rai. Zancen duniya da baya Suya sai gashi mahaifiyarsa da su ke ?an maza zar da Baba Maje sannan ?ar mace da namiji da Iyaa ta zo har gidan neman ?arin bayani.

Yayinda Ummi take ta tsula tsiyarta a makaranta bata taSa tunanin akwai idon sani da za su iya kawo zancenta gida ba. Sai gashi a hawan hawa maganar bullying Winta da haura katanga tana bin samari yawo ta dawo. Maganar ayi ?arya ko kwaskwarima ma ba za ta yiwu ba. Dole su ka faWi gaskiya da ro?on rufin asiri.

"Maganar nan ba za ta taSa fita daga bakina ba in sha Allahu. Amma fa aure babu shi Fisabilillahi"

Baba Maje ya kalli ?ar uwarsa, sai dai bai ji haushinta ba sosai. Ko shi ne zai iya yin haka.

Washegari ya mayar musu da kuWin aurensu. Kayan kuma su ka ce a barsu. A ranar babu wanda ya runtsa a gidan. Ummi kusan hauka tayi musu tuburan. Kuka da magiya harda barazanar tana son auren.

"Kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa. Ke ki ka ha?awa kanki wannan ramin. In kina da hankali sai ki canja tsarin rayuwarki don gujewa maimaici."

Tana gunjin kuka ta ce "yanzu Baba akan Wan daudu da ?arsa ka gwammace rayuwata ta zama haka? Baka barni nayi jarabawa ba sannan auren ma ka kasa hana a fasa shi?"

"?an daudun ne kuma yake ta fafutukar ganin kin koma makaranta ba." Ya ce da faWa "amma da yake kin daWe kina taSa mutumcin mutane Allah Yana yi miki talala yanzu ai kin ga ishara. Duk ?o?arinsa abu ya?i ci ya?i cinyewa. Ni kuma da hannuna ba zan sake kai ki wata makarantar ba."

Gidan da su ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login