Showing 24001 words to 27000 words out of 182745 words

Chapter 9 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

89

gani a ?waryarki."

Fuskarta yaSe yaSe da majina da hawaye ta ce "Baba ka yafe min."

"Ba dole na ba? Idan nayi miki baki rayuwarki ai sai tafi haka lalacewa. Ki tashi ki haWo kayanki don kin gama karatu kenan."

"Alhaji ba ayi haka ba." Principal ta sa baki "ka bari mu Wauki matakin da ya dace."

"Maje kada ka Wauki hukunci cikin fushi."

"Kun san Allah Waya ne ko? To wallahi yarinyar nan ta gama karatu a ?ar?ashin ikona."

Ya kalli Uncle B ya yi wani irin murmushi mai ciwo sannan ya Waga waya ya kira Wan yayarsa police. Makarantar ya kwatanta masa.

"Ku taho yanzu don Allah."

"YallaSai da ka bari an kira masa ?an sandan dake kusa da nan. Ka san kowanne laifi ana shigar dashi a unguwar da ya faru."

"A kira su. Shi wannan Wana ne saboda haka ina jiran zuwansa saboda ina son komai ya tafi da jagorancin wani nawa."

Suna wannan zance Uncle B ya matsa gefe yana ta bige bigen waya da hargagin iska. Bayan ya gama ya cigaba da masifa yana doka teburin Principal.

"Baki san ko ni waye ba a garin nan wallahi. Ina da damar sanyawa a rufe makarantar nan baki Waya a yau idan na so."

"Ka daWe baka aiwatar ba. Mutumin banza. Girma da matsayinka basu ?ara maka komai ba sai sanya hannu wajen Sata tarbiyar yaran mutane."

A cikin minti talatin motar ?an sandan da VP ya kira ta iso makarantar aka yi awon gaba da Uncle B. Baba Maje da Ummi da VP Win su ka tafi tare dasu. Principal ta sanar da mal???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?amanta wajibcin neman iyayen yara a kurkusa domin tattaunawa da gujewa maimaicin abin da ya faru.

Hamdi da Abbanta su ka fito tare fuskokinsu babu walwala sosai. Shi yana cikin damuwar halin da abokinsa ya sami iyalinsa, ita kuma tana cike da kunyar ya san irin matsayin da ta ajiye shi a matsayinsa na uba. Hannunsa ta ri?e ganin yana raSewa gefe guda.

"Abba in kai ka ka ga ajujuwanmu?"

"A'a Hamdi." Ya zame hannunsa.

"Ba ka yafe min ba ko?" Idanunta su ka kawo ruwa.

"Ban taSa fushi dake ba. Ba dai na son sake bar miki abin faWi a cikin abokan karatunki." Ya ce a sanyaye.

Wannan furuci nasa ya sanyata kuka sosai. Ta ro?e shi da ya jirata a nan inda yake za ta dawo bayan ya hanata kukan. Tana tafiya ta samu Walibai na dinning hall ana cin abincin rana. Duk da yadda take wasiwasi amma da ta tuno da maganar da Principal tayi mata sai taji zuciyarta ta daina tsoron komai.

"SS3 A" ta ?wala kira da ?arfi.

Tashi su ka yi wasu kuma su ka amsa da baki.

"Ku zo ku gaisa da Abbana."

Ai kusan rabin hall Win ne su ka fita a guje. Aka kasa controlling Win su. Tana gaba har inda ta barshi tsaye. Kawar da kai taga ya yi tayi murmushi ta zaga gabansa.

"Abba an zo gaishe ka."

Tunda yake kullum yaransa su ka zo gida da ?awa basa taSa cewa a gaisa da shi. ?awayen ma bai san kowa ba sai na dangi ?a?an ?an uwa.

Ya juya suna ta ina wuni shi kuwa ya kasa amsawa saboda kada jin muryarsa yasa a yiwa ?arsa dariya.

"Abba ka amsa mana" Hamdi ta ce tana dariya kamar ba ita ba. Yarinyar da kullum take cikin ?unci da damuwa.

Ya buWe baki ya dinga amsa musu. ?an matan nan maimakon nuna ?yama sai yake ganin kamar ya burgesu. Wasu basu taSa ganin Wan daudu a kusa haka ba. Kamar wani abin sha'awa su ka dinga girmama shi. Kan Hamdi ya kumbura suntum saboda daWi. Ranar da taimakon malamai aka ?ora su duka har ita cikin makaranta sannan ya samu ya tafi wajen Baba Maje.

***

Ganin su Inna ya yi saurin Waukewa Taj damuwar da ya shiga. Sai gashi ya zage yana ta hira kamar ba shi ba. A cikin hirar ne ya tambaye su ko akwai wani abu a tattare dashi da zai sa ayi masa kallon namijin da bai cika ba.

Ya naWe hannun rigarsa har saman kafaWa irin yadda yara su ke yi.

"Saboda son burge Alhaji har gym nake zuwa ina motsa jiki. Yanzu wannan..." ya nuna dantsensa "bai isa a kirani namiji ba?"

Kamal kula ya yi da Salwa da ta shigo Wauke da tray Win abinci da yadda tayi saurin Wauke ido daga kallon hannun Taj. Shi kuma gwanin ya kama ?asan riga zai Waga wai ya nuna musu packs Win ?irjinsa. Gudun kada Wan uwansa ya kunyata shi ne ya kai masa duka a hannun.

"Dalla malam rufe wannan sandar raken."

Taj da yaji zafi ya rama dukan "Wan ba?inciki in ka isa ka buWe naka mai kama da taliya."

"Mama kina dai jin abin da yake faWa min ko?" Kamal ya faWi yana mi?ewa tsaye.

"Laifinka ne fa Kamal. Kai ka fara dukansa" Mama ta goyi bayan Taj.

"Saboda ya dawo daga America za ki nuna min wariya? Ke fa ki ka hana raini tsakaninmu."

Su Hajiya sai dariya su ke yi. Taj ya sami goyon baya ya cigaba da tsokanarsa.

"Ka ci sa'a ban auro baturiya ba da kaga asalin wariya. In taho da ?an ?a?ana farare su na Mom...Dad...who is this black man" ya nuna Kamal aka sake tuntsirewa da dariya. Ya cigaba da tsokanarsa "Duk ?an uwa su taru a kansu ana son burgesu. Kai kuwa naka sai dai kaji ana cewa 'Sule maza tafi wurin babarka ta goge maka majina' "

"Banza ?azami. Wai majina kamar tashin Soron Winki. Kuma don wula?anci ba ma Sulaiman ba Sule zan haifa?" Kamal ya faWi yana shure shi da ?afa.

Taj dariyar da ya san za ta ?ular dashi ya cigaba da yi.

"Sule Kamalu Hayatu Sule. Irin ?an chubby yaran nan masu Wan ?aton ciki ba."

Ba ka jin komai a falon sai dariyar iyalin ta farinciki. Salwa da take ganin duk motsin Taj wani salo ne daban mai tafiya da zuciyarta ce kaWai ta ?are da murmushi.

Kamal da Taj su ka gaji da wasansu na dambe da girma bai hanasu yi ba su ka koma cin abinci daga plate Waya su na hirar da babu mai ji.
RAYUWA DA GI?I 9




Batul Mamman=ؖ?




***

Irin kukan da Iyaa tayi bayan jin tsiyar da Ummi take shukawa dole ya bawa mutum tausayi. Bayan an kai ruwa rana a station Win da su ka je Baba Maje ya gane duk inda yake tunanin Ummi ta wuce nan. Fitina da gagara ta ?an matanci kam tana bugawa a bayan idonsa. Ya sake yarda ba a shaidar Wan yau. Ba don da bakinta ta amsa laifukanta ba da ya yi rantsuwar sharri ake yi mata. Ummin da ya sani daban. Wadda ya dawo da ita gida daban.

Abin ba?inciki shaiWanin tsohon najadun da yafi kowa hure mata kunne Uncle B ashe makanike ne. Matansa biyu da ?a?a goma sha uku. Sau Waya ake Wora tukunya a gidansa. Irinsu Ummi ke cinye Wan abin da yake samu. Ita da yake tunanin raba hanya da ita saboda rashin bashi haWin kai tuntuni ashe silarta asirinsa zai tono. Sai da ya yi sati guda a ?ulle kafin a yarda a bada belinsa. Shi ma kuma an haWa masa da muguwar tarar da zai ji jiki wajen biya.

Hantara da kyara su suka marabceta daga dawowarta gida. Ta zama mujiyar da bahaushe yake kira mai ba?in jini. Iyayenta ba su dake ta ba don ciwon abin da tayi ya kai ma?ura. Yayanta Baballe ne dai ya kasa zama bayan yaji kukan Iyaa yayi yawa a waya da tana labarta masa. Ya ni?i gari ya taho Kano ya sakar mata ?arfinsa. Zaneta ya yi ciki da bai babu wanda ya hana shi. Sai ma dare da jikinta ya yi mugun tsami ne Iyaa ta tada ta zaune.

"Sau nawa ki ka zubar da ciki Ummi?"

Duk soyewar zuciyarta da ya hanata kukan dukan da ta sha wannan tambaya sai da tayi sanadin zubar hawayenta. Hannu ta Wora akan bakinta tana danne kukan.

"Iyaa? Ciki kuma?"

"To Ummi meye abin mamaki a ciki? Samarin da su ke kashe miki kuWi ?annen uwa ne ko na uba da za a ce zumunci suke yiwa?"

Hawaye take ita ma ga tsoron kada Ummin ta amsa zargin da su ke yi mata ita da Baba Maje.

"Wallahi Iyaa ban taSa yarda na bada kaina ba."

"To me ki ke basu ko me su ke samu a madadin kuWinsu? Don dai bana jin shaiWancin naki ya yi tsamarin da za ki asircesu su dinga bin umarninki."

Shiru Ummi tayi. Hankalin Iyaa ya sake tashi ta dinga kai mata duka da hannu ta ko ina.

"Ki faWa min gaskiya kafin zuciyata ta buga."

"Iyakarsu tattaSani amma bana yarda da..."

Da sauri Iyaa ta tashi don bata son kuma jin ?arshen zancen.
"Ya isa. Kin yiwa kanki."

Fita tayi ta bar Ummi tana kuka. Kuma duk wannan abu bai zama ishara ya tuna mata yadda ta dinga cin zarafin mutane dole rana irin ta yau ta zo ba. Sunan Hamdi kawai ke yawo a zuciyarta. Ko harararta aka yi laifinta take ?ara gani. Musguna mata da ta dinga yi a makaranta ai bai shafi komai na karatunta ko rayuwarta ba a tunaninta. She was just having fun. Ba ita kaWai bace senior mai yi wa na ?asa da ita hawan karkatacciyar kuka, saboda haka bata ga dalilin da zai sa ita kaWai ce rayuwarta ta kife irin haka ba. Da me ake so ta ji? Sanin waye Uncle B ko fitowar sirrinta? Ko kuwa rabata da makaranta a matakin ?arshe da iyayenta su ka yi don ta Wauki bidiyon Wan daudu?

"Wallahi sai na rama Hamdiyya. Babu wanda ya isa ya saka ni kuka ban saka shi ba."

Da wannan kalaman ta goge hawayenta a fusace ta kwanta tana shure Siyama da ?afa don ta Wan matso Sangarenta cikin bacci.

***

Kwanaki sun ja inda a farko farkon watan August Waliban sakandire su ka kammala jarabawar fita. An yi WAEC har ta fito kafin a gama NECO. Da taimakon Allah da kuma dagewar karatu Hamdi ta sami kyakkyawan sakamako.

Kwana biyu bayan kammala jarabawar makaranta ta shirya gagarumin taron sallamar Walibai. Iyaye da Waliban suna shiryawa wannan rana wasu tun farkon shiga SS3. ?inkin ankon wata shuWiyar atampa su ka yi mai adon fari da yellow. Tun kafin hutu aka fitar amma lokacin Hamdi bata ?arSi ?yallen ba. Saboda ko kusa bata sa ran zuwa. Sai bayan faruwar lamarin nan taji a jikinta ta daina Wararewa. Allah Ya taimaketa kafin a gama jarabawar lokacin visiting da Sajida da Zee su ka zo mata ta basu.

"Abba fa ya bar sana'arsa Hamdi. Ki ha?ura kawai a kawo miki ko cikin kayan sallarki ne." Zee ta faWi bayan ta gama kallon atampar.

Mangareta Sajida tayi "Yaya bata gargaWeki akan faWa mata ba?"

"Gaskiya fa na faWa mata don kada ta sa rai." Zee ta bata amsa tana ?un?uni.

"Ya Sajida me yake faruwa? Ba don saboda ni ya daina ba?" Hamdi ta tambaya hankalinta na tashi.

Bayanin abin da ya faru su ka yi mata. Sannan Sajida ta ce kada ta damu in sha Allahu za a saya a Winka kafin ranar.

"Na ha?ura." Hamdi ta ce a sanyaye tana tuhumar kanta a matsayin wadda ta kasa godewa mahaifinta a lokacin da yake yi musu.

"Anti Labiba ce ta bani kuWi da zan taho. Allah zan iya saya miki." Sajidan ta bata amsa tana dariya.

Daga nan su ka koma wata caftar mai daWi. Sajida tayi saurayi a Abuja daga zuwa taya cousin Winsu zaman jego. Mutumin da gaske yake. Yana aiki da rufin asirinsa. ?an maza zar su ke da mijin Anti Labiban (?a a wurin babbar yayar Abbansu Anti Zinatu).

?an matan uku su ka haWa kai su na ta murna kamar ma anyi auren an gama.

Zee ce ta dakatar da shewar tasu "Kin dai yi masa bayanin Abba ko?"

Fari Sajida tayi da idanu tana faWaWa murmushinta "Kada ku damu. Ya ce sai da su ka yi magana da mijin Anti kafin ma ya yi min magana. Yanzu dai ku sa rai da zuwansa nan da wata guda. Lokacin ma kin dawo gida ko?"

"Su Ya Sajida an fara kashe murya a waya kenan." Hamdi ta tsokaneta.

"Zan Wauko rahoto kafin ki dawo. Dama bata yi na gani ba don kada na fesawa Yaya."

"Kin fa raina ni Zee. Ni da na raineki."

Dariya Zee da Hamdi su ka yi. Ita Zee SS2 take don tsiransu da Hamdi babu yawa.

***

Aikin gini ya soma kankama son Taj ba Sata lokaci ya zo yi ba. Shawarar Amma ya karSa ya yi ginin a iya restaurant da shaguna ?alilan. Wani Architect ya kwatantawa abin da yake so. Nan da nan aka zana masa plans kala uku. A ciki ya zaSi Waya. Shi da Kamal kullum sai dare su ke komawa gida. Shi ya tafi gidan Ahmad, Kamal kuma ya koma don muddin ya kwana zai gamu da fushin Alhaji.

Tsarin da aka Wauko ya bada ma'ana sosai. Gini ne da aka yi Sangare uku manne da juna. Na tsakiyar yafi girma da faWi kuma shi kaWai ne aka Worawa bene. Na hagu anyi kitchen ?ato da komai domin aikin fulawa. Cake, doughnut, meatpie, samosa, pies da dangoginsu. A wadace yake sai dai babu wurin zama a ci a ciki. Idan mutum baya son fita akwai ?ofa da za ta sada shi da tsakiyar wato ainihin restaurant Win. ?angaren dama wanda shi dama za a fara tararwa shi kuma kana gani za ka san na masu gashin nama da kifi ne. Ko yanzu da ake matakin gini kaWai kana gani zai burge ka. A tsakiyar sama gabaWayansa kujeru da teburan zama ne. Sai wasu Wakuna biyu domin masu gudanar da taron da zai iya cin mutane hamsin. Meeting, seminar, reunion da sauransu amma banda biki. ?akunan Waya normal ne Waya kuma VIP. A ?asa ma da wurin cin abincin sai Sangaren masu haWa natural juice da za ayi bayan kayi order. Saii kuma makeken kitchen Win Taj da ma'aikatansa. Har ila yau a farfajiyar wajen an keSe wani waje da aka soma tayar da garden. Za a ?awata wajen da liluka da wajen guje guje da wasan yara. Sai kuma cikon al?awarin da ya yiwa kansa. Zai gina madaidaicin boutique da gininsa zai kallon restaurant Win ya bawa Kamal amma bai faWa masa ba.

Yau sun bar wurin duba aikin da wuri sakamakon zazzaSi da ya rufarwa Taj gadan gadan. Kamar wasa ya ce kansa na ciwo, sai gashi kafin su isa gidan Ahmad yana rawar sanyi. ?auke hanya Kamal ya yi su na cikin tafiya. Taj ya Wago kansa da ya yi nauyi da ?yar ya dubi hanya.

"Sayar dani za ka yi don kaganni haka Happiness?"

Kamal ya yi murmushi "kwantar da hankalinka. Ai an taya kuma naji ba tsada za ka yi ba."

"Ka ci bashi don sai na rama."

"Allah Ya baka ha?uri. Yadda nake jin yunwa idan kayi fushi dani da alama Salwa ba za ta bani abinci ba yau."

Wani irin kallo Taj ya yi masa na neman ala?ar fushinsa da cin abincin Kamal amma ya kasa ganewa.

"Wani abu ne ya haWaka da ita?"

"No" Kamal ya bashi amsa mischieviously.

"Meaning?"

"A bar zancen sai ka warke."

Taj bai matsa ba. Kansa kuWa yake kamar zai cire. Asibiti Kamal ya kai shi duk turjiyarsa. Abu ya kai da ?arin ruwa don likitan ya ce jikinsa babu kuzari. Gashi sakamakon gwaji ya nuna yana da malaria da thypoid duk shi kaWai. Sun haWe da rashin hutu sun kayar dashi lokaci guda.

"Amma ba kwana zan yi ba ko?"
Ya tambayi likitan bayan an gama saka masa canula a hannu.

"Ka godewa Allah da ka iya shigowa nan da ?afafunka. Your temperature is abnormally high."

Da Kamal ya barshi ya rufe ido don ya gaji sosai. Bayan fitar likitan da Alhaji yaji Kamal Win yana waya. Ya sanar dashi halin da yake ciki. ?aguwa ya yi yaji me Alhajin zai ce don kamar ya ?waci wayar a hannun Kamal. Ya dai daure har su ka gama. Shiru bai ji Kamal ya isar da sa?on Allah Ya ?ara sau?i ba.

Sai da ya bari ya gama waya da su Inna da Ahmad sannan ya tambaye shi.
"Bai ce komai bane?"

"Yana hanya ne da alama ba ya ji na sosai" Ita ce kalmar da Kamal ya ?ir?iro ya faWa masa.

"Hmmm"

Kamal ya dawo kusa da shi "Happy kayi ha?uri sannan mu cigaba da addu'a."

Abinka da ?an dangi. Lokaci ?an?ani asibitin ya fara cika da ?an uwansu. Kowa ya zo faWan rashin hutu yake yi masa.

*

Don son tabbatar da zarginsa, Kamal kiran Salwa ya yi ya faWa mata bayan ya sanar da Ahmad. Tunda yaji ya ce baya gida shi ne ya kirata. Ai kuwa abin da ya yi tsammani yaji. Rikicewa tayi ba tare da ta sani ba.

"Ya Kamal yana iya magana?"

Ya yi murmushi "eh, ko in bashi ne?"

Da sauri ta ce "a'a" kunya na lulluSeta da ta fahimci za ta bada kanta. Awa guda bayan sun yi wayar ta kasa sukuni. Jira take Zahra matar Ahmad tayi maganar zuwansu dubiya tunda tayi arba'in yanzu amma taji shiru. Bini-bini ta Waga waya ta duba lokaci. Da ta kai matakin da ba za ta iya ha?uri ba sai ta tambayi Zahran.

"Anti Zahra na ce ko sai Hayat ya taso in an kai shi islamiyya za mu wuce asibitin?"

Zahra ta zaro idanu tana laluben wayarta "ba ki da lafiya ne Salwa? Ina yake miki ciwo? Bari na faWawa Daddy."

"?alau nake Anti. Dama maganar duba Yaya Taj ne."

Zahra tayi murmushi "lahhh kada ki damu. Daddy ya ce zai biyo muje yanzu. Ke kuma ki zauna saboda Hayat."

"In zauna?" Salwa ta ce ba shiri.

"Ina jin babu lallai ya kwana tumda yace min suna ta waya da Kamal. Meeting ne ya hana shi fita da wuri."

Rasa bakin magana tayi ta fita kawai. Zahra ta bita da ido ba tare da kawo komai a ranta ba.

Da Ahmad ya dawo ko shiga gidan bai yi ba ya kira Zahra ya ce ta fito bayan la'asar. Kafin ta gama shirya Aisha Salwa tayi saurin fita wajensa.

"Ya Ahmad kana ganin daga gida ba za su fassara rashin zuwana duba shi ba ace don ba Wan uwana bane?"

"Ke, gidanmu babu irin wannan kin ji. Bana son Hayat yayi missing islamiyya shi yasa nace ki zauna."

"Naga kamar zamu iya dawowa kafin ya taso."

Wani irin kallo mai tattare da tuhuma ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login