Showing 3001 words to 6000 words out of 182745 words

Chapter 2 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

72

kuWaWe da sponsorship. Sai kawai na yarda da shawarar gina ?aton mall irin wannan lokaci Waya da duka kuWin? Kai baka hango ganganci a cikin yin haka ba?" Ta nuna zanen ?ayataccen ginin da yake kan laptop Winsa wanda nuna mata da ya yi ne ya kawo rigimar.

Marairaice fuska yayi "Tafiya ce ba kya so nayi ko Amma? Nayi miki al?awarin zama har ki yi ritaya."

"Bani da son kan da zan yi amfani da gudun zaman kaWaici na da?ile maka rayuwa."

Bakinta kawai ya kalla ya yi murmushi. Wata hausar idan ta Wauko duk nacinsa sai ya tsinci kansa da rashin ganewa. Laptop Win ya rufe ya fuskanceta.

"Yanzu me kike so nayi?"

"Ka fara da restaurant Win mana. Idan kaga riba sai ayi planning for expansion."

Tana gama magana ya sake buWe laptop Win ya nuna mata sakamakon bincikensu. Tabbas akwai ?an kasuwa da yawa a Kano. Tada ginin mall ba wani abu bane a wajensu. Kuma yana samun karSuwa sosai. Ayi ta tururuwa ana zuwa. To amma fa bayan lokaci ?an?ani yawanci da wuya ka sami motoci biyu sun ziyarci wurin. Wasu ma kayansu har ?ura su ke suna expiring saboda rashin zuwa. Da wannan su ka haWa bayanai wurin yin abin da ya saSawa wanda mutanen su ka saba dashi.

"Kinga na farko zamu yi shi a wurin da bai yi nisa da talaka da mai kuWi ba."

Bata ce komai ba. Ya ?ura mata ido sai ta gyaWa kai don ya cigaba.

"Dole zamu dinga canjawa with current trend. Idan ban yi shi da girma ba chanjin zai dinga bani wahala. Maybe wani ya saye space Win kusa dani in rasa hanyar expansion. Sannan yin babba da zan iya bada hayar shops for diverse businesses zai taimaka. Idan mutum bai je don cin abinci ba maybe yaje wurin tailors, grocery shopping, wasan yara and the likes."

Ta?aita masa bayanin tayi ta hanyar nuna masa ta gane. Yana son yi mall mai Wauke da shaguna daban daban amma na brands da suka yi suna. A haka nasa Sangaren wato wurin abinci ko bai yi kasuwa sosai ba zai dinga samun kuWin haya daga waWanda suke ciki. Burinsa talaka da maikuWi kowa ya WanWana ababen more rayuwa a ?asarsa cikin jindaWi. Goyon baya ta bashi amma ta yi masa hannunka mai sanda akan tsoron da take ji da kuma ?an gyare gyare.

"Kamal jininka ne. Kuma na san irin sha?uwar dake tsakaninku. Amma kada ka manta mutane irinmu da yawa living in diaspora (?asar waje) muna fuskantar matsala guda. Sai mu tura kuWi gida domin wani aiki musamman gini. Idan mun koma mu tarar babu aikin babu kuWi. Kuma family su nuna basu yarda muyi ?arar wanda ya cucemu ba."

Da rashin jindaWi ya ce "Amma Happiness ne fa."

"Shi Win fa. Ka tafi gida ayi komai a gabanka. Sayen fili, kafa foundation da dukkan wani abu da ya dace ka sani. Daga cikin abubuwan da su ke dur?usar da business harda rashin kulawar wanda ya samar da shi. An bar komai a hannun ma'aikata. Sai abu ya lalace a zo ana complain."

Sai kuma ta bashi shawarar maimakon mall ita dai tafi son ya yi ?aton restaurant tunda da girki ya yi fice. Idan an gina sai ya ware wurin wasan yara domin janyo mutane. A Sangare guda ya yi wurin da masu gashin nama ko tsire zasu iya haya. Da kuma inda masu kayan fulawa kamar cake da su meatpie zasu yi nasu. Maimakon mall indai akwai wurin da aka keSe domin yara to fa tabbas iyaye za su zo. A ?arshe ta ce ya tabbatar wurin an yi shi yadda zai burge mai kuWi sannan bai yiwa talaka tsadar zuwa ba.

Sosai yaji daWin shawararta. Ya ce zai sa a sake yi masa wani zanen. Amma fa dole zai samarwa Happiness wurin da zai kafa nasa shagon. Addu'a tayi masa da fatan Allah Ya Worar da zumuncinsu shi da yayan nasa. Sai da su ka tabbatar sun daddale komai ya ce,

"Ni fa nafi son mu tafi tare."

"Ya kamata kaje gida uwayenka su ganka haka nan."

Tashi tayi ta juya masa baya amma bata tafi ba.

"Tajuddin ka sani cewa if your intension is not honourable (idan niyarka ba mai kyau bace). Ina nufin in kana son fara business Win nan ne kawai domin ka nunawa Yaya Hayatu cewa kayi nasara duk da yadda ya nuna ?iyayyar sana'arka, to lallai Allah zai kunyataka. Domin Ya karrama darajar iyaye. SaSanin fahimta da rashin goyon baya daga garesu ba dalili bane da zai sa mu nuna musu raini."

"Korata fa ya yi" jijiyar kansa da idanu su ka firfito a lokacin da yake maganar.

"Shi kuma Allah Ya zaSa maka a matsayin uban. Ya kuma rayata ha?o?in junanku a kan ku. Idan ya take nasa kada ka kuskura kayi nufin binsa da ?ulli. Wallahi duk wahalarka ta shekarun nan sai ta tashi a banza."

"Amma..."

"Ka tsaftace niyarka Taj. Everything will just fall into place. Goodnight"

Juyowa tayi ta sumbaci goshinsa sannan ta Wauki wayarta ta shige Waki ta bar shi a tsaye yana kai gwauro da mari. Maganarta a kullum umarni ce a gareshi. Ta san yana yi mata biyayya gwargwadon iyawarsa. Me yasa bayan tsayin lokacin nan don zai tsaya da ?afarsa za ta ce ya tafi gida?
RAYUWA DA GI?I 3


Batul Mamman=ؖ?


Masu tambaya littafin ba na kuWi bane.


***

Auren Habibu da Jinjin ba na son zuciya bane kamar yadda ?a?ansu suke hasashe. Yar mahaifinsu da suka fi Worawa alhakin saboda sunanta da Zee tace wato Anti Zinatu ma ba laifinta bane. Abu ne na karamci da sanin darajar wanda ya kiyaye taka darajar.

Aure ne na zumunci domin kuwa kamar yadda Iyaa da Baba Maje suka fito daga zuri'a Waya su ma iyayensu mata sha?i?an juna ne. Mahaifiyar Habibu ita ce babba. Tayi aure a Kano da ?a?anta maza uku da mata biyu. Shi ne na biyu. Ita kuwa mahaifiyar Jinjin a garinsu ?atagarawa dake Katsina tayi aure. Bata sami haihuwar ba da wuri sai akanta. Ta haifota kyakkawa mai kama da dangin mahaifiyar. Idan ka ganta da ?a?an Inna Batulu za ka rantse ita ta haife su duka. Sunanta Khadija amma ake kirantan Jinjin (jinjinniya don ?auna). Soyayya da gata gwargwadon hali ta taso tana gani wurin uwa da uba kafin Allah Ya jarabceta da cutar shan inna tana da shekara biyu da rabi. Lokacin da iyayen su ka farga ?afar ta mutu ba ?aramar damuwa su ka shiga ba. Idan tana tafiya kafaWa da Sangaren ?irjinta na dama sai ya balla?o waje. Wannan abu ya tsayawa uban a rai. Har ta kai indai yana wajen da ta mi?e zai ce,

"Don ubanki koma ki zauna. Kina faman tafiya kamar wata tsuntsuwa babu kyan gani."

Ko ya ce "wannan da ma ciwon tafiya ya yi dake kika huta. Meye haka don Allah?"

Da bata da wayo uwar ke kuka idan yana wannan rashin albarkar. ?arshe ma yayi aure shi da matar da lafiyayyun ?a?an da su ka haifa su ka taru su ka mayar da rayuwar Jinjin ?untatacciya. Yanzu ita ke kukan uwar na rarrashi. Watarana Inna Batulu ta kawo musu ziyara ta tarar da ?a?an kishiyar ?anwarta suna dukan Jinjin. Abin takaici uwarsu da ?anwar na kusa amma wai kawaici ya hana ta ?waci ?arta. Garin cangala ?afa ta kifar da garin masarar tuwon dare. Kuma gudu ma take saboda an biyota za a ci zali.

Inna Batulu na gani tayi kukan kura ta dam?o yaran nan su uku ta bi kowa ta feffela musu mari. Ta ?are musu zagi irin nasu na Katsinawa.

"Banda raini ba yayarku bace?" Ta juya ga ?anwarta "shiga ki haWo min kayanta yanzu zan wuce da ita tunda ba kya so."

"Ba haka bane Yaya."

Da takaici takalleta "kunyar marasa kunya asara ce Luba. Gidan nan kaf har mijin naki ban ga wanda ya dace ki ragawa akan kyautar da Allah Ya yi miki ba."

Jijjiga Jinjin tayi a gabanta ta ?ara da cewa "don bala'in gidan nan ?ar shekara goma sha uku ji ?irjinta kamar anyi daSen siminti."

"Kai Yaya Talatu?"

"Allah kuwa. Zuwa yanzu ai yaci ace an fara ganin..."

Da Wan gudunta Jinjin ta bar wajen don bata son ?arasa jin hirar iyayen.

Kamar wasa maigidan na dawowa Inna Batulu ta sauke masa nashi kwandon masifar ta ce kuma jiransa take a bata ?a.

"Gata nan har abada da gaban abada na bar miki." Ya furta ko ajikinsa.

Luba sam bata ji daWi ba amma haka ta shirya mata kaya su ka tafi. Bata da wani farinciki ko nishaWi a gidan idan ba Jinjin take gani ba. Da ita take hira tunda miji ya juya mata baya. Sau?inta Waya ta san cewa yanzu za ta sami ?anci ta wataya kamar sauran yara.

A Kano tabbas taga gata da soyayyar da tasa har take manta da nakasar dake tare da ita. Inna Batulu da maigidanta harma da yaransu sun mayar da ita ?ar gata. Matsala guda ta kula akwai a gidan ita ce ta yayanta Habibu. Lokacin yarintarsu tana iya tuna shi da yawan wasa da dariya. Yanzu kuwa kullum iyayensa cikin kukan sabuwar Wabi'arsa suke yi.

Shi ne tafiya yana rangwaWa da karairaya jiki kamar mata. Ga uwa uba muryarsa da bata san ya aka yi ta motse ba. Idan ya yi magana sai ka rantse wata budurwar ce. Duk wasu take taken daudanci yake nunawa. Indai zai yi sallama a gidan daga su Inna Batulu har ?an uwansa basu da nutsuwa.

A yau da take da kusan wata biyu a gidan sallamar wata matashi suka ji a gaggauce. Babu kowa a gidan sai Jinjin da ta dawo daga makarantar islamiyya. Fita tayi ko kaya bata cire ba ta sami wani mutum da bata sani ba. Da gani magidanci ne ya sha shadda wagambari da Sakar Wara a ka.

"Inna Batulu ko Baba nake nema" ya ce kafin ta gaishe shi.

"Duk basa nan."

Kallonta ya sake yi ya tuna sun taba shiga gidansu wurin iyayensa da Inna Batulu tace ?arta ce daga ?atagarawa. Shi yasa kawai ya faWa mata abin da ya kawo shi.

"Ki ce musu Habibu na gani a gidan abincin wasu ?an daudu yana girki a kasuwa."

Rasa abin cewa tayi don fuskar mutumin tayi nuni da matsanancin Sacin ran da ganin hakan ya janyo masa.

"Kin fahimci abin da nace kuwa?"

"Eh, zan faWa musu in sha Allahu."

Juyawa ya yi babu sallama zai tafi ta tambaye shi wa za ta ce musu.

"Hayatun gidan Alh. Sule."

Sunan da taji bayan tafiyarsa ya dawo mata da hirar da ta taSa tsinkaya daga mutan gidan. Akwai gidan wani mai kuWi nan kusa dasu wanda aka ce Wansu Hayatu ya Wauki Habibu tamkar cikinsu Waya. Saboda ladabi da ?o?arinsa a shekarun baya ya kasance duk wata lalurar karatunsa Hayatu ya Waukarwa kansa. Irin abin nan na maikuWi ya cicciSi talaka domin inganta masa rayuwa. Ance da Habibun ya fara canja akalar rayuwa Hayatu ya shiga Sacin rai sosai. A son sa yaron ya ginu ya zama mutum amma kullum ana yi masa faWa yana daWa kangarewa. Me za ayi da namiji mai girki a ?asar hausa? Har dukansa taji ya taSa yi watarana da ya ganshi da Waurin zani a ?irji ya fita. A ?arshe ya ce masa zai iya tsaya masa ya koyi girkin harma ya mayar dashi sana'a amma sai ya ajiye duk wani abu da yake kamanceceniya da mata. To Habibu dai ana faWa ta kunnen dama zancen na ficewa ta hagu.

Da Inna Batulu ta dawo ta sanar da ita sai da tayi kuka. Shi yasa ba a son zama unguwa Waya da wanda ake ganin zai iya jan ra'ayin yaran unguwa. Daga yawan aikensa siyan abinci a wurin wasu ?an daudu dake bakin titi ita dai bata san yadda aka yi ya dinga rikiWewa ya koma wannan Habibun na gabansu ba.

Ranar anyi masa faWa sosai. Baba ya zage ya yi masa dukan mutuwa. Garin Allah na wayewa aka neme shi aka rasa. Wurin wata uku ana nema kafin daga bisani su sami labarin ya tafi Saudiya da wani ubangidansa. Sana'ar abinci su ke yi a can Win.

Akwai abubuwa da kan sami bawa ya rasa silarsu. Ka haifi Wa kayi masa duk iyakar ?o?ari amma idan ?addara ta faWa masa kana ji kana gani zai zaSi hanyar ta bata Sullewa. Irin haka ta sami Habibun Inna Batulu. Dangi su ka sanyo su a gaba da yawan magana da famin ciwo. Wasu in sun sami zuwa ?asa mai tsarki a unguwar su yi ta kawo labaran yadda aka ganshi ya Washe saboda shafe shafe. Zantuka barkatai harda wanda ya ce wai an faWa masa ya yi aure da wani Wan daudu irinsa.

Zancen da ya tayar da hankalin Baba fiye da kowanne kenan. Ya sayar da gonarsa da wani gidan haya ya haWa kuWi a shekarar ya tafi Hajji. Bai wani sha wahala ba aka sada shi da gidan da Simagade yake haya da abokan sana'arsa. Lokacin shekararsa tara baya gida. Jinjin ta gama sakandire har ta fara sana'ar kitso a gida tunda aure ya gagara. Ta kai matakin da kowane iri tana son samu saboda yadda mahaifinta ke jifanta da maganganu idan taje gida.

Baba fashewa yayi da kuka da yaga Wan nasa sanye da jallabiya ya Wora zani da Wankwali. Ga ha?oran Makka har biyu. Tamkar ba a Jidda ba suna ta ?azaman zage zage shi da wani da suke faWa. Ganin mahaifinsa ne ya sagar masa da gwiwa ya yi shiru. Sai hankalin kowa ya kai kan tsohon dake zubar da hawaye.

"Shiga ka sako kaya ka zo ka rakani masallaci."

Ba Habibu ba hatta abokan zamansa duk jikkuna sun yi sanyi. Ya shiga ciki ya samo aron wasu pakistan na maza ya saka. Ya fito tafiyar nan babu dama ne. Masallaci mafi kusa Baba ya shiga dashi. Ya umarce shi da yin sallah raka'a biyu sannan ya fuskance shi bayan sun idar.

"Saboda ka taka dokar Allah Habibu yau alwala da sallarka ma in ni nake karSa ba za su bar rufin masallacin nan ba zan jeho maka kayarka."

Kai ya sunkuyar cike da kunyar kansa.

"Daga wannan rana ba zan sake yi maka faWa ko nasiha ba. Zan kuma ro?i Batulu da kada mu sake zubar da hawaye a kanka. Na barka da duniyar da ka zaSa wadda nan da kwanaki kaWan za ta daina yayinka. Idan tayi maka rawar ?an mata ina jin za ka yi hankali har ma kayi tunanin dawowa gida. In na mutu tun yanzu ka sani na yafe maka. In kana da rabon shiriya ka zo gida kafin ba?incikinka yayi ajalin mahaifiyarka."

Yana gama faWin haka ya tashi. Habibu zai bi shi ya ce baya so. Haka ya koma ya gama kwanakin da su ka rage ya dawo gida. Habibu kuwa komai ya daina yi masa daWi. Nadama mai raWaWi ta shiga Wawainiya dashi. Ana gama kwaso mahajjata ya tattara komatsansa ya dawo gida.

Bai fi wata biyu ba Baba ya kama cuta har ya cika. Yayi kuka kuwa kamar ba gobe. A gefe guda yana godiya ga Allah da Ys bashi damar dawowa. Tun daga lokacin ya soma neman gyara rayuwarsa. Sai dai kuma jama'a da dama suna gagarar yiwa mai laifi uzuri ko ya tuba. Da yake har yanzu in ba jallabiyar nan ya saka ba sai yaji kamar yayi tsirara, amma yana bakin ?o?arinsa wurin yin abin maza. Matsalar dai an bar kari tun ran tubani. Murya ta gama sha?ewa. Karairaya ta zame masa jiki duk da ya rage. Ya yi ta neman aikin yi ya rasa. In ya kasa kayan sayarwa irinsu kayan miya babu mai saye. Har wurin Hayatu yaje amma ya?i taimaka masa ya zama yaron shago kamar yadda ya nema. Allah Ya Wora masa ?yamar ?an daudu sosai.

Da ya rasa yadda zai yi ne ya ro?i Inna Batulu ta yarje masa tafiya Lagos sayar da abinci. Ya tabbata a can da babu wanda ya san shi kuma girki ba a Wauke shi sana'ar mata kaWai ba zai sami sau?i.

"Idan ka tafi Habibu ina jin tsoron kada ka koma ruwa. Gashi nayi imanin babu mai baka mata ka aura a halin da kake ciki." Ta goge hawaye.

"Ki yafe min Inna. Na san na cuci kaina amma nayi miki al?awarin ba zan komawa waccan rayuwa ba."

Duk zancensu a kunnen Jinjin. Kafin tafiyarsu ta sake jin maganar ana yi tsakaninsa da ?an uwansu. Ta kula Inna tana cikin damuwa. Barinsa babu abin yi matsala ne. Sannan zuwansa shi kaWai akwai haWari. Bayan dogon nazari irin na yarinta ta nemi izinin zuwa gida ta shawarta da mahaifiyarta. Luba ?ar halak ko mijinta bata bi ta kansa ba ta sako ?arta a gaba su ka taho Kano. A gaban ?a?an gidan da mahaifiyarsu ta ce ga amana ta sake dam?a musu.

"Jinjin miskiniya ce na sani. Ban sani ba ko bawa Habibu ita zai zama gwaninta ko abin Sacin rai a gareku."

"Allah Ya kiyaye Gwaggo Luba" cewar yayar Habibu tana taya Inna Batulu kuka don ta kasa magana.

Sun yiwa uwa da ?ar godiya kamar su ari baki. A wata guda aka yi komai aka gama su ka koma Lagos da zama. Rayuwar ta fara daWi Allah Ya karSi ran Innarsa. Shi ne dalilin dawowarsu kuma ya kasa komawa.

Habibu yana ?aunar ?a?ansa?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? kamar rai. Yafi kowa sanin akwai lokutan da basa son nuna shi. Shiyasa ya kan kame daga za?e musu don kada ya Sata rawarsa da tsalle. Matarsa Jinjin kuwa duk duniya baya haWata da komai. Shi ya sani cewa tayi masa alfarmar da da ace ana auren ?anwa ko ya nasa ba za su taSa aurensa yana Wan daudu ba.


**

Alh. Hayatu Sule Maitakalmi mashahurin Wan kasuwa ne a Kantin Kwari. Takalma dai na mata da maza daga shagunansa an gama magana. Karansa ya kai tsaiko a kasuwanci. Sunansa ya zaga duk inda ya dace a dama da shi. Mutumin cikin ?waryar Kano ne daga unguwar Soron Winki. Yana da kirki da ?o?arin cicciSa na ?asa da shi sai dai akwai tsatstsauran ra'ayi kuma baya tan?waruwa. Duk wanda ya san shi ya san kaifi Waya ne kamar bakin wu?a.

Matansa huWu kuma duk a gida Waya suke. ?aton gini ne na masu kuWin da wanda yake yawan shan gyara domin ya tadda zamani. Ainihin gidan akwai ?aton falo wanda in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login