Showing 153001 words to 156000 words out of 182745 words

Chapter 52 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

109

kika je? Kin jefa ni a wani irin tashin hankali."

"Allah Ya huci zuciyarka Yayana Habibu. Tuba nake Abban Sajida."

Murmushi ya yi "yanzu kina ina?"

"Asibiti."

"Baki da lafiya ne?" Ya sake tashin hankalinsa

"A'a, alfarma nake nema domin babu lokaci."

"Kin fara tsorata ni. Me ya faru?"

"Yaya Habibu mijin Jinjin miskiniyar Allah. Da uwata da ubana Allah Ya gatance rayuta da iyayenka. Kirari nake maka mijina a duniya da ?iyama. ?anin Zeenatu uban Zeenatu Wawisun zuciyata. Domin isa da alfarmar Mai Duka kayi min lamuni in share hawayen wata uwa kamar yadda Allah Ya share mana ranar auren yaran nan"

"Me kike so?" Ya ce da tsinkakkiyar zuciya.

"Ceton rai zan yi!"

"Kiyi min magana yadda zan gane."

"Wallahi ba zan iya ba. Amma ina so ka sani cewa ikon Allah ne ya kawoni ba tanadinmu ba. Komai da yake faruwa damu daga tsarin Mai Kowa da Komai ne."

"Jikina rawa yake yi. Idan na hanaki za ki ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ha?ura?"

"Sosai kuwa. Amma ina da ya?inin cewa kai Win kafi kowa kyawun zuciya a duka mutanen da na sani. Duk abin da za kayi domin ka taimaki wani kana yi. Shi yasa Allah ba Ya barin kowa yaga bayan ka."

"Khadija." Ya kirata da sunanta na gaskiya.

"Yayana." Ta amsa da dakakkiyar murya don bata son komai ya karyar mata da zuciya.

"Ki kira ni idan kin gama. Tsoro mai girma ya shiga zuciyata. Amma naji ba zan iya hanaki ko mene ne ba. Allah Ya baki ikon yin taimakon ba tare da kin wahala ba."

"Amin."

Sallama su ka yi ta ce ta shirya. Likitan ya kira hukumar asibiti ya sanar. Komai cikin gaggawa ake yi saboda Kamal ya kai wata gaSa mai sammatsi. Aka gama cike ciken takardu sannan aka bata form ta cike da taimakon mai sharar nan da yake karanta mata ya fassara.

Daga nan lab aka je aka yiwa Yaya dukkan wani gwaji na dacewa. Sakamakon da aka samu sai shukura. Likitan ya ce su je wajen su Alhaji ta ce a'a. Kawai a zo ayi. ?aki VIP aka bata ta zauna kafin a shiryo Kamal. Tana zama ta dubi mai sharar nan. ?an dattijo ne kamar Abba Habibu.

"Yaya sunan ka ne Malam?"

"Salisu."

"To Mal. Salisu recoder nake so ka kunno min a waya zan yi magana. Idan an fito daga aikin ka kunnawa su Alh. Hayatu."

A wayarsa ya kunna ya bata. Ta kara a bakinta ta soma magana. Kalaman da take yi sun shige shi fiye da tunani har ta kai yana zubar da ?walla.

*

A ?ofar Wakin su ka dinga zubewa suna sujjadar godiya ga Allah. Likita ya ce an sami donor amma ba a bari sun san waye ba. Mubina sai da ta tuno Yaya. Sai tayi murmushi tana godiya ga Allah da bata yi mata magana ba.

Kamal bai san a inda yake ba har aka gama komai aka shiga tiyata. Kamar wasa sai da su ka kwashi awa huWu ana abu Waya sannan aka kammala. Addu'a kam da shi da Yaya duk sun sha ta sosai.

*

ICU aka gangara su su biyun domin kulawa ta musamman sannan wanda ya jagoranci aikin ya zo ya sami su Alhaji. Fuskokinsu duka babu nutsuwa. Yana tsayuwa su ka taso gabansa.

"Alhamdulillah, it was a success."

Kowa sai hamdala da ajiyar zuciya suna rungume junansu.

"What about the donor?" Alhaji ya yi tambayar dake gabansa.

"He" likitan ya nuna Mal. Salisu yana murmushi "will explain."

Kallon rashin sani su ka yi masa. Ya murmusa ya ce dama basu san shi ba. Shi kuma bashi da wata ala?a da donor Win. Amma ga sa?on da ta ce a kunna musu idan an fito. Daga gyaran muryar Mubina ba ?aramin kaWuwa tayi ba da ta gane Yaya ce.

(Assalamu alaikum wa rahmatullah. Suna na Khadija Yusuf wadda aka fi sani da Jinjin matar Habibu.)

"Wannan ba muryar Yayan Hamdiyya bace?" Umma ta soma magana da wata irin kaWuwa.

"Ku saurara" Alhaji ya karSi wayar don ji yayi duk wani gashi na jikinsa ya mi?e tsaye.

(Na bawa Kamal ?oda ba bisa tilastawa ko cinikayya ba. Cikin Hikimar Allah maigidana ya biya min kuWin Umara da tanadin shekaru. Sai gashi ina zuwa Allah Ya yi sanadin da naga Kamal a yanayin da nayi imanin ?an uwansa na gida basu sani ba. Kuma ni kaWai ce Allah Ya ni'imta da damar taimaka masa a kusa. Lallai Girman Ubangijina ba abin wasa bane. Ya tsara komai daki daki ni wace ce da zan fahimci hakan kuma na juya baya? Na aminta saboda Kamal na zo a wannan rana. Allah Yasa lafiyar ta samu. Ina fata mahaifinka ba zai ?yamaci rayuwarka da ?odar miskiniya ba. Abu na biyu kuma idan ban tashi ba don Allah ku faWawa Abban su Sajida ba a bina bashi kuma ni ma bana bi. Na sallami kowa kafin na taho. Akwai banki a ?asan gadona. Na tanadin auren Halifana ne. Sajida, Hamdi da Zeenatu don Allah ku haWa kai ku zama sirrin juna da ?aninku. Ina yi muku fatan Allah Ya albarka ce ku a duk inda kuke. Allah Ya tsayar da ku duka akan ?afafuwanku ta yadda babu wanda zai zamewa wani nauyi a gaba balle har ya ?osa a sami tawayar zumunci. Ku bawa Abbanku goyon baya ya sake aure. Yaya Habibu Allah Ya gatance maka kamar yadda kayi min. -Cikin kuka ta cigaba da magana- bakina ba zai taSa daina yabonka ba har numfashin ?arshe. A wajen wasu ka gaza, a wajena kuwa a wannan zamani babu mai martaba da daraja kamar ka. Allah Yasa Habibu ne mijina a lokacin da Allah Ya sabunta min halitta da mi?a?en jiki a aljanna. A ?arshe don Allah ku ro?a min gafarar iyayena. Ku cewa Baba ina gaishe shi. Ku bawa Innata ha?uri.) Sai ta Wan ja hanci (umara na zo ashe bani da rabon ganin Wakin Allah da ziyarar masoyina. Amma Alhamdulillah. Kamal da zuciya Waya zan taimaka maka. Allah Ya bamu alkhairi. Nagode.)

Audio Win a nan ya ?are. Mal. Salisu ya faWa musu yadda ta sanar dashi zuwanta asibitin. Mubina ta biyo ba tare da ta sani ba.

"Wallahi ban sani ba. Kuma ni bamu yi zancen da ita ba." Mubina ta faWi a ruWe.

"Hikimar Allah aka ce Dr. Mubina. Magana ta ?are." Inna ta faWi tana Wan bubbuga mata baya.

Alh. Hayatu kuwa juyawa yayi zai bar wajen. Ahmad ya bi shi da sauri. Su Hajiya ma tambayarsa au ke yi ina zai je a wannan yanayin.

"Ashe duk baku ji lokacin da ta ce Umra ta zo ba?"

"Mun sani dama. Taj ya so mu jinkirta tahowarmu tunda ita kaWai ce mu ka ?i. Ashe saurin da muke yi ita ce maganin komai."

"Ahmad samo min mota na koma hotel na sako harami na."

"Alhaji..." Inna ta soma magana.

"Idan bata tashi ba fa? Umrar zan yi mata. Ai ya halatta ka yiwa wanda bashi da dama ko?" Yayi tambayar ga Mal. Salisu.

"Ana yi."

"Nima zan yi mata" Hajiya ta share hawaye ta mi?e tsaye.

"Nima"
"Nima"
"Nima"

Sai da ya rage Bishir kaWai sannan Alhaji ya ce ya ha?ura kada a bar asibitin babu kowa. Ahmad ma zama ya yi saboda Alhaji ya bashi aikin neman visa da ticket ko nawa za a kashe domin kawo Abba Habibu.

Da su ka fita a mota abin mamaki ga iyalinsa dake baya bai wuce yadda yake ta goge idanunsa da bayan hannu ba. Yau Alh. Hayatu ne yake kuka akan wani ba jininsa ba. Tun yana yi a zuci har ta kasance suna jin shesshe?arsa. Wannan yasa babu wadda bata bayyana nata kukan ba. Direban tasi Win yana son tambayarsu amma kasa. Sai ha?uri kawai yake basu.

Jiransu su ka bu?aci yayi su ka shiga hotel Win su ka yi haramar Umra kamar yadda yake a tsare cewa mai shiga Makka daga Jeddah nan ne Miqatinsa. Mutum biyar su ka fito a tare. Alh. Hayatu, Haj. Gambo, Mama A'i, Umma Jamila, Inna Abu da Sulaiman Hayatu Sule (Abba) da niyyar yiwa Jinjin Win Abba Habibu Umra a ?asa Mai Tsarki.

_In sha Allah last post ba zai kai Lahadi ba._
RAYUWA DA GI?I 37



Batul Mamman=ؖ?




ALLAH YA SANYAYA MUKU ZU?ATA GWARGWADON HA?URINKU.
INA SO KU SANI CEWA BA DA GANGAN BANE.






***
Salati a jere a jere Amma ta dinga yi a yayinda Alh Babba yake sanar da ita abin da yake faruwa. Tana yi muryarta na rawa bata ma san cewa ta fara kuka ba sai da taji yana rarrashinta.

"Yaya Babba dashen ?oda fa ka ce..." muryarta ta sar?e a tsakiyar zancen.

"Godiya ya kamata mu yi wa Allah ba kuka ba. Banda haka da yanzu wani zancen ake ba wannan ba."

Da ta tuna hakan sai taji wani irin tsoron Allah Ya sske shigarta. Barin ma da ya Wan labarta mata yadda aka yi Yaya ta je asibitin.

Bayan hankali ya Wan kwanta tayi masa zancen yaushe za su tafi.

"Mu bari zuwa nan da kwana biyu tukunna. Sannan don Allah ki kama bakin ki kiyi shiru. Su Taj basu san komai ba. Haka ma shi Habibu da yaransa. Ke kaWai da sauran ?an uwa na faWa wa domin Hayatu yana cikin ruWani. Lallai yana bu?atar tausasawa daga wajen ?an uwansa."

***
Tashin hankali mara misali ne ya kama Abba Habibu bayan sun gama waya da Yaya. Awanni shida sun wuce amma ya rasa inda zai tsoma ransa. Ya sake kiran layin da ta bada numbarsa su ka yi magana yafi a ?irga ba a Wauka. Lokacin likitan yana cikin tiyata ana transplant surgery Win. Da ya fito kuma wasu abubuwan su ka Wauke masa hankali.

Can bayan isha ya dawo daga masallaci sai ga wayar Ahmad. Shi dai tunda yaga ba?uwar lambar Saudiyya kawai ya Wauka da sauri. Sallama ya yi yana jiran ta amsa sai yaji muryar namiji. Zuciyarsa bata ?ara tsinkewa ba sai da Ahmad Win ya gabatar da kansa.

"Ahmad ne, yayan Taj."

"Ahmad kana da labarin halin da iyalina take ciki ne?" Ya tambaya da sanyin jiki. Zuciyarsa ta bashi dalilin kiran kenan.

"Alhamdulillah." Ahmad ya kasa Worawa daga nan.

"Hamdala ai wajibin musulmi ce ko a bakin kura yake. Ina nufin labarin da zan iya bawa ?a?anta. Kuma tana da uwa da uba a raye. Su ma ina neman abin faWa musu." Ya ce da wani irin yanayi mai raunana zuciyar mai sauraro.

"Haka ne" Ahmad ya yi jim kaWan sannan ya cigaba da magana "akwai abokina da zai zo nan gidan ka yanzu. Na faWa masa sunan unguwar. Idan ya zo zai kira ka."

Allah kaWai Yake ri?e da Abba Habibu. Maganganun Ahmad sun sake dulmiya shi cikin fargaba.
"Abokin ka? A gida na? Me zai kawo shi?"

A gurguje Ahmad ya ce ticket za a saya masa inji Alh. Hayatu. Idan anyi sa'a yana da visa to a gobe zai sami damar tahowa sai dai ba jirgin su Hamdi ba.

"Ni Win Musulmi ne Ahmad. Kullum ina adduar kada Allah Ya Wora min ?addarar da tafi ?arfin imani na. In sha Allah idan ka faWa min gaskiya ba zan kasa Wauka ba."

Cike da jin nauyi Ahmad ya ce "Don Allah kada ka tambayeni. Ba zan iya faWa maka ba. Na dai san tana nan lafiya."

"Hakan ma amsa ce. Da ranta kenan."
Sai ya ?ara da cewa "ina Alhajin?"

"Nauyin ka ba zai bari ya iya yi maka magana a waya ba. Ya tafi yiwa Maman Hamdiyya Umra amma ka kwantar da hankalinka da ranta. Wannan shi kaWai ne abin zan iya faWa maka."

"Nagode."

Da ya ajiye wayar sai hawaye ya sauko masa. Ya sharce su da sauri. Yawan kuka yana daga cikin abubuwan da yake gudu saboda kada a danganta shi da mata.

"Me kika yi Jinjin? Wane irin taimako ne?"

Abokin Ahmad ya kira shi. Ya bada passport ya koma cikin gida. Zee da Halifa basu san wainar da ake toyawa ba. A wannan yanayin na zulumi ya kwana bai runtsa ba. ?arfe tara da rabi na safe abokin Ahmad ya kira shi ya ce su haWu a airport nan da uku na rana. Jirgin da zai bi takwas zai tashi na dare.

KaWuwa iya kaWuwa Abba Habibu ya gama yi. A haka ya dinga Soyewa Zee da Halifa saboda rashin sanin amsar da ta dace idan sun nemi ?arin bayani. Kaya kala uku ya iya haWawa a wata ?aramar jaka. Suma Win don ya san dole ne dai ya canja ba don haka ba da a haka zai tafi. Agogon bangon Wakin ya kalla. Goma ma bata yi ba. Gani yake kamar ya jawo lokaci ya ganshi tare da Yaya ko a wane hali take kuwa.

"Abba in yi tuwon shinkafa da rana?"

Muryar Zee a ?ofar Wakin yaji. Sannan ya tuna ai bashi da damar tafiya ya barsu su kaWai a gida. Dole wani ya san me yake faruwa. Shiru ba zai kai shi ko'ina ba.

"Abba?" Zee ta sake yin magana a hankali don ta fara tunanin ko bacci ya koma.

Tasowa yayi ya buWe ?ofar ta matsa masa ya fito.

"Kada ki Wora komai yanzu sai iya wanda za ku ci. Shi ma Win kaWan. Zan Wan fita unguwa na dawo."

Yanayinsa ya bawa Zee tsoro. Ta kalle shi a tsanake.
"Abba baka da lafiya ne?"

"Me ki ka gani?" Ya ?ir?iro murmushi.

"Wallahi duk kayi wani iri." Ta faWi da sanyin jiki. A zuciyarta kuwa tunani take ba zai wuce kewar Yaya yake yi ba.

"Bacci ne bai isheni ba. Matata ta tafi ta barni."

Zee ?umshe baki tayi tana dariyar sha?iyanci. Da haka Abba Habibu ya samu ya fita ba tare da ta tsananta bincike ba.

*

Anti Zinatu da sauran yan uwan Abba Habibu sun shiga mummunan tashin hankali bayan ya gama faWa musu halin da ake ciki. A gidan Anti Zinatun suka haWu domin ya kikkira su kafin ya iso gidan. Cikin sa'a kuma duka babu mai uzurin da ya hana shi fitowa akan lokaci.

"Wai ba da dangin mijin Labiba ta tafi ba? Ya aka yi cikinsu babu wanda ya bi bayanta?"

Wadda tayi tambayar tana rufe baki Abdul?adir ya yi musu alama da hannayensa akan yana so su saurare shi. Sai da yaga sun dawo da hankali gareshi ya dubi Abba Habibu cikin yanayi na jin nauyi.

"Gaskiya ina tsammanin abin da nake ji yana faruwa a Iyafot Win ?asa mai Tsarki fa gaske ne."

"Me kaji?" Suka haWa baki wajen tambayarsa.

Sai da ya Wan jajantawa kansa girman maganar kafin ya fitar da ita.
"Yaya Habibu kayi ha?uri da furucina amma magana ta gaskiya ita ce yanzu an tsananta kame da binciken masu nakasa."

Da sauri Abba Habibu ya canja zama "me? Me ka ke nufi?"

"Naga ya faru a unguwarmu. A'ilo Gurguwa ko ?asar bata shiga ba aka aunota gida. Kuma kusan kowa ya sani cewa bara ta tafi yi."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya Salam. Subhanallahi..." Abba Habibu yake ta faWi shi kaWai. Sauran ?an uwansu kuwa sai sallallami.

Abdul?adir ya dubi Abba Habibu "bani da tabbas amma ina zargin haka Win ne. Idan ba haka ba me zai sa a kama ta?"

"Ni fa ban ce an kama ta ba" Abba Habibu yaci gyaransa da wuri "iyalin Yaya Hayatu sun san halin da take ciki. FaWa ne ba za su yi ba a waya."

"Ba da nufin tozarci nake yi maka zancen nan ba. Na faWi abin da na sani ne saboda ka tafi da shirinka wajen kareta."

"Maganganunka tsorata ni suke yi Abdul?adir. A bar zancen nan kawai."

Anti Zinatu tana zubar hawaye ta ce "Habibu ko mun ?i ko mun so fa da ?amshin gaskiya cikin zancen nan. Kamar yadda yace ne ka tafi da shiri a zuciyarka kada gaskiya ta baka mamaki. Zuciyata sam bata son wannan tunanin to amma shi kaWai ne muke iya hasashe."

Abba Habibu gani yayi bashi da wata hanyar kashe maganar. Sun riga sun ?arfafa zarginsu. Shi kuwa tunanin kaWai ma ya ishe shi fargaba. A Saudiyya, Sijin (prison) suke kai kusan duk mai laifi irin wannan su ajiye. Idan na korowa gida ne daga can ake kai su airport. Masu hukuncin kisa....inaaa. Zumbur ya mi?e ya zura takalmansa.

"Bari na ?arasa gidan na sanar dasu su shirya su taho. Wannan magana kuma don Allah ayi shiru sai naje na ganewa idanuna."

Zaman bai ?ara masa komai ba sai tashin hankali. Ya yi imanin basu faWi komai domin cusguna masa ba. Iya gaskiyar da suke iya hangowa ce aka faWa masa.

A hanya yayi ta tufka da warwara akan abin da zai faWawa su Zee. Da fari tunanin ya ce musu Inna Luba ce babu lafiya. Da sauri ya girgiza kai da ya hango saurin gano shi da za ayi. Idan basu bishi ba tabbas zasu kirata a waya domin jin yanayin jikin nata. Daga nan ita kuma nata hankalin ya tashi. ?arshe dai gaskiyar da yake gudu dole ya faWeta domin duk inda yace musu zai tafi dole za su kira waya.

*

Abba Habibu ya kasa hakuri ganin ya gama bayani amma Halifa da Zee ko motsi basu yi ba. Zuciyarsa tana cike da fargabar kada su matsanta masa da tambaya akan kwaskwarimar da ya yiwa zancen. Nuna musu yayi cewa Alh. Hayatu da kansa ya kira shi yace bai dace Yaya ta tafi ita kadai ba. Shine yasa aka yi masa komai cikin gaggawa don ya tafi da wuri.

Kamar ba za su yi magana ba sai kuma Zee ta fashe da kuka. Tana jan hanci tana magana.

"Wallahi Abba tun zancen tafiyar tunanin da nake ta yi kenan nima. Kasan ko taimako take nema ba lallai ta sanar da abokan tafiyarta ba. Gashi Allah Ya kawo mata sau?i da wurwuri."

Murmushi Abba Habibu yayi da jin zancenta.

"Hamdala ya kamata kiyi ba kuka ba."

Halifa kuwa cewa yayi
"To yanzu dai gidan wa zamu je mu zauna don wallahi tsoron gidan nan zan ji idan mu biyu ne kacal"

Zee ta ce "Abba mu tafi gidan Anti Zinatu ko?"

Da tsokana Halifa ya ce "Malaminmu dai ya ce mata masu aure su dinga yin komai da izinin miji."

A fusace Zee ta tashi. Halifa ya fita da gudu ta bishi. Abba Habibu kuwa ya jinjina taimakon Allah mara yankewa. Ya gama tayar da hankalinsa sai gashi cikin sauki ya sami mafita.

*

Da Wokin tafiyar nan Hamdi ta wuni jiya. Amma zuwa dare gabaWaya jikinta ya mutu. Zee da Sajida da su ka yi waya ma babu ?ar zolayar nan da suke yi mata na ba saban ba za ta shiga jirgi. Hirar tafiyar Abban nasu ma sama-sama ta saka musu baki. Halifa kuwa dama list ya ce zai tura mata kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login