Showing 108001 words to 111000 words out of 182745 words

Chapter 37 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

106

Bata sani ba ashe Taj ya kirata ya kai sau shida. Amma ce ta turo shi Wauko musu amarya. Fitowar tasa ma sai da tayi da gaske. Anti Zahra tun safe ta bar gidan. Su na can gidan Alh. Lurwanu yayan Inna don a nan za ayi Kamun. Saboda ?urewar lokaci basu iya samun event centre ba.

A waya ta faWa masa cewa ana la'asar yaje ya Wauko Hamdi. Hankalinsa a take ya tashi. Wato ?an kwanakin nan da ya soma dawowa daidai babu abin da yake gudu kamar haWuwa da amaryar tasa. Da wane baki zai bata ha?uri akan marin da ya yi mata? Inna bata ce masa komai akan asiri ba tunda Yaya Malam ya gargaWeta da zargi. Gani yake girmansa ya gama zubewa a idanunta. Namiji mai dukan mata bashi da wata daraja a idonsa.

"Bari na faWawa Happiness ya shirya mu tafi da wuri."

"Kai Happino. Nace happino" Amma tayi magana a fusace "Wauko matar auren naka ma sai da shi? Ince ko daren farkon ma tare za ku."

Da mamaki ya ce "Amma me ya yi zafi? Kamal nake nufi fa."

"Shi Win fa! Ku yanzu sam baku iya lissafi da zurfin tunani. Dama me yasa ake haWa angwaye da ?an rakiya? Ai saboda gudun fitinar zamani ne. Ku kuwa tunda an riga an Waura aure me za ka yi da Wan rakiya?"

Dariya sosai ta bashi ya ce "to Allah Ya baki ha?uri. In kina so ma sai na Waukota na kai muku ita har kujerar da za ta zauna."

"?an banza mai bakin tsiya. In baka yi wasa ba wallahi har wurin zaman sai in ce ka kawota mu ga ?arshen rashin kunya."

"Cewa dai za ayi tarbiyarki ce." Ya ce da tsokana.

Ita ma da ta san hali bata san me ya sa ta biye masa ba. Rabuwa tayi da shi bayan ta tuna masa ?arfe biyar daidai su ke son farawa.

Da ya faWawa Kamal yadda su ka yi a wayar dariya su ka dinga yi son ransu. Kamal na cewa Happy ya girma shi kuma yana baya so.

"Ni wallahi kunyar haWuwarmu ma nake ji."

"Hamdi fa bata da matsala. Kawai ka bata ha?uri a wuce wajen."

"Kaga last faWanmu kuwa da na kai mata kati? Tana faWa ina yi kamar wasu kaji. I am seriously ashamed og myself." Ya rufe fuska da tafukan hannayensa.

"Dalla kada ka bada maza. Kawai ka sabunta mata karatu yau yau Winnan. Su fa mata kana rarrashinsu ka gama dasu."

Taj ya gyaWa kai "Allah bari in samu a kai min rigimammiyar nan gida. Zan yiwa su Mama famfo akanka sosai. Dr. Mubina will be Mrs Happiness."

Kamal murmushin ya?e kawai ya yi. Taj ya yi wanka ya saka shirt da wando abinsa ya zo zai fita.

"Wani sabon salon wula?anci ne wannan ko me? Ina kayan da Abba ya karSo daga wajen tela?"

"Direba fa zan yi. Amma ta ce ba zan shiga ba. Kuma kawai sai na saka sababbin kayana su yamutse?"

"Kaina ciwo yake Happy. Bani da ?arfin yi maka surutu. Kayi abin da ya dace ka fita."

Kamar ya yi musu sai dai yaga babu alamun wasa tattare da Kamal Win. Dama kuma tsokana ce tasa shi saka waWancan. Ya canja da wasu sababbi cikin na bikin. Sai gashi yayi kyau sosai. Ya tambaye Kamal ko zai sha magani ya ce a'a. Gajiya ce.

Taj na fita ya kira Mubina ya faWa mata jikinsa fa babu daWi. Tana hanyar zuwa wurin kamun ita da ?anwarta don har gida Yaya Kubra ta aika mata katunan bikin duka. Dole ta juya ta koma asibiti. A hanya ta sauke ?anwar ta ta tace mata patient gareta.

Ruwa ta saka masa da wasu magunguna masu ?arfi har ya dawo daidai.

"Ban faWawa Dr. Kubra ba saboda bana son raba mata hankali. Ciwon nan mun barshi tsakaninmu zuwa lokacin da za a gama bikin Wan uwanka kamar yadda ka bu?ata. Idan bata faWa ba ni zan je har wajen Alhajinku wallahi."

Ranta a Sace yake. Kamal ya yi mata murmushi.
"Wannan faWan duk don na hanaki zuwa cin shinkafar biki ne ko?"

Harara ya samu "Wasa ma ka mayar da abin?"

"Sorry Doc." Ya Wauko wayarsa dake gefen gadon "zo mu yi hoto."

Yadda ya yi maganar ya taSa mata zuciya. Tayi murmushi duk da tana ?o?arin nuna masa fushinta. Ya gyara zama ta koma gefensa ta zauna tayi musu selfie. Tana tashi ya Wauketa wasu. Bai taSa ganinta da kwalliya irin ta yau ba. Kasa ha?uri ya yi ya ce da ita,

"A misali da zan warke za ki iya aurena Mubina?"

Abin control Win gudun ruwan da take ?ara masa take dubawa da ya yi tambayar. Yasa ta kusa ture ?arfen gabaWaya saboda yadda zancen ya taSa ta. Allah Yasa bayanta yake kallo da yaga halin da ya jefa zuciyarta. Tattaro nutsuwa tayi

"A'a."

"Ni? Ni?" Ya nuna kansa kamar yato ya sanyata dariya "nayi tsammanin za ki bani amsar da zan ji daWi."

"Baka cancanci hakan ba Kamal. You are very stubborn. Rantsuwar dake kare ala?ar likita da patient ce kawai ta hanani yi maka handsfree."

"Na nawa kuma? Ba kin faWawa Yaya Kubra ba?"

"Da kai da ita akwai wanda zai rantse cewa na faWa? Magani ta gani ta zo tayi tambaya."

Kallonta kawai yake yi yana jin inama ?alau yake. Da ita ma tana wajen Kamu ana kama masa ita.

"To da ace ni Win patient ne mai bada haWin kai irin yadda kike so, za ki iya aurena idan na warke?"

Sai da ta kalli idanunsa sannan ta bashi amsa "Da gudu" sai kuma ta soma hawaye "please let us help you Kamal. Akwai dama indai mu ka sami donor. Kada ka Wora min zawarci tun kafin nayi aure don Allah."

Tana gama faWin haka ta fice saboda kukan da take shirin yi a gabansa. Shi ma hawaye ya goge bayan ta fita. Yana tsoron sanya rai da rayuwa bayan samun lafiyarsa ba abu bane mai sau?i. Shi yasa yake ta kaucewa sanar da mutane. Amma zai bi shawararta. Idan an gama bikin Taj da kamar sati Waya da kan shi zai faWawa iyayensa.

*

Mota Sajida da Fadila su ka rako Hamdi bayan an rufa mata wani net ja wanda dama an faWa musu da shi za ta fara shiga. Sai an yi kamun za a cire mata. Haka aka rufe motar gabanta yana matsanancin faWuwa.

A hankali yake tu?i cikin nutsuwa. ?amshin da take yi ya kwance duk wani notin arzi?i na kansa. Yana son yi mata maganar abin da ya faru amma yana jin nauyin hakan. Kamal ya ce ya bata ha?uri. Amma idan kuma ya bata ta sake yi masa maganar da wancan yanayin zai dawo fa?

Tsoron da yake ji bai kai nata ba. In ka cire gaisuwar da tayi masa a gaban su Sajida bata sake ko da Waga kanta ba. Kwata kwata bata yarda da bakinta ba. Yanzu dai lafiya ?alau su ke tafiya. Idan kuma tayi magana irin kalaman nan dake fita da kansu su ka bar harshenta fa?

Kowa kama bakinsa ya yi. Da Salwa za ta ga yadda aikinta ya yi tasiri a wajen nan da ta daka tsallen ?an bori ta dire don murna.

Shirun damunsa ya yi ya kunna musu rediyo. Tashar farko da ya samu ya bari. Aka yi dace ko rashinsa domin kuwa a daidai lokacin mai tallan maganin gargajiya ce take ta kwararo bayanin maganin basir.

(Wato shi fa basir idan yaci jikin magidanci sai kaga ko kukan jarirai an daina yi a gidansa. Cikinsa kullum a ?ulle tamau kamar yarinya tana koyon Waurin zani. Da shi da matarsa babu maraba. A jaraba maganin nan domin kawo ?arshensa. Akwai mai tsiro, da mai jini.)

Cikin kujera Hamdi ta shige saboda tsabar kunya. Mai magani ta cigaba da Saro zance mai nauyi. Aka barta da satar kallon Taj. ?an duniya da ya fahimci kunya take ji sai ya ?ara volume. Can sai cewa yayi

"Nagode Allah ni dai ?alau nake. Masu fama kuma Allah Ya yaye musu."

Shiru tayi tana ?ifta idanu. Gara yayi mata wa?o?insa akan wannan magana.

Kallonta ya yi ya saki murmushi. Wani irin jindaWi da nutsuwa yake ji a ransa.
"Ko kina da shi in saya miki..."

"Innalillahi..." ta kalle shi babu shiri ta yaye lulluSin.

Numfashi ya ja da ?arfi da su ka haWa ido. Tayi masa kyau ba kaWan ba.

"Ni lafiyata ?alau wallahi."

A daidai lokacin mai maganin ta zaSi Wora zancenta da dawowa kan mata.

(Na dawo gareku matan gida. Ina da magunguna sahihai waWanda mu ka gada tun kakanni. Maganin sanyi da magungunan mata masu gigita maigida.)

Hannu ta kai za ta kashe rediyon ya dam?e shi yana murzawa a hankali.

"Don Allah ka canja."

"Shhh...an zo wajen naku. Bari mu ji."

"A ji me?" Ta tambaye shi looking horrified.

(Mace sai ta bari sanyi ya gama cinye mata jiki. Sai miji ya mayar da ita bora sannan za ta fara neman magani. Ina mai fama da ?ai?ayin...)

Hamdi ta dube shi kamar tayi kuka.
"Allah idan baka kashe ba zan iya yin kuka."

"Allah Ya baki ha?uri. Daga taimako?"

"Ba na so." Ta turo baki.

Soyayyarta da ta kwanta wucin gadi ta dawo masa sabuwa fil. Ba ?aramin kewar wannan Hamdin yayi ba. Yana son faWa mata amma sun riga sun iso gidan Alh. Lurwanu. Inda zai ajiyeta Amma ta faWa masa bayan ya shiga ciki da motar. Yana hango masu rakata wurin zamanta su Zee da su Firdaus.

"Wanne zan saya miki? Kin dai ji ance mace bora take zama idan bata sha ba."

Tsuke bakinta tayi. Sai da ya buWe lock za ta fita ta yi magana a hankali yadda babu mai ji cikin ?an rakiyarta.

"Nafi ?arfin zama borar gida."

"Za ki maimaita wannan maganar nan da saturday."

"Allah Ya kaimu" ta faWi sannan ta ?ifta masa ido don tsokana.

A tunaninta za ta samu guduwa ne a lokacin. Sai gashi su Firdaus sun dage sai sun yi musu hoto kafin a shiga da ita ciki. Fitowa yayi daga motar ya tsaya a gefenta.

"Kai Uncle Taj. Irin wannan hoton tun zamanin su Mama. Ku Wan ?ara matsowa mana."

Hamdi bata ankara ba taji ya janyota kusa dashi. Hannunsa Waya a tsakiyar bayanta. Jin kamar za ta faWi sai ta Wora nata hannuwan a kafaWunsa.

"In miki wa?a?" Ya ce a saitin kunnenta. Hakan ya bada style na hoton masoyan da su ka yi nisa da ?aunar juna.

Ta san tsokanarta yake yi shi yasa tayi dariya. A haka aka Wauki hoton. Ya yi kyau sosai.

Bayan an gama taro mai ban sha'awa da Firdaus ta koma gida ta dinga Wora hotunan kamu a status. Kuma wannan hoto shi ne na farkon da Salwa ta fara cin karo dashi. Zuciyarta a take ta Wauki zafi. Ta juya ta kalli Mami dake kwance tana bacci ga yawu yana dalala ta gefen bakinta. Dole taje Kano ko ta wane hali. Wayarta ta Wauko ta kira Ahmad ta faWa masa hatsarin da Mami tayi da ro?onsa akan ya dawo dasu Aminu Kano Teaching Hospital saboda a nan Bauchi babanta ya?i sakin kuWi a dubata yadda ya dace (a ?aryarta). Duk da baban nata ya gargaWesu da ?an uwanta da su yi shiru har sai ta farfaWo saboda bai san me zai cewa Ahmad Win ba. Yana kunyar yaron kuma yana tsoron sake Satawa Alh. Hayatu rai.

"Me ya sa zai ce kada a faWa min? Kwananku nawa a asibitin? Shi ne kullum idan na kira ki ke min ?aryar ?auye ta tafi" Ahmad ya ce cikin tashin hankali.

"Sharri aka yi mata wai tayi masa asiri."

"Zan kira shi mu yi magana. Ku shirya, idan na zo gobe in sha Allah sai mu taho tare."
RAYUWA DA GI?I 27





Batul Mamman=ؖ?



_For Maryam Yusra because you deserve it! Allah Ya baki lafiya._






(Don Allah duk waWanda su ka biya kuWin talla na cikin labari kada su ?osa. Saboda kun fi son wanda zai fito cikin labarin dole sai an zo gaSar da zai dace. Ina fatan jinkirin ba zai sa muku damuwa ba. Har kullum ina godiya. SonSo)





***

A mafarki ko ido biyu, Alhaji bai taSa tunanin zuwan wannan rana ba sai da ta zo Win. Yau dai zahiri ba zance ba shi ne yake zaune a cikin falonsa babu kowa sai masu gadi da direbansa dake bakin gate su na hira da daddare. GabaWaya gidan ana idar da sallar magariba su ka daWe. Duk an tafi wajen dinner Win Taj da Hamdi. Hatta masu aikin gidan babu wanda aka bari. Kasa zaman falon nasa ya yi ya shiga Sangaren matan gidan. Nan kam sai da zuciyarsa ta motsa da tausayin kansa. Shiru ne mai ratsa Sargo. Sai kayayyyakin ?a?ansa da jikoki da ba a gama tattarewa ba. Wasu ma a ?asa su ka bar nasu.

"GanWoki" ya yi murmushi yana mai du?awa ya Wauke kwalbar turaren da aka bari a ?asa.

Samun kansa ya yi da tsince duk wani abu dake ?asa wanda bai kamata ba. Yana yi ransa na tunatar dashi cewa duka mutanen da su ka shirya a wajen nan da Wakunan matansa fa nasa ne. Zuri'arsa ce. Shi kaWai a shekarunsa sittin da takwas ya tara jikoki sama da arba'in. Ga ?a?a ga tarin dukiyar da ko yau ya a????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? jiye kasuwanci ba za su bu?aci komai ba a shekara goma masu zuwa.

Ya auro mata masu mabambantan tushe amma waWanda su ka yi tarayya wajen taya shi gina gida irin wannan. Tabbas shi ma ya sani cewa arzi?insa ba a naira da kwabo yake ba. Iyalinsa sune arzi?insa. Banda dai abubuwan yau da gobe da ba a rasawa amma ya tabbatar cikin ?a?ansa babu fasi?i. Allah Ya yi masa gamdakatar Ya shirya masa zuri'a. Kuma komai ya ce ya zauna daram kenan a gidan. Duka ya Wauka ?arfin ikonsa da tsare gida ne wanda cikakken namiji kaWai ke iyawa.

Sai gashi an wayi gari sun haWa kai suna neman juya masa baya. Jiya sun tafi wajen kamu ?wai da kwarkwata. Bayan saboda girman gidansa ?a?an dangi ma suna cin arzi?in ayi bikinsu a nan. Shi su ka tafi gidan Alh. Lurwanu don su nunawa duniya gazawarsa. Yau kuma Hajiya ta ce masa event centre za su je kuma sai an gansu. Abin tambaya a wajensa yanzu shi ne wai me yasa su duka su ke ganin aibun hukuncinnda ya yankewa Taj? Anya sun san yadda illar dake tattare da daudanci? Habibunsa fa daga son girki ya fara kamar wasa. Idan a baya Taj bai yi Wabi'un mata ba yanzu zai iya. Surukuta ta shiga tsakaninsu da Wan daudu kuma ga aiki suna yi tare. Ya numfasa a yayinda ya zauna ya kula cewa gyara sosai ya yiwa falon. Dole ne ya raba Taj da Hamdi. Barazanar da ya yi a Bauchi bata nufin ya karSi wannan aure. Salwa ce ba zai taSa bari ta kusanci danginsa ba. Duk lalacewar Wan daudu yafi mushriki a wurinsa.

***

?ememe Yaya ta?i shiryawa,wai ba za ta je wajen bikin ba. Duk ga ?an uwa za su wakilceta. Za ta zauna a gida da Innarta Luba da ta zo jiya. Aka kaWa aka raya ta?i chanja shawara. Gashi ?an matan nata duka ukun basa nan. Yanayin gidansu bai basu damar yin ?awaye ba. Shi yasa duk wani abu da za ayi da ?awa tare su ke yi.

Tun azahar Safwan ya kwashesu zuwa event centre Win inda a saman wurin ne za a rangaWa musu kwalliya. Kowacce mijinta ne ya biya mata. Ita Hamdi lalle aka fara yi mata. ?aya daga cikin yayyen Taj tana da saloon da wurin lallen amare da na matan ?walisa. Wadda tafi iyawa ta tura ta yiwa Hamdi ba?i da ja. Tun kafin a gama ake santin kyawun da yayi. Ana gamawa aka koma kwalliya bayan tayi sallar la'asar. An fito da ita fita ta girma. Sai wanda ya sani ne kawai zai iya gane ita Win Hamdiyya ce Wiyar Habibu Simagade. A haka kuwa za ka yi zaton ?ar wani ?usa ce. Ana kammala kwalliyar tayi sallar magariba sannan ta saka kaya.

Anti Labiba ce ta kira Sajida ta faWa mata rigimar da ake yi da Yaya akan ta shirya. Sajida tana ji ta san babu wani kunya ko kawaici da yasa mahaifiyar tasu son zaman gida. A nata tunanin rashin zuwan zai taimaka ya Wago darajar ?a?anta a idon mutane. Bata son yin abin da zai janyo mata ido harma ayi ta ambaton ita ce maman amarya, daga nan wanda bai sani ba a bashi labarin cewa babansu ma tsohon Wan daudu ne.

"Don Allah ba ta wayar Anti."

Harara kala kala Yaya ta gama yiwa Anti Labiba kafin ta karSa.

"Yaya me yasa ba za ki je ba?"

Caraf a kunnen Hamdi. Ta karSi wayar ana yi mata Wauri da wani yadi haWe da net mai santsi.

"Yaya ba za ki ba?"

Shiru tayi saboda taji yadda muryar Hamdin ta canja.

"Yaya?"

"Ina jin ki. Ga iyayenku nan. Kowa zai je. Me zan je yi ni kuma?"

Zee da Sajida kusa da Hamdi su ka dawo su ka kara kunnuwansu. Kowacce tana iya gane zancen na Yaya akwai damuwa a ciki. Hamdi sai cewa tayi,

"Wallahi Yaya idan baki je ba nima daga nan gida zan taho." Su Zee jinjina mata su ka yi da thumbs up da ta faWi haka.

"Ke ba na son rashin kunya."

"Allah Yaya. Zan zauna a saman nan har sai kin zo."

Sajida ta mi?awa wayarta ta koma aka cigaba da Wauri. Sai dai ana yi ?walla na sauko mata. Mai kwalliya tabi ta tada hankali. Idan kwalliyar ta caSe ko amarya bata sauka da wuri ba za a sami matsala.

"Za fa ta zo tunda taji kin yi rantsuwar nan." Cewar Sajida.

"Ke ma ai bata je naki ba." Zee ta tunatar da ita.

Ita dai me kwalliya ha?uri ta soma bawa Hamdi ganin wankin hula yana neman kai su dare. Sai da ya rage pins kawai za a saka a jikin mayafi da head Win sannan kukan nata ya ?aru. Daga can ?asan zuciyarta take yinsa. Ta ?ara jinjinawa uwa a duk inda take. Babu yadda za ayi ace Yaya bata son ganin ?a?anta a wajen bikinsu suna walwala kamar kowacce uwa. Amma kawai don kada a aibata mata su saboda yanayin tafiyarta shi ne ta zaSi zaman gida.

Da bikin Sajida duk sun Wauka kawaicin uwa ne. Musamman da basu ga mahaifiyar Safwan a wajen event Win nasu ba (baban Safwan ya hanata zuwa). Yanzu kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login