Showing 177001 words to 180000 words out of 182745 words

Chapter 60 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

131

da tayi ba hatta iyalin Alh. Hayatu sai sun fitar da ita kunya.

Purewater ta Wauko guda Waya ta sako akan plate ta zo ta ajiye a gaban Ahmad. Ya bi ta da kallo ita da ruwan ya watsar.

"?auke abin ki ba ruwa na zo sha ba."

Kunyar taji ta ce "Ko na fita na siyo maka mai sanyi? Ko zoSo?"

"Zauna."

Zaman tayi tana godiya ga Allah da bai nemi hakan ba don ko sisi bata ajiye ba. Sadakinta ma ta nema ta rasa a cikin gidan. Ta san wanda ya Wauka amma a yanzu tsoron tada maganar take yi.

Ahmad ya sami damar ?are mata kallo daga sama har ?asa. Abin tsoro. Auren da bai fi wata guda ba duk ta ?are tayi ba?i sai idanu a cikin loko kamar mujiya da ha?ora gayau. Falon da ta ajiye shi babba ne irin wanda kowacce amarya za ta yi farinciki da mallakarsa. Fitilu na alfarma, POP ceiling da dukkan wani abu da zai sa ace gida ya haWu akwai shi. Abin da babu shi ne funiture da electronics. Kuma da alama har cikin Wakuna da kitchen haka abin yake. Shima a yanzu akan tabarma yake zaune. ?akin kwananta ma tabarmar ce. A cikin Wakin Alh. Usaini kuma katifar maigadi ya Wauko bayan mahaifinsa ya kira maigadin ya ce ya bar aikin gidan.

"Salwa wannan rayuwar ce ashe take jiranki shi yasa ki ka kasa kwantar da hankalinki akan rashin samun biyan bu?atar zuciyarki ko?"

Ta ina za ta fara faWa masa tayi nadama amma a lokaci irin wannan da bata da amfani? Yanzu ta gane cewa idan so cuta ne da gaske ha?uri magani ne. Da ta ha?ura da Taj da tuni Mami ma bata gamu da hatsarin nan ba. Everything would have been fine. Rayuwar gidan Alh. Usaini babu daWi ko kaWan. Har yanzu bata gabansa, hakan bai dame ta ba kamar yadda ta zame masa wajen huce haushi idan ya fita bai samo komai ba. Mahaifinsa bai barshi da komai ba sai gidan nan albarkacin auren da ya yi. Duk inda yake ajiya a banki ya sa an rufe masa da dogon gargaWi akan kada ya kuskura ya tada maganar.

"Na san irin wada?ar da kayi min da dukiyata. Idan zan bi kayana na tabbata baka da kuWin biyana saboda haka magana ta mutu a tsakaninmu. Duk ranar da ka dawo mutum ni kuma nayi maka al?awarin dawo maka da komai naka. Idan ba haka ba kuwa sai dai ka jira gado in na riga ka."

Yanzu rayuwarsa ta koma bibiyar abokai da tsofaffin yaransa yana maula. Wataran a dace wataran kuma a wula?anta shi. Da ya gaji ne ma ya goranta mata rashin gara da kayan Waki. Ita kuma saboda Wanyen kai ta kira Anti Zabba'u. Ranar anyi sa'a ?anwarsa ta zaga ta bayan idon iyayensu ta aiko masa da kaji da jallof Win shinkafa ta gaske. Kafin ya dawo daga wajen abokinsa sun cinye tas. Ita kanta Salwa bata ko WanWana ba. Tana ta magiyar kar su taSa aka rasa mai sauraronta ma. ?an uwa aka ce rabin jiki. Ahmad ya tausaya mata sosai. Kayan Waki da electronics babu abin da bai tanadar mata ba amma ta watsa masa ?asa a ido.

Suna zaune ya danne fushinsa yana ta yi mata nasiha tana ta kuks sai ga Alh. Usaini. Takalman namiji kawai ya gani ya yi jifa da ledar hannunsa ya zare belt ya afka musu. Salwa na ganin shi ta tashi ta tsaya a gaban Ahmad ta bubbuWe hannuwa da ?afafu ta kare shi. Ai kuwa belt ta sauka a jikinta ta gantsare don azaba. Ya sake Wagawa karo na biyu Ahmad ya mi?e. Kwarjini da cikar mutumtakarsa su ka sanya Alh. Usaini yin la?was kamar dafaffen alayyahu.

Ahmad ya ri?e belt Win tare da hannunsa ya nuna masa Salwa.

"Duk abin da za ka yi, musamman wanda ya shafi mu'amala da mutane kaji tsoron Allah. Da kai da ita da gurSatacciyar rayuwarku ku ka haWu amma hakan ba yana nufin da ita za?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ku ?are har ?arshen rayuwa ba in kun so."

Ficewa yayi ko waige babu. A waje yaci karo da ledar da Alh. Usaini ya yar. Taliya ce leda Waya sau mai, maggi da kayan miya na naira Wari biyu. Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Yanzu Salwa ake ciyarwa a haka? Lallai kowa ya?i sharar masallaci zai yi ta kasuwa.

Ya koma gida cike da damuwa. Ya kira Abban Salwa akan maganar kayan Waki ya ce ya rabu da ita. Darasi yake so ta koya a cikin auren nan. Hujjojin da ya bashi duka ya gamsu da su. Duk da haka washegari ya tura ?ar ?ur?ura gidan sha?are da kayan abinci.

"Idan da kuWi a wayarka don Allah ka bani aro na kira Yaya Ahmad nayi masa godiya."

Tsaki ya banka mata ya tashi ya fita da sauri ya bi bayan mai ?ur?urar nan da gudu. Sai da ya kusa ?arshen layi ya tsaya. Yana faman haki ya ce ya taimaka masa da numbar wayar wanda ya aiko shi. Mutumin ya karanto masa ya kwafa. Da numfashinsa ya daidaita ya kira shi.

"Dama godiya na kira nayi maka."

"Ku dai ku ji tsoron Allah daga kai har Salwa. Rayuwar da kuke ciki Allah Ya azurta masoyanku da fin ?arfinta. Cikin minti guda za a iya canja komai ma rayuwarku amma Allah bai bayar da iko ba. Hakan kaWai ya isa ya zame muku izina. Allah Ya kyauta."

Tunawa yayi da wani kalamin da yaji daga bakin Abban Salwa wanda shi kuma Baban Alh. Usaini ne ya faWa masa a lokacin da ya nemi shawararsa game da makomar rayuwar yaran nasu.

"Yunwa, ?ishi da rashin kayan more rayuwa zai sa su yi laushi harma ka ga nadama nan ba da jimawa ba a tare da su. Biyewa wannan ba ?aramin ganganci bane. Yunwa ta ishi kowane shege darasi. Yanzun nan za ka ga mutum ya shiga taitayinsa. To amma fa ?oshi shi kuma yana fito da Wan iska cikin mutane. Da zarar tumbi ya Wauka sai kowane rashin daraja ya biyo baya indai mutum ba nagari bane. Shin Alhaji ba ka ganin yadda almajirai su ke rashin mutumci a unguwa idan abinci ya wadace su? Wani fa a ?ofar gidanka zai zubar da abinci ya ce ka bashi gaya ko babu nama."

Abban Salwa ya gyaWa kai "wannan gaskiya ne."

"Ina son Usaini amma nafi son gyaruwarsa. Idan mu ka yi saurin karaya akan su to ka sani komawarsu gidan jiya abu ne mai sau?i. Irinsu bayan addu'a da nasiha dole a bari su gane cewa kyautatawa ce daga Allah privileges Win da su ke samu ba wai dolensu bane don sun isa. Suna bu?atar duniya tayi musu atishawar ?an tsaki!"

Abu ne mai wuya iyaye su iya Wauke kai idan ?a?ansu su ka shiga irin wannan yanayin to amma fa wani lokacin dole a tauna tsakuwa don aya taji tsoro.

***

"Zancen Port Harcout naji tana yi a waya wallahi. Don Allah kayi wani abu kafin ta ?arasa shiga duniya mu shiga uku."

Iyaa ke wannan maganar da Baba Maje tana kuka sosai. Sababbin tsare-tsare Baba Maje ya kawo cikin gidan bayan fitowar Ummi daga police station. An karSe babbar wayarta sannan ba a barinta ta fita ko ?ofar gida. ?awayenta tun daga soro ake sallamarsu. Dangi kuma aka sami abin so. Kowa ya buWe baki a gidan biki ko suna zancenta ake yi ana aibata halinta. Isassu ma har gidasu ke zuwa su faWi maganganu son ran su. Yarinya a cikin gidansu ta zama mujiya. Tsangwama ta ko'ina fuskantarta take yi.

Watarana Iyaa ta fita sai tayi mantuwa. Ta dawo za ta wuce Wakinta sai taji Ummin tana waya tana faWawa wanda su ke magana ya saya mata ticket Win luxurious bus za ta fito nan da kwana huWu. Iyaa ta sulale ta fice bata bari ta san da zuwanta ba. Sai dare ta sami Baba Maje ta faWa masa.

"Ummi tamkar ba jinin mu ba. Yarinya sai azabar taurin kai da son zuciya. Duk abin da yake faruwa bata saduda ba" Tana kuka tayi maganar.

"Kada ki yi furucin da zai kai ki ga nadama akan Ummi. Ni dai na fahimci hanyoyin da muka Sullo ba za su haifi Wa mai ido ba. Ina kuma tsoron ace jini na ta shiga duniya."

"To yanzu meye abin yi?"

"Aure zan yi mata."

"Da wa? A dangin mu wa za ka tursasa ya bari Wansa ya aureta?"

"Kofur ?anliti zai auri Ummi" Baba Maje ya faWi da wani sense of relief.

Iyaa tayi shiru kafin daga bisani ta ce "haka ne."

"Ko kina da wata shawarar? Irin wannan auren ba shi mu ke yi mata sha'awa ba tsakani da Allah."

Magana su ke yi ?asa-?asa cikin alhini gwanin ban tausayi.

Iyaa ta numfasa "yanzu za ayi ta aibata auren ana yamaWiWi da mu a cikin dangi da unguwa idan aka ga mijin da ta aura. Wasu ma su ce Allah Ya ?ara pi."

"Sai mu toshe kunnuwanmu tunda ba a canjawa tuwo suna. Mune dai iyayen Ummi duk inda za a je a dawo."

"Amma kana ganin za ta zauna? Mutum irin Kofur Winnan yana da abin ri?e mata sama da guda?"

Shima kansa Baba Maje ba wai son zaSin nasa yake yi Wari bisa Wari ba. Da babu ne dai gara babu daWi.

"Haka za mu ha?ura don sau dubu gara ace abinci ne bata da shi a gidan miji da dai ta shiga duniya. Indai da rai da lafiya ba zan bari yunwa ta kama ta ba alfarmar Annabi SAW."

"Wahala za ta ?aru a kan ka. Ba gara mu nemi wata dabarar ba?"

"Ummi bata jin magana kema kin sani. Kuma wannan shawarar da na yanke ba rashin so bane ya janyo. Ban san yaya lahira take ba amma a iya abin da Allah Ya hore min in ji a duniya game da iyalina, sai nake ganin ko aljanna na samu ba zan ji daWinta ba idan wani cikinku bai riskeni ba a can. Ina tausayin makomar ?ata idan ba ta yiwa kanta karatun ta nutsu ba." Kawai sai ya soma hawaye.

Kusa da shi Iyaa ta koma su ka ri?e hannu suna kuka mai ratsa zuciya.

"Bawa baya sanin matsayin ibadarsa sai ya koma ga Allah. Kuma muna yi ne cikin kyautata zato da cikar ya?ini to amma bamu san baWini ba. Yaya kike ji za ta kasance ace duka gidana babu wanda ya dace balle ya ceci sauran? Ai ance ana bawa salihan bayi ceto ko? Shi yasa na damu sosai."

"Kafin ma a kai ga lahira ba ka ganin kamar iyalin Habibu sun ja baya da mu? Ka duba fa hatta aikin da aka yiwa Jinjin sai Baballe ne ya ji a wajen Zinatu."

"Kai anya kuwa? Kada mu Wauki ha??insu." Baba Maje ya faWi duk da yafi yarda da zancenta.

A sanyaye ta ce "nima bani da tabbas, hasashe ne kawai duba da abubuwan da su ka faru. Ka san Allah da Siyama ce ta auri yaron da ya fito daga irin gidan nan namu sai na sa an sako min ita. Zan ji tsoron kada Ummi ta cutar da ita."

"Kamar kin shiga zuciyata. Ina ta tunanin ko dai in sa ya sauwa?e mata. ?ila sun kasa faWa mana ne saboda kawaici."

"Allah Yasa bai taSa musu ?a ba. Ka san yaran yanzu da mugun rashin ha?uri."

"Zan tuntuSe shi. Tunda auren dama ba na soyayya bane. Zumunci mu ka so ?ullawa kuma da alama ba zai yiwu ba."

Wani abu Ummi taji ya wuce mata mai Waci. Ta juya a hankali ta koma Wakinsu. ?azu ta ga fitar Iyaa sai ta zargi ko ta ji wayar ds tayi. Shi ne ta biyo ta da Babansu ya dawo. Jikinta Sari ya dinga yi har ta isa ta faWa kan gado. Da yake zuciyar ta jima babu tunanin komai sama da son kai, hassada da sharholiyar duniya, sai ta kasa kuka. Ta kuma rasa addu'ar da ya dace tayi. Haushin kanta kawai take ji da takaicin jin wayarta da Iyaa tayi.

*

Kofur ?anliti har gida ya zo neman auren Ummi bayan fitowarta da kwana Waya. Ta zauna ta sille shi da rashin albarka iri-iri. Baba Maje sai ya bashi ha?uri ba don komai ba kuwa shi ne yadda yake gudun me zai je ya dawo. Ummi idanunta a buWe suke. Kada tayi wa ?anliti abin da auren zai zo ya mutu da wuri. To amma da alama zai iya ri?onta duk botsarewarta. Haka dai yake gani amma bashi da tabbas. Saboda haka bayan shawararsu da Iyaa, sai ya kira shi su ka yi magana.

"Me yasa kake son auren Ummi duk da ka san wani abu cikin halayenta?"

?anliti ya yi murmushi da confidence "ina sonta ne Baba."

"Me yasa kake son mace irinta?"

"HaWi daga Allah. Kuma da naji laifinta sai na tuna da tawa samartakar." Gyara zama ya yi domin jindaWin abin da zai faWa.
"Baba ni fa tsohon Wan daba ne."

Kallon Baba Maje yayi yana jiran ganin tsoro ko firgici sai yaga babu ko Waya. Neman ?arin bayani kaWai yake iya gani. ?anliti sai ya yi masa tun kafin ya tambaya.

"Nayi dabanci da shaye-shaye sannan na taSa tsibbu." Baba Maje yaji hankalinsa ya tashi amma kuma a yanzu dai bashi da wani zaSi.

"Abubuwa ne da na san za ka sami labarinsu idan ka tashi bincike a kaina shi yasa nake faWa maka. Na riga na tuba tuntuni ina aiki kamar yadda ka sani."

Wata zuciyar tana ?wan?wasarsa akan ya fasa yayinda wata take tuna masa da me zai iya faruwa idan Ummi ta shiga uwa duniya.

"Na baka amanarta. Don Allah idan ka ga abin yafi ?arfinka ka dawo da ita gida. Bana son a kai ?adamin da za ta gudu domin yanzu ma i?irarin da take kenan." Yanayinsa ya nuna tsantsar damuwarsa "ba na son zama abin nuni da kwantace ace ?ata ta shiga duniya."

"Ba za ta shiga ba da yardar Allah. In Allah Ya so sai kayi alfahari da bani ita."

Da daddare a ranar ya faWa mata shirinsa a kanta bata ce komai ba. Abin ya bashi mamaki sosai. Haka dai yana ta tsoron kada a wayi gari ta gudu kafin auren amma yaji shiru. A fuska da baWini bata son auren amma ta rasa gane me yasa ta kasa kataSus. Auren tubabben Wan tsubba zata yi bata sani ba. Surkulle da siddabaru babu wanda bai iya ba, kuma babu wanda bai shirya yi ba a kanta domin ya samu ta zauna dashi. Ko bayan zuwansa na farko ba wai ha?ura ya yi ba, shiri ya tafi sakewa.

?an uwan Baba Maje da ya neme su akan bikin sun yi murna ?warai. Ashe kowa na tsoron kada ya ro?i alfarmar haWata da nasa Wan saboda mugun halinta. A ranar da ya kamata ta gudu, a ranar aka shafa fatiha tsakaninta da Kofur ?anliti.


***

BAYAN WATA UKU

Taj da Kamal sun du?ufa aikin gyara ko ace jeren sabon gidan Abba Habibu da Yaya. Hawa na uku kuma na ?arshe a ginin gidan abincin da aka bashi ya mayar gida. Ko sisi basu bari ya kashe cikin kuWin da Dr. Hadifi ya ba shi ba. Iyalin Alh. Hayatu musamman Kamal su ne suka yi komai.

An sallamo su daga asibiti jiki ya yi kyau sosai. Duk da haka Taj ya hana shi ayyukan ?arfi. Shi da Abba su ke ta kai komo. Abba Habibu da Alh. Hayatu kuma sun fita ana ?arasa cike-ciken takardun shaidar mallaka da sanya hannun hukumomin da su ka dace.

A can gidan da Alh. Hayatu ya kama kuma Inna Luba da Baba Malam (Alhaji ne ya biya masa) sun iso kwana biyu da su ka wuce. Su Amma da Yaya Babba ma duk sun zo amma sun wuce Madina. Sai an gama gyare-gyaren gida da restaurant gabaWaya za su rankaya dukkaninsu su tafi gida. Su Abba Habibu za su koma su kimtsa a tsanake sannan su koma a fara sana'a.

Hamdi da Mubina sun biyo su amma sun fita saya musu abinci. Da su ka dawo da ledoji ni?i-ni?i masu sauke kaya duk sun tafi tare da Abba. Babu kowa sai mazajensu.

?ata fuska Hamdi tayi suna shiga falon ta zube ledojin hannunta.

"Happiness kaga rigima ko? Don Allah ban ce su zauna in siyo abincin ba? Yanzu gashi nan ta dawo tana wani Sata rai."

Kamal ya tashi cikin nutsuwa don har yanzu baya yarda ya saki jiki kamar da.

"Angel me ya sami ?anwata ne?"

Mubina ta kalle shi ta mayar da dubanta ga Hamdi wadda abin mamaki ta fashe musu da kuka.

"Kun gama da Wakunan?" Mubina ta tambayi Kamal.

"Eh amma me ya same ta?"

Shi da Taj duk sun shiga damuwa. Taj ya koma kusa da ita yana son Wago mata kai ta?i yarda. Mubina ta nuna hanyar Wakunan da ido, Kamal ya fahimta sai ya tashi ya bi bayanta. Suna shigewa ciki Hamdi ta faWa kan Taj ta sake dasa kukanta daga farko.

"Don Allah ki yi min bayani mana. Me na yi miki?"

Cikin kuka ta labarta masa "naje sayan ice cream wai sai da aka zo kaina mutumin ya ce babu chocolate."

Mamaki ya kama Taj "shi ne kike kuka? Yaushe ma ki ka fara son chocolate flavour Win?"

"Yau shi nake so."

Tashi ya yi "bari na fita na nemo miki I am sure ba za a rasa.

"Ba zai zama irin nasu ba. Ni shi nake so."

Taj yaga abin na gaske ne sai ya koma lallaSata.

"Ko in yi miki? Mine will taste even better."

"Na su nake so" ta tura baki.

"Ahhh to gaskiya Mubina ta zo ta duba min ke. Alamu sun nuna rigimar nan ba nan kusa za ki daina ta ba." Ya rungumeta yana dariya.

Ture shi tayi "ni lafiyata ?alau kawai ka samo min chocolate ice cream."

"In ki ka ce nima na zama cream Win ai zama zan yi maman babyn Taj." Ya dinga kashe mata ido.

Kunya taji ta rufe ido tana dariya.

"Auuuu. Kin ma sani kenan. Tun yaushe?"

LeSenta ta taune tana murmushi "a hanya Mubina ta sa mu ka tsaya a clinic."

Rungume juna su ka yi Hamdi tana tunanu. Yanzu haihuwa za ta yi ta zama maman wani? Kuma idan an Waga baby a ce na Taj Winta ne. Lallai Allah ne mai juya al'amura yadda ya so.

Katse mata tunani ya yi "zo mu ci abinci." Ta zauna ya ce "mun kusa komawa gida na sami ?ancin dafa miki abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login