Showing 33001 words to 36000 words out of 182745 words

Chapter 12 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

86

ganin Kamal ya yi sosai. Su ka gaisa sannan Kamal ya Wan rissina kai.

"Na san za ka yi mamakin dawowata bayan yadda nayi a wancan zuwan namu."

"Babu komai. Allah dai Yasa lafiya."

"Alhamdulillah"

Shiru ya kuma biyo baya har sai da Abba ya sake tambayarsa sannan ya yi magana. Da farko ya fara da bashi labarin burin Taj tun ?uruciya da duk wani abu da ya biyo baya.

"Wallahi ban hana shi don ?yama a gareka ba. Amma indai Alhaji ya sami labarin kuna tare bana jin zai zai yafewa Taj."

Kallonsa Abba ya yi sosai yana jinjina kai "to amma a ina mahaifin naku ya sanni."

"Soron Winki. Shi ma mutumin cikin gari ne."

A karo na uku Abba ya sake ?urawa Kamal idanu na wasu ?an da?i?u sannan ya yi murmushi.

"Yaya Hayatu ne mahaifinku?"

Da sauri Kamal ya kalle shi "ya akayi ka gane?"

"Da gaske ku ?a?ansa ne?" Abba ya kuma tambaya yana mi?ewa tsaye.

"?a?ansa ne." Ya faWi yana gyaWa kai.

Jiki a matu?ar sanyaye Abba ya ce. "Ka faWawa Wan uwanka kada ya sake zuwa gidan nan. Kai ma ka tashi ka tafi."

Kamal bai jidaWin yadda Abba ya koma ba. Da alama ba mutum bane mai son hayaniya. Amma jin waye mahaifinsu ya canja yanayinsa. Hannu ya sanya ys fiddo dubu Warin da ya tanada tun a gida.

"Ga wannan ka ?ara jari don..."

"?auke kuWinka yaro. Bana so ko da wasa Yaya Hayatu ya yi tunanin da gangan na kusanci rayuwarku."

Ciki ya shige ya bar Kamal ri?e da kuWin yana fargabar yadda za su kwashe da Taj idan ya sami labarin zuwan nan nasa.
RAYUWA DA GI?I 12



Batul Mamman =ؖ?


Wannan shafin yana Wauke da tallan _LUCIOUSBITES_ gidan kashe ?walama. Mazauna garin Abuja ga taku ta fito da kanta ba sa?o.

Taron biki, suna, conference, seminar ko reunion ne? Ko kuwa sha'awar kashe kwaWayi ce ta tashi? To ku sha kuruminku. Hauwa aka luciousbites.ng ta fito domin fitar daku kunya a ko ina.
Domin ?arin bayani kuna iya tuntuSarta a kan wannan layi 08174821831.




***

Da gaske ciwon kai ke damun Taj saboda bai iya sanya abu a rai ba. Ya so ?warai ya ja Abban Hamdi a jiki. Ba don neman soyayyarta ba, wannan da kansa zai yi ba ya bu?atar taimakon kowa sai Allah. Mahaifinsa yake son nunawa a rayuwa kowa da ?addararsa. Kuma a kowacce sana'a indai ba addini ne ya haramta ta ba, akwai mutumin banza da nagari. Don al'ada ta ?yamaci wani abu ba shi yake nufin yinsa laifi bane. Sannan uwa uba akwai uzuri ga ?an Adam domin ba kowa ke dawwama cikin saSo ba.

A ganinsa rashin aikin Abban Hamdi wata hanya ce ya samu da zai iya sako shi cikin tasa sana'ar. Idan Allah Ya sanya musu albarka kasuwa ta buWe Alhaji zai iya fahimtar kowanne bawa akwai hanyar arzi?insa. Sannan ko iyaye ba sa so indai Allah bai haramta ba sannan Wan bai kasance mai saSawa kowa ba, albarka za ta iya binsa duk inda yake.

?arar wayarsa ce ta tashe shi daga kwanciyar da ya jima yana yi. Sunan Salwa da ya gani ya sanya shi yin tsaki. Ita bata san gudunta yake yi ba? Har yau yana mamaki da bata yi tunanin kamar yadda mata ke killace kayansu na ciki haka kowanne namiji da ya san mutumcin kansa yake yiwa nasa ba. A iya saninsa ?iwa da rashin son aikin namiji ba zai sa ya bawa ?anwarsa sha?i?iya wankin ?ananan kaya ba. Ballantana kuma wadda babu wani abu da ya haWasu.

Bari ya yi kiran ya katse sannan ya kirata.

"Don Allah ka buWe min ?ofa na manta mu?ullina a ciki."

Falo ya fito sanye da dogon wando na sanyi ruwan toka da farar shirt. Ya buWe mata jamlock Win ya juya zai koma Waki sai ta kira sunansa.

Tun ranar da ta gyara masa Waki da faWan da Ahmad ya yi mata ta rage kuzari da karsashi a komai. Fargabarta ita ce Sacin ran da ta gani tare da Taj da kuma shawarar da Ahmad Win ya bata akan ta cire shi daga ranta. Da za ta iya da tun kafin ta zubar da ajinta ta cire shi ta ?arfin tsiya tunda ta fahimci bata gabansa ta fuskar da take so.

Sake kiransa tayi da bai juyo sosai ba.

"Ya Taj don Allah ka yi ha?uri akan abin da ya faru rannan. Na fahimci kuskurena."

"Ya wuce, kada ki damu."

Fasa tafiya ya yi da ya tuna ?anwar Ahmad ai ?anwarsa ce shi ma. A matsayi guda duk su biyun su ke zaune a gidan. Shi yasa yaga dacewar ya bata shawara.

"Ko don gaba ki kiyaye irin wannan. Ba ni ba, ko Yaya ki ka wankewa undies bana jin za ki burge shi." Kai ta sunkuyar sai ya yi murmushi "ku mata ba kwa son a taSa koda jakarku. So just imagine ace ni nayi miki wannan karambanin. Will you realy be happy that I helped?"

Kunya maganar tashi ta bata. Ta rufe ido ta shige ciki da sauri tana mayar da numfashi. Da tunanin yadda ya yi maganar a tausashe ta ?arasa Waki. Sai da cire kaya za ta shiga wanka ta kuma tariyo zancen sai taji faWuwar gaba. Shin magana ya yaSa mata ko kuwa ya sauko ne?

Domin tabbatar da matsayin maganar da sai ta tura masa SMS da yamma da ya fito falo suna hira da Ahmad. Daga kitchen ta le?o bayan ta tura tana kallonsa ya duba sa?on, ya kuma rubuta reply. Da wani irin sauri ta koma ciki ta buWe. Nata ta fara bi inda ta rubuta masa sa?o kamar haka.

(Ya Taj nagode kuma ina mai sake baka ha?uri. If I am forgiven please give me a chance to be your friend.)

Shi kuma ya rubuta wannan amsar.

(Kada ki matsawa kan ki da son neman wani relationship dani bayan already akwai. ?anwar Yaya Ahmad ?anwar Taj ce.)

Ranar da ?yar ta gama girki. Sa?on dake cikin amsarsa ya fito Saro Saro. A matsayin ?anwa kaWai ya Wauketa. Daga yau za ta gwada cire shi daga zuciyarta. Sai dai abin da wuya domin son bai yi shawara da ita ba ya yi mata kamun kazar kuku.

***

FaWa Yaya take kamar ta ari baki a waya. Sajida da Zee su ka matsu ta gama ta basu labarin me ya faru. Sun dai fahimci Hamdi ce tayi wani laifin. Ita kuma Anti Labiba da su ke wayar banda dariya babu abin da take yi.

"Abin dariya ki ka Wauki abinnan Labiba? Wace ?ar arzi?in ce za ta guji girki kamar ba mace ba?"

"Yaya ki barni da ita don Allah. Na faWa miki ne fa kawai saboda kada ku ji shiru bata dawo ba. Zan Wan ri?eta ne in sauke mata gammon da ta Wauka." Cewar Labiban tana murmushi.

Yaya ta gyara zama tana hararar masu matsowa jikinta don son jin me ake cewa "amma fa samun wuri ne. Bata taSa gwada min wannan shegantakar a nan ba. Iyaka dai in tana gida girki ya faWo kanta tayi ta cika tana batsewa kenan. Ita a dole bata son sana'ar uban da yake wahaltawa rayuwarta."

Ha?uri Anti Labiba ta bata "ki barni da ita kawai Yaya. Girki kuma tunda ta iya ai magana ta ?are."

A haka su ka yi sallama bayan ta sake ro?on alfarmar kada Yaya ta yiwa Hamdi magana idan sun yi waya. ?arfe uku bayan yaranta biyu sun tafi islamiyya ya rage jaririyar da take goyo da yayarta mai shekara biyu da rabi. Ta fito abinta cikin shiri ta sami Hamdi a falo tana kallo.

"Hamdi zan fita amma ba jimawa zan yi sosai ba. Ga kaza can na fito da ita ki yi pepper chicken kafin na dawo. Sai ki haWa coleslaw. Na riga na dafa jallof Win shinkafa."

Jin abin da ta ce ba shiri ta kashe TV Win.
"Anti ni zan girka?"

"Kina nufin zancen da mu ka yi jiya da gaske ki ke?" Anti Labiba ta ?an?ance idanu.

"Anti wallahi ni..."

"In fasa fitar kenan komai mahimmancinta in ?arasa girki ko?"

"A'a Anti. Amma naga tattali ma yana da kyau. Tunda anci kifi da rana a bar kazar sai gobe."

?iris ya rage Anti Labiba ta fashe da dariya. Fuskar Hamdi na nuni da cewa da gaske take. Lallai idan ta biye mata ba za ta sami biyan bu?ata ba.

"Abbansu ne ya aikeni. Gashi kuma yana hanya tare da abokinsa. Na zata ke me fitar dani kunya ce..." ta sauke mayafinta "nagode da ki ka nuna min ban isa ba."

Jikin Hamdi rawa ya fara. Bata son ayi fushi da ita ko kaWan. Musamman mai kyautata mata. Da sauri ta bar falon ko kallon Antin ta ta bata kuma yi ba ta shige kitchen. Anti Labiba ta ?unshe dariyarta ta fice.

Bata zame ko ina ba sai bayan National Military Cemetary da an Wan wuce National Stadium a nan cikin umguwarsu Karon majigi. Wurin aminiyarta Hauwa taje don nan ne take da tabbacin za ta juyawa jin kunya baya. Daga bakin ?ofa su ka rungume juna saboda sun Wan kwana biyu basu haWu ba.

"Sannu da zumunci Labiba. Ina ta wa?ar sake zuwa ganin baby amma kwanakin nan orders suna neman fin ?arfina." Cewar Hauwa tana karSar goyon Anti Labiba.

"Mu ai haka muke so. ?an kasuwa baya kiran yawa. Ki dai ce kasuwa tayi albarka ki kuma godewa Allah."

"Alhamdulillah ala kulli hal."

Hira su ka Wan taSa sannan Labiba ta faWi abin da ya kawota.

"Ni kuwa kina Waukar Walibai ki koyar dasu?"

"Ban fara ba amma na gama duka shirye shiryen da ya dace. Nan da ?an kwanaki za ki ji sanarwa."

Anti Labiba ta saki jiki "Masha Allah. Nayi sara akan gaSa. Dama ?anwata nake son kawo miki. So nake ta goge sosai a harkar snacks Win nan ita ma."

Hauwa ta ce "akan ?anwarki ki ke tambayar class dama? Ai kin san ko bana yi dole na koya mata."

"Allah Ya ?aro kasuwa. Nagode sosai."

"Babu komai. Ai yiwa kai ne."

Hirarsu su ka cigaba da yi inda Labiba take ta koWa daWin kayan ciye ciyen da Hauwa ta ajiye mata. Da za ta tafi ta sayi frozen samosa.

*

Da yake babu wani abu da zai Wauke mata hankali, bata wani jima ba ta gama ta gyare kitchen Win. Tana jin an taSa ?ofa kuwa ta soma murmushin neman shiri. Ita kuma Anti Labiba sai da ta zo bakin ?ofa ta daina fara'a. Fuska a cinkishe ta shiga gida.

Hamdi ta shiga damuwa. A irin miskilancinta Waki za ta tafi amma ita shaida ce. Ganin Sacin ran Anti Labiba na nufin anyi mata abin da ya Sata mata rai sosai.

"Anti zo ki gani. Na gama."

"To an gode." Ta bata amsa ko kallonta bata yi ba.

Fuskarta canjawa tayi kamar tayi kuka ta ce "Allah na daina Anti. Ki yi ha?uri."

Ledar pack Win samosan ta bata ta ce ta soya. Wannan karon ko kaWan bata nuna komai na rashin jindaWi a fuskarta ba. Da ta gama Anti Labiba ta ce ta ci ta faWa mata ko da daWi.

Tunda ta gutsira ta kama murmushi.

"Yayi miki?"

"Da daWi sosai."

Sai lokacin Anti Labiba ta saki fuska ita ma tayi murmushi.

"So nake ki koma gida da sana'ar hannu. In sha Allah nan da kwana huWu za ki fara zuwa wurin Hauwa koyon waWannan abubuwan."

Farinciki sosai ta gani a tare da Hamdi. Ta dinga dariyar yadda ta canja lokaci guda.

A zahiri tana yiwa ?annen nata uzuri idan su ka nuna ?yamar wani abu na Abbansu. Maganar gaskiya duk kirkinsa akwai abin da fa dole ya tsayawa mutum a rai. ?a?a yawanci babu ruwansu da talauci ko arzi?in iyayensu. Indai akwai jin?ai da kulawa a tsakaninsu za ka ga suna ?aunar abinsu da zuciya Waya. Amma duk lokacin da kaga ?a?a na kunyar nuna iyayen a wasu wuraren, za ka samu nakasu ta wanni fannin. Inma dai daga Sangaren ?a?an in aka samu marasa godiyar Allah, ko kuma daga iyayen idan sun shuka wani abin da zai kunyata yaransu.

Ga dai shekaru sun ja. Amma har yanzu kallo Waya ya ishi mai idanu gane waye Abba Habibu. Irin haka ne abin da ake gudu. Kayi abu ka barshi amma tasirinsa ya gagara barin rayuwarka komai tsahon lokaci.

***

Kwana biyu Kamal ya Wauke ?afa daga gidan Ahmad. Taj ya ?ule iya ?ulewa. Kuma ya naWe ?afa ba ya zuwa site Win aikinsu. Kamal Win kaWai ke zuwa ya wuni yana monitoring komai. A rana ta uku ne ya gaji da gudun rigimar da za su yi da Taj akan zuwansa gidan Abba yaje gidan Ahmad Win. Bari ya yi sai gabanin azahar lokacin da ya tabbatar yayan nasu yana wajen aiki sannan yaje.

Babu kowa a gidan sai Taj da Zahra dake kitchen. Fitowa tayi su ka gaisa sannan yaje ?ofar Wakin Taj. A rufe take, ya yi sallama sannan aka buWe.

Taj bai jira shi ba ya koma ya zauna akan gado ya cigaba da aikin da yake a laptop Winsa.

"Wai nan gaba kake dani?" Kamal ya faWi da sanyin jiki.

"Kai zan tambaya da ka daina zuwa gidan nan." Taj ya mayar masa rai a Sace.

Tausayinsa Kamal yake ji. Bayan abubuwan da yake rayuwa yana ha?uri da rashinsu, baya jin zai juri wani abu ko yaya yake ya haWa su rigima ba. Zai fara bashi ha?uri sai aka kira Taj Win.

Abinka da sabonsu na rashin Soyewa juna komai. Gaisawa kawai su ka yi da Amma ta sako zancen Anisa. Ya kunna speaker ya yafito Kamal da hannu.

"Taj kana ji na kuwa?"

"Ina ji yanzu Amma. Me kike cewa?"

"Maganar Anisa. Kai baka ce min komai ba. Na share don ina zaton sai ka dawo za mu yi magana. To jiya Hajjo ta kira ta ce za ka wula?anta mata jika. Idan ba ka so ka faWa ta samo mata wani."

Hannu Kamal ya dinga juyawa yana son sanin me take nufi.

"Amma da kin bari na dawo dai."

"Ai ka san halinta. Yanzu sai ta juya zancen. Ba ka son Anisan ne?"

?ar dariya ya yi daga ji bata kai zuci ba. Baya son karSar abin da zai zame masa matsala don ko babu Hamdiyya shi bai taSa kallonta a matsayin da ya wuce ?anwa ba. Idan kuma ya ce baya so nan ma duk wanda ya san tarihinsa sai ya zage shi.

"Wa zai ?i mace kamarta?"

"Wannan wace irin amsa ce?"

Sarai ya ji Sacin rai a cikin muryarta. Ya kalli Kamal yana neman agaji. Shi kuma sai ya raWa masa a kunne cewa ya faWa mata zai je Abujan su fara fahimtar juna. Haka kuwa ya faWa mata. Nan da nan sautin muryarta ya koma daidai. Ta dinga shi masa albarka. Bata ga laifin Hajjo ba da take so wa jininta Taj. Da tana da sauran ?a ma kafin Hajjon tayi masa tayim Anisa za ta haWa su. Abu guda ne dai ta ajiye a ranta. Idan yaje yace baya so to fa dole a ha?ura. Don sun ri?e shi bata so ayi amfani da hakan a matsayin dalilin yi masa tilas. Zai zamana ba don Allah su ka taimaka masa ba.

Dariyar mugunta Kamal ya dinga yi bayan Taj ya gama faWa masa yadda su ka yi da Hajjo.

"Salwa kuma fa? Ko har yanzu ba fahimci ta mato maka ba?"

"Hmmm, ai baka san me tayi min ba..." ya sake kwashe labari ya sanar dashi.

Kamal dariya harda faWowa daga kan gado. FaWan da su ka manta dashi kenan aka koma hirar masoyan Taj.

"Yanzu dai da gaske Abujan zamu je."

"I'm not interested Happiness. Ina tsoron kada naje su zata na amince."

"Sai mu yi mata bayani mu nemi haWin kanta" ya Wan kalli Taj Win "akwai wadda ka ke so ne?"

Kamar ya faWa sai ya tuna reaction Win Kamal akan Abban Hamdi kawai ya fasa. Shiryawa su ka yi su ka tafi site tare. A hanya

"Na fa yi maka laifi Happy. Naje na sake lalata chance Win Mal. Habibu ya karSi aiki da kai."

Ana kukan targaWe, ga karaya ta zo. Taj ya gama sauraron Kamal ya ma rasa abin da zai ce.

"Kayi shiru" Kamal ya furta yana satar kallonsa.

"Ka san bana ganganci da rayuwata. Ba don haka ba duka zan maka."

"Sai da naje nake ganin kamar ban kyauta ba. Amma ni yadda ya Wauki zafi da jin sunan Alhaji yafi damuna. Kana ganin ko shi ma yadda yayi maka haka yayi masa? Naji Yaya Hayatu ma yake kiransa."

Da daddare Taj ya kira Hajiya ya tambayeta game da Abba Habibu. Don kada ta zargi komai sai ya ce,

"Hajiya don Allah mece ce ala?ar Alhaji da Habibu Winnan?"

"Me yasa kake son sani?"

"Don na kiyaye. Kada na taSa bari girki yasa nayi koyi da irin tasa rayuwar"

Hajiya na jin haka kuwa tayi masa bayanin da yake nema. Alhaji ya so Habibu tamkar ?aninsa na jini. A rayuwarsa kamar yadda ?a?ansa su ke gani yana son kyautatawa duk mai mayar da hankali a harkar ilimi. To Habibu sai dai ace masa gifted. Kana faWa yake kwashewa. Sai ka rasa wace irin ?addara ce ta karkata masa rayuwa ta mayar dashi Wan daudu. Gashi a lokacin daudancin mafi akasari ba a raba shi da kawalci da sauran alfasha mai zubar da mutumci.

"Da ya dawo daga Saudiyya yayi ta bibiyar Alhaji yana neman ya taimaka masa da jari ko ya Wauke shi yaron shago. Amma waccan ?yama da yake masa tun farkon fara daudun tasa yayi masa kora ta wula?anci."

Jikin Taj ya yi sanyi sosai. Idanunsa su ka kaWa su ka yi ja.

"Bai taimake shi ba?"

"Inaaa. Ka san shi da kafiya. Tunda ya juya masa baya bai ?ara waiwayarsa ba. Ni dai ?arshen labarinsa da naji ance ya buWe shago yana abincin sayarwa."

Shiru taji ya yi da tana magana. Ta rage murya,

"Taj ba za ka sauke naka ?udurin kayi yadda yake so ba?"

"Hajiya ba haram bane. Ki cigaba da sani a addu'a. In sha Allah ba zan taSa yin abin da za ku yi ba?incikin zaSina ba."

***

A cikin wata guda mamallakiyar Luciousbites.ng wato Hauwa ?awar Anti Labiba ta san tana tare da hazi?ar Waliba. Duk snack Win da su ka wuni koya to in sha Allah washegari idan Hamdi tayi kuskure ba zai yi yawa ba.

Ita babu ?iwa ko ha'inci, Waliba kuma mai ?o?ari. Aikin nasu yana tafiya yadda ake so. Wasu dama ta Wan iya sai dai yanzu ta koyi hanyar da ta dace da zamani wurin inganta saninta. Sannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login