Showing 30001 words to 33000 words out of 182745 words

Chapter 11 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

87

babanta ya tashi ne ma ta Wan sake da mutane."

Interest ya nuna na son jin me ya faru da baban nata. Firdaus kuwa ta zage ta kora masa jawabi tiryan tiryan. Har hukuncin da makaranta ta Wauka akan ?awayen Ummi tunda ita an cireta.

Tana gama jawabin ta tashi tayi gaba abinta. Ta bar shi da shiga ruWani da mamaki. Ba kuma komai bane ya sanya haka illa tuna sunan mahaifin Hamdi da kuma sana'arsa da Firdaus ta faWa.

Tunani barkatai ya shiga yi game da yadda aka haihu a ragaya. Indai shi ne Habibun da Alhaji yake ?yamar ya yi koyi da halayyarsa to yaya aka yi ya yi aure? Me ya faru da rayuwarsa? Kuma wace irin rayuwa yake yi yanzu?

Tabbas zai so sani. Shi Tajuddin zai so ?warai ya shiga cikin rayuwarsa ba don ?arsa kaWai da ta tarwatsa masa zuciya ba. Wasu burika ne suka mamaye zuciyarsa wanda zai so ya cimma in har shi ne wanda Alhaji ya sani Win.

Kwana biyar kacal su ka Wauka shi da Kamal wurin neman Habibu Simagade na Soron Winki. Sai gashi an kai su har ?ofar gidansa. Mutumin da ya rako su magidanci ne amma har su ka isa hirarsa akansa bata wuce alkhairinsa da kyakkyawar tarbiyar ahalinsa ba.

"Ai wato banda ance kowa da ?addararsa da in kaga wani aka ce maka zai sami sauyin rayuwa sai ka ?aryata."

"Me yasa ka ce haka?" Kamal da Taj bai Soyewa komai ba illa son Hamdi ya tambayi mutumin.

Shi kuwa ya daina tafiya tare da binsu da kallon rashin yarda. Sannan ya nuna Taj.

"Ka ce min kai sana'ar girki kake yi. ?an uwanka kuma kasuwanci."

"Haka ne."

Da faWa-faWa ya cigaba da magana "zamanin yanzu ai babu yarda a tsakanin mutane. Da naji aikin naka na zata taimakon Habibu ka zo yi. Shi yasa ma zan kai ku gidan."

Taj ya yi murmushi "sana'ar girki yake kenan?"

"Watannin baya ba. Kafin ?an hassada su sako shi a gaba su ka ?wace wurin da yake haya. Banda haka ko garau garau Habibu ya dafa maka wallahi sai ka ji bambanci."

Duk surutun mutumin nan bai ?ara yarda ya ara daga inda yake tsaye ba yana ji??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ran su faWa masa gaskiya ko su waye su sai ga Abba ya fito. Daga yanayin tafiyarsa da kamanni da ya gani da Hamdi Taj ya gane shi. Kafin ya iso wurin da su ke ya tsaya ya fi sau huWu yana gaisawa da mutane. Wannan abu ya sake burge Taj sosai har bai san lokacin da ha?oransa su ka bayyana da farincikin da ya shiga ba.
RAYUWA DA GI?I 11




Batul Mamman=ؖ?





Yadda ya gaisa da kowa da zai wuce haka ya tsaya su ka yi musabaha da wanda ya rako su. Sannan ya Wagawa Taj da Kamal hannu yana Wan ran?wafawa kamar yadda ya gaisa da sauran mutanen da su ka gani.

"?an samari barkanku dai. Ya sanyi sanyi? Ya ayyuka? To Allah Ya yi jagora." Ya dubi mutumin da da ya yi mu su rakiyar ya ce "na barku lafiya."

"Dakata Mal. Habibu. WaWannan fa kai su ke nema."

Tsayuwa ya yi ya sake kallonsu sai dai bai tuna taSa haWuwa dasu ba.

"To Allah dai Yasa lafiya" ya ce muryarsa na raguwa saboda rashin sanin ko ba da alkhairi su ka zo ba.

Kamal ne ya amsa masa "lafiya ?alau." Sannan ya gabatar da kansa da Taj.

Jin cewa Taj chef ne kuma a yanzu haka ginin restaurant yake sai Abba ya sami kansa da daina saurin zuwa uzurin da ya fito dashi. Zancen bai wuce fita nema ba dama.

"Dama nayi tunanin maganar ba za ta wuce ta Waukarka aiki ba. Shi yasa na rako su. Bari na wuce."

Abba ya yi masa godiya sosai sannan ya nunawa su Taj gidansa. "Ko mu ?arasa daga soro mu zauna?"

A duk lokacin da ya yi magana sai Kamal yaji zuciyarsa ta karye. Allah Ya sani a yau ya daina ganin ba?in Alhajinsu. Tabbas da wannan rayuwar Taj ya faWawa da shi ma sai ya yi kuka ba iyayensu ba. Ta yaya zuciya za ta jidaWin ganin namijin da ya cika a halitta yana irin wannan muryar? Don ma bai san lan?wasar jikin da sau?i yanzu ba.

Gidan su ka bi shi. Daga soron ya Waga murya yana ta kiran sunan Zee amma sai da ya yi kamar sau biyar su ka ga ?ar budurwa ta fito a guje. Don shi Kamal ji ya yi kamar ya taya shi kiran saboda muryar ba ta tashi yadda ya dace.

"Abba yi ha?uri ban ji ba ne."

Mutanen da ta gani tare dashi ne yasa ta saurin komawa da baya don bata fito da lulluSi ba. Ta bayan ?ofa ta gaishe su. Su duka biyun yadda tayi Win ya burge su sosai.

"Tabarma za ki kawo da ruwa."

Bata jima ba ta dawo da hijabi a jikinta ta shimfiWa tabarmar. Abba ya sake gaisawa dasu sannan ya bu?aci jin neman da su ke yi masa.

"Kamar yadda Wan uwana ya faWa maka gidan abinci nake ginawa. To sai na sami labarinka a wajen mutane. Duk da ba haka ake so ba ance ka rasa wurin sana'arka."

"Eh. Amma yanzu ma haka wani waje zan je dubawa. Idan mun daidaita sai na kama haya."

Babu wani dogon tunani ko shawara Taj ya ce "hayar kafi so ko za ka iya aiki tare dani?"

"Kai da baka gama gini ba Happy? Zai yi ta jira ne har lokacin?" Kamal ya yi saurin katse shi.

"Me ya kawo ku wurina tsakani da Allah?" Abba ya tambaya da sakin fuska.

"Aiki nake so mu yi tare amma wurin nawa da saura kamar yadda ya faWa maka. Ina so nayi recruiting ma'aikata da wuri kafin na gama ginin."

Kamal da ya yi zaton ganinsa kawai su ka zo yi sai yaji hankalinsa bai kwanta ba. Me yasa Taj yake neman abin da zai ?ara nesanta shi da Alhaji? Ina shi ina aiki da wannan mutumin daga jin ance baya aiki?

Abba ya ?are musu kallo sai ya yi murmushi. Da alama shawararsu bata zo Waya ba don yaga irin kallon da Kamal yake yiwa Taj.

"Samari nagode amma ina mai baku ha?uri. Ina da mata da ?a?a huWu. Zama haka a yanzu ma yana damuna balle kuma na wasu watanni. Sannan ina da ma'aikata biyar da har yanzu dani su ka dogara."

KuWi Taj ya ciro daga aljihunsa da sauri.
"Zan fara baka albashi tun yanzu kafin mu fara aikin."

"Happy!"

Taj ya yi biris da Kamal. Shi kuwa bai barshi ba ya dubi Abba da kyau.

"Kayi ha?uri don Allah. Bari mu tafi."

Taj ya Sata fuska "Da gaske nake ina son aiki da shi Happiness."

Abba sai ya nuna kamar bai ji haushi ba. Yana ?ar dariya ya yi musu godiya kawai ya tashi. Kamal kuma ha?uri ya yi ta bashi sannan ya janye Taj su ka tafi. A mota kuwa kafin su isa gidan Ahmad anyi faWa kaca-kaca.

"So kake Alhaji ya mutu da ba?incikin ka ko me? Kai yanzu rayuwarka tana yi maka daWi?"

"Kai baka ji komai ba da aka ce bashi da aiki yanzu?"

"Sai ka taimaka masa da kuWi." Kamal ya ce har zuciyarsa.

"Are you serious? Yanzu da aiki da kuWi wanne ya fi?"

Da wannan cacar bakin su ka koma gidan. Don takaici Kamal ko shiga bai yi ba. A waje ya sauke shi ya tafi.

"Masifaffe." Taj ya furta yana harar motar.

*

Ikon Allah Zahra ta gani yau tun dawowar Salwa gida. Kwananta shida a Bauchi da aka yi musu gajeren hutum mid-semester. Abin da aka bayar da kwana goma har weekend ya kama shabiyu, a daddafe tayi shida ta dawo. ?arya ma ta yiwa mamansu wai field work za su je. Da yake Agricultural Extention take karantawa. Nan kuwa kewar Taj ce ta isheta har tana neman zautar da tunaninta. Abin ba?inciki kuma shi ne tunda ta tafi ko sau Waya bai kirata ba. Ita ce ma da ta gaji tayi masa waya harda Wan ?orafi.

"Idan mutum yaje gida baya son damu Salwa. Tunda ba daWewa za ki yi ba gara duka time Win ki ya zama na family."

Ji tayi kamar ya faWa mata magana. Ta daure ta ce "Ba ka cikin family Wina kenan?"

"In ji wa? Idan kin dawo zan baki wayata ki gani a yanzu zan chanja yadda nayi saving sunanki."

Zuciyarta ta harba da wani irin farinciki ta ce "me za ka saka?"

"?anwata Salwa. Yadda nake saving sunan ?an gidanmu. Manyan kuma ina saka musu Yayata" Kuma bai barta ta gama jin haushin hakan ba kamar shi ys kira ya ce "bari na barki ki huta haka. Sai da safe."

Azahar a Kano tayi mata. Tana zuwa gidan ko hutawa bata yi ba ta karSi girkin dare. Zahra tana ta faWa mata ta jira ayi la'asar amma ta ce gara tayi da wuri tunda tuwo ne. Daga nan ta haWa juice Win abarba, mangwaro da Wanyar citta saboda ta kula Taj yafi son fresh fruit juice. Da su ta taho tun daga Bauchi.

Bayan tayi sallar la'asar ta shiga Wakin Taj. Yana ?ullewa idan zai fita amma baya taSa zare key Win. A cewarsa tunda masu gidan suna da kaya a ciki me yiwuwa za su bu?aci shiga idan baya nan.

"Salwa me ki ke nema a nan?" Zahra ta taho da sauri da taji alamun buWe ?ofar.

Tsintsiya ta sameta tana gyarawa Wauri. Tana ganinta tayi murmushi.
"Anti Zahra gyara Wakin zan yi."

Curiosity yasa Zahra ta Wan le?a. Baya bu?atar wani gyara na a zo a gani.

"Yana gyarawa. Ki fito don yayanki sai da ya yi min warning akan bari ke ko mai aiki ku shiga Wakinsa."

"Yau Waya dai Anti. Ai gara ayi masa gyara sosai. Tunda baya gida zan yi sauri."

Tafiyarta tayi ta soma da wankin toilet. A sink inda ya tara boxers da singlets da socks ta haWa komai ta wanke. Sai ta bar masa a bucket yadda zai shanya idan ya dawo. Wankin ma ana yi ana rurrufe ido saboda kunyar da ta dinga ji. ?aki ya fito fes dashi don har bedsheet sai da ta canja masa. Bayan ta gama komai ta rura gawayi akan gas cooker ta wuce da robar turaren wutan da ta siya online. Tun Zahra na bin ta da ido har tsananin mamaki yasa ta koma cewa 'uhmmm'. Yau ko Wakin miji ne aka yiwa haka ai dole ya yabawa matar balle wanda a iya saninta babu soyayya a tsakaninsu.

Ahmad ne ya fara dawowa gidan. Lokacin tuni Salwa ta gama har tayi wanka. Doguwar rigar atampa ta saka da ?aramin mayafi ta zauna a falo tana ta ?amshi. Wannan karambani duk aminiyarta ce ta kitsa mata. A cewarta da kyautatawa ake sayen soyayyar namiji. JindaWin yadda take kula da shi zai kwaWaita masa mallakarta a matsayin matar aure.

Wuraren ?arfe biyar da rabi Taj Win ya shigo da sauran fushin faWansu da Kamal. Sama sama ya gaisa da Ahmad. Ya Wauki baby Aisha bayan gaisawa da Zahra. Salwa kuwa sai da tayi masa magana ya kula da ita.

Ya dakata da tafiya "Har hutun ya ?are? Ko dai kin dawo birnin da yafi ?auyenku?" Ya ce da ita da zolaya.

Murmushi kawai tayi. Ahmad ya girgiza kai. Dama tunda ta dawo da wurwuri ya san ba zai wuce saboda taji cewa Taj ya kusa komawa bane.

Da Aisha ya shige Waki a kafaWarsa ya kwantar da ita a kan gado. Ya yi mamakin yadda ya sami Wakin. Waye ya gyara? Komai an killace shi gwanin sha'awa. Ya shiga toilet nan ma ?amshi kawai yake tashi. Da sauri ya duba sink da ya tuna ya bar kaya da zai wanke sai yaga babu. Nan fa yaji wani abu ya taSa masa rai. Yana duba bokiti kuwa sai gasu a wanke an matse. Ya fiddo gajeren wandonsa Waya ya tabbatar dai a wanke yake. Bai san lokacin da ya sake shi a bokitin ba. Ya Wauki Aisha ya koma falo fuska babu annuri.

"Anti Zahra waye ya gyara min Waki ne?"

Ahmad ya yi saurin kallon Zahra ita kuma ta nuna Salwa dake faman doka murmushi tana sunkuyar da kai. Sau?in hali irin na Taj bai hana shi nuna Sacin rai ba kuwa.

"Ke ki ka wanke min underwear?"

Idanun Zahra waje su ka yo. Ahmad kuwa bai san lokacin da ya ce "underwear kuma?"

Da me tambayar da kuma yanayin maganar Ahmad sai Salwa taji tsoro.

Taj ya murtuke fuska.
"You shouldn't have. Next time please kada ki taSa min." Ya du?a ya mi?awa Zahra Wiyarta sannan ya dubi Ahmad "Yaya zan Wan kwanta kafin magrib. Da headache na dawo."

Shigewa ya yi ya barsu. Da Zahra taga irin kallon da Ahmad yake yiwa Salwa sai ta tashi tsam ta shige Waki.

Ai kuwa kamar jira yake ya soma faWa.
"Wannan wane irin rashin daraja kai ne haka Salwa? Are you crazy or what?"

Kai ta sunkuyar tana kuka. Ba kuma na faWan yayanta ba. Fushin Taj da tsoron kada gwanintar ta tayi sanadin nesanta ta dashi kawai take gudu.

"Ba tun yau na kula kina son Taj ba..." sai a lokacin ta kalle shi hankalinta na tashi. Ya taSe baki "wanda bai damu da lamarinki bane kawai ba zai gane ba."

"Yaya..."

Tausayi ta bashi don ta soma kukan gaske. Amma hakan ba zai hana shi faWa mata gaskiya ba.

"Kin san komai dake faruwa a gidanmu da dalilin zamansa a gidan nan. He is trying his best ya daidaita da Alhaji. Kina tunanin soyayyar Taj dake, ?ar matar da ya saka zai faranta masa rai?"

A tsorace ta kalle shi "Yaya ni meye laifina?"

"Salwa kin fini sanin rigimar Mama tunda a gabanta ki ka tashi. Ke shaida ce irin yadda ta fitini Abbanku. Abubuwan da take yi bana jin akwai wanda Alhaji bai sani ba. Tun da in naso zuwa wajenta hutu baya son bari saboda yana gudun kada na koyo abin da zai haWa rigima a gidanmu."

Hawaye ta goge da mayafinta. Da muryar da kuka ya gama dusashewa ta ce "To ni yaya zan yi? Ba ni na Worawa kaina ba"

"Kada ki yi komai sama da neman zaSin Allah. Sai kuma tsare mutumci da darajarki ta mace. Ke kin sani da ina nan ko Wakinsa ba za ki shiga ba. Ba kuma don ban yarda dashi ba. Amma wankin underwear...haba Salwa? It was totally wrong."

Daga ?arshe rarrashinta ya yi da jaddada mata lallai kada ta ?wallafa rai akan Taj domin indai Alhaji bai amince ba da wuya ya aureta.

***

Hutu yana ta daWi. Hamdi ta zaga gari sosai da Anti Labiba da yaranta. Basu da ?an uwa sosai a garin sai abokan arzi?i. Shi yasa yawon nasu yafi ?arfi a wuraren sha?atawa da ciye ciye.

Wata rana sun dawo da yamma li?is Anti Labiba ta ce da Hamdi ta Wora abinci. Tayi tu?i ta gaji ga bebinta na ta tsala ihu. ?aki ta shiga domin yiwa yarinyar tsarki amma har ta fito Hamdi bata Wora komai ba. Gyaran kitchen Win take yi saboda ana gama cin abincin rana su ka fita.

"Hamdi baki ji na ce ki Wora jallof Win macaroni ba?"

Murmushin ys?e tayi "Anti Labiba don Allah ki Wora. Duk wani yanke yanke zan miki."

?an?ance ido Anti Labiba tayi. Sai kuma ta tuna wata hirarsu da Sajida lokacin da ta zo mata zaman bi?i. Tabbas ta faWa mata a duniya babu abin da Hamdi ta?i jini bayan namijin da ya iya girki kamar girkin kanshi. Ita duk abin da za ta Wora akan wuta mai suna abinci zuciyarta bata son yi. Ba kuma komai ya janyo ba illa tsohuwar ?iyayyar da take yiwa sana'ar Abbansu. Kuma fa da yake a wurinsa ta koya da wuya ka ci abincinta baka yi santi ba.

"Baki iya girkin bane ko me?"

"Idan na dafa ba lallai na iya ci. Don Allah ki Wora kinji Anti..."

Sosai abin ya bawa Anti Labiba mamaki. Hamdi bata taSa yi mata ?iwar aiki ba. Ga iya sammako ta gyara gida tun zuwanta. Amma fa duk cikin aikin nata bata taSa yin girki. Ita kuma Anti Labiba bata damu ba saboda mijinta baya son cin girkin mutane musamman a gida.

Abincinta tayi ta gama. Hamdi sai taji babu daWi don sai da aka matsa mata taci abincin. Bayan sun gama ta bita Waki ta bata ha?uri.

"Ni ban yi fushi ba. Kawai ina mamakin yadda aka yi ki ka zafafa akan harkar girkin nan."

"Idan ina yi sai Abba ya dinga faWo min a rai. Wallahi Anti Labiba bana son ganin shi a kitchen kwata-kwata. Yanzu ma ina ta fatan Allah Yasa ya sami wata sana'ar tunda an karSe gidan abincin." Magana take yi muryarta tana rawa.

Anti Labiba ta sa?ala hannunta a kafaWarta.
"Nayi zaton kin daina abubuwan da ki ke yi da naga yanzu kullum sai kun yi waya dashi."

"Ni me nake yi?" Ta tambaya da zumSura bakin.

"Babu komai." Ta shashantar da zancen "snacks da pastries fa? Su ma kamar girki ki ka Wauke su?"

"Don ban iya bane amma ina so."

"Saboda basa cikin girkin da Abba ya koya mu ku ko?"

Sunkuyar da kai Hamdi tayi a kunyace. Ita kuwa Anti Labiba sai wani tunani ya Warsu a zuciyarta. Ba dai za ta ce komai ba sai ta tuntuSi ?awarta Hauwa gobe. Idan Hamdi tayi sa'a za ta koyi small chops da youghurt from one of the best a garin Abuja.

***

Kwana biyu Taj ya yi baya zuwa site Win aiki. Idan Kamal ya zo sai ya ce kansa na ciwo. Abu ya taru ya dami Kamal sosai. Lokacin tafiyar Taj na gabatowa amma ya sanyawa ransa wani abu daban. Shi kuma yafi son ko zai tafi ya zamana aikin da ya rage ba mai yawa ba. Gara aci ?arfin komai a gaban mai wurin.

Yau da ya bar gidan Ahmad wucewa ya yi gidan Abba Habibu. Bai wahala wurin gane gidan ba. ShaWaya na safe ta Wan wuce. Ya tura wani yaro ayi masa sallama da shi. Wata budurwa ba wadda ya gani a zuwansu na farko ba ce ta fito ta gaishe shi.

"Abba ya fita amma yanzun nan zai dawo. Ba nisa ya yi ba."

"Ke ma ?arsa ce?" Kamal ya kasa daurewa sai da ya tambaya. Ita da ta rannan da ya ri?e Zee aka kirata su na kama sosai. Kyawawan ?an mata ne masu nutsuwa.

"Eh."

"Yaya sunanki?"

"Sajida." Ta amsa masa.

Kujerar roba ta kawo ta ajiye masa a soron ta koma ciki. Kimanin minti goma a tsakani sai ga Abba ya dawo.

Mamakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login