Showing 168001 words to 171000 words out of 182745 words

Chapter 57 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

115

fa? Sai dai na zo na tarar da mummunan labari? So kayi ka tafi ka barni da tunanin irin halin da ka shiga yana haunting Wina?"

A raunane Kamal ya ce "ba haka bane."

"To yaya ne?" Bai san ya fara hawaye ba "I was happy Kamal. Ina dariya ina nishaWi saboda na auri wadda nake so kuma na samu Alhaji ya yafe min. How could I be happy. I shouldn't..."

Kamal ya marairaice masa "Da ka zauna mun yi kukan nan kawai mun share. Wannan mitar bata da amfani. Laifi ne na riga nayi kuma na karSa. Haba Happy na Happiness." Ya kama murmushin ganin ya soma samun kansa "nace kai ma ka na kallon finafinai kenan ko? Na ga sai wani blaming kanka kake yi irin abin nan na masu Wan uwa."

Cije leSe Taj yayi yana harararsa. Daga ?arshe ya yi kwafa gami da jinjina kai.
"Za mu haWu."

Daga nan hirar ta koma kan tambayar jikin Kamal da yadda yake ji a yanzu. Motsi kaWan zai yi Taj ya dinga tambayarsa me yake so. Shi kuwa tambayar da su Alhaji su ka yi ta kakkaucewa amsa masa ya samu ya yi.

"Happy wa ya bani ?oda?"

Alamun alhini Kamal ya fara gani a tattare da Taj shi yasa ko da ya wayance da cewa
"Ban fahimce ka ba? Masu alhakin faWa maka Win shiru su ka yi don su ji?a min aiki?" Ya tashi zai fita "bari na kirawo maka Alhaji."

"Ka ajiye maganar wasa don Allah. I need...I must know."

Allah Ya sani bai so haka ba amma kuma rashin amsawar ba komai zai janyo ba sai tashin hankali ga mara lafiya, wanda kuma ko kusa ba a son haka.

"Kamal, Yaya ce tayi donating. Yaya mahaifiyar Hamdi."

Da wani irin yanayi Kamal ya zabura sai da Taj ya danne masa kafaWa.

"Yaya fa ka ce. Let me go." Ya doke hannun Taj "ka sake ni mana. Taj ba fa wasa nake ba. Ka ?yaleni na tashi."

"Ina za ka idan ka tashi? Wai ma so kake aikin ya buWe ka mayar da hannun agogo baya?"

Kawai sai Kamal ya sanya tafukan hannunsa ya rufe fuska ya fashe da kuka. This time around fassara kukan nasa ma abin wahala ne.

"She is fine fa Happiness. Wallahi jikinta da sau?i sosai."

"Me ya faru? Na kasa fahimtar komai."

Taj took his time ya labarta masa abin da Mubina ta sanar da shi da Hamdi jiyan bayan komawarsu masauki. Guilt ke damunta har lokacin shi ne ta zaSi sanar dasu yadda aka yi Yaya ta fara tunanin binta daga hirarsu a jirgi. Hatta recording Win sa?on da ta bari ya fayyace masa.

"Na kasa murna Happy. I feel...Subhanallah" idanun Kamal cike fal da hawaye ya rirri?e Taj "ka kai ni wajenta don Allah ko na tafi da kaina."

***

?akin yayi shiru sai sautin kuka da yake fitowa daga wayar Ahmad ta speaker. Whatsapp call ya kira ta wayar Sajida. Ita da Zee da Halifa babu wanda ba ya kuka. Hamdi ma kukan take taya su. Yayinda Abba Habibu da Yaya murmushi su ke yi kawai wanda babu komai cikinsa illa dauriya. An Waga mata gadon ta yadda bayanta yana jingine da filo.

Muryar Halifa ce ta fito daga wayar yana shesshe?a "don Allah a mayar da kiran nan bidiyo mu ganta."

"Yanzun nan kuwa" Ahmad ya saita wayar akan Yaya bayan ya juya call Win.

Yaya tayi saurin gyara yanayin fuskarta gami da faWaWa murmushinta.

"Kun ganni fa. Wallahi naji sau?i sosai. Ku kwantar da hankalinku."

Hamdi ta ?ara musu da cewa
"Da a ce da matsala kun san ba zan Soye muku ba."

"Wai me ya kai ki gidan mutane da sassafe Sajida? Nan yanzu ba na jin bakwai ta yi." Abba Habibu ya yi maganar yana duban agogon wayarsa. Awa biyu ne tsakaninsu da Nigeria. Tara saura ?an mintuna yana nufin a can bakwai ne saura.

Sai lokacin Anti Zinatu da take ta aikin matsar ?walla tayi magana. Tun dare da Abba Habibu ya sanar da ita halin da ake ciki ta karSi lambar Safwan da dabara a wajen Zee. Ta sanar da shi komai sannan ta bu?aci ya kawo Sajidan wajenta a lokacin da za a sanar da su. To ashe shi Win ma mutum ne mai saurin ruWewa. Daga wayar nan bai sake yin wani abin kirki ba, ko bacci Sarawo da ?yar ya sace shi. Ai kuwa ana sallame asuba ya ce ta shirya su taho.

"Ni dai yanzu alfarmar da zan ro?e ku don Allah kada wanda ya tayarwa Innata hankali. Ku bar zancen nan har sai na dawo in sha Allahu. In lafiya ta samu yadda ake so ma ba sai ta sani ba."

Shawarar Yaya rabi ce ta sami karSuwa a wajen Alhaji. Batun a rufe maganar kuma ya ce ba zai yiwu ba.

"Sadaukar da ?oda babban abu ne wanda a halin da muke ciki yanzu da wuya maganar ta Suya. Idan wani bai faa ba, wani zai iya faWa. Saboda haka za mu jira ki sami sau?i sai mu auna mu gani shirun da faWar gaskiyar wanne ne yafi ko kuwa Habibu?"

Tattaunawa su ka cigaba da yi cikin lumana da girmamawa na Wan lokaci. Hamdi ta ji duk ta takura. Zantukan nasu sun shafe su amma bai kamata ta tsaya musu a wajen ba. Tunanin dabarar ficewa ta fara yi sai ga kiran Bishir ta wayar Hajiya. Ya faWa mata yana ?asa tare da Mubina. Wai tana son tafiya Madina ne yau shi ne ta zo tayi musu sallama.

"Amma don ragon azanci ta kasa faWa mana mu taho tare?"

Dariya taji ya soma yi yayi magana da zolaya "Hajiyarmu ta gargajiya kenan. Yanzu duk Sarin hawayen da ta gama yi a asibitin nan baki gane komai ba?"

"Me aka yi?" Kafin ya bata amsa ta soma murmushi "kai Bishir ka tabbata?"

"Kin gano kenan" ya kama dariya sosai. Mubina dake gefensa ta sunkuyar da kai tana ?o?arin Soye murmushin dake neman kufce mata. Ta ji abin da yake cewa ta kuma gane me hakan yake nufi.

Hajiya cewa tayi su hawo da sauri sannan ta zaga bayan Mama ta faWa mata yadda su ka yi da Bishir. Baki ya kasa rufuwa da Mama ta fesawa kowa zancen. Yaya ma daga kwance ta taya su murna. Sannan ko kusa bata yi mamaki ba. A ganinta dama soyayya ce kaWai za ta sanya Mubina biyo bayan patient har wata ?asar.

Alhaji da Abba Habibu ma sun nuna farinciki ?warai. Hamdi sai ta sake amfani da wannan damar za ta sulale ta gudu kafin su farga. Kamar haWin baki ta na buWewa Taj ya turo Kamal akan wheelchair.

Hirar iyayen a take ta yanke sai tambayar me yake faruwa.

"Wajen Yaya na zo." Kamal ya ba su amsa da kansa.

Murmushi Yaya ta yi masa da su ka haWa ido "ai bai kamata ka fito a wannan yanayin ba. Taj da ba ka kawo shi ba."

"Nayi ?o?arin hana shi Yaya amma wallahi ya ?i. Dole na kira wani Nurse shi ne ya Wora shi a nan" ya nuna wheelchair Win.

A daidai lokacin kuma Bishir da Mubina su ka shigo Wakin. Hankalin Kamal ya yi gaba bai kula da su ba da farko. Ya ce Taj ya matsar da shi daf da gadon Yaya. Ya tura shi kuwa jikin gadon sosai. Kamal ya mi?a hannunsa na dama dake Wauke da canula saboda ?arin ruwa da ake yi masa ya ri?e nata hannun sannan ya kalli Abba Habibu.

"Abba na riga na zama Wan Yaya shi ya sa ban nemi izinin taSa hannunta ba."

Abba Habibu ya gyaWa kai yana murmushin nan nasa. Ragowar kuwa duka aka yi shiru ana sauraron Kamal.

"Duk wahalar dake tattare da Waukar ciki da haihuwa a wurin mata a ?arshe tana da riba Yaya. Za a kalli mace a kira ta UWA ko da Wan ba a gabanta yake rayuwa ba. Su kan su mata abinda ya sa su ke jurar wannan wahalar komai tsananinta bai wuce domin samun wannan matsayin ba. Mace za ta zama mai cikakken iko akan wani bawan Allah da yake rayuwa da jinin jikinta." Ya ja numfashi "Allah Yana biyan wahalhalun da ta sha akan ?a?anta da mafi ?ololuwar daraja. Ya bata martabar da babu mai kamo ta a wajen wannan bawa har ?arshen rayuwarsu su biyun." Ya yi murmushi idanunsa fal hawaye. Ko da ya Waga kai ya kalli Yaya sai hawayen ya zubo. Nata ma ya zubo...idan ka cire Alhaji, Abba Habibu, Ahmad da Taj, duka waWanda su ke Wakin sai da su ka zubar da ?walla.

"Yaya wace daraja ki ke tunanin Allah Ya tanadarwa matar da ta bawa Wan da bata da ala?a da shi ta jini wani Sangare na jikinta don ya rayu? Bayan kin san cewa wahala, azabar ciwo da fargabar me zai je ya dawo a dalilin sadaukar da ?odarki ba zai mayar dani Wan ki ba. Taki juriyar na?asu ce a jikinki da lafiyarki. Babu wata riba ta kurkusa ko ta nesa don ban ga abin da za a biya ki da zai maye gurbin Sangaren jikin ki da ki ka bani ba Yaya."

"Kamal ka yi shiru don Allah. Jikin ka babu ?wari." Yaya ta faWi cikin kuka.

"Yadda Wa baya yin godiya ga iyayensa akan haihuwarsa da su ka yi, haka ni ma ba zan yi miki godiya akan kyautar da ki ka yi min ba. Alfarma kawai na zo sake ro?a domin Allah."

"Ina jin ka Kamal. Don Allah ka daina kukan nan."

"Yaya idan kina lissafin ?a?anki ki dinga farawa daga Kamaluddeen Hayatu don Allah." Kuka sosai yake yi a wannan gaSar.
"Idan kina da sirri irin na uwa da Wa don Allah ki yi dani." Yaya ta gyaWa kai.
"Damuwa ko wacce iri ce irin ta uwa da Wa kada ki tsallake ni." Nan ma ta sake nuna amincewarta.
"Bu?ata ko wacce iri ce ta uwa da Wa ki fara faWa min tunda kin ga Halifa ?arami ne. Su Hamdi kuma mata ne ma su rauni."

"To Kamal" Yaya ta amsa cikin kuka.

"Idan su Sajida sun yi miki laifi don Allah kada ki Soye min. Ki rufa musu asiri a wajen Abba amma ki sanar dani. Zan yi mu su faWa tamkar cikin mu Waya."

"Na sani Kamal, ko babu wannan abu ai kai me tsaya mu su ne."

Kamal ya girgiza kai "a da sai dai nayi kara, yanzu kuwa duk abin da ya shafe ki Yaya ya zama dolena."
Ku san sai a lokacin ya lura da tsayuwar Mubina a Wakin. Sai ya yafito ta da hannu. Ta so cogewa amma Mama da kanta ta kaita kusa da Kamal Win.

"Kin amince da zaSina Yaya? Idan na auri Mubina ?ar mu ta farko in sha Allahu sunan ku Waya. Sunan ta..." ya kalli Hamdi yana jiran ta ba shi amsa.

"Khadija."

"In sha Allahu sunanta Khadija."

Yaya ta rasa abin cewa. Tana gudun za?al?alewa a gaban iyayensa. Gashi kuma ya tsare ta da idanu yana kallonta with so much adoration.

Alhaji ne ya yi stepping in da ya ga ta kasa magana.

"Ba ki ce komai ba game da zaSin Wan naki Yaya?"

Yaya ta Waga kai a rikice ta kalli Abba Habibu tana neman agajin sa. Ita fa komai bambarakwai take jin sa tun shigowar Alhaji Wakin nata. Ba ta son yin abin da zai sake janyo wa mijinta abin magana.

Cikin nutsuwa Hajiya ta matso ta kama Wayan hannun Yaya a yayinda Wayan har lokacin ya na cikin na Kamal.

"Ko ba ki karSi tayin da Kamal ya yi miki bane na zama uwa a gare shi?" Ta haWa hannuwanta biyu tana magiya "Don Allah ka da ki kasa yi masa wannan alfarmar. Kamar yadda ya faWa babu zancen biya ta kowacce fuska tsakanin mu. Hakan raini ne ma akan girman abin da ki ka yi mana. ?ara shi cikin zuri'arki ne kaWai abin da za mu iya duk da cewa mu ne dai da sake samun riba."

"Don Allah ku daina magana irin haka. Domin Allah nayi." Ta zame hannunta dake cikin na Kamal ta nuna ?irjinta "Karamcin Ubangina a gare ni mai girma ne. Shi Ya nufe ni da zuwa a lokacin da Kamal yake tsananin bu?atar hakan ba tare da sani ko shirin wanin mu ba. Kuma Ya azurta ni da dakewar zuciya na cika umarnin ?addara. Ni da har yau nake tsoron allura sai gashi na kawo kaina inda za a yanka min ciki. Na fi ku riba wallahi. Allah Ya bani ikon ceton rai sannan Ya ?ara faWaWa ?a?ana." Ta sanya hannu ta shafa kumatun Kamal. Shi kuwa ya Wora hannunsa akan nata ya lumshe idanunsa cikin farinciki.

Maimakon kuka kuma sai farinciki ya mamaye Wakin. Mubina ta kasa daurewa ta bawa Yaya ha?uri domin tana ganin cewa ita ce ta jawo mata zuwa nan Win.

"Kada ki sake magana irin wannan Dokta. Mu duka mu na yin komai ne cikin tsarin Ubangijinmu. Ba ki yi min laifi ba amaryar Wana."

Kunya ta kama Mubina. Ta koma kusa da Hamdi ta sunkuyar da kanta.

Da jindaWi Alhaji ya ce "Tunda abin ya zo da haka ku ba ni dama na yi mu ku karambani akan Baban Khadija da Maman Khadija mana."

"Innalillahi..." Mubina ta faWi a kiWime da jin furucin Alhaji tana mai ?an?ame hannun Hamdi. Ita ma dai babu halin zolaya kunyar ce ta kama ta.

"Abban Kamal ka yi shiru."

"To Alhaji mun ba ka dama." Abba Habibu shi ma dai yana cikin jin nauyin wannan sabon lamari.

Shi kuwa Alhaji dama da gayya ya yi. Yana so ne ya canja takun mu'amala a tsakanin su tun wuri saboda a sake sabon lale tun kafin su koma gida. Waya ya Waga a gaban su ya kira kawun Dr. Mubina, yayan mahaifinta. Ita kanta ba ta san inda ya samo numbar ba tunda bai tambayeta ba. Maganar su ta ?arshe ita da shi sosai dai tun kwanciyar Kamal a asibiti ne inda su ka fara haWuwa har ya ce ya san Marigayi mahaifinta.

Ya fara da gabatar da kansa wanda da alamu hakan bai yi wa kawun nata wahalar ganewa ba. Daga nan ga mamakin dukkanin su ya Wauko maganar su da Kamal. Ya soma yi masa bayanin rashin lafiyar sa sai kawun ya ce ya gane shi. Bai dai san cewa Wan Alhajin ne patient Win da ta dinga ro?onsa har ya barta tahowa duba shi da yin Umra ba.

"Tunda dai har an dace ya sami ?odar, ina ganin kawai ta zauna ta ?arasa ladanta. Ina fata ka fahimce ni."

A take Alhaji ya danna speaker yana murmushi sosai. Komai ya zo masa da sau?i fiye da yadda ya yi tsammani. "?warai kuwa. Na saka ka a speaker a gaban iyalina, Kamal da ita Mubina. Zan so ka maimaita abin da ka ce domin nima dalilin kiran kenan. Ina son a san da zaman mu zuwa lokacin da Allah zai sa ya sami lafiya ya dawo gida."

Kawu ya maimaita "Ka fi ?arfin haka Alh. Hayatu. Me yiwu wa ba za ka iya tunawa ba amma ni abin yana raina sosai. Mun taSa zuwa wajen ka nema wa yaran wasu ?auyuka kuWin jarabawar SSCE har su Wari da sittin da bakwai. Bayan ka biya ka Wauki ukun farko ka biya musu kuWin jami'a in full sannan ka sa mu ka yi al?awarin ba za su taSa sanin kai ne ba. Shi ya sa wasu lokutan taimako yake zuwa ga bayin Allah ta inda ba sa zato. Sadaka babban jari ce."

Alhaji ya yi Wan murmushi kawai. ?an Adam ba ma'asomi ba. Kullum mu na cikin iyo tsakanin dai-dai da kura-kurai. Yawan tuba, ?o?arin fifita aikata ayyukan alkhairi da uwa uwa kyautatawa Allah SWT zato shi ne babbar maslahar rayuwa. Zai iya cewa a tsukin lokacin nan ya ?ara fahimtar rayuwa ta fuskoki mabambanta. Da fari ya yi karo da tsohon kuskurensa sannan yanzu ya gamu da tsohon alkhairi. FABI AYYI AALA'I RABBIKUMA TUKAZZIBAN

Kawu kuma ya Wora maganar sa.
"Mubina ki zauna ki ?arasa ladan ki har a sallame shi ."

Mamaki tayi sosai "Kawu aikina fa? Kuma ..." ta saci kallon su Ahmad "ba ya bu?atar zama na."

"Ai kuwa ki shirya domin kowa zai tafi ya bar ki da shi. HaWa ni da Alh. Hayatun."

Jikin Mubina ya yi sanyi ?alau har ta kasa motsin kirki. Zuciyarta kawai ke harbawa da daidai da fitar kalmomin godiya daga bakin Alhaji domin ya cire wayar daga handsfree. Bayan Wan lokaci ya mi?a mata wayar.

"Je ki waje ki amsa"

Da sauri ta fita har lokacin tana ri?e da hannun Hamdi. Ita kuma ganin haka sai ta nemi zare hannunta. Mubina ta dube ta da raunin murya.
"Raka ni don Allah."

*

Shiru Mubina tayi tana sauraron Kawunta.

"Alh. Hayatu ya ce zai sake kira na anjima kaWan mu ?ar?are magana. Idan komai ya tafi daidai in sha Allahu yau zan sauke amanar Wan uwana, zan aurar dake ga mutumin da na tabbatar ki na so sannan ga dangin da nake fatan ba za su taSa wula?anta ki ba."

"Amma Kawu..."

"Na san ban shiga ha??in ki ba da na yanke wannan shawarar. Soyayya ta Fisabilillahi ce kaWai ta saka ki kusan zaucewa akan yaron nan kafin ki tafi. Yanayin ki ya bani tsoro shi ya sa ban hana ki tafiya ba da ki ka bu?aci zuwa Umra ke kaWai saSanin yadda mu ka yi shirin tafiyar gida cikin ?an uwa."

Kuka ta fashe da shi.

"Ki bar kuka Mubina. Ina son amincewar ki ne domin yanzu zan tafi wajen Umman ki. Ki amince?"

Da ka ta fara amsawa sai ta tuna ba ya ganin ta shi ne ta ce "Uhm" a hankali.

"Allah Ya yi miki albarka."

Rungume Hamdi tayi bayan ta gama wayar. Hamdi ta dinga bubbuga mata baya saboda kuka ne take yi sosai. Bata taSa zato ko da wasa akwai ranar da burinta zai cika akan Kamal ba. Ta fi karkata da tunanin cewa zuwa yanzu ya ma bar duniyar.

"Ki daina kukan nan haka Matar Yaya. Ni ce ke sujjada zan yi domin wannan babbar falala ce daga Allah SWT." Hamdi ta rarrasheta.

"Nagode Hamdi. Abin ne duk wani iri. Kin ga ana shirin aurar dani babu kowa nawa."

"Gani." Ta sakar mata murmushi "Don Allah ko da wasa kada ki taSa yi min kallon matar ?anin miji. ?an gidansu sun yi min tarbar ?a kuma ?ar uwa ba suruka ba. Ina ganin rashin adalci ne zai sa mu kuma mu Wauki kan mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login