Showing 150001 words to 153000 words out of 182745 words

Chapter 51 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

91

da kwana shida zamu taho in sha Allah."

"Ba na ce Taj ya bari Hamdiyya ta sami visa ba?"

Yaya Hajiyayye tayi dariya "ai ta samu. Surprise mu ka so yi muku. Yanzun nan nayi tunanin kada fa garin surprise mu yi saSani."

Farincikinsa ya nuna. Ya ajiye wayar sai yaji sanyi yana ratsa shi. Yaya zsi yi da matansa? Dama yana kusa ne da sau?i.

Haka nan ya yi ta maza ya kira Hajiya. Tunda taji ya ce ta keSe za su yi magana gabanta ya faWi. Ya fara da wa'azi ds tunatarwa akan sharuWan imani.

"Na yarda da ?addara. Ka faWa min kawai me na rasa." Ta ce da rawar murya.

"Baki rasa ba amma duk wani hope yana neman ?are min."

Jikinta taji yayi nauyi ta sami waje ta zauna. Duk yadda Alhaji ya so rage mata raWaWin da za ta ji ta hanyar amfani da kalmomi masu kwantar da hankali abu ya faskara. Kamal yana dab da rasa rayuwarsa saboda rashin dacen mai bashi ?oda.

Yayi zaton za ta yi kuka sai yaji shiru. Can ta numfasa.

"Yaushe ne akwai jirgi kurkusa?"

"Zan bincika..."

"Ka duba ka biya mana. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Sai ta katse kiran.

Alhaji ya yi ta kiranta ta?i Wauka. Mama ya nema yace su haWu da su Inna yana da magana. Su ukun nan kuka suke yi babu mai rarrashin wani. Su ka shiga Wakin Hajiya su ka sameta tana haWa kaya.

"Ku ma ku gaggauta haWawa domin ko gobe aka sami jirgi zamu tafi tare ko?"

Cikin kuka Umma ta ce "dolenmu Hajiya." Inna da Mama kuwa ko bakin magana babu.

Basu bari yaran sun sani ba. A kwana uku aka gama yi musu komai. Yaran nasu suna ta mitar me yasa basu jira su tafi tare ba. Mama tayi ?arfin halin cewa mijinsu ke nemansu. Aka mayar da abin sha?iyanci ana dariya.

*
Tafiyarsu da kwana biyu shi ne lokacin tafiyar Yaya. A airport su ka haWu da abokan tafiyarta. Su Hamdi su ka yi mata rakiya da mazajensu. Abin da ya bawa Taj mamaki da kuma tayar masa da hankali bai wuce ganin Dr. Mubina tana fitowa daga wajen check in ba. Ta rame sosai kamar wadda ta jima tana ciwo. Duk wasu alamun rashin kwanciyar hankali sun bayyana gareta. Da ta gan shi da farko gabanta ya faWi kuma ya gani. Ta basar shi ma ya nuna bai gane komai ba. Hamdi ya kira su ka gaisa ya ce

"Ku fara ?awance don da alama ita ce Mrs Happiness."

Hamdi sai murna ta zolayeta

"Umra za ki ko Ya Kamal za ki bi?"

Dr. Mubina tayi murmushi kawai. Taj ya nuna mata Yaya ya ce ga ?arin abokan tafiya ta samu tunda yaga kamar ita kaWai ce.

"Na gode kuwa."

Da aka kira su Hamdi da Taj na kallo Dr. Mubina ta haWa akwatin ta da na Yaya tana ja. Sun ji daWin hakan kuwa. A ?ofar jirgi inda ake nuna boarding pass Yaya za ta Wauko nata ta haWa da ?ar takardar da su Hamdi su ka gani wadda aka saka cikin passport Winta. Ita ce mai Wauke da bayanin lalurarta da su blood group ko da wani abu na emergency zai sameta. Bata san ta yar ba tayi gaba. Mubina ce ta Wauko mata. Tana shirin bata ta kula da bayanin da yake jiki. Zuciyarta sai da ta girgiza. Ta mi?a mata da rawar hannu.
RAYUWA DA GI?I 36





Batul Mamman=ؖ?







***

A dalilin ba lokaci Waya aka saya musu ticket ba, wurin zaman Yaya da na abokan tafiyarta daban daban ne. ?an saurayin cikinsu Yaya tayi niyar bawa boarding pass Winta domin ya duba mata wurin zamanta, haka Abba Habibu ya sanar da ita tayi. Ya ceba inda mutum yake so zai je ya zauna ba. Ta Waga hannu za ta bashi Mubina ta riga karSa. Ta kaita har wurin kujerar ta taimaka mata da Wora hand luggage a sama sannan ta Waura mata belt. Ko ba a faWa ba ta riga ta gane Yaya bata raSa shiga jirgi ba.

Yaya tayi ta godiya da sanya mata albarka. Ita kuwa Allah Ya sani da biyu take yi. Kafin jirgi ya tashi bayan kowa ya zauna ta zo ta ro?i wadda take kusa da Yaya da cewa mamanta ce su ka yi musanyen seat. Wannan abu yasa Yaya jindaWi matu?a. Ta saki jiki da Mubina suna ta hira. Da jirgin zai tashi duk wani tsoronta Mubina ce ta dinga kwantar mata da hankali. Har aman da ta dinga ji Mubina leda ta bata sannan ta dinga shafa mata baya tana cewa ta hura iskar bakinta a ledar. A haka har su ka daidaita a iska.

"Allah Ya yi miki albarka Ya raya miki zuri'a. Ya ji?an mahaifa."

"Amin Mama."

"Yaya yaran su ke kirana. Kema in babu damuwa ki dinga kirana da hakan."

Da murmushi Mubina ta ce "to Yaya."

Lokacin da aka kawo abinci Yaya bacci take yi. Mubina ta tasheta ta ci sannan da dabara ta sako zancen da ta zauna dominsa.

"Takardar nan ta passport Win ki naga jininki O- ne ko?"

"Ban dai ri?e ba amma tun a gida yara ke cewa O. Wani abin ne?"

Da sauri Mubina ta girgiza kai tana mai son Soye zallar farincikinta sai dai Yaya ta fi ta wayo.

"Babu wata matsala. Jinin naki mai kyau ne domin babu wata lalurar da za a bu?aci wani abu na sassan jiki da ba za ki iya taimakawa ba."

"Ikon Allah. Ki ce idan na koma in nemi ?arin sadaki a wajen Abban su Hamdi."

Dariya Mubina tayi kawai sannan ta kuma tambayarta ?a?anta nawa.

"HuWu ne."

"Kin taSa yin Sari?"

"Wai, sosai kuwa. Biyu nayi kafin babbar. A tsakaninsu kuma yaran na ?ara uku. Wani lokacin sai na sa rai da cikin sai ya zube."

Mubina bayani gamsashshe tayi wa Yaya game da rhesus da irin rawar da yake takawa idan aka sami saSaninsa a tsakanin mata da miji wurin haihuwa.

"Ilimi kogi. Dole ake cewa tafiya mabuWin ilimi. Kinga zaman abin da bai kai wuni ba amma na ?aru." Da yake ita Win akwai zurfafa tunani sai ta tambayi Mubina me yaja hankalinta har take ganin farinciki a tattare da ita game da jinin.

Kunya ta kama Mubina.
"Allah ni likita ce. Yana ?ayatar da mu ganin masu abin da wasu su ke bu?ata ido rufe." Tayi dariya "kada ki ce yau kin gamu da mayya."

Yaya ma dariya tayi. Sai dai kuma daga lokacin ta dinga karantar Mubina. Akwai abin da take ganin ta Soye mata. Kai gani ma take tana son faWa mata amma kamar tana jin tsoro. A zuciyarta ta ce 'Allah Yasa alkhairi ne'.

***

Yau sun tashi jikin na Kamal kwata kwata babu daWi. Anyi alluran, an saka ruwa amma duk da haka ciwo ya?i sauka. Su Umma ke kuka Hajiya na rarrashinsu. Tun zuwansu ko sau Waya bata zubar da hawaye ba. Halin da ta riski Kamal a kullum gani take ba zai shiga wata sa'ar ba. Sai dare take zuwa asibitin. Kullum tana hanya daga Jeddah inda asibitin yake zuwa Makka ta wuni a Harami tana ibada. Ta zabge sosai kamar ba ita ba. Masu rarrashin nata kuma sun fita nuna rauni. Suna tausayin Kamal suna tausayinta.

"Yanzu Alhaji ace Kamal yana cikin wannan yanayi amma Taj bai sani ba? Anya kun yi musu adalci kuwa? Ka yiwa sauran ?an uwansa adalci? Yau ko addu'a su ke yi masa ai zai sami rangwamen ciwo." Cewar Mama tana zubar da hawaye.

"Kin fi kowa sanin cewa dukkaninsu sai sun taho. Ina gudun su zo a yanzu su haWu wajen kashe masa ?arfin gwiwarsa da koke kokensu."

"Ka yi ha?uri amma wannan magana fa ba hujja bace. Yaron da ya tashi a gidan gandu irin namu ace yana jinya da jama'ar da ko rabin gidan basu kai ba ai zai ji babu daWi."

"Hajiyayye bata faWa muku za su taho ba?"

"Ta faWa. Kayi ha?uri. Na rasa me ya dace ayi ne." Ta cigaba da kukanta "ko sake auna jinin nasa za ayi a tabbatar? Ko kuma..."

"Mama ki yi ha?uri"

Kamal ne ya yi maganar yana mai runtse idanuwansa. Komai a jikinsa ciwo yake yi. Magana ma da ?yar yake cijewa ya yi.

Muryarsa da su ka ji ce tasa su duka matsowa kusa da gadon nasa suna yi masa sannu. A lokacin Bishir ya shigo da waya a hannu yana kallon Alhaji.

"Ya Taj ne wai yake ta neman Ya Kamal. Ya tayar da hankalinsa wai tun jiya basu yi magana ba. Me zan ..."

"Kira min shi."

Inna ta hana "Kamal yanzu ba lokacin da za ka biye masa kuna hira bane."

"Bai sani ba Inna. Ki ka sani ma ko bamu da rabon sake ga.."

Umma bata bari ya gama magana ba ta ce "Ya isa. Kira masa shi Bishir."

Kiran yayi amma Kamal ba zai iya karSa ba sai Bishir ne ya kara masa a kunne.

"In ka fara neman mutum kamar tsohuwar bazawara ta fito neman miji." Kamal ya faWi yana murmushi da ?yar.

Taj ya yi murmushi "Ba zan ji haushi ba balle bu?ata ta ta?i biya."

"Me ka ke so?"

"Tambaya zan yi maka. Please ka matsa daga inda su Alhaji su ke."

"Na matsa. Mene ne?"

"Me Alhaji yake Soye mana ne Happiness? Tun tafiyarku hankalina ya kasa kwanciya. Amarcin ma na kasa sakin jiki nayi abuna yadda ya dace."

"In na yarda da kai in tafi a tsaye. Akwai damuwar da zata sa ka kasa amarci?" Yana maganar ne ido a rufe don baya son haWa ido da iyayensa.

Ai kuwa hatta Alhaji sai da duka su ka yi dariya. Kamal ya nuna wa Taj lallai komai lafiya ?alau. Ba yadda ya iya dole ya yarda.

"Mun haWu da Mubina a airport da mu ka raka Yaya. Anya ibada ku ka je yi kuwa?"

Nan ma Kamal dariya yayi. Shi da Alhaji sun san da zuwanta. An kuma faWawa su Hajiya. Ta ce duba shi za ta zo yi amma kowa ya san zuwan nata na sallama ne. Bakunan su ne dai ba za su iya faWin abin da yake zuci ba. Sun cire hope.

"Happiness amana..."

"Me?" Kamal ya dawo daga tunani. Bai ji me Taj yace ba.

Taj ya sake maimaita cewa zai bashi amana. Ya sanar dashi lalurar da ta same shi da abin da su Salwa su ka yi. Shi ya so fara faWawa amma ya gagara samunsa a waya. Hankalin Kamal ya tashi sosai.

"Ka yi min addua kafin na zo. Idan ban warke ba to ka shirya. Ni yara 12 za a haifa min kuma cin mu da sha duka wuyanka zai dawo."

"Har wasa kake yi da abu mai mahimmanci irin wannan?"

"Ina da kai Happiness mene ne zai dame ni? Amma nayi tunanin za ku j8 zancen a wajen su Alhaji fa. Sai naga da kai da su Bishir shiru. Ya Ahmad kuma kunyar nemansa nake yi."

"Da gaskiyarka. Amma na san ba zai ri?e ka a rai ba. Yana masallaci."

Suna gama wayar, Hamdi dake zaune kusa da shi tana shirya akwatin tafiyarta ya fuskanta.

"Kin san Allah, akwai abin da yake faruwa mai girma da su Alhaji. Yau kwana nawa a ce babu wanda ya faWawa su Happiness abin da ya faru?"

"Maybe don kada su tashi hankalinsu tunda ibada su ka je" ta faWa domin kwantar masa da hankali.

"Allah Ya kai mu gobe. Idan ma akwai wani abu zan gani."

"Me yasa ba za ka yi tunanin komai lafiya ba?" Hamdi ta sake faWi.

"Saboda jikina yana bani cewa akwai problem. Kin tuna abin da ya faru daga ciwon kan da nayi a wurin dinner? Saboda damuwa gida Alhaji ya mayar dani. Sai yanzu da na faWa musu hancina da harshe sun zama useless ne su ke nuna min rashin damuwar da nayi tsammanin gani."

Zungure shi Hamdi tayi tana murmushi "wannan dai rigima ce kawai da shagwaSa. To taho in jajanta maka. Ni ai ba na kira komai naka useless ba."

Taj ya saki fuska yana murmushi. "Allah ko Mrs Happy?"

"Kana musu ne?" Ta kashe masa iso.

Aikin da take yi ya nemi rabata da shi taki yarda tana yi masa dariya. Yanayin damuwar da ya shiga ya kau. Ya koma tsakaninsu sai tsokanar juna.

"Wannan akwatin kin haWa shi ya kai sau goma."

"Ba fa zan damu ba idan ka tsoka ne ni akan wannan tafiyar. Kuma baka ga komai ba. Rawar kai sai na saka harami." Ta tashi tana buWa kafaWa "kai dai Allah Ya kai mu."

"Amin."

***

Daga airport ya kamata su raba tafiya da Mubina. Su Yaya Madina za su fara tafiya ita kuma cikin Jeddah za ta ?arasa asibitin da Kamal yake mai suna King Abdul Aziz Medical City. Yadda ta dinga bin Yaya tana taimaka mata da abubuwa duk da cewa abokan tafiyarta ma suna ?o?ari duk sai ya dami Yaya. Jikinta ya bata akwai wata a ?asa. Kafin tayi tambayar ne Mubina ta ce za ta shiga banWaki. Yaya sai ta nemi su jira domin su yi sallama.

Zuciya cike da tunani da fargaba Mubina ta shiga banWaki. Ta shige guda ta rufe kanta kawai ta fashe da kuka. Duk yadda take son Kamal ta sani cewa idan Yaya mahaifiyarta ce ba za ta yi na'am kai tsaye ta bada ?odarta ba. Uwa fa aka ce. Ina adalci da sanin ya kamata idanta ingiza wadda bata sani ba tayi abu saboda nata son zuciyar?

"Allah Ka yafe ni" ta faWa tana sake goge hawaye.

Tana buWe ?ofar tayi ido huWu da Yaya.

"Lafiya dai ko Mubina? Na ji ki shiru."

Murmushi ta kama yi na dole "abu ne ya shigar min ido. Kin gan shi yayi ja ko? Mu je na Wauki kayana kada na sa ku yi dare a hanya."

"To" Yaya ta ce ba don ta yarda ba.

Da su ka fito taxi Mubina ta shiga. Yaya na kallo motar kawai taji wani abu ya tsungule ta. Jakarta ta hannu ce kawai a jikinta ta dubi matan tawagar tasu ta ce musu tana zuwa.

"Maman Sajida ina za ki?"

"Ku wuce Madinan don Allah. Zan same ku da yardar Allah."

Suna ta tsayar da ita amma ina. Da irin nata saurin ta shiga tasin gabanta ta nuna masa wadda Mubina ke ciki tana shirin barin harabar airport Win.

"Haza sayyara" ta nuna motar, shi kuwa ya gane ya gyaWa kai "to yalla-yalla, ta'al-ta'al. Ku
i, uhmmm, riyalai haqibatun" ta jijjiga masa jakarta.

Bawan Allah damuwar da ya gani a tare da ita ta ishe shi. Kuma duk da?i?ancin mutum dole ya gane me ta faWa. Zama ya ce tayi ya kwashi mota su ka bi su Mubina.

Tafiya kamar ba za ta ?are ba. Wajen minti talatin sannan motar ta tsaya a bakin asibitin. Yaya ta bari sai da Mubina ta shige ta wajen wata ?ofar gilas da wani yaro mai fuskar Taj yake tsaye yana jiranta sannan ta bi bayansu. Haka kawai ta dinga jin faWuwar gaba. Tana tafiya basu ganta ba har su ka shiga lift. Nan fa ake yinta. Na farko bata taSa shiga ba kuma bata san inda za su je ba. Ita a tunaninta ma ?ofar Waki ce. Ta tsaya a jiki ta fara ?wan?wasawa sai ga wani mutum. Ya tsayar da lift Win taga ?ofa ta buWe amma basa ciki.

"Ya Hayyu Ya Qayyumu. Ina su ka Sace kuma?"

Kamar daga sama sai taji kuka a bayanta. Juyawar nan da za ta yi taga Hajiya ce a birkice. Babu Sata lokaci sai ta shiga tunda Hajiyar ma ya shiga kuma san bata lura da ita ba. Addu'a take yi tana wani irin kuka. Alhaji da kansa ya yi kiranta ya ce ta dawo jikin Kamal babu daWi.

"Allah na gatan bawa. Ya Rabbi ga Kamal. Ubangijina ka ?ara rufa min asiri akan ?addarar rayuwa. Allah kada in yi saSo. Ka taimakeni Ya Rabbi. Wayyo Allah. Allah Ka dubi Kamal."

Yaya ta gama sarewa da lamarin nan. Me ya sami Kamal wanda su Taj basu sani ba? Tayi imanin babu abin da zai zaunar da Taj yana raha a gida bayan lalurar da same shi da ya san Wan uwansa yana wani hali.

Da sassarfa Hajiya ta fita daga lift ita ma Yaya tabi bayanta. Don ma tana Wan jiri saboda rashin sabo. ?ofar Wakin a buWe take. Tana hango Kamal a kwance da likitoci a kansa. Fuskarsa Soye cikin abin sha?ar iska. Don dai taji Hajiya ta ambace shi ne ta gane shi. A ?ofar Wakin Yaya Kubra ce ta rungume Alhaji tana kuka. Inna, Umma da Mama kowacce fuska ji?e da hawaye. Mubina kuwa gefen bango ta samu tana wani irin kuka a hankali. Bata yi tunanin ?arasawa garesu ba. Ta tuna kalaman Mubina ne kawai. Wani likita na fitowa daga Wakin Yaya ta bishi da sauri. Hankalinsa a tashe kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya tausaya mata. Saurin da take yi da ?afarta a haka ya san akwai wahala.

Yaya ta nuna Wakin ta sake haWo larabcinta na islamiyya a karo na biyu.
"Haka gurfa..." ya gyaWa kai "to ma haza Kamal?"

Likitan ya kalleta yana son yi mata bayani amma sauri yake yi. Juyawa yayi sai ta kuma kiransa. Da ya juyo zai nuna mata inda za ta je reception idan taimako take nema sai ta mi?a masa takardar nan da aka rubuta jininta.

"O netif (negative)" ta nuna ?irjinta "Kamal ahali (Wan uwanta ne)."

"Alhamdulillah" ya fara cewa zai koma Wakin ta girgiza kai.

"Hausa...a nemo mai yi min Hausa."

"Hausa? Nigeria? Kano?"

"Nace maka ahali ai su Win" ta kuma nuno Wakin.

Ya gyaWa kai kuwa ya ce ta biyo shi. Suna tafe yana buge bugen waya. Bata san cigiyar mai jin hausa yake yi ba. Ba a wahala ba ya samu. Mai shara ne amma ya tadi gida. Ba shi da nisa dai. Wuri mai kyau aka bata ta zauna har mutumin ya zo. ?an Katsina ne yake aiki a nan. Shi likitan ya faWawa ya tambayeta ala?arsu. Sun yi mamakin wai wan mijin ?arta ne Nan da nan ta faWa. Sai ya sanar da shi ciwon Kamal da abin da yake bu?ata. Yaya ta dafe ?irji da fari. Sai kuma kawai ta fashe da kuka tana faWin,

"Allah Hakimu. Allah Hakimu." Daga ?arshe ta Wauko wayarta ta nuna nambar Abba Habibu ta ce a kira shi. Likitan da kansa ya kira.

Yana ganin ba?uwar namba ta Saudiyya ya Wauka. A kiWime yake sosai. Abokan tafiyar sun kira gida sun ce a faWa masa abin da ya faru. Bai riga ya sanar da su Sajida ba amma ya gama gigicewa.

"Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login