Showing 54001 words to 57000 words out of 182745 words

Chapter 19 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

95

halak. Bai san zama ko kaWan.

"Ina jin ka. Kada ka ce min budurwa gareka. Tunda ban san da ita ba, ba za ta zama silar da za ka watsa min ?asa a ido ba." Baba Maje ya ce a kausashe.

"Ba haka bane Baba" Baballe ya ce a ladabce "?ar uwarta nake so. Na Wan jinkirta faWa mata ne saboda wasu dalilai. Gaskiya ba zan iya aurenta ba alhali ina yiwa ?anwarta so na aure." Ya ?arashe kai a ?asa.

Gumi ne ya tsatstsafowa Baba Maje. Ya dubi ?ofar cikin gidan.
"Dan?ari! To yanzu ya kake so nayi? Me yasa ku ke da zurfin ciki ne? Da na sani ko baka faWa mata ba ai ba zan yi wannan karambanin ba."

"Idan zai bani ?anwar sai ka sanar da su Kawu a ayi auren goben a madadin na Sajidan. Sai a jinkirta komai tunda ban shirya ba." Baballe ya furta da hope Win baban zai amince.

"Dama ko wace ai zan faWa musu. Ni damuwata ma ita Hamdiyyan za ta yarda ne? Ko ka manta yadda su ka yi da Ummi a makaranta?"

Da sauri Baballe ya ce "Zeenatu ce ba Hamdi ba."

"Wace Zeenatu kuma?" Baba Maje ya ce don kansa ya ?ulle.

Baballe ya yi murmushi "Zee. Naga bata gama makaranta ba. Niyata zuwa ?arshen shekara idan ta gama na san lokacin na Wan yi tari. Sai na gabatar da kaina."

Kamar Baba Maje ya make shi don takaici ya ce "banza, kana can kana shiri wane zai shige tsakani sai dai kaji ana batun an kawo kuWi."

Shi dai tunda yaga kamar ya sauko sai ya kwantar da hankalinsa. Ciki su ka koma tare. Kowa ya zuba musu ido. Baba Maje ya Wan rissina kai na jin kunyarsu ya faWa musu yadda su ka yi da Wansa.

"Alhandulillahi ai duk gida ne." Cewar Abdul?adir.

"In kun amince dashi maimakon a fara kiran mutane ana cewa an fasa auren gobe, me zai hana a Waura nasu. In ya so sai ta tare bayan ta ?are karatunta."

"Hakan ma ya yi. Bari su dawo daga wajen taron sai a faWa musu."
In ji Inna Luba.

*

Banda gunjin kukan Zee babu abin da yake tashi a tsakar gidan. Sai da kowa ya watse sannan Inna Luba ta kira su har Halifa Wakin Abba ta faWa musu. Sajida ko uffan bata ce ba. Tashi tayi da mutuwar jiki ta koma Wakinsu. Yaya za ta bita Abba ya hana.

"Ki barta ta sami sararin yin kuka har taji sanyi a ranta."

"Ita kaWai?" Ta share nata hawayen.

"Wata damuwar tana bu?atar kaWaicewa kafin zuciya ta karSe ta. Idan tana bu?atarmu da kanta za ta neme mu."

Zee ya kalla da ta faWa kan kakarta tana kuka kamar wadda za a zarewa rai.

"Shikenan sai a fara yi min aure bayan ina da yayye?"

Inna Luba tana shafa mata baya ta ce "Ja'ira. Ashe kukan ba na ?in mijin bane. To ai da sau?i. Yayyenki kuma ki sani kowacce lokacinta yana hannun Mahaliccinta kamar yadda naki yake."

"Mijin ma bana so Inna." Ta ce tana ?ara sautin kukanta.

"Bana son rashin hankali. Ihun da kike yi ma?ota za ki tara mana ko me?" Yaya ta faWi cikin fushi.

Tana son Iyaa da Baba Maje a matsayin aminansu. Amma auren ne bata da tabbas a kai. Auren da aka yi ta soyayya ma gashi nan bai kafin ayi ya tashi. Ina ga wanda ya yi kama da cushe? Duk son su yi aure da take yi, bata so a wula?anta su.

Hamdi ce ta ri?e Zee su ka koma Waki. A nan ta tarar da Sajida akan abin sallah. Kuka take yi amma babu sauti. Sai kwararar hawaye kawai. Sau tari ma'anar sunanta tana binta. Mutum ce mai yawan kai goshinta ?asa wurin Allah.

Zee daina kukan tayi ganin yayarta ta fita nutsuwa. Hamdi ta fita tayi alwala ita ma ta zo ta shimfiWa abin sallah kusa da Sajida. Ganin haka ita ma Zee sai tabi sahu. Sun riga sun yi sallar isha tun Wazu. Don lokacin shaWaya ma ta kusa. Al?ur'ani kowacce ta Wauka ta buWe inda ya samu su ka fara karatu. Idan ka gansu abin tausayi kuma abin sha'awa. Yayinda ta ?an uwan biyu ke nemawa kawunansu zaSin Allah da sassaucin abin da ya tunkaro su, Hamdi su duka biyun take yiwa addu'ar zaSin alkhairi. Tana fata kowacce ta sami aminci a ?addarar dake jiranta a gobe. Kuka kuwa idanuwansu ko gauta albarka.

Duk wannan abu wayar Sajida vibrating take da kiran Safwan. Ita kuwa tayi al?awarin sake haWuwarsu ko jin muryar juna sai in sun haWu bisa kuskure. Ba za ta Wauka ba balle ace ta kasa ha?uri da wanda babansa ya zo har gida ya ci mutumcin nata uban.

***

A Sangaren Taj yadda abubuwa su ka kasance sai addu'a kawai. Ro?on Kamal ya yi akan ya kai shi gidan Yaya Babba ya ce babu ruwansa.

"Ina son rabuwa da iyayena lafiya. Naga kai wannan is the last thing on your mind. Duk nasihar da nayi maka bata shige ka ba."

"Don Allah Abba bai baka tausayi ba?"

"Ya bani, amma addua ce kaWai taimakon da zan iya yi masa. Da za ka ha?ura da auren Hamdi ni kuma nayi maka al?awarin auren Sajida."

Haushin Hamdi da yake ji ya tuna, sai dai kuma wannan bai isa dalilinsa na ha?ura da ita ba. Wannan tsiwar yake son ?urewa da salon soyayyar da ya tanadar mata. Zafin kai kuwa ya yi imani da cewa bata kai shi ba. Zai gayyato ta cikin rayuwarsa su hau sama su faWo tare. Barinta ne dai ba zai iya ba. Domin duka wannan rigimar tasu bata kama ?afar son da yake yi mata wanda ya yi masa shigar farat Waya ba.

Bari ya yi sai da Kamal ya bar gidan Ahmad sannan ya fice. Ya kusa isa gidan Yaya Babba sai kawai ya canja shawara. TaSo mai adaidaita sahun ya yi.

"Don Allah ka yi ha?uri. Kantin Kwari zani."

"Malam lissafin kuWinka fa zai canja."

Taj ya zura hannu a aljihu ya zaro dubu uku sabbi fil ya bashi.

"Ko akwai ciko?"

Mai adaidaita ya saki murmushin da ya koma dariya.

"YallaSai sai dai idan kuma sadaka za ka ?ara min akan wa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nnan."

Taj dake neman taimakon Allah sai ya ?ara masa dubu biyu.

"Idan mun je in jira ka ne YallaSai?

"Da ka kyauta. Inda ka auko ni zan koma."

*

Alh. Hayatu na zaune a cikin ofishinsa dake hawa na biyu a katafaren ginin store Winsa mai suna Maitakalmi Enterprises dake kantin Kwari yaji ana ?wan?wasawa tare da sallama lokaci guda.

Muryar wani yaron shagon ce wanda ya kasance Wa a wajen wata da su ke ?an maza zar da ita.

"Kawu dama..."

"Matsa na shiga" Taj ya ce da Wan saurayin.

Da sauri ya yi gefe, yayin da Alhaji ya tashi tsaye saboda gane muryar da ya yi.

"Me ya kawo ka?" Ya ce da kakkausar murya.

Yaron da ya nuna masa office Win don bai taSa zuwa ba tunda aka yi ginin sai yau ya kalla. Cikin sauri ya rufe ?ofar ya bar wajen. Taj ya juyo ya kalli mahaifinsa sai kawai ya sauke gwiwoyinsa duka biyu a ?asa.

"Alhaji na zo neman izini da amincewarka ne." Ya faWi yana kallon uban.

"Dama nayi wannan isar a rayuwarka ne?"

Zuciyarsa dokawa take da ?arfi saboda fargaba. Amma ya san cewa indai ya rasa goyon bayan Alhaji, ba zai taSa auren wadda yake so ba.

"Ka fi ?arfin komai a rayuwata."

"Shi yasa ka zaSi barina akan ka ajiye burinka?"

Taj ya girgiza kai "baka bani zaSi ba a lokacin da ka koreni Alhaji. Hukunci kawai ka yankewa kuskurena."

Zuciyarsa hasala tayi. ?an nasa ya fishi gaskiya. Wannan ne ya Sata masa rai.

"Rashin kunya ka zo ka yi min?"

"Ban isa ba." Ya Waga kai daga dur?uson da ya yi "aure nake so ka yi min gobe don Allah."

"Ka fara shan ?waya ne Tajuddin? Ni za ka tunkara da wasan kwaikwayo irin wannan?"

"?ar wajen Habib Umar ce. Simagade na Soron Winki."

Yana gama magana ya rufe idanuwansa saboda jiran saukar mari daga Alhaji. Da yaji shiru na wasu da?i?u sai ya buWe idanunsa. Abu na farko da Alhaji ya fara ce masa shi ne,

"Me ka ke ta?ama da shi ne Taj? KuWin da kayi ne kake jin ya isa ka kawo min zancen banza irin wannan?" Ya nuna ?irjinsa "Ni? Ni za ka cewa kana son auren Wiyar Habibu?"

"Bana ta?ama da komai Alhaji sai matsayina na jininka. Ka juya min baya a karo na farko amma Allah Ya tsareni daga faWawa rayuwar da kake guje min. Ba yin kaina bane. Ba kuma isarka bace ko tawa. Albarka ce kawai daga Allah wadda na tabbata kullum kana ro?a min."

Kallon mamaki kawai Alhaji ya dinga yi masa. Yana kuma tuno kalaman Gwaggo na ?arshe ?arshe a gare shi da take cewa Taj tamkar shi ne a madubi. Yadda yake haka ya haifo Wa irinsa. Duk lokacin da yake son ta?wara Wansa, to ya fara bari shi ma duniya ta tan?wara shi.

"Shi yasa yanzu ma ka shirya saSa min saboda kana jin komai zai tafi yadda kake so?"

"Wannan karon ina jin tsoron idan ka barni kada na saSawa Allah akan soyayya..."

"Kai Taj ka kiyayeni. Ni kake faWawa waWannan maganganun?" Alhaji ya furta kansa na yi masa wani irin nauyi.

"Ina sonta Alhaji." Ya faWa kai tsaye abinsa.

"Ita ?ar Habibun?"

"Eh."

"Zo ka zauna"

Don dai shi tsayuwa tana neman gagararsa. Kan kujera su ka koma. Alhaji ya daWe yana tunani kafin ya ce da Taj,

"Ka tafi gida ka jirani."

"Gidan Yayan za ka zo?" Ya tambaye shi da wata irin murna don ya san ina yake nufi.

"Gidana nake nufi Tajuddin. Ka je can ka jirani."

Godiya ya yi ya tashi ya fita. Sanin me Alhaji zai ce sai Allah. Shi dai bu?atarsa ita ce ya sami damar yin auren da zai fidda Abba daga kunya gobe da izinin mahaifinsa. Ha?uri ya bawa mai adaidaitan ya ce inda za shi ya canja. Mutumin ko a jikinsa tunda ya caski kuWi.

*

Mutane sun kai biyar da Alh. Hayatu ya bawa aikin yi masa duk wani binciken da ya dace akan Abba Habibu. Kafin isha'i dukkanin bayanai sun riske shi. Tun daga zamansa a Lagos bayan ya yi aure har batun auren babbar ?arsa da za ayi gobe. A duka bayanan yafi mamakin dalilin da yasa Taj da Kamal nemo Simagade. Da kuma aikin da Taj ya bashi. Share wannan ya yi ya kira mahaifin Safwan domin kuwa ya san shi duk da ba wai abokai bane. Shi kuma yadda yake mutunta Alhajin yasa ya faWa masa auren nan fa babu da dalilinsa. A ?arshe yadda ya fahimta wanda kuma da ?amshin gaskiya a ciki, auren ragewa Habibu ba?inciki Taj yake son yi.

Dariya ce ma ta kama shi. Wato ta wannan hanyar Habibu ya zaSi ya dawo cikin rayuwarsa. Lallai zai nuna masa kuskurensa a lokacin da ya dace.

*

Gida kowa murna ganin Taj ya shigo kuma ya ce Alhaji ne ya yi masa izini. Inna harda kukan farinciki. A gidan ya yi Magriba sannan Kamal ya dawo. Yana ganinsa ya sha jinin jikinsa.

"Wace tsiyar ka ?ulla?"

"Alkhairi dai. Zancen auren Hamdi nayi masa."

A harzu?e Kamal ya ce "ba ka da hankali ko? To wallahi yana da bindiga. ?arshenta ma harbeka zai yi."

Taj ya ?yal?yale da dariya. Kamal ba dai tsoro ba. In anyi magana kuma ya ce Taj Win ne matsoraci.

Wuraren tara na dare Alhaji ya dawo. Yana hawa sama ya kira Taj. Bai nuna masa ya san komai ba. A gabansa ya kira Yaya Babba ya yi masa magana.

"?anka ne ya Wauko aure bagatatan. Wasu matsaloli ne su ka taso da su ka sanya auren dole ayi gobe. Zan zo gidanka da safe kafin lokacin mu yi magana."

Yaya Babba farincikin jin Alhaji ya tsayawa Taj bai bashi damar zurfafa tambayoyi ba.

"Kana iya komawa gidan yayan naka. In sha Allahu gobe za a Waura."

Godiya mara adadi Taj ya yi masa.

"Ba sai ka faWawa matana na ba domin ko Abu ba za ta baka goyon baya ba. Zan yi musu magana da kaina."

Duk da cewa a zuciyarsa yana jin kamar shigo shigo ba zurfi Alhaji yake masa, sanin cewa baya magana biyu yasa bai ji ko War ba. Ya tabbata za ayi auren in sha Allah.

***

Gidan Abba Habibu tamkar ba shi bane jiya da yamma ake ta hayaniyar shirin zuwa sisters' eve. Yau shiru kamar babu mutane. Gashi dai ba a yi shelar me ya faru ba. Amma ganin ?an biki babu walwala sai kowa ya sha jinin jikinsa.

Banda ?an mazan gidan Alhaji babu wanda ya san da maganar Waurin auren sai ?an uwansa maza. Su duka mamaki bai hanasu haWuwa a masallacin juma'ar da za ayi auren bayan an idar da sallah ba. Kamal ne ya bawa Taj sababbin kayansa masu babbar riga. Ya tu?osu a mota zuwa masallacin. Sai dai jikinsa tamkar anyi masa duka. Gani yake akwai abin da zai biyo bayan wannan Wanyan kai na Taj. Alhaji ba zai barshi ya sha ba.

Ana idar da sallah Liman ya yi sanarwar Waurin aure kamar yadda aka faWa masa. An fara da Abubakar Maje Garba (Baballe) da Zeenatu Habib Umar akan sadaki naira dubu hamsin. Masallaci ya auki kabbara.

Abba yana share ?ar ?wallar farinciki sai yaji an taSo shi. Yana juyawa damansa ya yi tozali da Alh. Hayatu. Ba ?aramin ruWewa ya yi ba kuwa.

"Kwantar da hankalinka. Sunan yarinyar wajenka da Taj yake so za ka bani. Ina fata ka yi masa izinin aurenta."

Abba baki ba rawa ya ce "Yaya Hayatu..."

"Kada ka damu. Nima short nktice da ya bamu ne ya hanani zuwa mu yi maganar. Ya sunanta."

"Hamdiyya."

Alhaji ya juya fuskarsa ba yabo ba fallasa ya faWawa Yaya Babba. Shi kuma ya sanar da Liman. Nan aka sake sanarwa. An Waura auren Tajuddin Hayatu Sulaiman da Hamdiyya Habib Umar akan sadaki dubu Wari biyu.

A karo na uku sai ga wani tsoho an gunguro shi akan wheelchair. Ba kowa ne ya turo shi ba kuwa illa Safwan. A gaban Abba ya tsayar da kujerar. Ya Wuka a kunyace. Tsohon ya dubi Abba da murmushi a fuskarsa.

"Ni ne mahaifin Sabi'u. Kuma ni zan yiwa jikana waliyyi. Ina fata za ka ha?ura da abin da ya faru jiya wanda bani da masaniya. Sai Wazu yake cewa wai an fasa. Shi ne na kira Safwan Win ya yi min bayani."

Baba Maje ne akan gaba wurin cewa sun amince. Nan take Liman ya Waura aure na uku. Safwan Sabi'u Mamman da Sajida Habib Umar.

Allahu Akbar
Abba sakaya fuska ya yi cikin babbar riga yana kukan farinciki.
RAYUWA DA GI?I 17



Batul Mamman=ؖ?




***
"Ayyyyyyiririiiiiiiii. Allah mungode maKa. Hajiya Jinjin uwargidan Habibu namu asa goshi a ?asa a mi?a godiya ga Sarkin sarakuna. Allah Ya kwashe miki ?an matanki a sa'a guda. Wannan farar juma'a ta amare uku ce rigis. Sai a saurari zuwan ?an dugwi dugwi iyalan Baba."

Ba kowa bane da wannan aiki sai ?ar Ficika daga soron gidan. Yana gama magana kuma yaransa su ka amshe guWar su na yi. Yaya fitowa tayi daga Wakinta inda ta fake da shiryawa ta zauna rarrashin Sajida da Zee. Hamdi na gefe ita ma tana basu baki tare da taya su kuka.

Anti Zinatu ce kaWai ta san zaman me su ke a Wakin. Ita ce ma ta tura musu Yayan domin wani ciwon uwa kaWai ke iya maganinsa.

Hamdi na jin muryarsa ta haWe rai bayan fitar Yaya daga Wakin.
"Wai namiji kenan. Mtsewww."

LulluSi Yaya tayi ta fita soron. ?ar Ficika ya wangale baki.

"Sai muka ji abin arzi?i ko Jinjin? Allah Yasa abokan zamansu ne."

Ita ma takaicin Waga muryar tasa take yi. Ga za?in murya gashi bai iya tausasa harshe. Ta tabbata kowa na jinsu a ciki.

"Da ka Wan rage maganar saboda ?an biki ba su san auren Zee aka Waura ba maimakon Sajida. Sannan kana cewa amare uku sai ayi zaton..."

"Ba zato bane Jinjin. ?a?an Simagade sun zama farinwata sha kallo. An so tozarta shi sai gashi Allah Ya aurar dasu lokaci Waya."

Yaya dai bata fahimci inda ya dosa ba. Gani take wani zancen yake haWawa da wani. Sai kawai ta koma ciki. Aka yi ta tambayarta me yake nufi kuwa don duk sun ji.

"Shirmen ?ar Ficika ne. Shi da ko wurin Waurin auren basu je ba?"

Rufe bakinta ke da wuya Halifa ya shigo gidan kamar an jeho shi daga sama. Haki yake da ?arfinsa saboda gudun da ya sha ba na wasa bane. Tun daga masallacin juma'ar unguwarsu har gida. Tafiyar kimanin minti talatin. ?afafunsa sun yi buWu buWu.

"Yaya! Yaya!!" Ya dinga ?wala kira kamar makaho na neman Wan jagoransa.

"Kai Halifa lafiyarka kuwa?" Wata ma?ociyarsu ta tambaye shi.

"Ina Yaya?" Ya faWi yana dariya.

Banda Yaya, duk matan da su ke gidan fitowa su ka yi. Yana ganinta ya taho da sauri, sai kuma ya tsallaketa ya rungume Sajida.

"Wai mene ne Halifa? Ka sanya mu a duhu" cewar Inna Luba.

Murmushi ya yi yana duban ?an uwansa.

"Yaya an Waura. Duka su ukun an Waura musu aure."

Dafa shi Inna Luba tayi zuciyarta na bugawa.
"Nutsu ka yi min bayani. Su waye su ka yi auren?"

"Ya Sajida da Yaya Safwan."

Sajida ta bar jikin bangon da ta jingina tayi da sauri, ta rufe bakinta da hannu. Wasu zafafan hawaye suna sauko mata. Hamdi ta rungumeta tana cewa "Alhamdulillah."

Anti Zinatu ta ce "Mata biyu aka aura masa kenan? Naji ka ci mutum uku."

Ya murmusa da farincikinsa "a'a, sai Ya Hamdi da Happy."

Inna Luba ta ware idanu a tsorace "Hafi? Mutum ne?"

Yadda yake murna kai ka ce shi ne angon mata uku. Gyarawa ya yi yadda za ta gane da kyau.
"Ya Taj. Shugaban inda Abba yake aiki yanzu."

Cikin Hamdi wata irin ?ullewa ya yi. Taji ya saki lokaci guda yana neman tsinkata a gaban mutane. Duk da haka danne shi tayi da hannu biyu.

"Kai ka san bana son wasa irin wannan. Wace Hamdin kake nufi?"

"Wallahi ke ce Ya Hamdi. Babansa kawai muka gani ya cewa Abba yana nemawa Wansa aurenki. Sadakinki fa dubu Wari biyu. Cash in faWa miki."

Daga inda ya yi rantsuwar ita Hamdin ta daina jin komai sai bugun zuciyarta. Wannan wane irin mugun wasa ne Halifa yake yi mata haka? Aure? Ita ce tayi aure kamar wata kayan wasa? Kuma wai da Taj. Waye ma Taj? Kamar ta san sunan.

Sama-sama taji muryar da ko gane mai ita ba yi ba tana cewa "Ku ri?eta...Sajida kama hannun. A'a rungumota kawai kada ta kai ?asa."

Luuu haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login