Showing 171001 words to 174000 words out of 182745 words

Chapter 58 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

120

da wani matsayi daban da na ?an uwan taka."

*
A cikin Wakin kuma bayan fitar su Mubina, Kamal ya ce Taj ya mayar da shi Waki. A hankali ya juya wheelchair Win yana mai kulawa da dukkan motsin da zai iya janyo wa Kamal jin zafi.

Sallama Kamal ya yi wa kowa. Da ya zo kan Alhaji sai cewa ya yi da Taj ya tsaya.

"Na ji kana ta magana a hankali ga Alhajin ka tambaye shi da kan ka?"

Taj ya yi turus domin gabaWaya bai gane me Kamal yake nufi ba. Ya kuma san cewa tunda ya yi haka to akwai abin da yake ransa. Lokacin wana shi ya samu. Sai ya rama Soye-Soyen da aka yi masa.

"Me ka ke son tambaya?" Alhaji ya zuba mu su ido don ya gano wayon Kamal.

"A bar maganar Alhaji. Zan dawo idan na kai shi Waki." Taj ya Wan tura Kamal sai yaji kujerar ta turje. Kamal ya saki burkin tayar don kada su tafi. Ya yi kalar tausayi.

"Ai gara ka tambaya yanzu saboda ni bana so ka tafi ka barni ni kaWai."

Abba Habibu murmushi ya yi. It is obvious Kamal a matse yake da son jin manufar maganganun Alhaji a waya. Ahmad kam dariya yake yi sosai.

Alhaji ya yi ?ar dariya shi ma
"Kamal ina jin ka. Me Taj ya ke son sani?"

"Cewa ya yi wai ya ji kamar ana maganar aure na."

Taj bai san lokacin da ya ce "Ni? Kamal yaushe?" Don bai yi tunanin tambayar da Kamal Win zai yi kenan ba.

Inna ta shigar wa Kamal "Ai tunda ya ce ka yi kawai ka yarda cewa ka yi Win don a zauna lafiya."

Da gangan Taj ya ce "Shikenan to."
Ya kalli Alhaji "na ji kamar ka na maganar aure na."

Ya yi nasarar tunzura Kamal kuwa don bai san lokacin da ya gyara masa ba.
"Aurenka kuma? Yaushe ka yi aure da har ka ke tunanin ?ari?"

"?arin aure kuma Allah na tuba ai ba abu bane mai wahala."

"To wai nufin ka Hamdi za ka yi wa kishiya? Happy akan su fa ni babu ruwana da dangantaka. Hamdi comes first yanzu. Da kai da mazajen su Sajida duk Waya ne a wajena. Kai suruki ne, ni kuwa Wa ne ko Yaya?" Shi ma ya rama zolayar da Taj ya yi masa.

Sai ga Taj da ri?e haSa. Aiki ya biyo ta kan ma su gida.
"Lallai ma! Happiness kada mu Sata daga farfaWowarka fa. Har za ka faWa min kusanci da Yaya?"

"Wannan ko shakka babu." Kamal ya ce kai tsaye "kai ?a kawai ta baka. Ni kuwa ?oda ta bani. Akwai jinin jikinta a tare da ni. Tsakanin mu ma babu haWi.

Mayar da rigimar tasu aka yi abin dariya a Wakin. Taj ya nemi taimakon Abba Habibu da Yaya ta gyaWa kai tana supporting Win Kamal.

"Abba ka na jin sa fa."

"?yale su Taj kai fa Wan maigida ne. Shi kuwa Kamal agolan gida ne, ka san su akwai rawar kai. Gida na hannunka. Duk yadda ka dama dole a sha ko ba a so."

Dariy???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a aka sake yi inda Kamal da Yaya su ka ce basu yarda da wannan mu?ami da Abba Habibu ya bawa Taj ba. A wannan halin Hamdi da Mubina su ka dawo. Taj ya ja Kamal su ka koma nasa Wakin. Ahmad kuma ya mayar da Mubina da Hamdi hotel. Yayinda Alh. Hayatu ya cigaba da nasa shirin daga nan. ?an uwansa maza ya kira ya sanar da su shawarar da ya yanke. Su ka yi na'am da farinciki. Yaya Babba ya shiga gaba su ka haWu da ?an uwan Hajiya, wani abokin Alh. Hayatu da ?an uwa sha?i?an sauran matan mutum WaiWai sai gidan Kawun Mubina. Shi ma kafin zuwan nasu ya riga ya faWawa duk wanda ya kamata. Ana idar da sallar la'asar wanda ya yi daidai da magrib a birnin Jeddah aka Waura auren a masallacin unguwa.

Asibitin gabaWaya ya kaure da murna. Ma'aikatansu waWanda su ka san Kamal da Yaya su ma duka sun taya su murna sosai.
RAYUWA DA GI?I 40
?ARSHE






Batul Mamman=ؖ?





Allahumma Balighna Ramadan...AMEEN






A can hotel Mubina ba ?aramar takura ta shiga ba. Aure dai an Waura amma kamar yadda ta ce babu kowa nata sai dangin miji. Duk sai ta koma abar tausayi. Yaya Kubra ta lura da haka sai su ka yi magana da Yaya Hajiyayye, aka kama mata Waki daban domin kwana biyun da su ka yi Wakunan da su ka kama na group ne masu gado hurhuWu.

"Hamdiyya ki koma wajenta ki tayata zama. Idan kuna bu?atar wani abu ki mana magana. Na san ba za ta sake da mu ba yanzu kuma sai a hankali."

Hamdi tayi murmushi harda rufe fuska da tafukan hannu "nima dama kunyar taku nake ji har yanzu."

Yaya Kubra ta harareta da wasa
"Ehhh lallai, wallahi ki ka sake cewa kina jin kunyarmu sai na yi mi ki handsfree a gaban Alhaji."

"Tsegumta min mana likita. Me ki ka gani? Tajo ya yi ajiya ko? Oh ni uwar babana. Aure ko wata biyu ba a yi ba. Dama na san za a rina. Taj ko kaWan bai yi kama da salihai ba.

Hararar da take yiwa Hamdi komawa tayi kan Yaya Hajiyayye.
"Ke fa daWina da ke sakin zance wallahi. Don Allah kina yi kina tauna magana kafin ki furzar. Me ya kawo batun salihanci tsakanin mata da miji banda abin ki?"

"Raini ya jima da shiga tsakaninmu dama Kubra. Gara ki kwaye min baya a gaban...." ta waiga babu Hamdi babu dalilinta. Can ta hangota ta kusa ?ure korido tana ta zuba sauri kamar ta kifa. Ita da Kubra su ka haWa ido su ka kwashe da dariya. FaWan da ba su ?arasa ba kenan.

*

?arfe tara da rabi Umma ta shiga Wakin su Mubina. Hamdi kaWai ta samu ta kashingiWe akan abin sallah. Umman na shiga ta tashi zaune.

Umma tayi murmushi "?anwar Ango ina amaryar yayanki?"

"Tana banWaki" ta amsa mata ita ma tana murmushin.

"Ai gara tayi wank..."

Caraf Mubina ta katse Umma daga cikin toilet Win da rawar murya. Tsoro muraran ya bayyana a tare da ita.

"Ba wanka nake yi ba. Alwala zan yi na fito."

"Ai ba laifi ki ka yi ba Mubina. Ki yi wankan ki shirya a nutse Alhaji ya ce ni da Hajiyayye mu raka ki asibitin."

"Na'am? Asibiti kuma" Ta buWe ?ofar ta fito a firgice. Idanunta zuru-zuru sai Sare-Sare take yi. Mubina akwai ruWewa sai a lokacin hakan ya bayyana.

Hamdi ta kalli Mubina sai taji wani tausayinta ya tsirga mata. Shi fa aure kwarjini gare shi na daban. Gashi dai da ?afarta ta taho ?asar amma yau Waya duk ta sauya saboda alhini.

Umma zama tayi akan gado ta yafito Mubina da hannu.
"Mene ne amfanin aure idan mace bata kasance tare da mijinta ba Mubina? Asibitin da kansu su ka ce sun yarje miki zama tare da shi tunda ke likita ce sannan sabon aure."

"Umma ni dai don Allah" sai kawai ta fashe da kuka.

Umma ta tashi tsam ta rungume ta.

"Kamal Win ne ba kya so?"

Mubina ta girgiza kai.

"Aure a irin wannan yanayin ko? Ba haka aka saba ba na sani, amma faruwarsa a hakan ya sa naku ya zama special."

Ba kunya Mubina ta Sare baki "ni dai Mamana, Umma don Allah wajen Mamana zan tafi."

?ago kanta Umma tayi ta ce "TamSali! Mubina? Shekararki nawa ne?"

Mubina ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana kuka tana murmushi lokaci guda.

"Na fahimce ki" Umma ta sake yin murmushi "?arasa abin da ki ke yi ki kwanta"

Ta juya za ta fita Mubina ta kira ta kai a ?asa saboda nauyinta da take ji.

"Umma ba za ku yi fushi ba?"

"Haba dai. Mubina ba na jin Kamal zai taSa samun soyayya irin wadda ki ke yi masa. Kin haWu da shi a halin ciwo kin so shi. Sannan a lokacin da dukkan wata ?ofa ta ?ulle sai Allah Ya yi amfani da ?udurinki na biyo shi domin..." muryarta ta karye "ku yi sallama sai Ya kawo mafita. Hamdiyya kina ganin akwai..." ta juya ko sama ko ?asa babu Hamdi sai kawai ta kama dariya "wannan ?anwar taki ta san yakamata sosai Mubina. A duk lokacin da take jin ana bu?atar keSewa cikin magana sai ki ga ta bar wajen da dabara."

"Nima na kula Umma."

"Idan ku ka rayu tamkar ?an uwa tare da sauran yaran namu da matar Ahmad ha?i?a kun gama yi mana komai."

"In sha Allahu."

"To amarya sai da safe."

Umma ta fita fuskarta babu komai sai annashuwa. Mubina kuwa wata ajiyar zuciya ta saki mai ?arfi ta faWa kan gado. Yanzu da Umma ba mai fahimta bace kawai sai a wuce da ita asibiti tin?is-tin?is. Gobe kuma a dinga zuwa dubiya ana ganinta a Wakin Kamal. Ai da kunya!

'Kamal' ta maimaita sunan a zuciyarta. Yanzu fa wai ya zama mijinta. Wani juyi tayi na farinciki tana ?ara yiwa Allah godiya.

*

Hamdi na fita Wakinsu da Taj ta wuce da niyyar ta Wauko kayan baccinta ta dawo wajen Mubina. She was just smiling idan ta tuna yadda ta baro Mubinan. Tana ji a jikinta Umma ba za ta matsanta mata ba. Nata key Win ta saka ta buWe Wakin. Tana shiga taji anyi sama da ita. Ta buWe baki za ta yi ihu Taj ya sauketa ya jingina bayanta da ?ofar Wakin. Ya tare mata hanyar wucewa.

"Kina yi su Alhaji za su zo kinga sai mu taru mu yi musu bayanin me ya firgita mu."

Ta harare shi "abin da ya firgita ni dai."

"Da na sani ma a toilet na Suya sai kin fi tsorata."

Hango irin tsoron da za ta ji tayi ta yi murmushi "da kuwa mai raba ka da yayana sai Allah."

"Kinga ki kiyaye ni da zancen yayanki Wan kalen dangi. Yana can gadon asibiti me zai iya? Taj will do what Taj wants." Ya ?are magana girarsa Waya a sama.

Kai ta girgiza "Gobe idan mun je ka maimaita abin da ka ce yanzu in koma gefe in sha kallo."

"You are looking for my trouble fa, and I will give it to you har sai kin ce ya isa."

Dariya ya bata ta kama ?ugu da hannu guda.
"Bring it on."

Janyota ya yi su ka nufi 3 sitter Win Wakin su ka zauna. Ta Wora kanta a ?irjinsa shi kuma ya sake rungumeta.

"?ar caras matar Tajuddeen." Ya kira ta affectionately.

"Uhmmm." Ta amsa muryarta can ?asa-?asa.

Kasancewarsu tare ya saukar mata da nutsuwa fiye da kullum a yau. Jikin Yaya yana ta ?ara kyau. Sai yanzu ta sami damar appreciating zuwa ?asa mai tsarki a dalilinsa.

"Yau ban ce miki ina son ki ba Hamdi na. I love you."

"Ni Win kake so ko ?ar caras?" Ta tambaye shi bayan ta zauna su na fuskantar juna.

"Why do you ask?"

Baki ta tura kafin ta ce "Tun ina yarinya ake cewa jiki zan yi idan nayi aure. Wai ?irar mu Waya da ?a?an Anti Zinatu."

"?ira kuma sai ka ce wata mota?"

"To dai ance zan yi ?iba. Kai kuma har wani ?ar caras kake cewa. Kada na fashe nan gaba na daina burge ka."

Damuwa sosai yake iya gani tare da ita. Ya yi dariya ya kuma zolayarta.
"Ki fashe kamar wata kwalba?"

"Happy manaaaa" ta buga ?afa a ?asa.

He hugged her tightly sannan ya yi magana a hankali.

"Ko me za a ce mi ki, ko me ki ka zama a gaba Hamdiyya ki sani cewa Taj is your home. You can be anything as long as Hamdin Abba Habibu ce ina son abata. Hamdi ?ar tsinke" ya fara ?irge da yatsansa "Hamdi ?ar doguwa, Hamdi ?ar gajera, Hamdi ?ar lukuta, Hamdi mai tumbi, Hamdi shafi mulera..."

Yana kaiwa nan wata wawuyar cakuma yaji ta kai masa tana rigima ya kwashe da dariya.

"Wai ina faWa ne don ki san cewa ke nake so ba jikinki ba."

Daga nan ya lallaSa abarsa su ka kwanta. Sai shabiyu saura Hamdi ta farka firgigit kamar an tsunkule ta.

"Mubina tana jira na mu kwana tare. Ya Subhanallah." Ta tashi tana neman hijabi.

Sai da ta saka tukunna Taj ya ce "to amara ?irjin biki dawo ki kwanta. Amarya tana wajen Angonta."

"Anya kuwa? Ban ga alamun za ta tafi ba." Ta faWa masa iya abin da ta gani da Umma taje Wakin.

Taj ya soma dariyar mugunta. Hamdi tun tana mamaki har ta koma kusa da shi tana jiran ya faWa mata me ya kawo dariyar.

"Kaza gashin Najeriya" ya ce da ?yar dariya na cin sa.

"Ban gane ba fa."

"Yayanki..." dariyar harda ?walla.

Hamdi ta kama baki "yau ina ganin ikon Allah."

Da ?yar ya saisaita kansa "ana cewa an Waura auren nan yayanki Wan kalen dangi ya sa ni fita neman kaza. Wai bai dace amarya ta zo babu wani abu da zai tuna mata al'adar gida ba." Yana kallonta ya cigaba da cewa "kin dai sanni da faWin gaskiya ko Hamdi na...to haka na aje kunya a gefe na nuna masa rashin fa'idar nemo kazar nan saboda kada amarya ta fassara shi yana kwance magashiyan." Ya sake yin dariya.

"Ba ka da kirki fa" ita ma ta soma dariya don ta hango inda zancen zai dire.

"Rawar kai irin ta ango sabon shiga ya ce bai yarda ba. Babe, tun la'asar nake neman kaza don ya ce dole na nemo gashin Najeriya mai Wan ?uli-?uli da yaji. Kuma bai yarda na tambayi su Bishir ba duk da sun fi ni sanin gari wai kada a raina shi. To cut the story short naji a jikina. Wurin ana layi haka nayi ta zama har na samo."

"Shi ne kake yi masa dariya?" Ita ma fa dariyar take yi.

"Sai da yasa na dawo na Wauko masa aron kayana. Ga ciwo ga wahala amma haka ya dage na saka masa shadda harda hula. A table Win gefen gadon na jera masa kazar amarci, juice, youghurt da biryani. Kaiiiii, wa zai cirewa Happiness kayan nan? Ko dai in kira shi ne? Ba za su yi daWin bacci ba."

Hamdi dariya, Taj dariya. Sai sun yi kamar sun gama da sun haWa ido sai a sake daga farko.

"Harda turaren angwanci yasa na nemo masa mai mugun tsada ya feshe jikinsa."

Hamdi ta goge ?wallar dariya da yatsa "Ni damuwata akwai fridge a Wakin?"

"Fridge kuma? Akwai."

"Yauwa dama don kada kazar ta buga."

Su ka sake tuntsirewa da wata dariyar that was just contagious. Da mutum zai shigo Wakin dole ya taya su. After 1am Taj ya raka Hamdi ?ofar Wakin Mubina. Ta shiga ta sameta tana sallah. They just smiled at each other sannan Hamdi ta Wauro alwala ta zo ta tayar a kusa da ita.

***

Yau dukkanninsu su ka tafi asibitin domin daga nan za su wuce su shiga jirgin ?asa zuwa birnin Madina. Hajiya dai ta ce da Abba Habibu babu inda za ta har sai Yaya ta fara tashi da kanta. Anyi-anyi da ita ta tafi saboda akwai kulawa sosai a asibitin amma ta rufe ido ta ce su ?yaleta. Alhaji ya goya mata baya tunda shi ma ba tafiya zai yi ba. Kamal kuma za a bar masa Abba da amaryarsa. Duk wannan zancen kafin su fito aka gama yinsa. Alhaji ya ce da Mubina idan tafi son fara yin Umrarta a nutse cikin ?an uwa babu damuwa. Sai kawai ta du?ar da kai. Mama ta fassara masa da cewa ta amince da zaman ne. Kuma hakan yake a zuciyarta. Tun asuba mahaifiyarta ta kira ta su ka yi magana akan yin abin da ya kamata. Wasu lokutan mutum ya kan ajiye kunya da tsammanin al'ada ya yi abin da ya dace da halin da yake ciki.

Daga Wakin Yaya su ka rankaya Wakin Kamal. Ango ya dinga cika yana batsewa. Taj ne kaWai ya san dawan garin. Ya yi ?o?ari sosai bai yi dariya ya tona masa asiri ba. Sun fara yi masa sallama a zaton sa harda Mubina a tafiyar sai ya kaWa baki ya ce,

"Mubina matso mu yi sallama, sannan ga kazar ki nan ki tafi da ita."

"Innalillahiiii...." ta tattaro numfashi kafin ta dire "wa inna ilaihi raji'un."

Ji tayi kamar ya tsomata a cikin ruwan sanyi saboda kunya. ?aki ya yi tsit kamar ruwa ya cinye su na wucin gadi.

"Ku fita mu tafi. Kamal, Allah Ya ?ara sau?i."

Ahmad ya yi ta maza ya kawo ?arshen kallon-kallon da ake yi. Ai kamar jira su ke yi su ka fita a layi ko waige babu. Mubina ko motsi ta kasa yi.

"Da alama anaesthesia bata sake shi ba har yanzu doctor. Lamarin Happiness sai kin haWa da ha?uri. " cewar Taj.

Kowa ya watse. Babu mutum guda da ya kalli Mubina ko ya yi murmushi ko da ?asa-?asa ne kuwa. Ba su isa ba ne. Duk barkwancin yayyensu sun san Yaya Kubra ko Yaya Hajiyayye ce ba za ta Waga mata ?afa ba. Sun san wasan da ya kamata su shiga da wanda bai dace ba.

"Ashe haka ka ke Kamal?" Ta faWi baki buWe don har yanzu tana mamakin wannan magana.

Ya juya mata ?eya "Me na yi?"

"Babu komai." Ta rage murya tana magana a hankali amma yadda zai ji "dama Taj ya ce na lallaSa ka da sauran allura a jikin ka." Ta sami wuri ta zauna akan kujera ta juya masa baya ita ma. ?akin ya koma shiru.

Da ya ga babu Sarki sai Allah sai ya sauko. Yana magana abin tausayi.
"Jiya ba ki kyauta min ba. I waited."

"Shi ne yasa ka bani kunya a gaban ?an uwanka?"

Briefly ya labarta mata yadda jiya ta kasance a wajensa. Mubina ta dinga girgiza kai ita a dole ya bata tausayi. Ya gane sarai abin nata harda tsokana.

"Kar ki yi min dariya."

That was it! Magiyarsa tamkar zuga ta koma a gareta. Dariya ta kufce mata ta kare baki ta yi.

Kamal samun kansa ya yi da zuba mata idanu kamar haWuwar farko. She looked so cute tana wannan dariyar. Ya ji zuciyarsa tana neman cika masa ?irji saboda farincikin da ya samu daga abin da take yi yanzu. Da ta gama dariyar tashi tayi ta dudduba Wakin bata ga alamun nama ba.

"Ka saka min rai kuma ni ban ga kazar ba."

"Laifin naki kenan."

"Me kuma ya na yi?"

"Na zama abin tsokana dai da alama. To ki kwantar da hankalin ki domin kema kin shiga one chance yadda na shiga jiya."

?ar dariyar da take yi ta daina babu shiri ta dawo kujerar gefen gadon ta zauna. Kamal ya sosa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login