Showing 6001 words to 9000 words out of 182745 words

Chapter 3 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

78

an shiga da ?ofofi huWu a jere a Sangaren dama. Kowacce in ka shiga falo ne babba da banWaki da kuma Wakuna biyu. Nan me Wakunan matansa. Bangon dake kallon Wakunan kuwa kitchen ne makeke da store sai Wakin masu aiki dake haWe da banWaki. A jikin bangon tsakiya ne da matattakalar bene inda Wakin maigidan yake da falonsa. Sai kuma Wakuna biyu na ?an mata suma kowanne da banWaki duk a saman. Sai an fita daga bayan ainihin ginin ne kuma za a tarar da Sangaren samari. Ta gaba kuma aka jona ginin falo da banWaki inda yake ganawa da ba?insa. Duka gidan ?a?a ashirin da takwas ne kuma a ciki biyar ne kaWai maza. Sai ?a?an ?an uwa da yake ri?o da ?annensa. Shi yasa kullum gidan yake a cike.

Uwargidansa ta lalle Haj. Gambo da ake kira Hajiya kaWai tana da goma. Ta biyun Mama A'i tana da uku. Sai Umma Jamila mai takwas. Sannan amarya Inna Abu mai shida. Ya taSa sakin mace Waya wadda ta kasance ta uku a jerin aurensa. ?a Waya ta haifa kuma shi ne babban namiji a gidan mai suna Ahmad. Da fitina ta zo shi kuma ba zai lamunta ba. Tun yana lallaSawa da yaga za ta wargaza masa tsari ya sallameta ya bawa Mama Wan. Tun daga lokacin babu wadda ta sake gigin tayar masa da hankali. Zaman lafiya ake da ?ullewar zumunci. Har ta kai idan mace ta haihu wani zubin Wan cikinta ma sai ya yi mata ?yuya saboda kulawar da yake samu a wajen yayyensa da sauran matan. Irin rayuwar nan ta daga ni sai ?a?ana bata da muhalli kwatakwata a gidan Alh. Hayatu.

Bayan Ahmad an Wauki lokaci kafin a sake samun Wa namiji. Don a haihuwa ta tara Hajiya ta haifi Kamaluddin. Yana da wata biyar Inna ta haifi Tajuddin. Bayansa tayi mata biyu sannan ta ?ara da maza biyu Sulaiman (Abba) da Bishir sai ta rufe da mace kuma autar gidan. Wannan yasa mazan su ka tashi a ?ar?ashin yayunsu mata tunda sun zo a sahun ?arshe ?arshe.

Kamal da Taj sun tashi tamkar ?an biyu sakamakon rashin tazarar haihuwarsu. Wasu har basa gane su don hatta pant duk mai sayawa Waya za ta sai wa Wayan. Bambancinsu da aka fi ganewa shi ne doguwar fuskar Taj da gashin fulanin Kamal wanda su ka gado daga uwayensu. Da yake jinin Alhajin akwai ?arfi duk inda ?a?ansa su ke basa Soyuwa. Musamman da cikakkiyar girarsu da ta zama wani sirri na ?arin kyawunsu. Mama uwar ri?on Ahmad ita ce maman mazan gidan. Duk abin da ya shafesu ita ce a kai tun ana goyonsu. Ita take yayesu shikenan yaro ya koma Wakinta.

Za a iya cewa Taj da Kamal wasu manyan jigo ne na farincikin gidan Alhaji. Indai suna gida to in sha Allahu dariya da nishaWi baya yankewa. Zolaya da wasa duk halinsu ne. Har suna su ka sanyawa juna. Kamal ya kira Taj Happy, shi kuma Taj ya kira shi Happiness. Irin faWan nan na sakonni da wuya kaga sun yi. Sannan daga yayyensu har ?anne ba za ka ji wanda ya kai ?ararsu akan sun masa ba daidai ba. Duk kuwa da kasancewar Taj mai tsokana lamba Waya. To amma yana da tsoron yin laifin da za a hukunta shi. Shi kuwa Kamal dama green snake ne. Sai ya yi abu ya koma gefe kamar ba shi ba.

Tun tasowarsu akwai wata irin sha?uwa ta musamman tsakanin Alhaji da Taj. Shi dai da zarar mahaifinsu ya dawo to ya gama wasu wasanni. Yana daga cikin lokutan da akan gansu wuri daban daban shi da Kamal. A gefensa yake zama yana yi masa tambayoyi musamman akan kasuwanci. Nan da nan ya zama sunansa abokan harkokin Alhajin su ka fi sani. Kowa ya buWe baki sai ya ce Taj. Har dai aka fara hannunka mai sanda a gidan ana cewa da alama shi zai gaji Alhajin. Yawan maganar yasa Inna ta fara jin abin yana damunta. Bata son rigima ta Sullo daga Sangarenta. Shi yasa wata rana su na zaune su biyu da Alhajin ta tayar masa da zancen.

"To ke banda abin ki mene ne a ciki? Duk uba ai yana son magaji a fannin da ya yi zarra musamman idan halattacce ne."

Wasa taga ya mayar da zancen ta girgiza kai.

"Kaga yana da yayye. Idan ana cewa magajinka wani zai yi zaton irin abin nan ne na son ture wasu don wata manufa."

Kallonta ya yi yaga sosai ta shiga damuwa.

"Ku mata sai a barku. Tunaninku kullum babu nisa. Musulunci dai ya riga ya gama mana komai. Yau ko dama na kwanta yadda shari'a ta tsara haka za a raba abin da na bari a bawa ?a?ana. Babu wani fifiko."

"Na sani"

"Amma duk da haka kina damuwa saboda kada a ce Hayatu ya fifita Wanki akan na sauran. ?ila ma kina ?arawa da cewa za a zargi ko don mahaifiyarki ?anwar mahaifina ce."

"A'a wallahi" ta ce da sauri.

Ya sake yin murmushi sannan ya Wan tuna mata baya. A gidansu cikin maza su goma sha uku shi kaWai ne Wan kasuwa kamar baban su. Sauran duk aikin gwamnati su ke yi. Shi kuwa ya ajiye kwalin tun daga degree na farko ya rungumi sana'ar gidan ba tare da an tauye ?an uwansa da komai ba. Duk abin da ya tara yanzu arzi?insa ne na guminsa. Ya ma zamana duka ?an uwan nasa duk wanda Wansa namiji ya gama sakandire sai ya tura masa shi kasuwa na shekara Waya. A haka yanzu akwai mutum bakwai cikin ?a?ansu da su ke jikinsa.

"Zan yi maganin damuwar nan anjima idan an zo cin abincin dare."

Bai manta ba kuwa. Dama al'adar gidan idan ba ba?i gare shi ba duka tare ake cin abinci a babban falo. ?an shekaru kusa da juna ake haWawa a kwano guda. Matansa ma yawanci tare su ke ci. Ana gamawa yaran za su nufe shi da bu?atunsu. Ko fensir ne ya karye sun fi gane su sanar dashi. Yana daga zaune zai sa a bashi reza don yafi gane mata ya fi?e. Wasu ya koya musu homework. Masu bu?atar kuWi ko wani abu makamancin haka duk a wannan zaman ake yi. Ana gamawa zai ja su sallar Isha sannan ya tashi. Su kuma daga nan za su Salle da hira. ?ananun da duk mai ra'ayi su tarkata su koma wurin Hajiya indai ba girkinta bane domin jin daWaWan tatsuniyoyi.

"Mal. Bishir wai me ka ke son zama ne idan ka girma?"

Bishir ya Wago kai daga rubutun da yake yi na homework ya kalli baban nasu.

"Shoe shiner."

Falon gabaWaya aka bushe da dariya harda Alhajin. Shekarar Bishir bakwai a lokacin.

Kuka ya soma yi yana cewa "Alhaji kaga suna yi min dariya ko?"

"Rabu dasu. Tambayar ma ta saraya a kanka sai ka ?ara girma. Duk wanda ya sake dariya kuma bana bashi da takalmin sallah. Dama kai zan bawa ka raba."

Da haka ya kawo ?arshen kukan nasa. Ya mayar da tambayar ka ga Abba.

"Babana fa?"

Murmushi ya yi "Alhaji ni police zan zama."

"Ni dai bana son khaki Abba. Don Allah ka zaSi aikin da ba zai dinga hana ni bacci mai daWi ba" cewar Mama.

Alh. Hayatu ya ce a ?yale yara a bisu da addu'a.

"Taj kuma fa?"

Abin nema ya samu. Kowa ya zuba masa ido ana jiran a ji ya ce kasuwanci irin na baban nasa sai ya basu mugun mamaki.

"Chef! Mai girki." Ya ce hankali kwance yana murmushi.

Da yake yafi kusa da Umma a inda yake zaune bata san ma lokacin da ta buge bakinsa ba saboda wani hargitsatsen kallo da Alhaji ya watsa masa.

"Bar dukansa Jamila. Barshi ya maimaita."

Ko War bai ji ba ya sake faWin abin da ya ce da ?warin gwiwa.

"Chef. Mai dafa abinci a restau..."

"TAJUDDIN!!!"

Tsawar ta gigita kowa. ?ar autarsu ma kuka ta saka harda zubar da abincin da aka ajiye a gabanta tana ci da kanta.

"Ku tashi ku bani wuri." Ya faWa a fusace.

Da yake a lokacin sun kai shekara sha huWu shi da Kamal duk da hankalinsu. Shi yasa Taj ya gane abin da ya faWa bai sami karSuwa ba. Bin sahun ?an uwansa ya yi ya tashi.

"Ina za ka? Zama zaka yi ka faWa min me ya burge ka da daudanci har kake tunanin kawo min wannan shaiWancin cikin gida."

A tsorace ya zauna yana kallo kowa ya tashi har iyayensu mata. Alhaji ya Wan sausauta murya don ji yake kamar ya fara duka akan Wan da yake matu?ar danne soyayyarsa. Ya tambaye shi ko ya taSa yin girki a rayuwarsa.

"Abincin da aka gama ci yanzu ma ni nayi miya. Wallahi Alhaji na iya girki sosai. Indai babu islamiyya ni nake na dare."

Sai da ya cije leSe don wani irin sarawa kansa ya yi sannan ya ce "kirawo min uwayenka ka ce su same ni a Waki."

***

A Wakin Hajiya su ka tare su huWu ashe suna ta caccakar Mama. Musamman Umma wadda ta jima da hango Sacin rana a dalilin wannan abu.

"Na sha faWa miki ki hana yaron nan shiga kitchen ki ka ?i. Tun ana Sare maggi har ta kai yana Wora sanwar gidan nan."

Mama da karayar murya ta ce "saboda Allah yanzu a ce mutum yana da yaro amma ba zai koya masa ayyukan cikin gida ba? Girki ai ba lallai sai mace ba. Kuma ra'ayinsa ne tunda duk yadda su ke da Kamal shi ko magin baya Sarewa."

Hajiya ta ce "Amma tun farko kin san Alhaji ya?i jinin ganin mazan gidan nan da tsintsiya ma balle girki. Yana gani yake cewa a daina saka su kada su zama ?an daudu. Ko kin manta tashin hankalin da aka taSa yi akan gugar kuSewa?"

Wata rana ne kusan shekara uku da su ka wuce mai aikinsu ta fita bata dawo da wuri ba. Girkin Hajiya ne ita ma sun fita dubiya dukkansu. Suna dawowa taga ba'ayi tuwon dare ba. Shi ne ta rabawa Ahmad, Kamal da Taj gugar kuSewa ita kuma da taimakon yan matan gidan ta Wora tuwo. Alhaji da ya shigo yaga suna aikin nan a falo ya dinga faWa ba ji ba gani. Sai da ya yi sati baya cin abincin gidan yana kuma gargadi da tuna musu aikin namiji da mace a gida ba Waya bane.

Mama ta Wan kalli Inna da tayi shiru kawai tana kallonsu.
"Ki ce wani abu mana. Ko kema laifina kike gani?"

"Laifi kamar yaya? Neman mafita kawai zamu yi kafin ya tasa mu a gaba don na san..."

Laluben Wakin da Taj ya Waga da sallama ya katse mata magana.

"Alhaji yana kiranku a samansa."

Hajiya kiransa tayi ganin jikinsa duk ya yi sanyi.

"Girki ko a gidanka kana da damar yi Taj amma kada ka sake cewa za ka zama mai abinci ko daWin ji babu. Duk wani namiji mai sana'ar abinci Wan daudu ne. Su kuwa Allah baya son su tunda sun zaSi jinsi kishiyar wanda ya basu."

Kai ya gyaWa kawai ya fice. Sanin cewa zai haWu da Ahmad da Kamal kuma lallai ba za su goyi bayansa ba sai ya gudu Wakin Inna. Wuri ya samu ya kwanta ya rufe idanunsa yana tunani.

Kasuwanci da yake nacin koyo a wurin Alhaji ba don komai bane sai don yana da muradin buWe gidan abincin da yake son ya yi suna. A rayuwarsa babu inda yake shiga yaji kamar an sabunta masa duniya kamar kitchen. Kuma a iya saninsa maza da yawa su na girki. Suna da shekara goma Alhaji ke kai yara Umra. Idan mutum ya yi shabiyar a kai shi Hajji. A Saudiyya in ka cire Takaru babu inda ya ga mata suna sayar da wani abu na ci. Maza ke girkawa su sayar. Maza musulmai magidanta waWanda basu da wata siffa da duk hangen mutum zai danganta su da mata. Idan sana'ar haramtacciya ce ga namiji da waWannan basu kai labari ba. Shi kam yana son girki kuma in Allah Ya so ita ce sana'ar da zai yi.

A Wakin Alhaji kuwa faWansa har falon ?asa. Don ma ?a?an kowa ya shige Waki. Manyan sun haWe kawunansu da ?ananan a Wakunan iyayensu a ?asa.

Ya fusata sosai don ko da su ka shiga Wakin maganinsa na hawan jini yake sha.

"Ni za ku ha'inta? Girkin nan ba yau ya fara ba tunda ya ce shi ya yi miyar dare. Ace ko sau Waya idanuna basu taSa gani ba. Abin da mamaki."

Mama ce ta fara bada ha?uri "na bari ne kawai saboda ganin yawanci gidajen da su ke da yara maza duk ana koya musu girki. Hakan bai sa sun yi koyi da Wabi'un mata ba."

Cikin faWa ya ce mata gidansa babu maza da yawa. A cikin mata ashirin da uku a rasa me yin girki sai maza? Shi yasa yake sanya ido sosai saboda idan ya yi sake tabbas mazan za su iya jin cewa kwaikwayon yayyensu mata ba laifi bane. Ko Wankwali ya gani a hannun Wansa ya dinga faWa kenan.

"Da irin wannan sakacin wani yaro a unguwarmu ana ji ana gani wallahi ya zama cikakken Wan daudu. Gidansu akwai mazan ma amma daga sai ga Habibu ya koma Simagade a unguwa."

Gashi dai faWa yake yi amma faWin wannan suna sai da ya sanya Hajiya da Mama yin ?ar dariya. Umma da Inna dai a murmushi su ka tsaya. Ai kuwa sun janyowa kawunansu sabon faWa. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Musamman Mama da a yau tayi nadamar amsa sunan uwar maza a gidan.

"Dole ki yi dariya mana tunda ba Wanki bane. Da alamu da gangan ma ki ka nemi Sata min rayuwar yaro saboda baki san daWin haihuwar namiji ba."

Ba ita da ya yiwa gori ba, dukkaninsu hankulansu tashi su ka yi. Mama ta saka kuka, Umma da Inna su na taya ta. Hajiya kuwa fi?e idanu tayi ta Wauki ragamar girmanta.

"A'a fa Alhaji. Akan ?a?anka ba za mu lamunci irin wannan ba. Kai ka koya mana zama da juna. Tunda mu ka kai yanzu kuwa wallahi ba za mu yarda ka haddasa mana rigimar da bamu yi da ?uruciya ba."

"Ba akan ?a?ana za ki ce ba. Ki fito fili ki faWa min cewa akan Taj ba za ku yi min biyayya ba." Ya dubi Inna ya cigaba da sababi "wato sai da ki ka ga lamari ya lalace sannan ki ka ankarar dani ri?on sakainar kashin da ake yiwa Wana don kawai ana ?yashin kusanci na da shi."

"Na shiga uku. Alhaji yaushe mu ka yi haka?" Ta faWi a Wimauce ganin ?an uwanta sun zuba mata ido.

Shi a ganinsa babu dalilin da zai sa taji wani War a zuciyarta. Ya riga ya santa da kawaici saboda haka don ana yabon Wanta a tunaninsa bai isa dalilin maganarsu ta Wazu ba. Tabbas ganin rayuwarsa ta Wauko hanyar gurSacewa a hannun uwar ri?onsa shi yasa tayi magana.

Su Hajiya ficewa su ka yi aka rasa mai tambayarta abin da ya faru ma. Tana kuka ta tashi za ta bisu domin kwance wannan Wauri da maigidan ya yi mata ya hanata fita. Dama girkinta ne. Sai kawai ya ce idan ta fita daga Wakin ba da yawunsa ba.
RAYUWA DA GI?I 4


Batul Mamman=ؖ?



***

Manyan gidan a wannan rana basu ga bambancin dare da wuni ba. Kusan babu wanda ya runtsa tsakanin maigidan da matansa. Abin da yake faruwa ba?o ne a wurinsu. Basu saba da rigima ba sai gashi dare Waya ana gab da samun gagarumar Saraka.

Ita dai Inna daga sallar asuba ta fake da Wora kunun karin kumallo ta sauko. Bata zame ko ina ba sai Wakin Mama. Akan sallaya ta sameta idanu sun kumbure. Jikinta a mace ta fita ta kira Umma da Hajiya su ka dawo Wakin tare. Kai a ?asa ta labarta musu ainihin yadda su ka yi da Alhaji jiya.

"Ni wallahi ba da wata manufa nayi maganar ba. Na tashi gidanmu babu ?an uba amma tsakanin yayyena sai babba ya kau ta hanyar aure ko barin gari sannan mai bi masa yake Waukar ragamar gidan. Ban san gudun kada a gaba yaran nan su sami raunin zumunci a dalilin haka ni zai jawowa matsala ba."

Umma ta kalleta babu wannan fara'ar ta kodayaushe
"To amma me ki ka gani a gidan nan da yasa ki tunkarar Alhaji da zancen? Cikinmu wata ta canja miki ne kuma ta nuna saboda kusancin Alhaji da Taj tayi haka?"

"Ko kusa. Nayi masa magana ne kawai akan ya dinga nuna sauran ?a?an musamman Ahmad da Kamal da su ke manya kamar yadda ya nuna shi."

"Maganar girkin fa?" Umma ta sake tambaya don ita so take a warware komai.

"Yadda ba ku Wauke shi laifi ba nima ban Wauka ba. Wallahi ko kusa ni ban yi masa zancen da ya shafi haka ba. Ba gashi a ranar girkina ya yi miyar ba?"

Wata tambayar Umma ta so yi Mama ta katseta.

"Ni ban sakawa raina komai ba. Jiya Hajiya ta ?ara min nasiha akan idan muka bari wannan maganar ta girmi haka to zaman gidan nan zai daina yiwa kowaccenmu daWi. Saboda haka zance ya wuce."

Inna sai godiya da farinciki. Bata fita daga Wakin ba sai da su ka koma wata hirar ana ta dariya. Da rana su ka kira Taj cikin lumana su ka rarrashe shi akan ya yar da wannan buri don ba mai yiwuwa bane. Mama tayi masa nasiha sosai akan yiwa iyaye biyayya.

"Ka cigaba da bin Alhaji kasuwa ranakun da babu makaranta amma daga yanzu tsakaninka da kitchen sai hange. Don Allah kada ka bari zancen nan ya koma tasowa a gidan nan."

Nuna musu ya yi kamar maganar ta mutu, ashe suma tayi.

Shi da Kamal sun kammala sakandire suna da shekara goma sha shida da sakamako mai kyau. Alhaji kamar ya zuba ruwa a ?asa ya sha ranar da su ka kawo takardunsu. Dama tuni ya tura Ahmad ?asar India inda yake haWa degree Winsa a fannin Computer Science. ZaSi ya basu tsakanin Dubai, India ko China. Burinsa su zaSa cikin ?asashen da su ke cibiyar kasuwanci.

"Alhaji mun fi son zuwa wurin Yaya." Cewar Taj.

Kamal ya yi Taj wani irin kallo sannan ya ce "ni dai Dubai."

Kallonsu ya yi a tsanake. Da wuya zaSinsu yake bambanta. Bai kuma saka ran samun haka ba ta Sangaren karatun da zai rabasu na ?an shekaru.

"Anya kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login