Showing 102001 words to 105000 words out of 182745 words

Chapter 35 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

111

yi masa ?arya sannan kuma baya son faWa masa gaskiya. Idan ya faWi gaskiyar girmansa da kullum yake tattali ne zai zube. Daga baya ne ya tausaya masa da yawan wayar ya Wauka ya ce ya ?ara wata guda. Saboda wasu uzurirrika da su ka taso masa. Alh. Mukhtar dai tunda ya sami amsar bawa Mami hankalinsa ya kwanta.

"Nufinsa sai waccan yarinyar ta tare sannan zai auri Salwa?"

"Ina laifi?"

"Ai kuwa akwai shi tunda nima ban zauna da kishiya ba. ?ata ma daga ita sai miji."

***

Girki ya faWo kan Inna ranar Juma'a. Da ta haWa abincin Alhaji Bishir na shigowa ta ce ya kai masa. Kuma bata le?a Sangaren ba kamar yadda su ka saba. Mai girki za ta je ta zuba masa abinci su yi hira. Idan ya gama ta aikawa sauran matan cewa ya dawo. Duk za su zo a Wan taSa hira sannan su tashi.

Abinci ya yi kusan awa guda Alhaji yana kallonsa. Ga yunwa ga gajiya amma ya?i zubawa. So yake yaga iya gudun ruwan Zainabu Abu. To dai tun bayan masallaci har la'asar bata shigo ba. Da ya dawo daga masallaci cikin gidan ya shiga ya wuce Wakinta. Jallabiya ce a jikinsa yana danna counter mai fasalin carbi ta sama.
Babu kowa a falo. Ya shige uwar Wakin. Yana sanya ?afa ita kuma tana Wora waya a kunne. Don ya san da wa take magana ta kira Taj da sabon suna.

"Angon Hamdi"

A tunanin Alhaji ko da gangan ta Wauki wayar. Hannu yasa ya karSe. Ganin sunan Taj da gaske sai ya mi?a mata. Ita kuwa ta saka speaker yadda ta saba idan ita kaWai ce a Wakin saboda wayarsu bata ?arewa da wuri.

"Inna kina ji na kuwa?"

"Me ka ce?"

Bai san yadda za ta Wauki maganar ba amma dole ya auki shawarar Kamal yau. FaWan da su ka yi da Hamdi a motarsa Allah ne kawai ya bashi ikon mallakar kansa ya buWe mata ?ofa ya ce ta fita. Daga zuwa kai mata kati cibi ya zama ?ari. Saboda yau ta iya bakinta bata ce komai ba shi ne ya ce ba a yi mata tarbiyar godiya ba. Ai kamar jira take. Tunda ta buWe baki ta fara surfa rashin kunya sai da yaji inama bai je gidan ba.

Gyaran murya ya yi "na ce ko za a fasa bikin?"

Alhaji da ya kama hanyar fita sai gashi ya dawo. Inna tayi sauri za ta mayar da wayar iya kunnenta ya harWe fuska. TaSe baki tayi a ranta ta ce ana so ana kaiwa kasuwa. Dama taji yadda ya rikice da yaji bashi da lafiya.

"Kai da ka san baka son biki ne yasa ka bari mu ka zazzage asusunmu? Ha?uri za ka yi kawai."

"Uhmmm, Inna ba bikin ba. Auren nake nufi."

Bata san lokacin da ta gyara zama ba.
"Ka fara shaye shaye ne? Auren? Saki fa kenan."

Baya son yawan tada maganar don ransa ?ara Saci yake. Amma dolensa ya faWa mata gaskiya.

"Matsaloli muke ta samu. Kullum sai mun yi faWa."

"Wannan shaiWan ne kawai. Ku dage da addu'a." Ta ce, hankalinta ya soma kwanciya.

"Inna har marinta nayi."

Shiru ya yi yana jiran yaji me za ta ce. Ta kalli Alhaji shi ma ya kalleta.

"Taj ka sameni a gidan Yaya Malam (yayanta na biyu.)"

Ta mi?e ta dubi Alhaji da ya yi tsaye kamar an dasa shi.

"Ka yi min izinin fita?"

"Jeki."

Hijabi kawai ta Wauka ta fita ta shiga Wakunan su Hajiya ta ce musu ga inda za ta je. Duk su ka bata sa?on gaisuwa ga iyalin gidan. Direba ta kira su ka tafi. Aka bar Alhaji da tunani. Yadda hankalinsa ya tashi sai da yaji kamar ya ce Taj din yazo gida. Abin da mamaki ace wai shi ne da marin mace. Wace irin tarbiyya Habibu ya yiwa ?a?ansa?

*

?asa da awa guda uwa da Wa su ka keSe a falon maigidan. Taj ya zayyane mata abubuwan da su ka faru. Bata ko tambaye shi me ya kai shi tafiya da Hamdi wurin sana'arsa ba.

"Idan na fahimta da kyau tun daga zuwan Salwa ku ka fara faWan?"

"Haka ne. Na so yi mata bayanin babu komai a tsakaninmu amma ta rufe ido tana gaya min maganganu."

Inna tayi salati sannan ta ce "ya maganar azkar? Kana yi?"

Kai ya sunkuyar "ina yi."

"Ni da kai ne Taj. Ka faWa min gaskiya."

"Allah ina ?o?artawa Inna." Ya kuma faWa don ta yarda da shi.

Aikin gama ya riga ya gama. Ko yana yi dama ba zai hana ?addara da ikon Allah faruwa ba. Sai dai ya sau?a?a.
GargaWinsa tayi akan kada ya yarda su sake haWuwa. Wayar ma ko ita ta kira kada ya Wauka. Sannan mafi mahimmanci ya tabbatar kalmar saki bata shiga tsakaninsu ba.

"Ka tashi ka tafi. Za ka ji ni in sha Allah idan mun gama magana da Yaya Malam. In ma sihiri ne to in sha Allah zai koma ya ci mai shi. Addu'a, sadaka, qiyamul laili da hanyoyin neman kusanci da Allah nake so ka runguma kaji ko?"

Ya gyaWa mata kai kamar yaro.
"Ki yi ha?uri na tayar miki da hankali. Alhaji ya kamata na nema..."

Wani irin tausayinsa ne ya kama ta. Ta dafa kansa tayi masa addu'o'in neman tsari wanda Ayatul Kursiyyu ke kan gaba. Sai da ya tafi ta fashe da kuka. Duk ya wani rame. Kana ganinsa ka san hankalinsa ne ba a kwance ba. A gidan ta zauna har yayan nata ya dawo ta faWa masa. Ya kwantar mata da hankali.

"Kada ki ?ulla sharri akan wanda ki ke zargi. Shi zargi dama bashi da kyau a addini. Zan kira shi ya zo gobe in sha Allah."

"Yaya har zasu yi lafiya kafin bikin?" Ta tambaye shi da damuwa.

"Ke ta biki ma kike wato?"

"A'a, tsorona kada ta tare yadda yake cewa yana jin kamar yayi ta dukanta yaje ya lahanta ?ar mutane."

Kwantar mata da hankali ya yi.
"Allah zamu ro?a ba mutum ba. Shi kuma ba ayi maSa gaggawa. Tunda ya ce idan mun ro?a zai bamu to ki saka ranki a inuwa. Ko daga ina matsalar take bata wuce Qulhuwallahu, Falaqi da Nasi ba."

Da ?warin gwiwarta ta fita daga gidan. A ranar yadda ta hana idonta bacci haka ta tada Taj. Shi kuma ya sami kansa da turawa Hamdi sa?o.

(Idan Allah Yasa kin gani kafin safiya ki tashi ki yi sallah da addu'a. Idan akwai alkhairi cikin aurenmu Allah Ya warware mana matsala.)

Sai uku da rabi ta gani da ta tashi fitsari. Ta Wauro alwala ta zauna tana ta kuka. Zee na jinta amma ta ?yale. Yaya ce ta bata aikin sanya mata ido saboda kwanakin nan kowa ya san ta canja.

A Sangaren Alh. Hayatu kuwa, yana ganin shigowar Inna ya kira Yaya Malam.

"Ka biyo sahun Wanka ne?" Malam ya faWi kai tsaye domin duka gidansu dai haushinsa su ke ji.

Murje ido ya yi tunda in ba a nan ba babu wanda zai tambaya kuma
"A gabana ta fara wayar shi yasa. Da gaske ya mari matarsa?"

"?warai kuwa."

"Kaga abin da nake faWa ai. Namiji mai irin sana'arsa fa ji yake kamar shi ma mace ne. Shi yasa yake daidaita tunaninsa da nata. Cikakken namiji ba zai fara kai hannu daga aure ko wata ba ayi ba."

Yaya Malam dai dariya kawai ya yi. Ya shaida duk wata rigima da yake yi bata yi tasirin hana shi son Wansa ba. Abin da yaji ya faWa masa. Ya yi godiya su ka yi sallama.

Washegari ya san da zancen kai lefe da maza za su yi. An kira shi ya gani bayan an kammala komai. Harda akwatuna huWun da Amma ta taho dasu waWanda kayan ciki su ka amsa sunan kayan ?ar gata. Tunda ba dashi za a yi ba babu wanda ya sa masa ido da ya yi sammakon fita. Ko matansa bai faWa musu inda za shi ba. Ya dai yi musu sallama ya fice. Yana zama a mota ya ce da direbansa Bauchi za su je.

"Bauchi Alhaji?"

"Ba ka san hanya bane?"

Da sauri ya hau bada ha?uri "na sani. Allah Ya kai mu lafiya."

"Amin"

Zuciyarsa a baka take da Sacin rai. Bai runtsa ba jiya tunda ya yi waya da Yaya Malam. Arzi?in rabon Ahmad dake tsakaninsa da Mami yasa ba zai haWata da hukuma ba. Amma tabbas sai tayi nadamar kai Wansa gaban ?an iskan bokayenta. Bai san bata da masaniyar abin da Salwa tayi ba.

***

Tun dare ?ar Ficika da yaransa su ke aikin kayan kwalamar da za a tarbi masu kawo lefe dasu. Shi ya ce da Abba lallai ko ruwa kada ya siya. Za su kawo komai.

"Abin zai yi yawa. Don Allah kada ka wahalar da kan ka. Kada ka manta girma fa ya cimmana."

Yar Ficika ya karya kai yana ri?e da ?asan jallabiyarsa.

"Haba Simagade, ina aikin yake a nan? Ai idan daWin miya bai karya ludayi ba, wahala ba za ta karya guga ba. Ka ganni nan..." ya bubbuga ?afa a ?asa "digirgir nake a tsaye. Abin da zan yi in daWaWa maka ba zai taSa zame min wahala ba."

Abba ya yi masa godiya. ?ar Ficika ya koma cikin kitchen Winsu inda ake ta yanka naman kaza. Guda cikin yaran ya samu yana gyara wutar gashi.

"Tasalluwa me za ayi da wannan uban garwashi?"

"Ba gasa naman za ayi ba?"

Duka ?ar Ficika ya kai masa a ?eya "sai shegen rawar kai yawa akwalan keke. Abin da ya kamata ba shi kake yi ba. A zafin nan za a gasa nama tun yanzu a ajiye? Ba sai ya buga ba?"

Tasalluwa ya Sata rai "daga abin arzi?i?"

"Idan aka basu naman yana hamami ai raini za ka jawowa Wiyar tamu. Ko baka san Wan Alh. Hayatu Maitakalmi take aure ba?"

Tasalluwa ya tafa hannuwa "eyyee, ashe abin babba ne, wai an kashe kwarkwata da taSarya. Aikin na bajinta zamu yi."

Wani dake kusa yana jin hirar tasu ya ce "ai ke dai Allah Ya kawo kuWi talauci yaji kunya. Nan da lokacin da za ta haihu kaji hamsin za mu babbake ba ashirin ba."

"Ahayyeeee"

Su ka dinga tafawa ana tsara irin girkin da za ayi idan Hamdi ta haihu. A cewarsu aikin yau ba ayi yadda ya kamata ba saboda tsadar rayuwar da ake fama. A haka kuma ba ?aramin ?a?ari ?ar Ficika ya yi ba. Kaji ashirin za su yiwa gashin tukuba, meatpie, donut da cake duka guda Wari Wari yaran da su ka ?ware a nan fannin su ke yi. Sai abincin gargajiya. Tuwon shinkafa da miyar gyaWa da kabewa wadda taji naman rago da alayyahu, waina, funkaso da alkubus kuma da farfesun kai da ?afar rago. Sai lemon ginger da zoSo da su ka ?ware wajen yi ana zubawa a sababbin robobi masu tambarin sunan gidan abincin nasu. Shi dai ya ha?ura ya san ya makara, da wuya ya haifa. To amma fa wanda Simagade ya haifo musu sai inda ?arfi ya ?are.
RAYUWA DA GI?I 26





Batul Mamman=ؖ?






***

Shirin fita zuwa wani katafaren wurin gyaran jiki da Amma ta biya kuma ta ce za ta turo direba ya Wauki Hamdi kafin ?an kawo lefe su iso take yi. Zee da ?anwar Anti Labiba mai suna Fadila ne ?an rakiya. Komai cikin mutuwar jiki take yinsa musamman da jiya bata sami isashshen bacci ba. Tayi ibada kuma tayi kuka sosai. Yawanci akan ce asiri birkita tunanin mutum yake yi har ya kasa gane ta?amaimai me yake damunsa. Halin da take ciki kenan yanzu. Tana son Taj, sannan kuma tana gudun kasancewa inuwa guda da shi.

A daren jiya ne da tana addu'a ta fara mamakin wannan sabon al'amari da ya tunkaro su. Ala?arta da Taj ba irin wadda ake shan wahalar farata bace. Lokaci guda su ka yi clicking kamar hagu da daman mayen ?arfe. Irin wannan rashin sakewar kafin a saba duk basu fuskanta ba. Lokaci guda su ka karbi juna a sabon matsayin da Allah Ya ajiyesu.

"HAMDIYYA!"

Firgigit ta dawo hayyacinta da jin kiran Yaya da ?arfi.

"Tunanin me kike yi haka?"

"Babu komai" ta mi?e tsaye tana neman mayafinta.

"Me ki ke nema?" Yaya ta tambayeta.

"Mayafina."

"Wanda ki ka yafa kuma fa"

Kallon jikinta tayi ta ce "au..."

"Zauna Hamdi. Magana za mu yi."

Bata kawo komai ba tunda a tunaninta ta Soye yanayinta sosai ta zauna. Yaya ta tsareta da tambayar me yake damunta kwana biyu. T?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? a fara rantse rantse Yaya ta ce bata san zance ba.

"Idan ba wata uwar gareki a waje wadda ta dace da sanin damuwarki ba ina son sanin me ya sanyaki kwana kina sallah da kuka."

Gaban Hamdi faWuwa ya yi. Ba za ta iya faWawa kowa Taj ya mareta ba. Haka kawai take ganin kamar za su yi rabuwa ta har abada idan aka sani.

"Yaya babu komai."

"Kina ganin saboda lalurata da yanayin Abbanku bamu isa mu share miki hawaye idan kina da damuwa ba ko?"

?acin ran uwa abin gudu. Nan da nan hankalinta ya tashi ta soma bata ha?uri.
"Ki daina faWin haka. Wa nake da shi bayan ku?"

Da wata irin murya mai ban tausayi Yaya ta ce "Ba yau ki ka fara ba. Tun ?uruciyarki na san kin tashi da ganin kamar bamu cika iyaye ba."

Kuka sosai Hamdi tayi. Wannan banzan tunanin tun yaushe ta ajiye shi. Ummi ta ankarar da ita girman mahaifinta a lokacin da take ganiyar gudun a ala?antasu. Yaya ce dama tun farko bata taSa rainawa ba. Tana son abarta a yadda take. Wannan furucin da tayi ne dai ya sake karyar mata da zuciya tayi ta kuka tana bata ha?uri.

Bayan wani Wan lokaci da Yayan ta ce ta ha?ura shi ne ta faWa mata rabin gaskiyar zancen. Akwai mai son Taj, ta dawo da wayar da su ka taSa yi ta ce ai matar har kiranta tayi ta tsorata ta.

"Wai idan na yarda na tare sai ta illata rayuwata."

Dariya taga Yaya tayi kafin kuma ta ce,

"Shi ne kike kuka? Kodayake Allah ki ke gayawa. Ya isar miki akan komai. Duk da haka cewa Yayi ka tashi In taimakeka. Kada ki yarda wata mace ta zama silar hawayenki a gidan miji."

"Ko da yafi sonta?" Hamdi ta tambayeta tana kuka.

Da yake Yaya bata saba ganin ?ar tata ta nuna rauni irin haka ba sai take ganin son da take yiwa Taj ne kawai bata son abin da zai shiga tsakaninsu. Kalaman da za su kwantar mata da hankali ta zaSo. A cikin ranta kuma tana ?udurta yi mata addu'a da sauran ?an uwanta akan kada Allah Ya haWa mazajensu da matan banza.

"Yafi son nata ya aureki? Ko kin manta ba tayinki aka yi masa ba?"

"Haka ne."

"Ki cigaba da addu'a sannan ki dage ki ?waci kanki a gidan aure. Mu bamu san boka da malami ba. Kuma bamu san makirci da sharri ba. Indai kin tsaya a tarbiyar musulunci ta zaman aure da kuma ri?o da dabarun zaman duniya za ki ga baki da yawan damuwa."

Kai tsaye ta ce "Yaya kin koya mana dabarun zaman duniyar ne?"

Yaya tayi dariya "Hamdi kenan. Da gaske ki ke son kare martabar aurenki. Hakan ya yi kyau. Lusarar mace bata taba burge miji dama." Ta gyara zama "su dabarun zaman duniya yau ce take koya maka. Sai kuma amfani da dama idan ta zo da kuma zurfafa tunani da hangen nesa. Sauri ko gaggawa a komai Sata lamura suke. Saboda haka don wata ta kira ki tana surutu kada ki yarda ya zama dalilin da za ki ce kin gama aure ko kin bar mata miji. Ki ?o?arta. Sai idan kin yi naki kin ga mijin ?wallon mangwaro ne sannan za ki jefar dashi ki huta."

Ji tayi kamar an sauke mata dutse daga zuciyarta. Ta faWa jikin Yaya tana dariya mai haWe da jin kunya. Yaya ta rungume abarta tana shi mata albarka. Da Zee ta le?o domin ta faWa musu zuwan direban da zai ka su tayi mamakin yadda ta gansu.

"Wallahi nima sai anyi dani."

Ta daka tsalle dama idan shirmenta ya motsa sai addu'a, ta faWa kansu. Sai washhh Win Yaya kawai kake ji tana cewa su tashi za su Salla ?ashin da bashi da ?wari.

***

Cikin ginin wani kamfanin robobi wanda a halin yanzu shi ne dukiyar ta?amar Alh. Mukhtar da iyalinsa direban Alhaji ya shiga. Akwai mota a gabansu ta wasu manyan ?an kasuwa guda biyu wanda su ma direba ne ya kawo su. Su ne su ka yi musu jagora har wurin.

Da su ka firfito da girmamawa su ka zo wajen motar Alh. Hayatu su ka sske tarbarsa tunda dama a hanya su ka haWu da farko.

"Alhaji ni fa ka sanya ni a duhu da ka ce mu faWawa Alh. Mukhtar lallai ya tafi kamfani yau duk da asabar ce kana son ganinsa. Allah Yasa lafiya dai." Cewar guda daga cikinsu.

Fuskar Alh. Hayatu babu fara'a ko Wigo ya ce masa "lafiyar kenan. Yana da kyau mutum ya dinga zaga dukiyarsa ne saboda halin rayuwa."

"Shakka babu uban Kantin Kwari da kewaye." ?ayan ya Waga hannu yana jinjina masa

"Ka san na faWa muku akwai wata ala?a tsakanina da shi."

"?warai kuwa. Saboda ka ce kuna da dangantaka. Lokacin kuma mu duka bamu shirya barin kasuwa mu zauna a nan ba mu ka bashi. Yanzu gashi cikin ikon Allah ya mallaki kaso ashirin da takwas cikin Wari. Kasuwa tayi albarka, shi yasa mu ka bari ya zama partner Winmu." Na farkon ya yi bayani a ta?aice.

Alhaji ya gyaWa kai yana tuno wasu ?an shekaru a baya. Lokacin Ahmad bai yi aure ba amma idan ka ganshi tamkar mai mata huWu da ?a?a goma. Ya fige tamkar kazar mayu. Kullum yana rama ga zafin nema kai ka ce wani yake ciyarwa. Matan gidansu su ka shiga damuwa. Alhaji ya tsananta bincike domin a lokacin Ahmad ?in faWa masa gaskiya yayi. Ashe karayar arzi?i ce ta sami Alh. Mukhtar. Mami ta taso shi a gaba. Ashana wannan idan suna bu?ata sai ta kira Ahmad. Ita bata yarda tayi rayuwa daidai da samun mijinta ba a lokacin. Ta ?untatawa yaron iyakar ?untata. Duk wata kadara da Alhaji ya mallaka masa ya sayar ya bata kuWin. Idan babu yawa tayi ta bala'i da kiran za ta tsine masa.

Ranar da Alhaji ya san gaskiya sai da ya yiwa Wansa hawaye saboda tsabar tausayinsa da yaji. Gashi kuma ya san cewa ba huruminsa bane raba Wa da uwa. Shi yasa bai taSa hana Inna mu'amala da Taj ba. Gidansa kawai ya hana shi shiga. To dama ya san da maganar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login