Showing 36001 words to 39000 words out of 182745 words

Chapter 13 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

96

a hankali ta ?ware wajen yin doughnut, samosa, meatpie, springrolls, chinchin irin na ?an gayu, gashin nama da kifi kala kala. Da kuma uwa uwa haWaWWen plain youghurt, coconut infused youghurt da yogo fura.

A gida irin farincikin da Anti Labiba ke gani a tare da ita har mamaki take bata. Mijinta ma sai da ya ce wai gani yake kamar an canja ta da wata. Yaran gidan kuwa tunda an yarje mata gwada abin da ta koya, sun kwashi gara ba kaWan ba. A ci a gida kuma aje makaranta.

***

Wannan wata gudan harda ?an kwanaki a Sangaren Taj cikin wahala su ka zo masa. Kacokan ya ajiye aikinsa bayan ya wayar nan da ya yi da Hajiya. Ya karkata akalarsa zuwa ga son lallai sai Abba yayi aiki tare da shi. Kamal da yaga ba zai iya hana shi ba sai ya bashi goyon baya.

Ranar farko tun safe ya shirya yaje ?ofar gidan Abba. Bai aika a sanar da zuwansa ba. Ya yi zamansa a cikin mota har Abban ya zo fita sannan ya tare shi. Ai kuwa yana ganin shi ya sauya fuska.

"Baka sami sa?ona a wajen Wan uwanka ba?"

Gaishe shi Taj ya yi. Bawan Allah yana faWan ya tsahirta ya amsa sannan ya cigaba.

"Bana son rigima da mahaifinku. Ban san me ku ka ji game dani ba. Amma ko ma mene ne nufinku ni da Allah na dogara."

"Don Allah ka saurareni. Da alkhairi na zo maka."

Cikin gida Abba ya koma. Bai ?ara fitowa ba har la'asar. Taj ya tafi amma bai karaya ba. Washegari ma ya sake zuwa. Ranar Abba ko sauraronsa bai yi ba ya wuce ya yi tafiyarsa. A haka su ka cinye sati guda. Wasu kwanakin duk sammakonsa idan ya zo zai samu Abban ya fita kafin ya zo.

A kwana na tara Taj sai ya canja tsari. Tare su ka zo da Kamal wanda ya ce zai bada ha?urin abinda ya yi kwanaki. A zatonsa ko shi yasa Abban ya?i sauraron Taj. Yaro ya tura ya ce a faWawa Abba su Taj sun zo kuma wallahi yunwa suke ji.

Sajida ce kaWai a gida da Yaya. Halifa da Zee suna makaranta. Sajida tana jin sa?on yaron ta figi mayafi ta fita. Yaya tana ta kiranta ta?i dawowa. Abba kuwa ?wafa ya yi.

"Bawan Allah zamu haWaka da ?an sanda wallahi. Bar ganin kuna da kuWi" ta harare su duka "wallahi muna da masu tsaya mana mu kara daku a hukumance."

"Ki yi ha?uri ?anwarmu. Aiki kawai ?anina yake son yi tare dashi. Shi ma sana'ar girki yake."

"To ya ce baya so. Ai.ya faWa mana ko ku su waye." Ta ce da tsiwa.

"?an tsaya mu yi magana" Taj ya ce bayan ta gama magana. Tsayuwar tayi tana karkaWa ?afa ita a dole ranta ya Saci.

Tarihinsa ya bata a ta?aice.
"I believe yadda nake son in dawo da ?imata a wurin Alhaji haka Abbanku zai so mutane su yi masa uzuri su karSi sabuwar rayuwar da ya gina."

Cikin mutuwar jiki ta ce "haka ne."

"Ina son yin aiki da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Abba amma a setting da ya bambanta da wanda ya saba. A inda maza masu yin komai na maza su ke girki. Burina idan an kwana biyu rayuwarsa tayi daidai ta yadda masu aibata shi a bayansa za su ji kunyar abin da su ka yi."

?walla ta saukowa Sajida "zai yiwu? Kana ganin wannan abubuwan na mata za su barshi?"

Kamal ya sanya baki "Allah aka ce. Ba yadda za ayi ka bar kowa ka kama Shi sannan kasa rai da ganin ba daidai ba. Taj only wants to help."

"Mece ce ribarsa idan ya taimaka masa?"

"Mutane su fahimci akwai sana'o'in da basu keSanta ga mata ba kawai. Sannan ?yama ba ita ta dace da irin wanda ya yi rayuwar Abba ba. In an bi hanyoyin da su ka dace shi ma zai karSu a cikin mutane kamar kowa" Kamal ya sake bata amsa.

Abin nema ya samu Sajida ta koma gida da murnarta. Abba na ganin hawayenta ya tashi.

"Me su ka yi miki?"

Ta fashe da kuka "don Allah Abba ka sauraresu. In sha Allah wannan wahalar neman wurin hayar zai ?are."

Fita ya yi ya sallame su. Taj sai ya ?i motsawa.

"Zan sa a nemo min mahaifinka ya zo ya tafi da kai."

"Zan tafi amma don Allah ka bani abinci. Yunwa nake ji."

Abba ya kallesu. Duk sun yi laushi.

"Ba ku karya bane?" Ya tausasa murya. Sai muryar tasa ta sake yin ?asa.

"Ni dai na sha tea. Happy kuma bai ci komai ba."

Abba ya kalli Taj da mamaki "Happy kuma?"

"Eh. Sunansa kenan" Kamal ya bashi amsa.

"Yana sallah kuma?" Abba ya tambaya harda matsawa baya.

Me kuwa za su yi banda dariya. Taj yana yi ya ri?e ciki. Abba ya sami kansa da yin murmushi bayan sun yi masa bayanin sunayen nasu.

"Innza ku ci ko indomie ce sai na karSo a shago Sajida ta dafa muku."

"Don Allah abinci muke so. Wanda ka girka." Taj ya ce da sauri.

Girgiza kai Abba yayi yana Wan murmushi.
"Ku jira nayi muku iso a ciki."

Sajida ce ta le?o ta kira su bayan ya shiga ciki. Aka yi musu shimfiWa a tsakar gida. Yaya ta fito da lulluSi su ka gaisa. Taj ya dinga kallon gidan yana ayyana wai fa a nan yarinyar nan da ya gani take rayuwa. Yana son tambayar ina take amma dole ya kama bakinsa.

Abba ya shiga kitchen suna iya hango duka motsinsa ta tagar dake tsakar gidan. Kai kawo kawai yake yi cike da ?warewa. Yaya da Sajida kuma suna jansu da hira jefi jefi. Kamal ne kaWai yake amsawa. Hankalin Taj ya yi kitchen. So yake kawai yaga yadda Abba yake aiki.

Yaya ce ta lura da hakan ta yiwa Abba magana. Yaran sun burgeta saboda babu girman kai a tare dasu.

"Nace ko za ka bari ya shigo ciki ya taya ka?"

"A'a, nagode."

Taj ya tashi "gani kawai zan yi. Ba zan saka hannu ba."

Sai bayan fiye da minti Waya sannan Abba ya ce ya shigo amma iyakarsa ?ofa. Ai kuwa da saurinsa ya shiga. Aikin daWewar shekaru wato experience yafi aikin iyawa. Taj yaga abin mamaki a tattare da kuzarin dattijon. Ga tsafta don ko ledar maggi babu a ?asa. ?amshi mai rura wutar yunwa ya cigaba da matse masa hanji.

Fried spaghetti ce yayi musu babu nama a ciki sai busasshen kifi. Ya juye a tray. Sajida ta kawo musu. Sannan ita da Yaya su ka koma falo. Samarin Alh. Hayatu su ka zauna suna zuba santi har su ka cinye.

Da za su tafi ne Taj ya bashi nambar wayarsu rubuce a takarda.

"Don Allah Abba kayi shawara."

"Naji. Ku tafi."

FaWan nasa bai hana shi raka su har mota ba. Kuma ya?i tafiya har su ka bar layin. Yana komawa gida ya samu Sajida tana naWe tabarmar da su ka zauna. A ?ar?ashinta sai ga farar takarda. Ta mi?a masa ya buWe. Ro?o da magiya ne daga Taj. Sai kuma ?arin bayani game da restaurant Winsa.

"...idan ka amince za ka yi aiki dani, zan kama mana wuri inda za mu yi developing recipe kafin a gama ginin. Bana son yin business Win da zai rushe kafin yaje ko ina. Ka taimaka min..
Happy Taj"

Da Yaya su ka zauna shawara. Sai dai washegari da kwanakin da su ka biyo baya kullum sai Taj yaje cin abinci. Har su ka yi masa kwano. Tun Abba yana basarwa har dai ya karSi tayin da yayi masa. Ba kuma komai ya janyo haka ba sai rasa wurin da zai kafa sana'arsa. Duk inda yaje sai an biyo shi da ?abali da ba'adi wanda shi ya san gaskiyar dai ita ce Wan daudu ne. Ba sa ma damuwa da jin ko ya daina. A gida idan yace zai yi kuma akwai iyalinsa da ba zai so mutumcinsu ya zube ba.

Haka dai bayan kwanaki yana kai gauro da mari ya ce ya amince. Ya kuma du?ufa addu'ar neman taimakon Allah.

A lokacin kullum Hamdi tayi waya da gida sai anyi mata zancen Taj. Yaya da ?an uwanta sunansa a bakinsu raWau. Ita kuwa lamarin bai burgeta ba. Wanda zai zo ya mayar da Abbanta cikin sana'ar girki ba masoyi bane.

Su Taj da su ka tabbatar sun sami kan Abba sai aka fara shirin zuwa wajen Anisa. Lokacin bai fi kwana goma ya rage masa ya koma ba. A motar Kamal su ka tafi. Da yake ya san gari basu wahala ba da bin kwatance ta google map su ka isa gidan.

***

Aikin snacks da Anti ta ce a tanada saboda zuwan su Taj, Hauwa aka bawa. Hajjo tuni ta fesa musu dalilin zuwan nasa. Anisa sai murna. Sai dai anyi rashin sa'a ana gobe ranar tafiya ta kama ta. A waya ta basu ha?uri ta ce amma akwai Walibarta da duk abubuwan da su ka zayyano za ta iya ba tare da sun ji bambancin taste ba.

"HaWani da ita" Anisa ta ce don in ba kayan Luciousbites ba, bata ganewa snacks Win.

A waya aka gama komai. Hamdi murna da godiya ta dinga yiwa Hauwa. Ita kuma ta dinga ro?onta kada ta kunyata musu brand.

?o?ari kam bakin gwargwado tayi. Meatpie, doughnut da samosa su ke so. Sai coconut infused youghurt. Shi ne kaWai Hauwan ta aiko mata da shi. Sauran kuwa babu komai a ?asa dole sai anyi. Bayan ta gama ta kira numbar Anisan da aka bata ta sanar da ita an gama komai.

"To ki bawa mai delivery. Zan turo address."

Nan fa Waya. Bata san kowa ba. Anti Labiba ma ta dinga kiran mutanenta amma kowa sai ya ce mai delivery baya kusa. Hamdi ta kuma kiran Anisa. Lokacin ita kuma bata jima da yin waya da Taj ba. Yana ?ara neman kwatance. A yadda ta ?iyasta bai fi minti goma zai kawo su gidan ba. Gashi babu wanda za ta iya aika. Gari an tashi da rashin mai. Duk wata motar gidansu tana layi sai guda Waya ta Daddy.

"Hamdiyya ko za ki Wauko bolt ki kawo min. Zan biyaki kuWin tranport Win. Fitar ce babu halin yi yanzu."

Hamdi ta faWawa Anti Labiba. Su ka rasa yadda za su yi. Mijin Anti Labiba a wajen gari yake aiki. Ita kuma babu mota. Tayi shahada kawai ta samarwa Hamdi bolt Win.
RAYUWA DA GI?I 13




Batul Mamman=ؖ?



Kada ku manta da bibiyar shafin Hauwa a instagram _@luciousbite.ng_ ko nemeta a waya ta wannan layin domin
_09078075182_ odar snacks da nau'ikan youghurt masu daWi.





***

Irin rawar jikin da Anisa da Anti suke yi da Taj tuni ya sha jinin jikinsa. Shi da ya zo don su haWu a sirrance ya zame ashe Hajjo tayi masa handsfree da alama. Kuma a Sangarensu zancen ya sami karSuwa.

?akin Hajjo aka kaisu. Tana ganinsu ta washe baki tana tarbar Kamal.

"Sai ga Haffiness Win Haffi a Abuja. Sannu da zuwa Kamalu."

"Har kin ?ara masa wasali a sunan nasa kenan." Taj ya faWi yana zama akan kafet. ?afafunsa ya mi?e da yake jin sun sage saboda zama.

Kamar ba da ita yake ba.Ta cigaba da yiwa Kamal magana
"Ya ka baro mutanen gida? Ya baban naku?"

Kamal ya amsa ta sake sako wata tambayar. Taj ya gaisheta har sau biyu bata amsa ba. Ya dai gane fushi take dashi. Bayan kuma shi ya kamata ya nuna Sacin ransa da tayi saurin sanya shi cikin tsaka mai wuya. Yanzu duk gidan nan za su so jin matsayarsa kan maganar Anisa. Tunda yarinya dai alamu sun nuna ta amince, ana jin zance ya sauya salo nan gaba kaWan za a Wora masa laifi.

Share su ya yi ya kira uwayensa Waya bayan Waya ya sanar dasu sun iso lafiya. Sai kuma ya kira Abba shi ma. Su ka yi magana akan Wan gyaran da za a ?arasa a wurin da Taj ya kama musu kafin ya dawo.

"Hajjo in kin gama gaisawa da Haffiness Win nima ki Wan bani lokaci don Allah. Yau za mu koma. Bana son mu yi dare."

A sukwane ta juyo rai a Sace "banten uba! Ku iso yanzu ka ce kuma komawa za ku yi?"

"To ya za ayi? Aiki ya sako ni a gaba."

Dariyar Kamal a dalilin zolayarta da Taj yake sai ta gane ba tafiyar za su yi da gaske ba. Sha kunu gami da nuna masa yatsunta biyar.

"Buhun ubanka Tajo."

"Toohhh" Kamal ya kalleta da rashin jindaWi. Dole taji kunya don bata ga alamun yana da idanu a tsakar ka irin na Taj ba.

"?an uwan naka ne bashi da kirki Haffiness. Na yi masa maganar ?anwarsa ya amsa rimi-rimi sai kuma ya shuka ni. Yanzu ma gajiya nayi ina ta tunanin ko yarinyar ce ta ce bata so shi ne na kira uwar na tambayeta."

Kai tsaye Tay ya tambayeta "Me su ka ce?"

Hajjo ta dan?ara masa wani irin kallo "me kuwa za su ce sama da murna. Ko kai makaho ne ya dace ace ka fahimci yadda ake ta nan nan da kai ya sha bamban da lokutan baya."

Shirunsa a yanzu daidai yake da cutar kai. Idan ya kuskura ya fita daga Wakin nan bai faWi abin da yake ransa ba to tabbas aurensa da Anisa da wahala in ba ayi ba. Gyara zama ya yi ya ce,

"To ni dai gaskiya Hajjo..."

Yau da gobe tafi ?arfin wasa. Kuma dai Kamal ya riga ya san ba so yake ba. Amma akwai kunya da kawaicin malam bahaushe. Rashin girmamawa ne idan Taj ya kalli tsabar idon Hajjo ya faWa mata baya son jikarta.

"Hajjo magana ta gaskiya yanzu Taj tsoron Wauko zancen aure yake."

"Saboda me? Yana da lalura ne?" Ta soma yi masa kallon ?urilla.

Ya girgiza kai "a'a, amma kin san matsalar da yake fuskanta daga wajen Alhaji."

"Alhajin me?" Ta fara sababi "in kai ma baka da labari ka sani daga yau. Kakarku wadda ta tsuguna ta haifi Hayatu aminiyata ce ta ?ud da ?ud. Duk taurin kansa bai isa na faWa ya faWa ba."

Kamal ya jinjina kai yana kallon Taj ko zai agaza masa. Shi kuwa shiru ya yi yana kallonsu.

"Nima ba nufina zai ?i maganar bane. Kawai dai shi Taj yafi son lokacin da zai yi aure ya kasance Alhaji ya daina fushi da shi. Baya son yadda ya kore shi daga gidan kuma ya hana ?a?ansa shiga su ma."

Hajjo ta jinjina lamarin "da gaskiyarsa kuma. To amma indai auren gida ne irin wannan ai ita Anisan ta san komai. Ga ku duka kuna ta zumuncinku. Su Haj. Gambo ma dai ko da satar hanya na san za su fito ganin jikokinsu."

"Ko kin san zuwan nan har bakin mota Taj ya bishi amma su ka ja mota aka baWe shi da ?ura? Shi ne ya yi al?awarin ba zai yi aure ba sai Alhaji ya yafe masa."

Zancen ya fara shigarta. Kamal ya zama kamar wani lauya wurin jujjuya zance. A ?arshe dai ya samu da kanta ta hango illar auren Taj a yanayin rashin jituwa da uba.

"Abin da za ayi ko Kamalu, ni zan sa a kira min Hayatun muyi magana. Na san ko babu komai idan yaji daga gareni zai girmama zancen. Ba zai wula?anta min jika ba."

Tamkar ya sanya ihu haka yaji a wannan lokacin. Ashe duk SaSatun da yake ita wani angle Win daban take kallo. Mi?ewa Taj ya yi ya fice ya barshi yana ta kame kame.

Falo ya koma inda ya yi sa'a babu kowa. Yana zama Kamal ya fito yana ta waigen baya.

"This woman is too smart Happy. Kana ganin ta toshe duk wata hanyar da zan Sullo don a kwantar da zancen nan."

Murmushi Taj ya yi "kaWan ma ka gani. Shi yasa na so faWa mata gaskiya. Kai kuma ka hana."

"Haba Happy, wani abin ai sai da siyasa. Kara wani abu ce"

Kai Taj ya ri?e kawai. Kwanakin nan gajiya da damuwa suna yawan sanya masa ciwon kai. Tunda ya sami kan Abba abin ya ragu. Amma fa daga lokacin da su ka saka ranar zuwa Abujan shikenan bashi da wata walwala.

"Kan ne dai?" Kamal ya yi tambayar da kulawa yana dafa shi.

"Wallahi kuwa."

"Ka daina damuwa. Ba a yiwa namiji auren dole fa" Kamal Win ya yi murmushi.

"Happiness bana son takura ne. Sannan bana son ungratefulness. ?inta tamkar ban godewa kyautatawarsu bane."

"Don ka taimaki mutum kuma bai kamata ka Wora masa nauyin da zai takura shi ba. Ni shawarata kawai tunda Hajjon ta Wan fahimta ka cigaba da jan ?afa. Kuna fara magana a fito mata as unromantic as possible. Kada ka sanya mata false hope. In anyi sa'a ta gudu da kanta."

Sai a lokacin Taj yaji sanyi a ransa. Ya mi?awa Kamal hannu.

"Happiness nawa ni kaWai. Yadda ka ce hakan za ayi. Thanks bro"

***

Hamdi bata taSa shiga motar haya a Abuja ba ita kaWai. Ko yawon da su ka dinga fita da Anti Labiba farkon zuwanta, yawanci mijin Antin ke kai su. Ko kuma Anti Labiban ta kira bold ko uber. Hankalinta kwance yake tunda akwai idon garin. Yau da take ita kaWai ne dai duniyar tayi mata zafi.

Na farko dai direban motar a ?oyasinta zai yi biyunta. Ga jiki da bai Suya ba. Sannan babu tantama ba bahaushe bane. Inda zasu je kuma bata sani ba. Anti Labiba dai ta ce mata zasu bi ta titin hanyar Central Mosque Win da su ka taSa zuwa. To gashi an fi minti shabiyar a titi amma babu masallaci babu alamunsa. Banda hawa da sauka akan wasu gadoji da ko wu?a aka Wora mata ba za ta gane ko Waya ba, babu abin da yake yi. Ga gudu da ta lura yana yi kamar wal?iya.

Hanjin cikinta su ka sami wuri su ka cure wuri guda. Zuciyarta tana harbawa kamar za ta fito waje. Sai kuma bisa rashin sa'a aka kira shi da wata wayar ba wadda take gabansa tana nuna hanya ba. Ya sanya earpiece a kunne Waya yana magana da yaren da bata ji. 'Passenger' da kuma 'get ready, I will be there soon' kaWai ta iya tantancewa.

Habawa, duk wani labari da ta taSa ji game da satar mutane sai da ya dawo mata. Jikinta ya dinga rawa. A hankali ta kama shesshe?ar kuka don bata so yaji. Ta fiddo wayar da Anti Labiba ta bata da za ta taho ta tura mata message.

(Anti zai sayar dani a hanya ban san inda muke ba amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login