Showing 129001 words to 132000 words out of 182745 words

Chapter 44 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

110

take tana nanatawa In sha Allahu ba za ta sake kiransa da Ya Taj ba. Sunan ko daWi babu ashe, bata sani ba sai yau.

Taj kuwa Hamdi kawai ya kalla tayi kamar bata jinsu. Murmushi ma take yi abinta da ?an uwansa suke ta nuna mamakinsu akan kwanan da tayi basu sani ba. Aka dinga yiwa ?an kwanan Wakin Inna surutu. Su ka ce ita ta sanya su yin shiru saboda kada su tashi Hamdin da hayaniyarsu. Shi da ya san akan tsini yake ba zai yi kuskuren sake Sata mata rai ba. Kawar da kansa ya yi kamar bai ji ba. Yana gudun me zai faru idan ya amsa. Ta sake sha?a har wuya. Abinci ?an uwansa su ka kawo wa Hamsi shi ne ya samu ya fita wajen Kamal.

Amma ta karanci duk motsinsu. Me yake faruwa ne wanda bata sani ba? Zama bai ganta ba. ?akin Mama ta shige inda Inna ta shiga ta zauna jin abubuwan da bata san da su ba. Mamaki mabayyani ta nuna akan wannan sabon al'amari.

"Ashe yarinyar nan bata da wayo ban sani ba? Ana soyayya dole ne?"

"GabaWaya ta Sata rawarta da tsalle. Halin da uwarta ta so nuna mana a gidan nan shi ne ita ma take son gwadawa."

Umma kallon Mama tayi da mamaki "kada ki ce min asiri ne ya koreta, don na tabbata ko ita ce autar mata akan ?an biye biye tsaf Alhaji zai nuna mata ?ofar gida."

Hajiya ta murmusa "ai har yau bai san mun san ainihin me ya dinga faruwa ba. Bayan wani asirin ma a gabanmu take yi kawai don ta san ta Waure mana baki. Ai ke dai anyi abu fa a gidan nan. Allah kada Ya maimaita mana kawai."

"Amin. Don dai kam ko Taj ya rasa mace in sha Allahu babu shi babu wannan yarinyar." Cewar Mama.

Hirar shekarun baya su ka koma yi. Inna ta sake kaWuwa da jin wace ce Mami. Ashe zama bai ganta ba kuwa. Dole ta dage ta nesanta Taj da Hamdi daga Salwa.

*

"Yaya haka Ahmad? Ni da na kira ka mu san abin yi sai ka kama kuka?"

Ahmad bai san cewa duk bayanin da yaji a waya bai kama ?afar wanda ya ji yanzu ba. ?odar duka biyu Kamal ya rasa kuma wai cikin su ashirin da bakwai babu wanda tasa za ta yi. Idan babu mai taimakon Kamal a cikinsu daidai yake da babu Kamal Win.

"Alhaji bayaninka fa yana nufin duk yawanmu ba za mu amfane shi ba tunda babu jinin wanda ya dace dashi."

"Haka su ka yi min bayani da likitan."

"Anya ba ya faWa bane kawai saboda baya son takura kowa?" Ahmad ya yi tambayar da basu san amsarta ba.

Alhaji sai ya shiga tunani. Tabbas kowa a gidansa ya yi fice akan wata halayya. Indai ana batun sadaukarwa to Kamaluddin Winsa shi ne na farko. Wuyarta ka nema zai baka ko shi ne abu na ?arshe a tare dashi. Ba abin mamaki bane in ya zamo ya?i yarda a cire ?odar kowa a dasa masa.

Wannan tunanin kaWai ya haskaka zuciyar Alhaji. Zai nemi Kubra ta haWa shi da likitan da ya dace a Aminu Kano Teaching Hospital. All hope is not yet lost.

Sun tattauna yadda za su yi idan aka yi rashin sa'a da gaske babu wanda jinin nasa ya yi daidai. Alhaji ya sanyawa ransa daga yau zuwa sati in ba a dace ba za su bar ?asar. ?an lokacin ma ya bari ne saboda su sami damar yin booking Win asibitoci a ?asashen waje. Duk wanda aka sami appointment da wuri, shi za su je. Baya son su fara tafiya a can ma ace ?odar ake bu?ata dole kuma babu mai bayarwa.

Da su ka gama ne Ahmad ya ce "maganar Salwa..."

"Yauwa..." ya tashi "mu je ?asan. Wani rami nake son toshewa kafin ya zama ?ofa."

Gaban Ahmad faWuwa ya yi "Alhaji ka sami labarin tana son Taj ne? Nayi mata faWa. Ko a hanyarmu..."

"Bana fatan abin da zai sa na ci zarafin jininka Ahmad. Amma tabbas idan Salwa ta cigaba a turbar da ta Wauka to lallai za ta fuskanci fushina."

Hankalinsa ?ara tashi ya yi. Me kuma tayi?

Bai sami amsarsa ba sai da su ka shiga mota ya matsa mata da tambaya saboda abin da Alhajin ya yi ya bawa kowa mamaki. Hamdi ya nema suna saukowa. Amma ta ce masa ya yi sa'a kuwa domin yanzun nan suke shirin fita ita da Hajiya da Na'ima wadda ke bin Hajiyayye za su kai ta gida.

"Da kun koma kun Waukota kuwa" cewar Alhaji yana shafa kan ?ananun jikokinsa "ni na kawota. Idan ba a jira na mayar da ita ba sai a nemi izini na kafin a kaita gida."

"Mun kusa yin laifi ashe. To Allah Ya bada ha?uri" in ji Umma.

Gabansa Amma ta kawo Hamdi. Ta dur?usa ta gaishe shi kai a sunkuye. Yadda ya amsa mata da sakin fuska har Inna sai da ta jinjina lamarin.

"Ni dai ba zan bar magana a cikina ba." Amma tayi maganar da ta janyo hankalin kowa gareta "da mun san aurenki ne zai dawo da Taj gidan nan Hamdiyya ai da ranar da ya fita zai dawo. Sannunki Hamdiyya tauraruwar Tajuddin."

Dariya aka kama yi. Ita kuwa ta cigaba da cewa "Allah kuwa da gaske nake. Ji fa irin fara'ar da kake yi mata Yaya Hayatu. Irin ka yi na'am Winnan da auren hands down."

Hararar ?anwar tasa ya yi ya ce "A'a hands up."

Yaran kuwa me zasu yi banda dariya. Da kowa ya nutsu ne Alhaji ya ce ina Salwa. Tana daga gefe ta kawo wuya da abubuwan da ake yi a falon. Tasowa tayi kamar ?wai ya fashe mata a ciki. Tayi zaton magana zai yi mata a gabansu sai ya ?ara gaba ta bishi. Kowa na gani amma ba a san me yake cewa ba.

"Kin ga matar Taj ko?"

Shiru tayi da farko. Ya nanata tambayar da wata irin murya mai cikar kwarjini.

"Kin ga Hamdiyya matar Taj ko?"

"Eh" ta gyaWa kai da sauri.

"Kin kuma fahimci me yasa na nuna miki ita ko?"

Nan ma eh ta ce ba tare da jiran ya kuma tambaya ba.

"To kada na ji, kada na gani Salwa." Ya juya mata baya "ki je Ahmad ya mayar dake gida."

*

"Yarinyar nan ya nuna min" ita ce amsar Salwa ga Ahmad da ya kusan kai mata duka akan ?in amsa masa tambayar me Alhaji ya ce mata da farko.

"Wace yarinya?"

Ciki-ciki ta ce "matar Ya Taj."

"You are the least of my problems Salwa so ko ki buWe baki ki bani amsa ko ki ri?e abinki duk ke ta shafa." Ahmad ya faWi da faWa-faWa.

Yadda su ka yi ta faWa masa. Ya kalleta yana mai taSe baki.

"Kina gab da yin nadama mara amfani idan baki dawo daga rakiyar zuciya ba. Duk wanda ya bari tasa ta mulki tunaninsa da wuya yake cin riba. Dubi yadda gabaWaya ki ka sauya akan wannan obsession Win naki. Kin zubar da mutumcinki ana ta takawa a banza."

Ci kanka bata ce masa ba. Yana magana ma Ummi take turawa text tana neman inda za su haWu yau. Ta riga tayi nisa bata jin kira. Burinta kawai Taj ya so ta ko iyayensa basa so kuwa sai sun yi aure.

***


GIDAN TAJ DA HAMDI

(Sponsored by annurifoods, nafsbedding and meensincense)

Jeren gidan amarya ba mai yawa bane ta Sangaren gidan Abba Habibu. Inna tayi rawar gani da nunawa fiye da tunaninsu. Ta cika gidan da komai na bu?atar amarya da ango. Sai dai kuma duk da haka Abba da Yaya basu fasa yin nasu ba. Makusantansu ma sun nuna bajinta ba kaWan ba. Kayan za?i na gara irinsu dubulan, alkaki, nakiya, gireba, bakilawa da cincin ?ar Ficika da mu?arrabansa ne su ka yi. Abin ka da tsofaffin takari, nasu ya sha bamban sosai da wanda aka saba.

Iyaa kuwa gidan ?anwarta taje a hotoro aka rakata wajen wata ?wararriya a harkar kayan kaWi da abubuwan abincin gargajiya. Samira Muhammad kenan, mai Annurfoods. Mace mai faram faram da iya mu'amala. Tun abin da ya haWa Ummi da Hamdi a makaranta Iyaa take neman hanyoyin daWa wanke iyalinta duk da su Yaya basu canja musu fuska ba. Bayan gudunmawar kuWi da su ka bayar shi ne ta haWo wannan. Da ta kawo kayan Yaya kasa rufe baki tayi. Wanda ta haWawa amarya dole ta ajiye domin babu yadda za a kai Hamdi ba tare da kayan annurfoods ba. Garin kuka da kuSewa masu kyau a madaidaitan bokiti. Sai daddawa wadda ana haWa kayan Anti Labiba ta ce ita dai ayi ha?uri sai ta Wiba saboda daWin ?amshinta. Babu warin nan mai hawa kai mutum ya rasa inda zai yi da ransa. Sai nau'in yaji daban daban. Jan yaji mai tafarnuwa da wanda babu, na daddawa da kuma na ?uli?uli. Ni?a??iya da kuma markaWaWWiyar gyaWa (gari da paste), garin Wanwake, garin kunu wanda yaji duka kayan haWi da kuma soyayyen man shanu mai daWin ?amshi. (Samira Muhammad 08039183880, instagram @annurfoods.ng)

"Altine wannan kaya basu yi yawa ba?" FaWin Yaya tana jin kamar tayi kuka saboda karamcin da ake ta nuna musu.

"Ina abin yake Jinjin?"

"Haba dai, wannan yafi ?arfin a bi shi da kalmar ina abin yake. Ke dai Allah Ya biyaki da mafificin alkhairi."

Iyaa ta ce "amin Ya Allah."

Sajida aka dam?awa kayan a hannunta da umarnin idan sun je gidan tunda da wuri za su fita kafin a kai amarya ta saka komai a inda ya dace.

Ana haka su Amma su ka yi sallama. Allah Yasa sauran safiya ce. Babu ba?in fuska a gidan. Aka sauke su a falo. Hajiya ta fara da bawa Yaya ha?urin tafiya da Hamdi da Alhaji ya yi. Don ta rufa masa asiri ma ta ?ara da cewa yayi haka ne kawai don ya kula suna cikin damuwar ciwon Taj.

Yaya tayi murmushi. Gashi dai an shigo gidan amma hannun Hamdi yana cikin na Amma a gefen Hajiya tayi mata ri?o na ?ar da ake ji da ita.

"Wallahi babu komai. Da nan da can duk Waya ne."

"Kin sami labarin Alhaji ya yiwa Taj izinin komawa gida?" Amma ta yi tambayar saboda ita fa a yanzu wannan yafi bikin ma a wajenta.

"?warai kuwa..." sannan Yaya ta taya su murna.

Cikin mutumci aka gama komai. Za su fita Amma da bata iya shiru ta ce da Yaya don Allah wane irin turare ne aka saka a Wakin yake fitar da ?amshin da su ke ji tun shigowarsu? Hajiya girgiza kai ta kama tana murmushi. Amma bata iya ba?unta ba. Sai dai idan bata ga fuska ba. Ta gode mata dai saboda ita Win ma surukuta ce ta hanata tambaya tun shigowarsu. DaWin ?amshin ba daga nan ba. Bayan kujera Yaya ta nuna musu. Inda aka ajiye turarukan wuta a cikin bokitai an rurrufe bakunansu da salatif.

"Ko kunnawa ba'ayi ba. Na gidan ?arku ne."

Tashi Hamdi tayi ta bar falon. Yaya ta ?walawa Zee kira. Tana shigowa ta ce ta Wauko a buWe musu su gani.

"Haba Maman Hamdi? Don Allah kada a buWe. ?amshin ne ya yi min daWi na kasa barwa cikina" Amma ta faWi da sauri.

"Ni dai ban ga komai a ciki ba. Nan kuke ta cewa an zama Waya" cewar Yaya tana kama guda Waya "in sun je gidan yanzu ma buWewa zasu yi su zuzzuba a rufe sauran."

Da ?yar su Hajiya su ka hanata buWe musu. Bayan tafiyarsu ta sanya a ranta lallai za ta sayi wani ta aika musu. Zuciyarta kuwa fari ?al don daWi. Duk da ana ta yaba ?amshin a gidan tayi zaton na ganin ido ne kawai. Sai yanzu da waWanda basu san dashi ba su ka yi magana ta kuma gaskatawa.

Matar Halliru ma?obcinsu Hairat ce ta dinga zuzuta kyau da ingancin turarukan wata ?ar garinsu Bauchi. Da farko Yaya har cewa tayi duk turarukan Kano ace sai ta nemi na wani gari? Matar Halliru ta?i ha?ura domin ta san me za su rasa idan ba a saya ba kamar na lokacin bikin Sajida. Na wajenta da basu da yawa ta kawo. Zee ta kunna da yamma. Sai da kowa ya fito tsakar gida ranar. Washe gari Yaya ta karSi numbar Amina (08036387204, instagram @meens_incense). Ta kira su ka yi ciniki akan farashin da idan ka karSi turaren ma sai ka ce sadaka kawai aka baka.

Da turarukan su ka iso kasa rufe baki tayi don murna. Ta dai Soyesu kafin Hamdi ta dawo gida ranar saboda ko za ayi mata faWa sai ta kunna. Soyayyarta da ?amshi ta daban ce. Ga dai turaruka kala kala, kwalaccam Winta kuwa abar du?an ?irji ce (I mean it, the scent simply calms the heart), sai kuma humra irin waanda sai hancin da yaci karo dasu ne kawai zai gane.

Haka aka tattara komai aka zuba a mota domin kammala gyare gyare kafin zuwan amarya.

***

BanWaki Ummi ta shiga da waya ta turawa Alh. Usaini sa?o cewa jiya ma Salwa ta sake shafawa Taj turaren nan. Kuma da alama anyi nasara domin ta sami labari a daren aka kai shi asibiti. Daga maganar da taji Baba Maje da Iyaa suna yi bayan wayarsa da Abba Habibu da safen ta fahimci ba rashin lafiya bace kawai ta kama shi. Salwa kuma ta tabbatar mata a text. Ita Iyaa da wuri ta tafi gidan bikin. Ta barsu in sun gama girki da gyaran gida sai su biyota kafin dai a fita da amarya. Yana karantawa ya kirata.

Da ta Wauka tsoro ya bata da taji ya fashe da wata irin dariya mara daWin ji.

Da jindaWi ya ce "?arshen wannan Wan daudun ya zo."

"A'a fa, ba Wan daudu bane" Ummi taji ba za ta iya shiru ba. Ko makaho ya shafa Taj ba zai kira shi Wan daudu ba, balle mai ido. Idon ma irin nata mai son abu mai kyau.

"Ummi kenan. Wai me ya hanaki cewa ayi aikin da za ki sami soyayyarsa maimakon wannan sakaryar Salwan?"

"Bana ra'ayin namijin da kowa ke rububi." Tana ji Alh. Usaini ya yi dariyar rashin yarda.

Tunanin Taj ya so ta bai zo kanta ba saboda tayi nata binciken akan waye shi. Labarin mahaifinsa kaWai ya isheta dalilin mayar da kwaWayinta. Sannan ta san cewa ko ana muzuru ana shaho a yadda Baba Maje yake ganin darajar Abban Hamdi, da wuya ta gaske a barta ta aure shi. Ita kuwa abin da take ji a kansa ba na irin mu'amalarta da banzayen samarinta bane. Ya girmi hakan. Shi yasa kawai taga babu mafita sama da rusa shi. Ita da Hamdi kowa zero. Mafi munin hassada kenan.

"Ki tabbatar kin je kai amarya kuma kin bibiyi me suke ciki na ?an kwanakin nan. Kin san na faWa miki aikinsa a hankali yake ci."

"Bana son yin abin da zai sa a zargeni. Ba wani shiri muke da Hamdi ba kuma kowa ya sani."

"Sai ki san yadda za ki yi." Ya Waga mata murya kamar wata ?arsa.

Bai san bashi da wani kwarjini a idonta ba. Yana shiru ta ce "Ban gane ba? Wannan abu fa duk kai ne da riba. Idan ka damu ka sa malamin da ya yi maka aiki akan Taj Win ya tura aljanu su binciko maka mana. Mtseww"

Wayarta ta kashe ta sake buga tsaki.
"Aikin banza. Ni za ka Wagawa mur..."

HaWiye maganar tayi cikin tashin hankali saboda haWa ido da tayi da Siyama. Ita kuma cikin sauri da ta karanci fuskar Ummin sai ta kama WaWWaga ?afa.

"Fitsari, fito don Allah."

Fitowar Ummi tayi tana wasiwasin Siyama taji wayar da tayi ko kuwa.

Gaba na faWuwa Siyama ta dakata a bakin ?ofa ta nemi mafita don kaWan daga aikin Ummi tayi mata wani abu idan ta san ta ji.
"Naji kina ta gunaguni da tsaki, ba dai flushing ki ka yi ya?i tafiya ba? Kada na shiga nayi gamo."

Ba kunya Ummi ta saki fuska harda ?ar dariya "shiga ki ganewa kanki" ta turata ciki. Siyama na nuna kamar bata son shiga ta bari Ummin tafi ?arfinta. Fitsarin da ya kawota da gaske ta daina ji. Tabbas akwai mana?isar da Ummi take shiryawa Hamdi da Taj tunda taji sunayensu. Hankalinta ya tashi. Har su ka tafi gidan bikin tana faman satar kallon Ummi.

Da zuwansu babu daWewa ta nemi keSewa da Iyaa. Ummi kamar an tsikareta ta tashi tayi musu laSe. Da taimakon Allah ta sami basirar lauya zancen. Wata maganar daban ta Wauko har Iyaa za ta fara yi mata faWan me yasa ta janyota akan shirme, sai ta ?ifta mata ido. Ganin haka sai ta kalli bakin Siyama da ta faWi sunan Ummi iya leSe. Wannan yasa ta fahimta.

"Iyaa za ki barni zuwa kai amarya har ango yazo? Ni fa ban taSa zuwa ba."

"To naji sai ki biyo yayanku don na san zai je ko don Wauko Zee."

Murna ta kama yi harda rungume Iyaa. Da wannan ta samu Ummi ta daina saka mata ido har ta sami damar sanar da Iyaa wayar da taji.

"Ban ji ance komai ba amma ko da wani abu zai biyo baya to da hannunta wallahi."

Sallamarta Iyaa tayi ta jingina da bango domin gabaWaya jikinta ya mutu. Nauyi taji jikin yayi mata ta sulale a wajen kawai ta zauna. Babu abin da take yi sai kiran sunan Allah da neman agajinSa. Ha?i?a kowane Wa da halinsa yake zuwa. Tarbiya bakin gwargwado sun bawa ?a?ansu. Amma tun ?ananun shekaru tan?wara Ummi ke wahalar dasu. Bata da bakin Worawa ?awaye alhakin Sata mata ?a domin kuwa duk inda Ummi ta zauna ita ke shugabantar waWanda take mu'amala dasu. Ita ce boss mai sawa da hanawa. Ko dai kawo ?ara da wasu iyayen ke buri da alfaharin gara a kawo musu ?arar ?a?ansu akan su kai na wasu da tayi ke bibiyarta? Duk inda Ummi ta zauna sai tayi faWa kuma ana bincike ita ce mara gaskiya. Kuskurenta a lokacin da suke cikin yaran yarbawa a tsakiyar Agege shi ne na jindaWi da Ummi bata taSuwa. Babu mai yi mata kwarjini ko ya bata tsoro. Kana cewa kule take ce maka asss. Wata ma?ociyarta bahaushiya a lokacin ta kan ce

"Iyaan Baballe ki daina murna. Duk da cewa ba ma son a zalinci yaranmu to amma fa idan sun fita ya dace ki dinga addu'ar kada su taSa Wan kowa. Babban abin alfaharin rayuwa shi ne kayi dace kai ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login