Showing 78001 words to 81000 words out of 182745 words

Chapter 27 - RAYUWA DA GIƁI COMPLETE HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

122

ta kusa yanke jiki ta faWi.

"Kamal? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."

Waya ta Wauka za ta kira Alhaji. Har ta shiga sai tayi saurin katse kiran. Duk yadda aka yi likitarsa ce ta turo sa?on. Kuma da alama hakan yana nufin tana son ganawa da ita domin tayi mata bayanin da ya dace. Kiran Alhajin ne ya biyo bayan nata. Ta Waga wayar a firgice.

"Doctor yaya? Haihuwar Nabila (?anwarta mai ciki) ce ta tashi?"

"A'a Alhaji. Kira nayi mu gaisa kuma sai network ya katse kiran."

Kwantar da hankali ya yi su ka taSa hira sannan ta tashi. Kao tsaye asibitin da Kamal ya kwanta ta nufa. Aka sanar da ita Dr. Mubina sai litinin za ta zo. Nambar wayarta ta nema a reception Win aka sanar da ita bata ?asar ne. Ta tafi Ghana amma ranar lahadi za ta dawo. Haka nan ta tafi cike da zulumi da fatan gaggawar zuwan litinin Win.

***

Wato ?an gidan Alh. Hayatu gwanaye ne wajen son shagali. Duk abin da zai sa su taru a gida komai ?an?antarsa basa raina shi. Daga su har ?a?ansu. To iyayen ma dai ba a barsu a baya ba.

Akan maganar zuwan Hamdi sai ka rantse bikin ne ya taso. Mama ce ta kira Yaya ta nemi izini tunda har yanzu a gida take. Bayan sun gaisa ta gabatar mata da kanta.

"Suna na Haj. A'i kuma Mama a gida."

"Allah Sarki Hajiya. Da fatan kuna lafiya."

Da jindaWin yadda Yaya ta tarbeta Mama ta ce "Alhamdulillahi. Allah Yasa Taj ya yi muku Wan bayanin gidan namu."

"Sosai. Ya ce Hamdi surukarki ce ke da Wayar maman tashi ta Abuja."

"?warai kuwa. To muna bada ha?uri tunda mace ita ya kamata a bi. Yanayin gidan namu ne Masha Allah. Muna da yawan da in muka zo za sai ?an unguwa sun fara tunanin ko biki ake baki gayyace su ba."

Yaya ta kama dariya. Da alama barkwancinsu Taj ba a ?asa su ka Wauka ba.

"Allah da gaske. Shi yasa mu ka ce gara ta zo. Kuma dai idan zuwan zamu yi Inna ba za ta bi mu ba. Ai kin san wacce ce Inna a cikinmu ko?"

Yaya tayi murmushi "na gane."

Mama ma dariyar tayi "tunda anyi auren ya dace mu san juna ko yaya ne. Ina fatan zuwan nata babu takura."

"Wace irin takura kuma ku da abar ikonku? In Taj cewa yayi ta tafi kenan ai sai dai mu bita da addu'a."

Da girmamawa gami da mutuntawa su ka gama magana. Taj zai Waukota bayan azahar.

***

Abba ya yi mamakin shigowa gida ya sami Yaya ta ta?ar?are tana gogewa Hamdi jiki da ragowar dilkan Sajida.

"Allah ?adiran ala mayyasha'u. Khadijatul Kubra yau ke ce da wannan aikin? Lallai Sajida rakiya tayo a gidan nan ga ?ar so nan kin saka a gaba" ya kalli Zee dake gefe tana fifita garwashi "kema ?ar rakiyar ce ko za ayi miki?"

Kunya ta kama Yaya ta tashi ta koma cikin falo. Hamdi da Zee su ka yi ta dariya. Da ?yar Hamdi ta yarda ake yi mata. Wai cikin mutane za ta je. Bata son a rainata ta. Zee ma nata kwaSin yana gefe. Ita kuma sai yau Baballe zai zo. Cinikin motoci ya kai shi Kwatano tun bayan auren. Yaya ta ce gara a ga ?a?an nata a yanayin da duk hassadar mutum sai dai ya kushe a zuci. Sai gashi Abba na sakota a gaba ta gudu.

Falon ya bita "dawo ki cigaba da kankareta kada mijin ya zo a barshi jira."

"Kankara kuma don Allah kamar wata faso?" Ta faWi tana ?ar harararsa cikin wasa.

?a?an da irin wannan abu ba ba?onsu bane su ka tattara su ka barsu a falon. Zee ce ta?arasa mata ita kuma ta yiwa Zee Win.

"Wai amma gyaran jiki kamar za a kai mu yau?" Cewar Zee da su ka sanya turaren wuta cikin lulluSin ?aton zani kowacce ta zauna akan kujera.

"Ke dai muyi kawai in ba kin shiryawa mitar Yaya ba. In taji haushi sai ta hanamu zuwa gidan Ya Sajida gobe."

"Kin tambaya ma kuwa kamar yadda ta ce? Ni fa na rasa ma me zan ce. Haka kawai yanzu shige ds fice na sai in bin wani bayan a gidanmu nake" cewar Zee.

"Na ma manta da tambayar. Zan dai gwada. In na kasa in rubuta a text." Shawarar ta yiwa Zee. Ita ma a text Win za ta rubuta.

Suna idar da sallar azahar Yaya ta umarci Hamdi da yin wanka ta shirya. Jinkirin fita na Waya daga cikin abubuwan dake saurin kawo saSani tsakanin ma'aurata. Ita dai nata to ne. Tana kaffa kaffa don sun gama shirya irin dabdalar da za su yi gobe da Sajida. Ga tanadin hira da neman shawara kowacce tana son ji daga babbar yaya.

*

Biyu da kwata Taj ya iso. ?ememe Kamal ya?i rako shi. Har cewa ya yi to wa zai shiga da ita gidan tunda shi a waje zai tsaya. Kamal ya ce masa in sun iso ya kira shi. Haka nan ya tafi yana mita. Sai da Hamdi ta fito ya shiga shi masa albarka.

Yana zaune a falo yana zubawa Yaya santin kunun ayanta da duk sanda zai zo sai ya nema tayi sallama. Ya juya a hankali su ka yi sa'ar haWa ido. Da ido kawai ake gani lallausar shaddar da ya saka wadda aka yiwa Winki irin na matasan zamani. Ruwan toka ne kamar kullum an ?aranta adon. Very classy and elegant. Bai saka hula ba sai gyaran fuska da ya yi.

Ita kuwa cikin Winkunansu na bikin Sajida ne ta saka guda da ya kamata su sa ranar Waurin aure. Riga da siket ne mai adon ja da shuWi mara turowa ne a jiki sai ba?i. Fuskarta yau ya fara ganinta da kwalliya irin wannan. Light make up. Komai cikin tsari babu hayaniya. Tayi Waurinta a karkace kaWan ta Wora shuWin mayafi daga rabin Wan?walin. Hannuta da lallen biki ya fara tafiya ta sanyawa abin hannu a Waya. ?ayan kuma agogo ne na silver.

"Gara ku tashi kada yamma ta same ku ko?" Yaya ta ce da taga kallon ya?i ?arewa. Taj ya ma manta inda yake da alama. Ita kuma Hamdi sai juya awarwaro take.

Da ya fita ta fara binsa sai taji kamar ta zura da gudu. Tsoro ya shigeta har zuciyata tana gudun famfala?i. Bakin wata mota da duk rashin sanin motocinta ta san wannan ta kai duk inda ake so ta kai. A idonta dai jeep ce tunda tana da tudu. Fara ?al da tambarin BMW a jiki.

BuWe mata ya yi ta shiga sai ta daina ganin hasken rana sosai. Gilasan masu duhu ta kalla ta ?ara jin wannan tsoron. ?amshin daWin da motar take fitarwa zai iya mantar da mutum a ina yake. Taj na zama a mazaunin direba ta kama kanta. ?an waigen ?auyancin ya ?are. Ya tada motar ya kunna AC sannan ya fara ribas.

"?an tsaya."

Hamdi ta faWi tana Wora hannu a ?irji.

Burki ya taka da hanzari "Me ya same ki?"

Idanunta har sun tara ?walla ta ce "Gabana ke faWuwa wallahi."

"Saboda me? HaWuwa da ?an gidanmu?"

Ta girgiza kai da dukkan gaskiyarta ta nuna shi.

Yana son honesty Winta. Juya kan motar yayi domin su hau titi ya ce
"Kin dai san ko ina satar mutane ba zan saci jinin Abbana ba ko?"

Tana jindaWin yadda yake girmama mahaifinta sosai. Amma da yake bakin baya shiru sai cewa tayi "na sani ko ka fara yau. Ka zo da mota a rurrufe ba a gano ciki ta waje."

"?ar ?auye zan ce miki ko matsoraciya? Amfanin wannan tint Win ga irinmu shi ne yanzu misali idan naji ya kamata..." Wauke ido ya yi daga titi su ka kalli juna.

"Ya kamata me?"

"Will you let me kiss you idan mun dawo? Ko yanzu in sami wurin parking?"

"Ya Taj???" Idanunta su ka firfito.

"Na'am. Ashe kin san suna na. Na zata Salman Khan za ki ce. Har na tanadi wa?arsa da zan miki." Ya yi maganar yana dariya.

Bakin tsiwa ya mutu murus. Ya Wan kalleta yaga hannuwanta kawai take kallo. Shi da ya tsammaci ta bashi amsa.

"Hamdi? Yaya? ZazzaSin ne yau ma?"

"Uhmm" ta gyaWa kai harda shafa wuya da goshi.

"Ki ce in tanadi maganin maleriya da thypoid ranar da za ki tare kawai."

"Allah da gaske nake. Jikina babu ?wari ma." Ta Waga hannu ta sake shi yaraf.

"Kinga mun kusa zuwa gidan. Ki rufa min asiri yanzu don za ki haWu da ?an jarida masu tambayar tsiya. Akwai ?an bugun ciki ma waWanda za ki iya faWa musu duk hirar da muka yi yanzu ba tare da kin sani ba."

A tsorace ta ce "da gaske?"

"Da wasa" ya furta a hankali yana yi mata murmushi.

A bakin gate Win wani ?aton gida taga sun tsaya. Ya Waga waya ya kira Kamal ya ce masa sun iso.

Tsoron nan bai barta ba ta ce "ba za ka shiga ba?"

"Alhaji bai yi min izini ba." Ya amsa mata da murya mai rauni.

Tausayinsa ya mamaye zuciyarta har taji kamar tayi masa kuka.

"Kada ki Sata min kwalliyar nan tun kafin na biya kuWinta don Allah."

"Ni ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ba don kai nayi ba" ta ce da tsiwar nan.

"Mala'iku suna jin ki dai."

Da sauri ta ce "Astagfirullah."

Bata ankara ba ya yi abin da tun shigowarta motar yake muradin yi. Hannunta mafi kusa dashi ya kama ya sar?e yatsun ya lan?washe su.

"Wa ki ka yiwa kwalliyar? Suna ji dai kada ki manta."

Tsuke baki tayi tana jin yadda Wumin hannunsa ke shigarta. Ita kam ta shiga uku. Wannan aure ta son ya Wore....Allah na tuba ta faWi a zuci.

"Hamdi?" Ya Wan matsa hannun.

"Kai na yiwa" murmushi ya soma yi ta ?ara da cewa "amma dai Yaya ce ta tilasta min nayi."

"Allah Ya biya Ya mafificin alkhairi. Now can I ki..."

Bata bari ya gama magana ba ta sanya hannu ta toshe masa baki.

"Kaga fa Ya Kamal ya fito." Ta kalli gate Win a firgice.

Dariya ta bashi ya cire hannun nata ya ri?e shi da Waya hannun.

"Idan ya ?araso sai na ce ya tayani ro?onki. Kinga fa a waje za ki barni for God knows how long."

Kamal har ya ?araso. ?wan?wasa gilas ya yi ta Sangaren Taj. Shi kuma ya zuge gilas Win ?asa.

"Happiness ta?i yi min sallama kamar bata san iyakata nan ba. In ta shiga ciki sai sanda suka ga damar sako min ita."

Sunkuyar da kai tayi don har lokacin hannuwanta suna cikin nasa. Tana ja yana sake ri?ewa.

Kamal dariya yayi kawai "Mrs Happy haka za mu yi dake?"

"Shi za ka zaSa?"

"Da me kike tunani? Ya zaSeki a kaina?"

"Naga wai ni ce ?arama" tayi kicin kicin da fuska.

A take Kamal ya canja she?a.
"Happy buWe mata. In ka kaita gida sai ku yi sallamar a can."

"To wallahi tayi al?awari a gabanka" Taj ya sha kunu da ya yi maganar.

"Ki yi mu shiga kinji. Su Umma ke su ke jira."

"Nayi." Ta faWa don idanun ?an uwan su biyu sun hanata sakat.

Sama Taj ya yi da gilas Win ya kai hannunta guda bakinsa ya sumbata. Hamdi ta rasa inda za ta tsoma ranta don kunya.

"Gidanmu ba irin wanda ki ka saba bane Hamdi. Duk inda ake da yawa komai is possible. Don Allah idan an Sata miki rai ki fara faWa min kafin su Abba. Zan baki ha?uri a madadin ko waye. Kin ji?"

Murmushi tayi har zuci. Ta Wan matsa hannunsa dake cikin nata sannan ta fita.

Kamal na buWe gate da su ka shiga ciki taji wata murya da ta so ta gane tana yi masa magana.

"Ya Kamal basu iso bane?"

Hamdi ta bi inda ya kalla da ido. Budurwa ta gani tayi kwalliya ta fitar hankali. Tayi kyau tamkar wata amarya.

"Salwa? Saukar yaushe?" Ya ce babu wani jindaWi a tare da tambayar.

"?azun nan na iso. Ina zuwa gidan kuma naga Anti Zahra za ta taho wai yau amaryar Ya Taj za ta zo gaishe da su Hajiya."

"Gata ku gaisa." Ya faWi yana kallon yadda shigarta gabaWaya ta saSawa sanin da ya yi mata a baya.

"Sannu amarya." Ta ce tana yin gaba "bari naje na taya Ya Taj hira kafin ku fito."

Kashewa Hamdi ido tayi wanda Kamal bai lura ba. Ta wuce su ta buWe ?aramar ?ofar gate Win ta fita. Komai ya nemi tsayawa Hamdi da ta tuna yadda su ka yi a waya. Sai da Kamal ya kirata sau biyu taji ta bi bayansa tana tunanin hanyar da zata bi ta nunawa Salwa tayi kuskuren shiga gonarta.
RAYUWA DA GI?I 22





Batul Mamman=ؖ?





This page is sponsored by _Scentmania_ by Sana. A Kano take, amma ?amshi babu ruwansa da gari ko ?asa. Wuyarta ciniki ya faWa. Za ku sami undiluted oil perfumes Winku a duk inda ku ke. Bayin Allah babu cika baki. Talla ne daga abin da na gani, na gwada kuma na amince dashi. Gashi babu ruwanki da jiran sai asusunki ya cika ya tumbatsa kafin ki shiga jerin mata masu aji. Da dubu biyar ma za ki haWa kwalabe daban daban ki gigita waWanda ya halatta su ji ?amshin jikinki da yawan tambayar wane irin turare ne wannan. Scentmania by Sana, na Naana Hauwa'u queen of oil perfumes. Domin neman ?arin bayani a tuntuSeta a wannan layin 07065525409.



Ko sakan 30 ba ayi ba tsakanin fitar Salwa da shigarsu ciki Taj ya turo gate Win. Kamal ya yi mamakin ganinsa tsaye daga waje. Shi kuwa yafito shi kawai yake da hannu. Cewa Hamdi ya yi ta Wan jira shi. Ko kallon Taj Win bata yi ba domin ranta a Sace yake. Bata son yanayin da take jin zuciyarta a ciki. So take ko dai taga dawowar Salwa ciki ko kuma ita tayi hanyar gidansu.

Kafin Kamal ya ?arasa gate Win sai ga Firdaus. ?ar wajen Yaya Hajiyayye wadda su ka gama FGC tare da Hamdi.

"Anti Hamdiyya Habib Umar" ta kirata da ?arfi cikin murna.

Tana rufe baki sauran jikokin su ka firfito suna yi mata oyoyo. Abin ya bata mamaki don gaskiya idan ta ce ta sa rai da tarba mai kyau daga zuwanta tayi ?arya. ?aruwa mamakin nata ya yi da Firdaus ta rungumeta.

"Wai ashe matar Uncle Taj ce ke ban sani ba duk zamanmu a school. Ai da ko ruwa wallahi ba za ki Webo ba. Uncle Taj is my favourite."

Hamdi tayi murmushi kawai tana mai jin kunya. Firdaus ta ja hannunta su ka shiga ciki. Anti Zahra ta taso da sauri.

"Ke matsa min. ?anwata ce. Ni zan kaiwa su Hajiya ita."

"To duk gidan nan dai idan aka cire Happiness kowa ya san nice ta gaban goshin Happy. So please allow me..." wata ?anwarsu ta janyeta "sannu da zuwa Sis"

"Meye haka jama'a? Ba babba babu yaro?" Umma tayi magana daga ?ofar Wakinta. Kowa sai ya sami nutsuwa "Za ku barta ta zauna ne ko kuwa sai kun gama tsorata ta da wannan hayaniyar?"

Sai a lokacin wata mai yawan murmushi ta zaunar da Hamdi akan kujera. Sai dai tana zaman ta zame jikinta ta koma ?asa. Akayi akayi sam ta?i komawa kujerar. Ga mayafi ta sa ta rufe fiye da rabin fuskarta. A haka ta gaishesu. Umma da su Hajiya su ka fito su ma. Cike da kunya da ladabi ta gaishesu tamkar iyayenta. Aka tambayeta mutanen gida ta ce suna gaishesu. Bakin Inna kasa rufuwa yayi. Surukar tata tayi mata ta ko ina. Fargabarta ma ta ganin wata halayya da za ta nuna nakasun tarbiyya a tattare da zuri'ar Abba Habibu ta Sace Sat.

Filin gabatarwa aka shiga inda Bishir ya nuna mata iyayensu da sunayensu. Sannan yabi ?an uwansa Waya bayan Waya su ma. Haddacewar dai sai a hankali. A wajen ya nuna mata mata goma sha biyar. Sauran sun yi nisa. Ga jikoki gari guda. Su kaWai sun ishi juna gayya.

"Za a saka ki a family group. A hankali duk za ki gane mu." Yaya Kubra ta faWi.

Tana cikin waWanda Hamdi ta ri?e sunansu saboda kana kallonta kaga ?ar gayu ajin ?arshe. Gashi ance likita ce. Ta lura dai duka gidan akwai wata kamanceceniya da ko baka san su ba za ka iya danganta su da juna.

Kai ta gyaWa har lokacin ta kasa buWe fuskarta da kyau. Hira ce ta Sarke kowa da irin tambayar da yake yi mata.

"A kawo abinci kafin ku cika mata kunne don Allah."

"Hajiya ai so muke ta buWe bakinta."

"Baki zai buWe ne babu abinci?" Mama ta fatattaki jikokin ta ce su tashi su fara Wauko kwanuka.

"Yau bamu ci komai ba muna jiran amaryarmu. Me za ki ci?" Wadda tayi maganar ta fara buWe food flask. Akwai fried rice wadda taji kayan haWi da hanta, tuwon shinkafa da miyar agushi, waina (masa), coleslaw, pepper chicken, farfesun kayan ciki da kuma nau'ikan lemo na kwali da ruwan roba. Abu kamar taro, kodayake taron ne tunda yawa garesu.

Kai a ?asa ta ce "Na ?oshi."

"Kada na sake jin zancen ?oshin nan Hamdiyya. Don Allah ki saki jiki don a gida kike. Girkin yau dukkaninmu uwayenki sai da muka saka hannu." Umma tayi magana tana hararar ?a?an nasu "daga cewa za ki zo gaishemu duk su ka baro gidajensu saboda fitina. Ai gashi nan kun cika mata ido ta kasa sakewa."

Dariya aka yi. Aka gama ajiye tarin kayan abinci kamar na biki sannan aka shiga zuzzubawa. Hamdi ta lura kusan sa'anni ake haWawa a tray guda. Firdaus ta nace a haWasu a tray guda amma fir aunties Winta su ka ?i. Wai matar aure ba sa'arta bace. Basu san ita babu yadda za ayi ta ci abinci da kowa a zuwan farko ba. Kuma ?ila na ?arshe.

"Idan ba za ki iya ci su ba a zubo mana tare."

Wani irin shiru falon ya yi na wucin gadi kowa na kallon Inna kamar ba ita tayi maganar ba. Kafin kuma su kwashe da dariya suna hailing Winta. Harda masu karambanin Wauko plate za su zuba musu.

Da wani irin sauri Hamdi ta matsa tray mafi kusa da ita harda gyara murya ta ce "Bismillahir Rahmanir Rahim."

WaWanda basu yi dariya da farko ba ma sai da su ka yi yanzu. Cikin ruwan sanyi Inna tayi musu maganinta. Inna ma murmushi tayi.

Abinci ya yi daWi. Ba don gidan surukai bane tabbas cin da Hamdi zata yi sai yafi wanda tayi na ba?unta. Su na ci ana kiran sallar la'asar. ?akin Mama aka ce a kai ta tayi sallah a can. Suna tafiya da Firdaus ne ta tambayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login